Showing 12001 words to 15000 words out of 41738 words
Chapter 5 - Aishah-Saddiqa book 4 end complete by Takori Kabara .txt
ta zama bazawara, at a very tender age ko a kirata sauta ga wawa, kuma bata so ya zama su Mallam Yunus sun yanke hukunci kawai daga bakin Petel gabanin jiran Dade da Nenne, da shi kansa Abdulrasheed din yace zai zo gobe.
Sun samu Baba Barau a gidansa a turakarsa yana cin abinci, ya yi mamakin ganin Aisha. Amma fuskarsu kadai ya kalla ya san ba zuwan ziyara ta yi ba, ba kuma na dadin rai ba. sai ya ture kwanukan abincinsa gefe yana cewa “Indon Legas saukar yaushe?”
Wajen zama ya bai wa kaninsa, sannan Aisha ta tsugunna gabansa ta gaida shi, ya ce, “In ce ko lafiya na ga Indo kamar daga sama? Ba ance min kun bar kasar ba zuwa turai?”
“Yanzu dai Petel ki fada masa komai da bakinki ya ji”.
Aisha ta maimaita wa Baba Barau kalaman Murjanatu kakaf. Da yadda ta tada bori sai ta taho. Baba Barau ya sunkuyar da kai na ‘yan dakikai, kafin ya dago ya ce, “Na ji, kuma sun yi da dan halak. Kin haifu Indo, daya tamkar da dubu ga iyayenta, kuma mun gode da wannan karramawa da kika yi mana. Allah yayi miki albarka tunda arziki, mulki da daular da kika samu kanki ciki rana daya basu sa kin sarayar da mutunci da martabar mu ba.
Ni kuma na yi miki alkawarin yadda na hada wannan auren haka zan tsaya in kwato miki martabarki. Taiwo ta ke ko Tuwo, sai ta san ba’a cin zarafin bafillace a kwana lafiya don ko sune Qaruna da Fir’auna don mulki da dukiya kin gama auren dan su”.
Ya ce, “Kuma a gidana za ki ci gaba da zama, don Zainaba tsaf kawarta za ta kalallameta ta zugeta su maida ki. Tunda uwarsa da ubansa kadai ke son auren. Shi dinma nataba ganin kafarsa a gidannanya zo gaishemu? Kullum saidai ace baya nan kamar wani tsuntsu. Don Zaynaba kam sanyin halinta bazai bari ta kwato miki ‘yanci ba, kuma kin san kawancennan nasu itada Sappa sai Allah”.
Farin-cikin goyon bayan da ta samu kadai daga iyayenta dattawan kwarai ya wanke mata zuciya ta saki numfashi na samun kwanciyar hakali. Ta san da wasu iyayen ne cewa zasuyi zasu maida ta kada sarauta da mulki ta wuce ta kansu.
Baba Barau ya sa murya ya kira matarsa Furera, ta shigo ya ce, “Maza Furera share wa Aisha dakin can na kusa da naki, ki kuma kama kaji a yanka ki mata farfesu yanzun nan. In kuma gashi take so sai a kaiwa Ayuba ya gasa mata. Ko me ta ke son ci a yi mata (baba Barau na kiwon kajin gidan gona masu yawan gaske a wani bangare na gidansa)”.
Sai bayan fitar Baba Furera ya tambayi Aisha, “bani wayarki kada ma ya kiraki. Shin kina da iddarsa a kanki??”
Kunya sosai ta kama Aisha. Ta sunkuyar da kai ta kasa amsawa.
Baba Barau ya ce, “Magana nake yi da ke Indo”.
Aisha ta girgiza kai a hankali, wato babu iddar Prince akanta. Wayarta kuma tace ai a wurin ta aje masa abarsa. Ba waya a hannunta yanzu.
Baba Barau ya kara fusata ninkin ta baya, yayi kuta ya ce, “Allah ne shaidata, ni ban yi la’akari da komai nasu ba na yarda na ba su aurenki, amma in suna ganin akwai wata manufa daga gare mu, ko in hankali bai kwanta ba gara da suka maido ki gabanmu da wurwuri.
Amma miji ya jingine mace mai lafiya har watanni tara babu sunna, kuma da sunan aure, sannan suna tare a gida daya ai wannan auren ma da alamar gurbacewarsa.
Babu inda zaki koma kin zo gida kenan inyaso su biyo ki da takardarki ni za’ayiwa iya shege da wulakanci?.
Idan kuma sun ki, na rantse ko da shari’a sai na raba auren nan. Mu za a wulakanta? Mu ake wa kallon kwadayayyu matsiyata?”
Baba Barau har ya fi Malam Yunus daukar zafi. Nan ya tafi ya bar Aisha a gidan Baba Barau yana ta ja wa Furera kunne kan lallai kullum ta kama kaza da zabuwa ta yi wa Aisha farfesunsu da suya ko gashi.
Nenne ta kira mahifiyarta ta ta gaya mata Aisha ta taho Gombe, sakamakon abinda Taiwo ta yi mata, da abinda ya biyo baya, wato tahowar Aisha gida.
Nenne ta nuna ma Oummana damuwarta sosai kan abinda ya faru a bikin na Princesses dinta, ga jama’a sun gayyato daga ko’ina ba damar ta barsu ta taho, sai an kai amare, shi ne Nani Oummana ta tace ta kwantar da hankalinta su gama bikin twins lafiya.
**** **** ****
Siddiqah ta wayi gari lafiya a gidan babanta Barau Hamza, amma zuciyarta ta ki yin dadi yadda ya kamata duk da gatan da ake gwada mata kamar ana goyonta, ta kowanne bangare zuciyarta ta rasa sukuni don da dazun da safe ma Ummanta ta yi danmalele mai rai da motsi ta aiko Sunusi ya kawo mata har gidan baba Barau. Danmalelen ya sha manja an shirbineshi da yajin tafarnuwa yadda Petel keso, ga salad da tumatur an yanka masa da albasa da cocumber.
Siddiqah wadda rabonta da danmalele har ta manta, watakila tun farkon zuwanta Lagos. Tayi matukar jin dadin samunsa, musamman da Umma ce tazauna ta yi mata shi da hannunta.
Furera matar Baba Barau kuma tana ta cika umarnin Baba Barau na fige kaji da zabbi har sun ginshi sha’awar Siddiqah.
Washegarin rana ta biyu ma cikinta baci ya yi saboda canjin cima da ta samu, ta saba da cin abincinsu na yarbawa fresh veggies. Don haka Danmalelennan sai da ya saka ta zagayawa toilet har sau uku tana saukeshi, sabida uban yajinsa.
Aisha data zo barci sai ta kasa koda runtsawa, saboda tunanin magananun Taiwo. Suka zo suna ta sukarta a kirji kamar allura. Hamma da rashinsa a gefenta, sabonsu ita dashi, na wasu watanni bai yi yawan da za ta kasa barci saboda rashinsa ba, amma abin mamaki barcin baya samuwa saboda tunani da damuwa akan halin data baro Hamma a dakin da Nenne ga sauka. Ita ta san bai mata laifin komai ba, Prince ya darajata ya mutunta yana kuma kan daga darajarta da soyayya abinda kowa baiyi zato ba,
Amma a ranta ta yanke ba ita babu komawa aurensa, duk da yadda can wani nesattaccen sako na zuciyarta ke bala'in kewarsa.
**** **** ****
THE PRINCE
Har ya dauki hanyar dakin da ya baro Taiwo wato inda ta sauka sai kuma ya fasa, ya juya da baya-da-baya ya koma masaukinsa na gidan Kakan nasu.
Wani tunani ne ya shige shi wato kada ya kulata sai a gaban Nenne da Dade, ba zai so su raba abin fada a cikin dangi ba, ya san dakin da su Taiwo suke ciki akwai sauran matan family dinsu a cikinsa ba Firdausi ce kadai a dakin tare da ita ba, alhalin ana musu kallon wadanda suka fi kowa hadin kai, kyakkyawar rayuwa, kaunar juna da kwanciyar hakali a kafatanin zurri’arsu ta Sarki Abdulrasheed dan Abdullateef Akanni.
Don a yadda zuciyarsa ke tafarfasa dinnan bai san hukuncin da zai yankewa Taiwo yau ba, he is afraid ya kai hanu jikinta da sunan duka, in ya yi ido hudu da Taiwo a lokacin yana iya marinta, kuma abinda zai biyo bayan hakan sai wani ikon Allah ne zai sanyaya shi.
Don haka Prince yayi koyi da maganar Annabi (S.A.W) ne, da ya ce, kada, kar ka yi hukunci a lokacin tsananin fushi.
In kana tsaye ne abun fushin ya sameka ka zauna, in kana zaune ne ka koma ka kwanta. That was why he decided not to talk at the moment.
Amma ya kudurce sai a gaban Dade da Nenne.
Su Nenne na dawowa dakin da Prince yake suka nufa kai tsaye. Nenne ta same shi a kwance, ya rufe fuskarsa da zara-zaran tafukan hannunsa, shi ya tabbata Taiwo ‘yar uwarsa ce, kuma makusanciya mafi girma a gare shi.
Amma wannan attitudes din data ke yi wa iyalinsa na mene ne? ya kasa fahimtar Taiwo. Mene ne haka wai a zuciyar Taiwo a kan matarsa?
In haka ne kawai Taiwo ba ta sonsa da rayuwar iyali kome? Tafi son shi da zama a gwauronsa har gobe, saboda ita tana aure har ta aje masu yi mata addu’a kome da shi zata kashe masa nasa auren? Don in banda haka ai in bata godewa Aisha-Siddiqah ba wadda iyayenta suka lankwasata har ta yarda ta yi biyayya ta aure shi da girmansa ita da yarintarta, bai kamata ta saka mata da zagin iyaye da gori mai tsinka zuciya ba. Ya rasa me ke damun Taiwo a kansa sai ka ce a kanta aka fara tagwaitaka.
Duk da cewa, tun asali halin Maman Kiki wani iri ne da shi kadai yake iya tolarating, amma shi ma yanzu ya yarda Taiwo annamimiya ce. Halinta bai da kyau, she’s full of pride and arrogance, watakila shi ya sa hatta mijinta uban ‘ya’yanta Toafeeq ba ya iya zama inuwa daya da ita na lokaci mai tsaho zai gudu, ya gwammace ya yi nesa da ita. Ya dinga ganinta lokaci-lokaci tunda ta zame masa dole.
In da ya bi hudubobin Taiwo na tuntuni kadan-kadan a kan Aisha, kafin ya gama fahimtar manufarta akan Siddiqah din gabadaya yanzu, da tuni ba su samu fahimtar junan da suka samu shida Siddiqah yanzu ba, da bai samu farin cikin da ya soma dandana da canjin rayuwar da ya soma samu ba.
Shi Aisha ce daidai da rayuwarsa. Ta ishe shi, ta masa daidai, more than enough, tayi kunnen doki da duk wani burinsa a kan macen kwarai. Ba ya so ya yi wa Taiwo hukuncin da a gaba za yi nadama, shi ya sa ya dawo daki, ya jira dawowar iyayensu.
Sai ga Nenne ta shigo dakin nasa fuskarta kamar hadari. Prince ya yunkura ya tashi zaune da kyar, idanunsa sun kada sun yi jazir sun kuma kankance. Nenne ta dube shi idanunta fal takaici da zallar bacin rai, ta ce,
“Hammansu yau na maida Aisha ga iyayenta, kamar yadda na dauko amanarta, tunda haka ku ke so kai da abokiyar tagwaitakarka.
Tunda tsoron Murjanatu ka ke, to shi ke nan, ta kashe maka aure, na amince na kuma yarda ta auro maka Haseenah da uku bayan Haseenah. Tunda itace uwarka ita ta haife ka.
Amma kada ka sake ka saka ni a maganar bikon Aisha, bazani ba, saboda ina tattalin mutuncina a idon masu ganina da kima, ba kaida Taiwo dinka da baku daukeni a bakin komai ba, inaso iyayen Aisha wato Zainaba da Malam Yunusa su yanke duk irin hukuncin da yafi musu daidai”.
Daga bayan Nenne Dade shi ma ya shigo, ya dora daga inda Nenne ta tsaya, ya ce.
“Ni kuma Dade dinku ka riga ka san cewa mijin ta ce din Nenne ne, tunda ta cire hannunta ni ma babu nawa, ko Gombe ba zan leka ba, wai ido da kunya. Sai ka je ka gyara barakar da ka yi sake ta faru da kanka, amma kada ka sake ka saka mu a ciki nida Nenne”.
Daga haka Dade da Nenne suka juya sua fice, suka bar Abdulrasheed na zufa daga zaune, yana tambayar kansa “me zai yi wa Taiwo ya huce?”
‘Yar halak din sai gata ta shigo minti goma da fitarsu Nenne, tana tafe da irin tafiyar nan tata ta kasaita da mulki tamkar dawisuwa cikin basarakiyar tafiyarta.
Murjanatu Taiwo Akanni, ta shigo dakin ta tsaya a gabansa babu alamun ta yi wani abu da ba daidai ba a kan fuskarta. Ta ce,
“Kehinde, wai don mun yi magana a kan yarinyar nan ni da su Ifedayo da Aunty Bola shi ne ta bar gidan? To don ubanta sai me? Sai aka ce da ita mata sun kare? Da ma ni ai so nake ku rabun, tun kafin ta haifa mana jikokin Malam Shehu a hada iri da talauci cikin gidannan. In dai mace ce ni zan samo maka daidai da kai, ko ba Haseenah ba tunda tayi aure ita, za ta sha mamaki don kuwa saidai ta dawo ta ganka da mace, wa za ta nuna wa zafin kai da rashin kunya?”
Prince kansa na sunkuye, ya kasa dagowa ya dubi Taiwo domin zuciyarsa cewa ta ke yi ya yi kwallo da ita a dakin, ya dauketa ya nunawa sama ita ya nana da kasa, wata na tuna masa Taiwo dinsa ce fa cikin wani halina ajizanci da batan basira, Taiwo ce wadda ta haifa masa Kiki. Wadda ta tsaya masa a kan komai nasa tun zuwansa duniya, ta yi sharing farin cikinsa da bakin cikinsa, ta tsaya da shi a lokutan rauni, ta bashi farin ciki a sanda duniyar da yake ciki ta yi masa kunci.
Waccan kuwa matarsa ce, barin jikinsa da yake fatan ta zama uwar y'a'yansa nan bada jimawa ba, wadda ko shekara ba ta cika da shigowa rayuwarsa ba.
A yanayin da ake ciki kuwa yanzu dole ya zabi dayarsu ya bar daya, don ba za su taba kara zama karkashin inuwa daya ba, in aka yi la’akari da muggan kalaman Taiwo a gare ta, musmaman da ya bayyana gare shi cewa ita din mai sanin darajar iyayenta ce da kiyaye martabar kanta.
A hankali Kehinde ya dago kai ya dubi Taiwo da rinannun idanunsa da suka kada ‘yan hanjinta. Ya ce, “Maman Kiki, please get out of here before I lose my temper!”
Taiwo ta zaro ido, ta ce, “Kehinde, ni Taiwo ka ke wa tsawa yau?”
Da karfi Prince ya ce, “Get out of my sight please Maman Kiki. I don’t want to touch you da sunan duka. I am disappointed in you, ki daina zuwa inda nake, in ba ni na neme ki ba”.
Taiwo ta bude ido da baki cikin mamaki da razana , shi kuma Prince ya ce.
“Karyar so ki ke min Taiwo, karyar ‘yan uwantaka ki ke min. Karyar tagwaitaka ki ke domin babu ita a ranki. Da kina sona a matsayin dan uwanki da kin so ni da farin ciki da cikar rayuwa kamar kowa, ko yaya ne da kin barni na tsira da farin cikin dana soma samu.
Ki zauna ki laluba zuciyarki Taiwo, zaki tarar babu kaunar Kehinde ko kadan a cikinta yanzu, ko tu daga sanda aka yi masa aure.
Wannan yarinyar da ki ka raina don basu da arziki da sarauta, ki ke kushewa a kunnena da idona dare da rana da zagi da aibantawa da gorin bata isa ba, ita ce din dai matar da Allah ya ga damar bani a matsayin kyautarsa, na ladan hakurina da gujewa saba masa ta hanyar zina, a tsahon shekarun kuruciyata.
Ni kuma tunda ta jure wa tsufana, nima zan jure wa yarintarta da ki ke rainawa, ita ce uwar ‘ya’yana, uwargidana har a gidan aljannah insha Allahu.
Sannan daga yau sai yau kada ki kara yi min zancen iyalina, tunda ba za ki taya ni sonsu ba, kamar yadda nake taya ki kaunar naki, to na shata babban layi tsakaninku har abin da zan haifa. Tunda da bakinki kin ce bazaki taba kaunarsu ba.
Mu yi zumunci wanda ya shafe mu, wanda shi ne dolenmu, ba ruwanki da Aisha-Siddiqah, for your information ki sani “ina matukar son MATATA!
Banida kowa da ya fiyemin ke sai iyayena sai kuma twins da ‘ya’yanki, kune duniyata komai nawa ya kamata ya zama naku ne. Daga yau kisa a ranki tunda kin kashe min aure zan rayu a yadda kike son ganina, kada ki kara ambata min kalmar aure tunda ba ke kika haife ni ba, ba ki da sauran haske a idanuna amma har gobe kina nan a ‘yar uwata sai ranar da ki ka gyara barnar da ki ka yi min”.
(Duka wannan maganar Prince ya furtata cikin harshen turanci ne).
Daga haka ya fice ya barta a dakin idanunsa sun kada zuciyarsa ta tabu. In duniya da amana Taiwo bazata zame masa cikas ga cikar farin ciki ba. Komai nashi nata ne da ‘ya’yanta haka komai yake yi a duniya su yake tunawa da samun farin cikinsu. Bashida wani buri da ya wuce itada ‘ya’yanta amma ace wai abu guda daya da ya nuna yanaso, Taiwo ta gagara son shi.
Dakin Nenne ya nufa, sai ya tarar