Showing 30001 words to 33000 words out of 41738 words

Chapter 11 - Aishah-Saddiqa book 4 end complete by Takori Kabara .txt

24 Nov 2024

2291

kace ka kara hutu. Allah kadai yasan sai yaushe zamu dawo.
Kayi hakuri ina gamawa ko Sunday ne na yarda mu tafi”. Prince ya numfasa, ya ce “it’s okay baby…. bakomi.
Amman I have to go on Thursday nayi mantuwa a Argentina, its vital kuma. Sai in hada abinda zan dauka Friday na wuce Qatar don in dan huta kafin Monday din, in yaso Monday din sai ki taho”.
Ke dai kiyi min addu’a kar in mutu before Monday”. Siddiqah ta bata rai tace “haba Hamma!” Yace “baby you wouln’t understand” ya riko hannunta ya kai bakin sa yayi kissin. Daga nan Hamma ya tashi yace “bari in tafi” tace “toh” suka fito a jere, Siddiqah ta ga dai ya tsaya ya sake kimtsawa.
Suka fito tana gaba yana binta a baya har dardumar su Ummanta, ba kowa. Ta leqa dakin Umma tace “Umma ga Hamma zai tafi” Umman ta fito sukayi sallama, Haj. Zainab tace “Baban naku ya shiga wanka”.
Yayi masu sai da safe. Ta raka shi har kofar gida tana tafiya lankai-lankai, tana kuma dama masa lissafi. Tace “da safe zaku wuce da Nenne?”. Yace “ai ni sai nazo na sallami amarya ta, so afternoon flight zan bi ko evening”. Tace okay. toh se da safe Hamma”. Yace “ban hannun ki, ta bashi, yasa hannu a aljihunsa ya dauko waya ya saka mata ciki, yace “I will call u tonight, don’t sleep”, tace “okay”, yasa hannu ya dan mata side hug da kiss, ya kalle ta yace “I love you so much Siddiqah. Sai na kira”, tace “okay”.
Har ya fita ya kusa shiga mota tace “love u too..” a hankali. Shi kuma Hamma da shegen ji, yace “Ayshah what did u say?” tayi cikin gidansu a guje. Zuciyar ta yau sai “lahaula wala quwatta illa billah….” don farin ciki ne ziryan a ciki.
Idan Prince ya tuno abubuwan da suka faru yau sai murmushi ya dawo, ba kowa a Falon Oummana shima bai neme su ba ya yi cikin dakinsa ya fada gadon sa ya kwanta
‘Re-play’ kawai yake na inda tace ‘babyyyyy!” And kissing him back, he don’t know why intensity din yau is different, ko don tana gidansu ne ya san he can’t have her… makes him want her more…
Ya ji zai daga ma kansa hankali yayi toilet ya saki cold shower akansa… yace yanzu with what he is feeling, ta ya za’ai satin nan?
Bayan ya fito yayi sallah kenan sai ga wayar Kiki. Suka gaisa, tana bashi hakuri kamar zata yi kuka. Antinta Firdausi told her all what happened, yace mata ai ya wuce yanzu ma ya dawo daga wurin Aysha din. Kiki tace tana ta kiranta off, yace zai tura mata sabuwar lambarta, Kiki tace “so you went to do ZANCE!”. Tayi ta yi masa shakiyanci son ranta.
Da suka gama hirar su da Kiki, ya kira mutuniyar a waya, sau biyu bata dauka ba sai a na ukun.
Siddiqah tace “Hamma!” shikuma yace “babyn Hamma… ba nace kar kiyi bacci ba?”
Tace “bansan nayi ba. Gajiya ce”. Hamma yace “me akayi har kika gaji… don’t be a lazy wife ooo, wallahi to gym zan saka ki kina isowa Qatar”. Siddiqah tayi dariya tace “hidimar biki fa… ka manta biki muka gama?” Yace “oh! Na dauka Hamma ne ya miki nauyi”. Siddiqah ta zaro ido tace “good night!” Kit! Ta kashe.

Sukayi bacci mai dadi da mafarkan juna masu dadi yau.
Da safe su Nenne suka wuce. Shi kuma jirgin sa se karfe shidda na yamma.
Yana yin sallar la’asar ya sallami Oummana da Uban kasa, yace daga nan zai biya wajen Aysha daga can ne zai wuce airport, gobe ne jirgin sa na Argentina da dare sha biyu na dare
Uban kasa da Nani Oummana suka masa addu’a sukayi masu fatan alkhairi. Oummana tace lallai yace ma Aisha tazo mata. yace “toh, na bata waya zata kira ki”.

Yau dai Prince wankan kananan kaya akayi. Duk ya zama dan yaro karami.
Da ya iso gidan Abba baya nan sai Umma. Suka gaisa, yace yana so yaje ya sallami Baba Barau. Umma ta ce Aisha ta raka shi. Nan ta saka hijabi Mal. Buhari ya kai su.
Suka shiga suka gaishe shi. Hamma yace “anjima kadan ze tafi” Baba Barau yayi masu nasiha. Ya saka masu albarka, yace in ya isa yayi settling ya kira shi sai a shirya mata tafiya ko bayan sati ne, sabida ya kimtsa. Da sauri Prince yace “ai Monday zata taho, Baba ba abin da za a kimtsa”. Baba Barau yayi dariya yayi masu sallama.
Suka fito suka dawo gidan su Aisha, a parlon Abban ta. karfe hudu lokacin, 5 ze tafi airport jirgin 6:15 ne.
Nan ya lalace a wurin ta, ta kawo masa abinci ya dan tsakura yana hira yana abubuwansa. Itama dai yau Siddiqah sakar masa jiki tayi yana kissing dinta tana mayar masa, abin nasu wane jiya. Ga Abba baya nan so free suke jinsu. Ita Ummanta ma bacci ne ya dauke ta. ta saba bacci tsakanin azhar da la’asar.
To dai romance kawai ake a falon nan, can Aysha tace washhhhhhh can kaji Kehinde yana kiran babyyyy…..
Malam Buhari daga waje ya duba agogo, yace shikadai, “yaran zamani, sai jirgin ya tashi ya barshi”. Mukuma nida team of editorial board dina muka ce “ko ina girman Prince Kehinde?” Domin gabadaya Prince ya zama yaro mai tashen balaga, a nan duk ya lalace, sai ji yai wayarsa na kara.
Mal. Buhari na tuna masa jirgi bazai jira shi ba. Nan dai ya dawo hankalin sa ya nutsu ya dauka.
A ladabce Malam Buhari yace “Yallabai, na ga biyar da rabi ne, ba shida bane tashin jirgin? Ka san akwai dan tafiya”. Yace “ina zuwa”, a gajarce yayi maza ya kalli agogon sa. 5:40 yace “Baby kinsa nayi missing flight dina” tace “ba ruwana” ya rungumo ta, ya dau wayar sa yayi dialling wata number, suka gaisa, yace “yanzu zan bar Je ka da fari, zan samu jirgin?” yace “to ba komai, a yankar min wani ticket na morning flight gobe”.
Aisha ta zare ido tana kallon sa…. ta tashi ta zauna, yana kallon ta lovingly, tace “Hamma da gaske ka rasa jirgin?” Yace “cewa yayi saidai inyi gudu, ni kuma ban son hanzari shine nace ya yanko min na gobe da safe.
Bari in tashi in tafi ina kallon ki haka dinnan bazan iya barin gidan nan ba”.
Aisha ta mike, shima Prince haka.

Har sunzo kofar gidan Prince yace “ina fa da gida a garin nan, ko muje ki gani?” Yana mata wani kallo ta ce “noooo!” tayi cikin gida ta barshi.
Har ta shiga gida sai ga message din sa, yace “anjima zai zo ya kai ta fadar Gombe, Nani Oummana tana son ganin ta”. tace “toh”.
Sai ga wayar Mal. Yunus, yace “Abdulrashid an tafi?” Yace “wallahi Abba nayi missing flight dinne, sai da safe. Karfe 6 ne amma nace se 5 zan tafi airport, toh kuma hold up” Abba yace “assha. Allah yasa haka shi yafi alkhairi” Hamma yace “amin”. Yace.
“Toh sai ka kaita wajen Oummana din da kan ka kawai. Daman nace zan kai ta anjima”. Prince ya ce “toh shikenan Baba”.

Suna tafe a hanyar zuwa fadar Gombe, Malam Buhari na gulmar Prince a ransa. Yana cewa wato jinkirin aure ga namiji ba sauki gareshi ba, ranar duk da ya samu mata ko yaya take komai yarintarta sai Allah, domin kamun kazar kuku mace take musu, dubi dai yadda 'yar yarinya ficiciya ta tashi kan Yallabai Abdulrasheed, yana can ya like mata ya lalace har jirgi ya tashi ya barshi.


Yawan shekarun nan nasa, matsayi da girman sarautarsa (mulkinsa na gado gaba da baya), da 'fame' din nasa na Polo (as African Polo Legend) duk an tashi kansu cikin dan lokaci ya dawo yaro daidai ita.
Domin tareda shi Malam Buhari din Nenne tayi ta zaryar nemawa Prince auren Aisha. Bata Lagos bata Gombe, har saida ta tabbatar sun daura auren sun daukota Ilorin.


Nani Oummana ma sai daga ido tayi taga Prince ya dawo. Bayan sun riga sunyi sallama ta karshe cewa daga can zai wuce airport ya tashi gida Lagos. Ba suyi dashi zai dawo ta nan ba.
Oummana tace "Yaya haka Hammansu? Mantuwa kayi?"
Ya zauna yana cewa "to ya za'ayi? Jirgin ya tashi ya barni Oummana". Wani miskilin murmushi Oummana tayi masa, tace "garin yaya toh? Kana can kana soyayya ko?" Hamma ya dukar da kai yana ‘yar dariya yace, "kusan haka, ai bakya karya Oummana" Oummana ta sake yin murmushi irin nata, ita tasan watarana za'ayi haka. Domin da alama AISHA INDO SIDDIQAH! Ta shigo rayuwar Yarima da zafinta. Zata murza kambu son ranta, ranar duk da Prince ya shiga komarta. Yarinyar nada tarin baiwa da kullum take tuna mata da auren Nenne da Dade.
Kusan tace tarihi ke maimaita kansa akan Abdulrasheed Dan Idris dan Abdulrasheed Akanni. Tana fatan wannan soyayya da Prince yake yiwa Siddiqah ta dore musu har tsufansu, su zama (typical replica) na Sappa da Idrisu.


Ganin Oummana bata ce masa komai ba sai murmushi take zabgawa yace cikin basarwa da hadiye kunyar da yaji.
"Amma gobe in Sha Allah bazan yi wasa ba Oummana, morning flight dani zai tashi karfe 6am, ko sallama bazan je mata ba".
Oummana me zata yi ba dariya ba, tace "to ni me kaji nace ne? Ko nace kayi laifi ne? Haka akeso abubuwa suyi daidai. Saika koma ka daukota ka kawomin ita yau da kanka. Daman nafi so in ganku a gabana tare". Yace "In sha Allahu Oummana, Baba Yunus ma da kansa yace yace inje in daukota in kawo miki, dama na gaya musu kinason ganinta.
Da nayi sallahr Isha zan koma na taho miki da ita".
Ya wuce zuwa dakinsa na sassan Oummana kai tsaye toilet ya fada don yin wanka, don yasan a yanayin da suka kasance da Aisha yau, bai yiwuwa yayi sallah yanzu bai yi wanka ba.


Saida Umma ta tashi daga barci taga Siddiqa a zaune a gefenta, tace "har ya tafi?" Tace "eh Umma, gashi har jirgin Lagos da zai hau ya tashi ya barshi. Dole sai gobe zai tafi gida".
Sannan cikin jin kunya ta gayawa Ummanta Hamma yace zai dawo su tafi wurin Oummana anjima, ta aikoshi tana son ganinta.
Nan Haj Zainab ta hau tunanin me zata baiwa Aisha ta tafiwa da Oummana, karshe tunaninta ya tsaya a kan turarukan ‘Oud’ da ‘Sandaliyyah’ na jiki dana turaka data sayo a Saudiyyah. Su ta saka a kyakkyawar leda tace Aisha ta kaiwa Oummana tsaraba.


Kafin sallahr Isha Siddiqah ta yi wanka ta kara shiryawa cikin wani tattausan cotton lace mai tsananin taushi da adon kananan duwarwatsu, kalarsa Orange ne da adon (milk color) furanni, tun lokacin hajjin bara Ummanta tazo mata dashi daga Jeddah, sannan tayi sallah Maghreb da Isha.
Aisha ta dauko turarenta Fahrenheit ta feshe jikinta dashi. Kana iya jiyo sanyin kamshinsa tun daga dakinta har tsakar gidansu zuwa dakin Ummanta.
Daidai lokacin Baba Yunus ya dawo, Siddiqah tayi masa sannu da zuwa ta karbi ledar hannunsa yace mata balangun Ayuba ne ta juye su ci ita da Umma shi sun ci shi da Baba Barau. Ya kuma ce ta shirya Hamma ya kira shi zai zo yanzu su wuce gun Oummana, Mallam Yunus ya gyara zamansa akan kujera yace "toh Indo nasan ba sai na maimaita miki ki kula da kanki ba, kuma ba sai na gaya miki ki zama ambassador din kanki da kanki ba a wurare irin wadannan.
Waje ne da yake bukatar nutsuwa da kamewa wadanda bana jinki a kansu Siddiqah. Tunda gidansu mahaifiyar sa ne".
Aisha tace "toh in sha Allah Baba". Daidai lokacin Sunusi ya shigo yace "wai mijin Aisha yazo daukarta, suna cikin mota".


Siddiqah ta dauki gyalen data tanada wanda yayi matukar shiga da kayan jikinta ta yafa wato off white, nan ta dauki karamar 'hand bag' dinta tun tana gida take amfani da ita, ta dauki ledar sakon Oummana ta yiwa Umma sallama. Haj. Zainab tace,
"to sai kun dawo. A gaida Nanin".


Prince ya mika hannun damansa ya budewa Aisha kofa barin hagunsa ta shiga. Malam Buhari na kokarin fitowa don ya rufe ya hutasheshi. Shi da kansa ya rufe mata kofar. Saukin kan Prince yana kara masa kima mai yawa a idon dattijon direban. Ya koma ya zauna ya rufe kofa ya jasu a hankali suka bar Jeka da fari, zuwa babban titin da zai kaisu gidan Sarkin Gombe.


Saida Prince ya san yadda yayi cikin dabara ya sanya tafin hannunshi cikin na Aisha. Ya sarkesu, sannan ya matsesu cikin nasa hannun. Taushin hannun kowannen su ya ratsa su. Suna tafe yana mata hira kasa-kasa amma ta kasa sakin jikinta dashi kamar dazu, don Ummanta ta jaddada mata ta kama kanta, ta rike kunyarta, don gidan su mahaifiyar shi zata je kuma zuwa na farko.


Da yake duhun dare ya shigo ba kowa ya ankara da shigar su sassan Oummana ba. Suka sameta har lokacin akan dardumar sallahrta tun bayan data idar da sallahr Isha tana zaune tana lazimi bata tashi ba.
Shigowarsu tasa ta shafa addu’ar da take yi, ta mike tana cewa "Jabbama da Indo Siddiqah, barka da zuwa, Indo Aisha". Aisha tayi kasa ta zube a gaban Oummana zata fara gaisheta cikin girmamawa, tsohuwar ta kamo hannunta ta mikar da ita tsaye, ta jata zuwa kan shimfidar fata irin ‘traditional rug’ dinnan da akeyi da fata wanda akanshi take zama a falon, da Tum-tum a kowanne gefe da gefe manya har guda hudu, Nani Oummana ta zaunar da ita a kusa da ita.
Kasancewar Oummana bata zama akan kujera sai wannan shimfidar tata. Prince ne ya zauna a kan two seater, a gabansa akwai karamin centre table dauke da ‘tray’ shake da kayan marmari. Prince ya dauki apple guda daya jawur da ita yana yankawa da karamar wuka kaiwa bakinsa yana ci.
Yana kallon Oummana ta rasa ina taka-saka -ina taka-aje da Siddiqah, kaunar da suke mata itada Nenne, ya tabbata daga Allah ne ta dalilin son da suke yi masa. Domin bayan Oummana ta zaunar da Siddiqah a kusa da ita, sawa tayi hadimanta suka cika gabanta da kayan motsa baki na alfarma, wanda ko tabawa da hannunta Siddiqah ta kasa yi, ji take kamar yau ta fara haduwa da Oummana.

Daga bisani ta gaida Oummana da fulatanci, Oummana ta amsa ta kuma tanbayeta lafiyar su Ummanta da Babanta da iyalin Baba Barau. Siddiqah ta amsa duka, kanta a sunkuye, murya a ladabce. Anan Oummana tace maqasudin kiran nata dama don tayi mata nasiha ne. Nan tace Hamma ya basu wuri. Hamma yace "Nani abin harda kora?" Tace "ai zan kiraka ne inna gama da ita, akwai abinda ba sai ka ji ba".


Prince ya shige dakinsa ya barsu. Oummana ta fara yiwa Aisha fada da nasiha kamar ita ta haifeta.






Nasiha ce ta manya sannan mai shiga jikin yaro, inda tace wa Aisha.
"Idan kana aure yana nufin ka girma. Abubuwa da yawa zasu iya faruwa a rayuwar auren mace, musamman da dangin miji, to idan irin haka ta faru ba komai ake fadawa iyaye ba Indo, sabida gudun bacin ransu.
Sannan shi aure rai ne dashi. In zama bai kare ba mace da mijinta sai su dawo su shirya, su manta komai cikin dan lokaci, amman iyaye basa mantawa.
Don haka toh a kiyaye irin haka anan gaba, kuma koda wani abu ya faru to Aysha kizo ki sameni ni Oummana ko Nennen ku, na tabbatar hukuncin da zamuyi wallahi Umman ki baza tayi ba. Kinji ko Indo?
Sabida Allah shine shaidata, yadda nake jin Hammansu a raina haka nake son ki babu bambanci a wurina, kinji?
Shiyasa nake so nan gaba ba fata ake ba abin Allah ya kiyaye, ko da wani abu irin haka ya faru toh dan Allah Aisha ki koyi magance shi tsakanin ki da mijin ki.
Musamman irin wannan da ya faru da Taiwo, mijin ki na matukar son ki, har Taiwo ta isa tasa kice kin bar auren ki?
Allah yayi maki albarka ya kawo muku yara masu albarka. Shi wannan da baya son sarautar nan tamu, wato ya gado ubansa, Allah yasa ya haifo min wanda zai so sarauta.
A zuciyar Aisha tace "Amin". Sai lokacin ta gane Hamma baya falon ya basu wuri itada Oummana.


Da ya tashi fitowa ba kayan da ya fita dasu ne a jikinsa ba, ya canza su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login