Showing 36001 words to 39000 words out of 41738 words
Chapter 13 - Aishah-Saddiqa book 4 end complete by Takori Kabara .txt
jiransu ba.
Aisha ce ta fara fitowa rike da jakar hannunta data Nenne, kafin su Nenne su biyo bayanta. Prince ya runtse ido ya bude yana kallon beautiful Aishah… tana takowa majestically zuwa gareshi, da wani madaukakin murmushin SO a fuskarta, hamdala yake a zuciyarsa, sai kuma ya hango Nenne daga bayanta itama ta taho, tana taku ita kuma cike da sarauta. Prince ya karasa da hanzari ya fara rungumar Nenne, sannan Dade, kafin ya dawo ga Aisha ya rungumeta itama, yace “Aysha welcome oooo, sai yau Nenne ta gama boyon naki ta kawo min?”
Dade yayi dariya, Nenne ta harareshi, Dade yace “yaushe muka boye ta din? Daga cewa zamu yi mata rakiya?” Duk suka yi dariya, nan Hamma ya karba mata jakunkunan hannunta, ya sake rungumota jikinsa yana cewa “welcome Aysha! Welcome oooo!”. Daga haka suka wuce mota.
Kasancewar Dade da Nenne duk sunada ‘Entry Visa’ na Qatar kuma zasu yi transit na awanni hudu a Qatar sai suka yi amfani da wannan damar suka rako Aisha har gidanta.
Prince na tuki akan hanyarsu ta isa gidansa, amma hankalinsa rabi na kan Aisha wadda jikinta duk ya nuna gajiya da lalaci, ta dauko wayarta daga jakarta ta kunna, ta soma kokarin roaming layinta domin ta samu ta kira Umma da Baba Yunus, ta gaya musu saukarsu lafiya amma ta kasa connecting.
Duk wani motsi da Aisha tayi a cikin motar sai taji idon Prince Abdulrasheed a jikinta, kai har a ruhinta, ita kuma ta ki yarda su hada ido da gangan kada taje ya bata kunya, don tun daga rungumar da yake mata a gaban su Nenne ta san komai ma zai iya (that’s his real identity of Yoruba demon), gashi duk dagowar da tayi sai ta hango Nenne ta cikin mudubin gefenta, wadda ke zaune a kujerar bayanta, Nenne waya take yi da Fatima a lokacin bata maida hankali a kansu ba sam. Aisha ce dai duk ta ji ta takura da idanun Prince dake yawo a jikinta. Kuma idanun nasa sun rikitata.
Finally, Abdulrasheed ya kashe motar a muhallinta wato ‘parking lot’ na kofar gidansa, yaron dake kula masa da gidan wani baqar fata ne dan Senegal mai suna Zaid, kuma har ila yau, Zaid is a good Chef for him, tun kafin su iso ya gama girki na musamman na larabawa, ya shirya a dining sai jiran isowarsu bisa umarnin Ogansa, tunda safe Zaid ya shiga kitchen yake aiki saboda zuwansu. Zaid ya shirya Lamb mandi, kebabs, fatoush salad, humus, Baba ganoush, ga kuma desserts da bakhlava ga arabic coffee. Duk ya tanadar musu kamar mai hada wata ‘yar kwarya-kwaryar get together. Saidai ba wai yayi da yawa bane daidai cin abincin mutum 4-5. So already table was set before their arrival.
Suna shigowa Prince ya budewa Aisha dakinta ya shigar mata da akwatinta ya ce “your room”. Su Nenne ma, ya bude musu wani dakin yace su shiga su yi alwala da sallah, nan ne Nenne ta gane Hammah yayi gyaran gida sosai, ta yaba mashi bisa wannan kokarin ta kuma dan tsokane shi da fulatanci “da angon Aisha ka sha kamshi, na Siddiqah bada kanka a sare”, nan dai duk suka yo alwallah har Aisha, Hamma ya jasu sukayi sallahr jam’i gabadaya, sannan suka fara cin abinci cikin nutsuwa suna yi suna duba agogo.
Da suka kammala Nenne tace a bata ‘black tea’ (lipton) ta kara, saboda Nenne bata shan coffee ita. Prince da kansa ya dafo shayin a kettle din dafa ruwan zafi, ya hado ma Nenne a kan tray da mug cup da liptons kala-kala na alfarma da yake ajiyewa don baki don shi in ka cire chamomile da lavender ba shayin da ya ke sha, ya ajiye mata bakidaya liptons din kala kala don ta zabi wanda tafiso cikin su, (and honey instead of sugar) don Prince baya shan sugar sai zuma.
Nenne na sipping zazzafan lipton Dade ya hada Prince da Aisha yana musu nasiha a tare. Ya ja hankalinsu kan su hada kansu su zauna lafiya, su zama sirrin juna, su kuma taimaki junansu akan komai. Yace ma Aisha, ko me Prince zai mata na rashin kyautawa ta doshesu kai tsaye. (They are always there for her) muddin suna raye. Ya roketa kada ta kara dosar iyayenta da matsala inba a inda taga sun gaza daukar mataki ba.
Shikuma Prince Dade yace dashi “har kullum ka tuna Aisha mace ce, kuma mai kankantar shekaru a kanka.
Yadda duk ka mikar da ita a haka zata girma.
Don haka sai ka nuna mata abinda kakeso da wanda baka so a hankali.
In tayi kuskure ka nuna mata ta lalama da jurewa kuruciyarta.
A karshe suka saka musu albarka shida Nenne, a bisa biyayyar da suka yi musu, suka roki Allah ya basu masu yi musu mafiyinta da gaggawa. Ya kuma sa ‘ya’yansu su kasance nagari masu bin iyaye kamarsu”.
Dade yace “saura ke Nenne ko?” Tace “ai you have said it all Dade, banida abin cewa, addu’a kawai zanyi musu, wadda kullum bana fasawa. Allah yayi musu albarka da zuri’a dayyiba albarka Annabijo”.
Daga haka duk suka mike, Prince ya dauki mukullin mota don ya maida su, yace ma Aisha, “Ayshah ki rufe kofar falon ta ciki, in na dawo zan bude da key dina, idan Zaid ya tattare wajennan ya tafi”. Ya gaya mata akwai yaron gidan, mai suna Zaid, amma baya kwana a gidan, da safe yake zuwa ya tafi karfe 6 na yamma in ya gama masa dinner.
Har sun fita tare dasu Dade sai yai excusing dinsu ya dawo kamar yayi mantuwa. Da sassarfa ya isa ga Aisha ya rungumota ta baya tana kokarin rage nauyin laffayar jikinta. Aisha tace cikin ‘yar rawar murya “Hammah, mantuwa kayi? Kada suma kasa jirgi ya tashi ya barsu fa?”
Prince kamar bai ji korafinta ba, ya sunkuya ya sumbaci bakinta dake maganar cikin shagwaba so lightly yayi sumbar, sannan a daidai kunnenta yace cikin shauki.
“Welcome Ayshah.. welcome to your abode! The lady of my heart, love of my life, mother of my children, the one that has completely changed and shaked my whole universe. I am coming back soon to welcome you Baby, kin ji?”
Ya sake kai mata sassanyar sumba a wuyanta da lips dinta, amma Aisha bata barshi yayi nisa ba ta kwace bakinta cikin jin kunya, tace cikin shagwabar da bata zuwar mata sai in tana gaban Hammah Abdulrasheed kadai.
“Hamma Abdul mana?! Dade da Nenne, suna bakin mota suna jiranka fah?!”.
Prince da kyar ya juya ya fita kuma da baya da baya, yana sumbatar hannunsa yana huro mata iskar, ita abinma sai ya bata kunya da dariya, tasa tafukanta ta rufe fuska tana kallonsa ta tsakanin yatsunta cikin idonsa da wani irin kallon SO, wanda yasa Prince yin tuntube a bakin kofar fita.
Da kyar Hamma yakai bakin mota, su Nenne dai tuni sun bude sun shige basu kara bi ta kanshi ba.
Bayan fitar Hammah Siddiqah ta yi unpacking ta fada wanka ko ta samu karfin jikinta daga gajiyar data kwaso, ta sille jikinnan tas ta zuba sassanyan turaren humra na “turarewutashop” (crème de la crème), tana gamawa ta dauko ‘lounge wear’ dinta wando da riga ta saka, sai ta dora hijab ta fito falon, tana fitowa taga wayam, Zaid har ya gama tattare wajen ya kunna bakhoor burner ya kwashe kayan abincin da wadanda aka bata, ya bar musu flasks na coffee da tea a dining din, da mugs da desserts harda da dan cup cakes ya tafi, ta kashe turaren don ya kare, sannan ta cire hijabinta ta kunna kallo.
Daman Hammah ya mata connecting wifi kafin ya tafi mayar dasu Nenne. Sai kawai ta kira Ummanta ta whatsapp vedio call, suka danyi hira akan saukarsu lafiya sannan Siddiqah ta haska mata wani sashe na gidan ta gani, tace “Umma kinga gidan” Umma tace “na gani Petel” ta sa albarka, bayan sun yi sallama da Umma ta kishingida a three seater din falon tana kallo, daga nan ne barcin gajiya ya dauketa. Kuma ko a cikin barcin nata duk mafarkanta Hamma Prince ne.
Saida su Nenne suka wuce priority lounge zasuyi jiran one hour kafin tashinsu Hamma ya juyo gida.
Yana tafe a hanya ya kira Zaid, yace kada ya zo masa gobe da safe sai ya neme shi da kansa. They will take care of themselves. A lokacin yana adana motar a muhallinta, ya dauko abubuwan da yake bukata ya fito ya rufe motar. Yasa mukulli ya bude kofar shiga falon.
Shiruuu baka jin komai sai hucin AC. Kafin ya ankara da Aisha a three seater tayi dai-dai akan kujerar tana sharar barcinta sadidan. Prince har da sakin ajiyar zuciya don ji yayi tamkar komai na rayuwa yanzu ya gama yi masa daidai (with his wife Siddiqah by his side). Hamma bai tasheta ba don ya ga alama tana jin dadin baccin, dakinsa ya wuce ya fada wanka.
Har Prince ya fito yayi sallah yayi changing zuwa kayansa na barci wasu ruwan tokar pajamas Aisha bata farka ba, a hankali Prince ya sunkuya yasa hannunsa biyu ya dauki Aisha, ya soma tafiya da ita a hannunsa, yana sumbatar kasan wuyanta da saman lips dinta softly, jinta dauke a hannun Hammah da wannan sumba da yake mata (soft and light kiss) Aisha ta bude idonta ba shiri, idanun ta suka fada cikin na Hamma Abdulrasheed (Prince).
Aisha tace “Hammah…” cikin magagin barci shi kuma yace “shhhh, cigaba da barcinki ban so kika tashi ba Baby”.
Sai Aisha ta mayar dasu ta sake lumshewa, ta kuma sunne fuskarta cikin kirjinsa don kunya, katuwa da ita an mata daukar jarirai. Prince ko a jikinsa don bata fice baby din ba a idanunsa.
A takiyar dakin Prince ya sauke Aisha, kasancewar ya kashe wutar dakin ga barci a idonta sai bata fahimci a inda suke ba, har sai da Prince ya kunna wutar dakin haske ya gauraye ko’ina ta gane masterbedroom dinsa na.
Aisha ta fara bude idonta a hankali cikin nutsuwa tana kallon yadda Prince ya shirya mata ‘special welcome’.
A kowacce kusurwa ta dakin kyawawan welcome cards ne na bature, da ‘scented flowers and rose petals’ zube akan gado, wai duk don maraba da saukarta, har saida abin ya so ya sata dariya ya kuma sata jin kunya da farin ciki sosai.
Daga bayanta Prince yasa hannu ya rungumota bakidaya zuwa jikinsa. Ya bata ‘fresh red rose bouquet’ a hannunta, bayeraben mijin nan nata yau zai kasheta da soyayya da farin ciki mai yawa, yace.
“Welcome my darling Baby! You have no idea how happy I am that you are here!”.
Ya sumbaci kasan wuyanta a hankali, Aisha na murmushi tana kara wartsakewa daga barcinta tace “thank you darling!”.
Sai ji tayi Hamma ya saka bakinsa a tsanake cikin nata, ya soma sumbatarta, deep gentle and cool kiss, wanda nan da nan ya soma shiga kwanyar Aisha ta soma kyarma. Hamma na iya jin yadda jikin Aisha ya soma rawa din. It obviously shows her nervousness and naivity, ta kuma kasa cewa Hammah komai, domin sosai kisses dinsa ke shigarta.
Prince ya kwantar da kan Aisha a kan kirjinsa, wanda hakan yasa dankwalinta ya zame ya fadi ta baya. “Yaa Subhanallah” kawai Hamma ya iya ambato, lokacin da kyakkyawan kitson Aisha akan gashinta mai laushi da baki da sheki ya bayyana, hasken lantarki kuma ya kara masa kyau, siraran jelunan kitson suka kwanto lambam akan wuyanta.
Prince kasa jurewa yayi, don bai taba ganin abinda ya masa kyau irin wannan gashin na Aisha ba, sai da ya shafo kitson da hannun damansa tun daga farkonsa har kasan jelunansa don kamar ba mutum ne yayi ba.
Wata rahma na sauka a zukatansu su duka. Yace “Aysha…” tace da kyar “na’am Hammah”, alhalin ilahirin jikin ta yana shaking, and he can feel it, wato yana jin irin rawar da jikinta ke yi a nasa jikin.
Sai ya soma shafar bayanta a hankali cikin lallashi da son saka mata nutsuwa, ya ce “Aisha are you nervous?” Murya can kasa, ita kanta muryar tata da tasa rawa take, kamar yadda jikinsu ma yake rawa da karkarwa irin nafarin shiga, because she can feel how aroused the Prince is which makes her more frightened.
Ta daure tace “a’ah Hamm… am not”, yace “to relax, kin ji Aysha. Ki saki jikinki dani, ba abunda zan miki in har zuciyarki bakya so yau.
I will never force you to be with me in this regard. I just want to feel your warmth in me and I feel it, so relax kin ji”.
Aisha har da ajiyar zuciya, ta fara nutsuwa. Kehinde yana rungume da Aisharshi kamar mai tsoron kada wani ya kwace masa ita, ko ta kara komawa Gombe ta barshi.
Yama rasa inda zai sakata cikin jikinsa da zuciyarsa ya zama contented. Daga bisani ya dora Aisha a laps dinshi suka zauna a gefen gadonsa, ya matseta sosai ya hadata da kirjinsa kamar zai hadiyeta.
Bata san meyasa wata irin kasala ta sameta ba a wannan lokacin da Prince yayi shiru kawai yana makale da ita, sai ta samu kanta da kwantar da kai a kirjin Hammah kawai, tana kara samun wata irin muguwar kasala.
Hammah kamar ya san halin da Siddiqah take ciki, cikin dabara ya kwantar da ita a tsakiyar gadonsa, ya kuma dora mata dukkan nauyinsa.
Prince ya soma yi mata hira, irin hirar masoya mai jan hankali, he’s just trying to make her comfortable with him.
A tsakiyar gadon Hamma suke kwance yanzu, yana kallon jan lallenta, ya soma jan yatsun da suka sha lellen yana mata hira mai ban dariya duk don ta saki jikin ta daga barin da yake yi, daga jan yatsu Hammah ya zarce da yiwa Aisha tausa a santala-santalan kafafunta, tausa mai tsada har ya isa ga inda yake son isa.
Kafin kace meye wannan gabadaya Abdulrashid ya fara kunna Petel din Umma, rawar da jikinta ke yi maimakon ya ragu sai ma ya karu. Kasala ta karu mata. Don Nenne ta bata abinda bazata iya resisting din Hammah a wannan daren ba; wato ciccibin Naggen yarbawa, ga touches din Hammah na kara shigarta very irresistible, amma duk da haka Aisha bakidaya a tsorace take da Hammah a matsayinta na yarinya budurwa a ranar farkonta, har tsoron da fargabar ya rinjayi sha’awar bakidayanta, don dai kasala ta hanata motsi ne balle ta noke masa.
Ya lura sosai da halin kasalar da take ciki, ko yatsanta bata iya dagawa, yace cikin lallashi “Baby please, be comfortable….kinsan nayi hakuri nayi kokari mai yawa tun aurenmu ko?”
Siddiqah ta gyada kai, duk don ta boye masa fargabarta da rauninta. Tuni barcin idonta daya daukota tana yi ya ware. Prince ya lura da hakan yace.
“Aysha na tashe ki daga barcinki ko? Haven’t you slept on the flight?”
Tace “wallahi nayi fa Hammah, ka san tafiya ko yaya sai tasa mutum jin kasala da mutuwar jiki”. Prince yace “yeah, that’s true. Muje ki sha tea dina na barci (chamomile) zai saki barci mai dadi da ‘bakhlava’ sai mu dawo nan in miki massege kinji Baby?” Aishah tace “ai Hamma bacci kawai zanyi, na koshi sosai. Kaga fa naci kebab sosai” ya sakar mata wata harara yace “toh ni zan sha tea din, zo ki raka ni in hado sai mu kwanta”. Aisha tace “okay” (wani irin innocently). In ka ganta a lokacin sai ta baka tausayi she looks pale, Hamma ya tashi ya mika mata hannu ta taso.
Ita de ta kawar da idonta daga kallonsa ta daga kai suka fita. Ya kunna wutar falon. He actually looks younger yau, ko kayan jikin sa ne? A duniya ta lura Hammah Abdulrasheed nason wannan ‘pallazo’ wandon ‘grey’ kuma ya lafe a jikin sa sosai, ga rigar ma haka tai masa cippppp! Masha Allah kawai Aisha tace a ranta, wannan sarbadeden saurayi Allah ya bata ita kadai in sha Allah…. sai tayi murmushi.
Hammah ya kalle ta yana zuba tea shima, tayi masifar kyau. Yau kuruciyarta ta fito sosai bakidaya, she looks adorable. Ga lallen da Kitson, amarya sakkkk! Sweet 16 mallam, dukiyar fulaninnan so perky…. ya tuno yadda ya samesu ranar nan a Gombe, ranar da yaje zance… “kai! Ya Ilahi!”. Hammah yace bai ma san ya fadi ba. Kawai sai jin zafi yayi a hannun sa, ya kuwa saki flask din kasa, “subhanallahi!” Suka ce a tare.
Siddiqah tace “Hammah ka qone? Mu gani?” Ta taso da rawar jiki ta rike hannun nasa, yace “no, I am fine” tace “kai ko Hamma Abdul me kake tunani haka har ka qone?” Yace “U, my darling”