Showing 15001 words to 18000 words out of 41738 words

Chapter 6 - Aishah-Saddiqa book 4 end complete by Takori Kabara .txt

24 Nov 2024

2292

ta rufe da key ta ciki, don ta san dole zai biyo bayanta da lallashi akan batun biko ita kuma so take ya dau mataki da kansa, tafi son ya gane da kansa Taiwo fitinanniya ce abinda bai taba yarda a baya ko za’a shekara ana fadin cewa Murjantunsa tana da hali. Itada ta haifesu ma ta kwana da sanin hakan amma shi bai taba yarda. Haka ya bi bayan Dade shima a nasa masaukin, Dade ya ki ganinsa a daren don har ya kwanta, dan lekowa yayi kadan ta tsakanin kofar bai bashi hanyar shiga masa dakin ba, ya ce.
“Please Kehinde, ka yi duk abin da ya dace da kanka, but count us out akan maganar Siddiqah da Taiwo, duukansu naka ne, ba wadda zaka zaba ka bar daya, amma akan maganar aurenka mu mun gama sauke nauyin duk da Allah ya dora mana a kanka, don haka duk wanui kalubale na rayuwar iyali sai ka nemi hanyar managing dinsa da kanka”.
Auren Princess Fatima da Princess Firdausi kenan bai zo wa kowa a iyalin Engr. Idris Akanni da dadi ba. Taiwo ta bata musu armashin komai don events na al’ada har uku Nenne ta soke, ta ce za ta koma Lagos. In yaso dangi su kai amaren gidajensu haka, tunda an gama mai wuyar daurin aure, sa yi dinner washegarin tarewa a gidan mazajensu.
Shi kuma Prince ta ki yarda ma ta ganshi har washegari tana doje masa da uzurin mutane sun mata yawa bata da lokacin kebewa dashi, shirin komawa Lagos suke yi itada Dade. Don haka Hamma Abdulrasheed Prince ya zama wani sukuku da shi a gidan, don Taiwo da zai samu ya kara hucewa a kanta da sassafe ta fice ba wanda ya san ina ta yi, kamar ta san ya ci alwashin sake cin ubanta da cin mutuncinta in style, ganin ta jawo hatta iyayensa sun daina sauraronsa akan laifin da ba nasa ba balle Siddiqah data dangwarar masa da wayarsa a inda yake tsaye, balle ya samu damar communicating da ita ya lallasheta kafin iyayensa su yarda su saurareshi asan abinyi a kanta.
Ba da sanin Prince ba Dade da Nenne da safiyar washegari suka kira Taiwo ta waya cewa tazo masaukin Dade suna kiranta.
Ba ta dade da dawowa gidanta ba don ta zame musu, ta yi sammako ta taho gidan ta, shigowarta kenan daga main house din kiran Dade ya sameta, kuma as usual Toafeeq ba ya kasar. Daga ita sai babban danta Hakeem a gaban motarta lokacin da dade ya kira ta.
Tare suka zo da Hakeem, tana sane ta taho dashi wai ko sa ga girman danta da yawan shekarunsa su raga mata, don ta san dai tatsuniyar gizo bata wuce koki ita kuma tunda Kehinde ya ce ya daina ganin haskenta akan Aisha, to kowa ma yayi kadan yasa ta so Aisha (she is very sorry to say) hatta Nenne da Dade saidai suyi mata fada irin wanda suka saba ya bi ta bayan kunnenta a wuce wurin.
Dade ya ce da Hakeem ya je ciki za su yi magana da Murjanatu, don haka Hakeem ya tashi a falon yayi musu sallama ya barsu, ya koma mota ya tafi gida.
Taiwo ta shigo masaukin mahaifinta, a zuciyarta ta rasa abinda ke mata dadi da abinda Kehinde yayi mata akan Aisha, wato ya zabi Aisha a kanta, a kan wata banzar yarinya ‘yar talakawa da bata ko kai matsayin house girl dinta ba Kehinde ya gaggaya mata magana haka. Ta kara tsanar Aisha Siddiqah, ta kara tsanar duk wasu ‘ya’yan malam Shehu irinta. Tana wannan tunanin ta yi sallama a kofar dakin Dade ta isa ga kofar falon ta bude. Taiwo ta ga uwa da ubanta fuskokinsu kamar hadarin da ya nausa ya yi gabas, ta tuna when last ta ga Dade ya hade fuska irin haka, Taiwo duk ta tsargu, don ta san ba banza ce ta sa suka kirawo ta ba, ko daga fuskokinsu, Dade ne ya fara magana inda ya ce
“da gaske ne abinda akace kin yiwa matar Kehinde?
In haka ne kuwa baki yi halin Nenne Sappa ba Taiwo. Balle me sunanki Olori Murjanatu.
An yi asarar kudin tara dai, kin zama babbar banza da wofi”.
Yana fade cewa cikin fushi mai tsanani da harshen yarbanci.
“Mu ba mu gaji cin zarafin dan Adam ba, saboda kawai Allah ya ba mu sarauta, ya ba mu aron ni’imar rayuwa daga cikin arzikinsa.
Allah da kansa da ya halicci dan Adam ya karrama shi, ke wace ce da za ki wulakanta dan Adam mai daraja a wurin Ubangijinsa?”
Dade yarbanci kawai yake saki tamkar ya fasa kunnen Taiwo, irin zazzafan yarbancin nan mara dadin ji da razanar da wanda ake yi mawa.
Nenne da bata taba ganin bacin ran Dade irin na yau ba, ba ta sanshi da fushi irin wannan ba, don hak ita kanta ta tsorata da temper din da ta gani tare da shi, Taiwo tana durkushe a gabansa, jikinta na rawa da bari, Nenne kuma ta ce cikin daga murya,
“in duniya da halacci har Taiwo ce za ta zagi matar Kehinde? Ko kunya baki ji ba? Iya kara a rayuwa Kehinde yayi miki, keda ‘ya’yanki da zurri’arki. Murjanatu baki kyauta ba sam, kin ci amanar tagwaitaka da zumunci. Haba! ai inda alkawari ko na munafurci ne ya kamata kiso Aisha, tunda kince kina son abunda yake so, ko ba kya son ta bazaki nuna ba ablle gaba da gaba haka, hakan shine adalci ga dan uwanki kuma da abinda kadai zaki saka masa dawainiya da soyayyarsa gareki da Kiki. Wato kiso iyalinsa.
Taiwo a shekarunki sama da arba’in kin san hakan, bakya bukatar sai an tuna miki, amma mun tuna miki, a matsayinmu na iyayenki, ya rage naki ki dauki tunasarwar ko a’ah a wannan gabar, in kuma halin tsiya halinki ne ki yi ta yi duniya ce. Amma ko Kiki duk wautarta ai ba ta rashin hankalin dake uwarta Taiwo ki ke yi”.
Dade kuma yace “Afuwa daya zan yi miki Taiwo shi ne, in kin je kin gurfana gaban Malam Yunusa, kin mayar da kalaman da ki ka jefe su da su daga bakinki mara saiti, kin dawowa Kehinde da matarsa dakinsa”.

Daga haka suka fice. Suka bar Taiwo a durkushe a wurin.
Taiwo sai kuka ta ke tana tsine wa wadanda suka kawo Siddiqah duniya.
Ba su jima da fita ba, Taiwo ta mike ta koma gidanta, nan ta hau hada kayanta.
Bari kawai ta hakura da aikin asibiti daga yau, ta koma wajen mijinta dindindin. Za ta wuce gidanta na Lagos, daga can ta yi shirin wucewa UK. Ba ta jin nan kusa za ta zo Ilorin balle gidan iyayenta a Lagos, tunda sun sallame ta a kan Siddiqah.
Ba wani biko da za ta je wa Kehinde, tunda shima yace bata da haske yanzu a idonsa. Yo da aurensa da wannan yarinyar ai gara mata zamansa yadda yake shi kadai a baya, da Dawakansa da soyayarsa da da kulawarsa gareta.

“Shin me ke damun Murjanatu-Taiwo exactly?”
Tambayar da iyayenta ke yi wa zukatansu kenan a ranar har suka koma Lagos, Kuma a washegarin ranar da suka koma suka ji labarin Taiwo ta baro Ilorin itama zuwa Lagos, kuma wai tayi resigning daga aikinta na asibiti, ba tareda ta yi shawara da kowa nata ba, sannan bata yiwa kowa sallama daga masarauta ba ta baro Ilorin.
Su dai sun san daidai gwargwado sun bata tarbiyya daya da Kehinde, sun mata nuni da sanin darajar kowanne dan adam, hali ne kawai, wato halayen dan Adam mabanbanta na halitta da dabi'a wanda bai da alaka da tarbiyyar da ta samu daga garesu.
Ko bahaushe kan ce hali zanen dutse ne. In ka shekara ba ka ga mutum ba tambaye shi wani abun daban amma banda halinsa. Tun tana yarinya suka fuskanci tana da nakasu a halayya da dabi’a.
Nenne a zuciyarta sai ta koma addu’a tunda nasiha da tunasarwa bazasu yi ba, ta soma addu’a tana rokawa Taiwo gyaruwar hali da saukin kai da halin tawali’u, da daukar duniya da sauki.
Don haka Taiwo ko kai amare gidajensu ba ta je ba, ta wuce gidanta na Lagos ta bar Hakeem a Ilorin.

*** *** ***
An wuce kai amare Lagos Prince ya samu ya sulale ya wuce Gombe.
Don ya gama yarda daga Nenne har Dade babu mai saka hannu ya lallashi Siddiqa ta dawo. Balle su je masa biko har gaban iyayenta. Ga shi ta ajiye masa wayarsa barin ma ya samu damar communicating da ita.
Ya sauka a Gombe yamma lis, kuma dama tun kafin ya taso ya gaya wa Malam Buhari direban Nani Oummana tasowarsa, don haka yana sauka ya tarar da shi yana jiransa. Malam Buhari akwai wannan kokarin ga iyalin Oummana sabida yadda suma suke kyautata masa. Yasa baya gajiya da hidimar zirga-zirgarsu a duk lokacin da suka bukata.
Prince na da gida wani madaidaicin gida flat a mahaifar Nennensa wato Gombe daya dade da saya tuntuni a GRA.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login