Showing 6001 words to 9000 words out of 41738 words
Chapter 3 - Aishah-Saddiqa book 4 end complete by Takori Kabara .txt
yake ba, biyayya yake yi musu don a rabu lafiya da kafaffun iyayenmu da basa shawara, su Nenne ke faman cusa masa ita kamar dusa, kamar ance lafiyayyun mata ‘yan asali na manyan gida sun gama karewa a duniya.
Na rantse idona idonta a Lagos ko Ilorin in ta sake tazo, sai nayi mata wulakanci da kaskancin da bazata kara kuskuren zuro jiki cikin zuri’ar Akanni ba, balle ta wani kwashi siraran kafafunta tazo mana biki irin wannan na girma”.
A dakinta na baya wato dakin Kiki aka sauketa, kafin ta kwanta saida ta kira Ummanta ta gaya mata saukarsu lafiya a Lagos, sannan ta kira Hamma don tayi masa saida safe ta kuma bashi hakuri da kalamai, amma sai ta samu ya kashe dukka wayoyinsa.
Haka ta kwana da tunani da damuwar Hamma a ranta.
Washegari da safe ita da Nenne ne suka shirya abin karin Dade da Hamma, sai wajen karfe goma na safe Prince yazo gidan kuma a gurguje suka karya shida Dade zasu fita, bayan yabi Nenne dakinta sun gaisa, yanaso ya tambayi Aisha amma ya dake. Sai gata tana shigowa dakin Nennen dauke da lemun tuffah da sassanyar madarada tanbulan na tangaran akan karamin tray, ta gefensa ta wuce zuwa ciki, taci ado har ta gaji gabadaya ta saje da ‘yammatan amarya da suka cika gidan tun jiya.
Ta ajiye a gabansa, don tun safe take dakon shigowarsa duk ta damu, tace a ladabce “Hamma ina kwana?” Yayi mata wani kallo yace “lafiya kalau, yaya gajiyarki?” Nenne aka kirata a waya sai ta fita daga dakin tana amsa wayar.
Aisha bata yi aune ba taji Prince ya kamata ya mikar daga durkuson data yi a gabansa ya jata zuwa kusurwar dakin ya matseta sosai a jikinsa, sannan ya manne ta a kirjinsa da wata zazzafar hug, ya rage tsaho ya sumbaci lips dinta lightly, yace,
“Aisha jiya banyi barci ba isashshe saboda rashin ki a gadona Aisha, I missed you and your sweet lips, me yasa kika yimin hakane wai?”
Ya yi mata wani kallo na so da sha'awar da baisan yaushe ya fito daga idanunsa zuwa nata ba, saida Aisha taji tasirin kallonnan har spine dinta, tsigar jikinta saida ya tashi yarrr, Hamma ganin haka ya sake manne bakunansu wuri guda yana kissing lips dinta hungrily, wannan karon zazzafar kiss yake extending Wanda ya rikita Aisha bakidayanta. Duk da haka tunanin a inda suke ya hanata nutsuwa ta amshi sakonnin nasa. Aisha ta soma kokarin kwatar kanta tana fadin.
“Please don Allah Hamma ka bari, ka sakeni kada Nenne ta dawo. Dakin Nenne ne fa!”.
Hamma yace “I don’t care, ai gara ta gani ta san yadda kuka taru kuka kwareni jiya, I missed your warmth, shine jiya kika ce nan zaki zauna ko? Don kawai kinga ina shirin angwancewa? Wannan ai mugunta ne Aisha.
Hummm! Ni na manta ma I am pissed at you na tsaya Ina romancing dinki”. Aisha tayi wani murmushi kawai ta kalleshi “ni dai don Allah Hamma ka sakeni kunya nake ji” ya sake mata kiss a kasan wuyanta sannan ya saketa jin kamar motsi a bayansu. Ashe Firdausi ce ta shigo neman Aisha, ganin abinda ke faruwa tayi maza tayi excusing kanta da gaggawa ta juya tana murmushi.
Firdausi na fita Nenne ta dawo, sai Aisha ta gusa ta basu wuri. Har Hamma ya gama gaisawa da Nenne ya fita daga gidan, wanda ya soma dinkewa da baki musamman kawayen amarya dana Nenne, bai kara ganinta ba. Kuma a washegarin ranar first flight ya tashi dasu zuwa Ilorin, shida Dade, Nenne, Aisha da amaren domin su samu addu’ar arba’in kuma a dauro auren a fadar Ilorin.
Da hantsin ranar suka shiga Ilorin Emirate, Aisha tana like da Nenne duk inda tasa kafa nan take mayaswa. A yanayin kalar fatar jikinsu da kamanninsu na Fulani sai suka fita dabam a gidan, kamar ‘ya da uwarta. Wadanda basu san matar da aka aurawa Prince bama a gidan a ranar suka ganta, masu yabawa nayi haka masu gatsinen yarbawa na kankantar Aisha. Amma maganar rashin wayewa ya fara barin jikin Aisha ta yi fes da ita ta kara cikowa ta fara cika idanun mai kallonta. Prince yana can fada tareda Uncles dinsa do a ranar ne ake shawarar wanda za’a bawa sarauta a cikin ‘ya’yan Emir. Idris Akanni y ace a’ah, ko dama Emir ya dade yana gaya musu su cire Idris da dan sa daga sha’anin sarauta. Basu kara yarda da hakan ba sai yau da Dade ya fitittike yace bazai karba ba, baida ra’ayin sarauta ko kankani, don haka ya barwa kaninsa mai bi masa wato Abdulyaqeen Akanni wanda shine Turaki of Ilorin.
Da wannan aka bar zancen cewa washegari bayan addu’a arba’in din za’a zarce da bikin nadin sarautar da daurin aure.
Da farko a dakin da Nenne ta sauka Siddiqah take amma da Aunty Taiwo tashigo yiwa Nenne barka da zuwa, suka gaisa, ta tambayeta Hakeem tace yana fada, tana kallon Siddiqah a kaikaice, taga alamar a dakin Nenne take nufin zata sauka sai tace da Nenne cikin yarbanci da tayi tsammanin Siddiqah bata ji sam.
“Nenne keda surukar taki daki daya zakuyi sharing ne? Ai ba’a yin haka a gidannan, ta tashi ta koma cikin matan ‘ya’ya, haba Nenne don Allah ki dinga jan ajinki akan yarinyar nan”. Nenne tayi sakatoto tana duban ‘yarta Taiwo kafin ta samu abin cewa Aunty Taiwo tace da wata baiwa dake gefe ta dauko kayan Aisha ta kai dakin da ta sauka.
Jin tace a kai dakin da take yasa Nenne tayi shiru bata tanka ba, koba komai zata so a samu shakuwa da fahimta tsakanin Murjantu da Aisha, bata son yadda Taiwo ke treating matar kanin nata.
Taiwo tace Aisha ta biyo ta, kamar kada ta mike don ba tun yau ba jikinta ya gama bata Aunty Taiwo bata sonta ko kowa bai gaya mata ba. Amma jin Nenne bata ce a’ah ba, kuma Taiwo dinnan diyar Nenne ne da bata da maraba da Hamma, sannan Maman Kikinta sai kawai ta zari hand bag din ta da mayafinta tabi ta nata dakin.
Babban bedroom ne a wani sashe na cikin gidan sarautar, dakuna ne a jere wasu na fuskantar juna duk iri daya, yawanci matan Uncles din Abdulrasheed da matan ‘ya’yansu in suka zo sha’ani duk anan suke sauka, dakin da suka shiga da Aunty Taiwo ya ji kayan alatun rayuwa na gargajiyar sarauta dana zamani, ga iya kwandishin mai ni’ma nata aiki, akwai tafkeken gado da wardrove, Aunty Bola matar wani Cousin dinsu da Aunty Iyabo matar Turaki da Fatima da Firdausi ne a dakin suna hira lokacin da suka shiga dakin. Jikin Aisha a sanyaye matuka don yarbanci kawai kake ji yana tashi a gidan da sauran dakunan, koda suka shigo ma duk ta tsangwami kanta duk da Firdausi na tsokanarta da fulatanci tana cewa duk ta wani takure, tafi son koyaushe gta like da Nenne, tace ta saki jikinta nan duk iyayen Hamma ne sai su kannensa. Fatima ta Harari Firdausi tace da turanci don kowa yaji “in taga dama ta daure jikin don Allah, kinsan bata son shiga cikin yarbawa kada su cinyeta, ba abin raini a wurin yarinyar nan irin Bayerabe. I wonder yadda na jita shiru kamar an aiki bawa garinsu tun isarta gidan Hamma kuma”. Ifedayo ta zaro ido tace “kamar yaya bata son yarbawa? Ewoo! Bata son kabila ta auri dan su, dan ma babban jikan sarkin Ilorin da muke fatan ta zama uwa ga kowa namu watarana?”
Aunty Bola tace “ke ko Ifedayo! Ai ‘yammatan hausawa ba don so suke aure ba, kwadayin su ba inda baya kaisu. Balle taji sarauta zam, taji Prince na kasashen turai ai nan ‘yammatan hausawa dana fulani suka fi kauri. Sai an yi auren kiga ba soyayyar da zata dauwamar da farin ciki a cikinsa”.
Kamar an yiwa Aunty Taiwo kunni, ko kuwa allura akan gyambon ta, ta dubi Aisha ta kyabe baki, tace “ku bar ganin laifinta, iyayenta ne manyan kwadayayyu da basu san darajar kansu ba balle na abinda suka haifa, amma ba ita ba, tunda ita batama san shi ba ko kafin a auro ta, su da suka dauki wannnan teenager suka aurawa Kehinde wanda a haife ya haifeta sune suka fiddo kwadayinsu da zalamarsu fili, ta yaya zaka aurawa danka wanda baka ko taba gani a zahiri ko a hoto ba? Sai kawai don jin su waye iyayensa.
Wai daga haduwar kan hanya aka baiwa Nenne sadaqarta ta aurawa danta saboda an ga mamora a jikinta.
Ni tunda nake ban taba jin aure na rashin mutunci irin haka ba, ban taba ganin auren rashin sanin darajar Da irin naki ba, ai a al’adarku ana lefe, ana yiwa amarya kayan hana gori, amma ke ko lefen bana jin an yi miki, ke suturar da zaki saka ma a gidanmu mu muka yi miki, da tsummokara kikazo, ko wanka babu, aka bi aka asirce mana uwa, bata zance sai naki, amma ku duba kuga daga shan jar miyar Ewedu har ta fara washewa, ku kuke kayan daki amma ke haka aka daukoki zikau! Aka kawo mana.
Mun miki komai domin mu suturtaki, mai nuna sadaqarki suka baima Nenne ta likawa Kehinde ta karfi da yaji.
Kuma shi ba so yake ba, ya fada ya kara bashi da lokacin soyayyah, bazai taba son ki ba saboda ya dade da gama soyayya tun a kuruciyarsa, akwai wadda yayi shekara da shekaru yana so tun samartakarsa har girmansa bai aureta ba. kuma har gobe ita zuciyarsa ke so.
Ni nasan Kehinde wallahi, babu kuma wanda zai gaya min waye Kehinde, ko a kafa aka daura masa ke nan gaba kadan zai kwance ya yar.
Kawai kun ga arziki da sarauta kun nace, watakila ma kuna tunanin Kehinde zai yi sarauta ne, to in gaya miki gaskiya inma wanan kukewa keda iyayenki to kije ki gaya musu Kehinde bazai yi ba.
Da aka aura masa ke aka kawoki guidanmu saida ya jingineki kusan shekara guda, saida su Nenne suka gaji da ajiyarki a daki ne suka tattara ki suka danna masa ganin wankin hula zai kaisu dare.
Da zuwanki gidansa na fahimci kun soma juya masa kai, iyayenki nata surkulle ga dukkan alamu, har wani dora ki yayi a status baya ko jin faduwa a ganshi dake a matsayin mata.
Nayi rantsuwa ni Taiwo abokiyar tagwaitakarsa, inma asirinku ne ya fara cinsa ko zan daina barci sai na warwareshi da karfin addu’a, in asiri kuke shiga jeji kuna jefa masa mu addu’a muke kwana yi, yadda kuka ganshi haka zaku kyaleshi. Kakan kakanmu Shehu Alimi, ya dade da tofe zuri’ar shi da kul’aquzai, daga duk wani sharri na masu nufin Kehinde da wani surkulle na magauta da irinku makwadaita”.
Duk maganar nan Taiwo na yinta ne cikin sassaukan turanci da fulatanci ziryan, don ma Aisha ta fahimta sosai.
Siddiqah dai tana zaune banda kallon bakin Taiwo ba abinda take yi. Kirjinta yana harbawa zuciyarta na matsewa. Fuskarta na rinewa daga yellow zuwa jazir.
Saida Aunty Taiwo ta gama cin mutuncinta tas, su kansu su Fatima da Firdausi wadannan maganganu na Yayarsu Taiwo sun san firgitasu domin sunji sun yi zafi da tsauri sosai. Firdausi jikinta rawa ya fara yi ta soma cewa “haba-haba Aunty Taiwo? Haba ke kuwa don Allah Maman Kiki? Wannanba girmanki bane”. Ganin yanayin da Aisha ta shiga ya firgitasu. Babu ko digon hawaye a fuskarta amma tsigar jikinta duk ta tashi yarr, tsokar fatar bakin ta har raurawa takeyi amma ba kuka ba.
Taiwo zata wuce toilet ta bar su a wurin suka ga gabadaya jikin Aisha ya dauki kyarma, idon nan ya koma kamar garwashin wuta ya kada yayi jazur… Ga dukkan mamakinsu Aisha ta mike da hanzari ta sha gaban Aunty Taiwo dake neman wucewa toilet wato ta gama zagin banza, ta sha lafiya zata wuce harkokin gabanta.
Aisha ta tsaya gaban Aunty Taiwo, gabadaya ta koma Aisha-Siddiqarta fitinanniya, masifaffiya, ta Billiri ikon Allah! Gang leader mara tsoron kowa, sannan mara kara wato mai keke - da kekenta da kowa ya sani, ta kalli Aunty Taiwo cikin ido ta soma magana cikin sarkewar numfashi.
“Na rantse yau kinci albarkacin haihuwa, kin ci albarkacin Kiki a wajeana, kinci albarkacin dimbin qaunar da ‘yar ki ta nuna min.Sannan kinci albarkacin girma da shekaru.
Sannan kinci albarkacin Nenne, mafi girma kuma kinci albarkacin tarbiyar da iyaye na suka bani akan wanda ya girmeni!!!
Kinci zarafin dattako da tarbiya da kamalar da Nenne take dashi kuma ta baku ku ‘ya’yanta, kin ci amanar tarbiyyar data baki!!!
Aunty Taiwo ta saki baki galala! Tana kallon yarinya karama haka kamar diyarta Kiki, ta tsaya a gabanta tana maida mata da martani, yarinyar da bata wuce second born dinta Kiki ba, duka mutanen dakin ma su Ifedayo da Aunty Bola sun sha mamaki domin basu zaci zata iya tankawa Taiwo ba sam, da yake cikin turanci take maida mata martanin duk suna ji, kallonta suke, shock duk ya kamasu.
Firdausi ta soma bata hakuri daman tunda Taiwo ta fara zuba rashin mutuncin Firdausi tana ta cewa “haba aunty Taiwo, ki bari bai kamata ba” Taiwo ta ce mata “shut up malama! Kada ki kara saka min baki in ina magana”.
Ganin haka gudun kada akai ga duka sai Princess Firdausi ta dauki wayarta jikinta nata kyarma ta yiwa Hamma text, tace maza ya bar duk abinda yake yi yazo don Allah ga Aunty Taiwo na cin mutuncin Aisha tana neman wulakantata a gaban dangi”.
A take Hamma ya kira Firdausi immediately, ai kuwa Firdausi ta saka masa a handsfree, yana iya jin muryar Taiwo na karasa wassafa ma Aisha… “ki dake ni mana ‘yar Mallam Shehu! Shine zan san kinyi fushi na zagi makwadaitan iyayenki da suka yi miki auren sadaqah.
An zagi iyayen naki, wata tsiya ne su? Ko zaki rama eh? Ke a karan kanki da dan hankalinki kinga dacewar ki auri Kehinde?
Banda kankanba irin ta talakawa da kai kai inda Allah bai kai ka ba, ina ke ina zuri’ar Akanni?
Ai da kin tafi kin auri mai kora shanu a kauye shine daidai ke…. Amma ba dan Sarki babban jikan Sarki ba…”.
Hamma be kashe wayar ba a haka ya karaso hankalin sa a matukar tashe. Aisha ta wuce ta gaban Taiwo a zuciye, ko ganin gabanta bata yi. Wani irin tafasa zuciyarta keyi. Babu kuka ko digo a idonta zuciyarta ta bushe. Bata so ta kara wata kalma bayan wannan don zuciyarta na iya bugawa a lokacin.
Firdausi ta kula da hakan ta taso ta biyo bayanta da sauri tana Siddiqah tsaya don Allah…. ko jinta batayi ba ta bude kofa, sai karaf! Tayi karo da mutum tsaye a bakin kofar.
Data daga kai ta kalle shi da idanunta kamar gauta sai ta kawar da kai, ta sake juyowa tana kallon Taiwo data biyo bayanta…. ganin Kehinde yasa Taiwo tsayawa standstill. Wani irin bayyanannen bacın rai ne a fuskar sa, zata iya rantsewa tunda take da shi bata ta a ganin wannan yanayin a tare dashi ba.
Ya bude baki zai yi magana sai jin Aisha yayi ta juya tana cewa da Auty Taiwo….
“Kuma kamar yadda kike ta tutiya kan cewa baya sona, haka zalika nima baya cikin lissafina balle na irin mazan da nake so, ki tambayeshi kiji biyayya duk mukayiwa iyayen mu, saboda sun isa da mu. Daga yau na bar miki shi. Gashinan ki jika shi ki shanye….”.
Tana gama fadin hakan ta wuce ta bar musu dakin, ga dukkan mamakin Taiwo sai taga Prince ya bi bayanta yana “Aishah Please wait…Don Allah tsaya…” ko kallonsa Aisha bata yi ba ta kara sauri, ta kara da gudu-gudu, shima ya daga kafa ya bita yana “please listen to me Aisha….”. Yayi sa’ar riko gefen gyalenta, Aisha ta juyo a fusace tace “cikani, daga yau na gama wannan auren”.
A lokacin sun kawo kofar dakin data baro Nenne. Kalaman Aisha na karshe a kunnen Nenne suka sauka, inda tace.
“na gama auren nan, na barwa Aunty Taiwo dan uwanta Kehinde ta jika ta sha, har abada baa auren!”
Da sauri Nenne ta taso suka game ita dasu a bakin kofar, ganin yanayin da Aisha ke ciki da rudewar dake fuskar Hamma saida gaban Nenne ya fadi.
Ta kama hannun Aisha suka shiga cikin dakin Prince da hanzari ya rufa musu baya.
Nenne na jin irin numfarfashi da ajiyar zuciyar da Siddiqah ke sassaukewa a jejjere, ta durkushe a gabanta, ta hada hannayenta wuri guda cikin roko tace.