Showing 21001 words to 24000 words out of 74305 words
na ke faɗi, kina da sanya hannu zundum cikin abin da a kayi min sannan kuma ke ce silar faruwar komai, dan haka you have stopped acting like a good to everyone bcoz nasan komai yanzu kin bani mamaki ina kallon ki da daraja da mutumci ashe .....
Ya isa! Na ce ya isa Dr Aliyu ka fara wuce gona da iri, ka gyara kalaman ka, kasan me ka ke faɗi ya zaka dunga ɗunkule zance kana jifata da munanan kalamai akan wane dalili?.
"A kan alaƙar da ke sakanin ki da Dr Mahmoud daman can kuna mummunar alaƙa ki ke nuna min bakya yi baki ma son shiga sabgarshi ashe ba gaskiyar bane to ki sani na san koma nasan asalin fuskar ki, dan haka ba za ki ci gaba da raina min hankali ba sbd nasan ke fasuƙa........
Saukan lafiyayyen mari ya ji kan fuskar shi sai da shatin zarazaran yatsun ta suka kwanta kan fuskar shi cikin ɓacin rai ta nuna shi da yatsa
Dr Aliyu mind your tongue, ka wuce gona da iri amman ka bani, na yi tunanin in da wani ne ya faɗi hakan a kaina you are the first person da zaka kareni shine yau ka buɗe baki har ka ke kirana da ƙazamin suna, lallai ɗan Adam na iya ƙanzawa i won't prove my self but abin da na sani shine you'll regret and be shame at the last.
Tana kaiwa nan ta fice cikin ɓacin rai ta nufo bangaren su kai tsaye ta wuce office nata ta shige tare da dukan teburin dake gabanta tana huce, ansha yi mata irin haka amma kuma jin hakan daga bakin Dr Aliyu ya dameta sai ta ji tana so yasan gaskiyan lamarin ya zama dole ta nemo hanyar da za ta yi exposing halin Dr Mahmoud da MD ta yadda zata kawar da zargi da shakka da kuma kokonton da Dr Aliyu ke yi akanta kuma ta sa a dawo dashi wannan bangaren, ta jima tana sake² cikin ranta sannan ta wuce general ward ta ci gaba da kula da patients nata, sai kusan to 1:00am ta dawo office ta ɗan kwanta sai bacci ya ɗauke ta. Da asubah ta farka ta hau shirya kayanta bayan ta idar da sallah sannan ta fito ta ɗau hanyar gida, ta shigo gidan shuru babu motsin kowa ta nufi ƙofar ɗakinta jin miryar Ammie ta yi ta kira sunanta
"Hamrah"
A hankali ta juyi, cikin sanyin murya ta ce
Barka da safiya Ammie ya ƙarfin jikin?.
"Hamrah da na buɗe ido na ganki nake jin bakin ciki da takaici bani da damuwa a duk fadin duniyar nan irin na ki, bana iya bacci bana iya cin abinci cikin kwanciyar hankali in na tuna kin ɗabi shekaru a gabana babu aure shin ki sanar dani da akwai abin da ki ke aikatawa ne da ya sanya baki son aure na sani na kuma san irin matakin da zan ɗauka ko kuma kawai so ki ke na mutu da bakin cikin ki"
Kanta a kasa tana kwalla tana jin zuciyar ta na yi mata zafi, to in dai mahaifiyar ta bata yarda da ita ba kuma ba zata iya shaidan ta ba kenan duk wanda ya yi mata hakan bai kamata ta ji babu daɗi a hankali ta furta
Ki yi hakuri.
"Hakuri a cikin shi nake kawai na fahimci ni ɗin ce baki son farin ciki na kin fi son ayi ta zance na cikin dangi da ƴan unguwar ace na ajiye ki naƙi aurer da ke kina duk abinda da ki ka ga dama, to ki sani ina gab da ɗaukan hukunci akan ki ko ni ba bar miki gidan ko ke ki bar min gidan sai ki je in da zaki ji daɗin ci gaba da abin da ki ka ga dama"
Jikin Hamrah ya soma rawa ta ɗago tana kallon Ammie anya waɗannan maganganun daga bakin Ammie suke fitowa, meyasa Ammie ke faɗin haka da tana da yadda za tayi da ko ta yi ko dan ganin farin cikin ta, meyasa Ammie ta tsaneta sosai ne, anya kuwa ba wani abin da bata sani ba ......
"Na faɗa miki har yanzu ina kan bakata zuwa ƙarshen wannan watan komai zaizo ƙarshe"
Ta juyo ta fice, da ƙyar Hamrah ta iya ɗaukar kafarta ta shigo ɗakinta, ta zaune daka ƙasan bed ta saki wani maraitaccen kuka wanda da ƙyar ta ke iya yin shi cikin tashin hankali a wajen aiki babu sauki a gida ma kuma babu sauki ina zata sanya ranta taji sanyi me, shasheƙar kuka take yi da tana ajiyar zuciya.......
"A'a Hamrah Please stop crying, kuka zai haifar miki da matsala....
Ture shi ta yi ta juya mashi baya tana ci gaba da kuka, hankalin Ammar ya matukar tashi ganin ta cikin wannan yanayin ya sake matsowa kusa da ita cikin muryar rarrashi ya ce
"Ki yi hakuri Hamrah, kada hakan ya dameki ni na yarda dake kuma ko da duk duniya zasu juya miki baya ni ba zan yi ba, ke mutuniyar kirki ce Ammie na gulma da segumin mutane ne ya yi mata tasiri, amma itama a hankali zata daina, kin ji I'm with you"
Sauke numfashi ta ɗago tana kallon shi duk ya tashi hankalin shi jikin shi har rawa yake idanuwan shi sunyi ja, ta ƙirƙiro murmushin dole ta ce
Ba kukan abin da Ammie ta faɗa ba nake kaina ke min ciwo.
Ajiyar zuciya ya sauke ai ko mahaukaci ne yaga abin da ya faru zai fahimci komai balle kuma shi da ya ke da cikakken hankali, ya ce
"To na ji, faɗamin me ki ke son ci?"
Duk abin da akwai.
"To ina zuwa"
Ya tashi ya fice, bai jima ba ya shigo ɗauke da trey ya ajiye a gaban ta ya haɗa mata tea ya miƙa mata ta soma ƙurɓa a hankali ya buɗe pepper soup na jan nama ya ɗeba mata cikin plate ya miƙa mata ta ƙarɓa ta soma sha, ta ya kura mata idanuwa a hankali tace
Kai fa ba zaka sha bane?.
Ya sauke numfashi a hankali ya ce
Zanje na watsa ruwa sai na nayi breakfast sannan na tafi office na Daddy.
Okay, thanks.
Ya miƙe ya fice, ta kammala ta buɗe drower ta ɗauko da emzor ta haɗiye sannan ta kwanta bacci ta jima tana bacci sannan ta farka, ta watsa ruwa ta ƙarashe shan raguwar pepe soup ɗin ta ji ana kiran sallah azahar ta shige toilet ta ɗauro alwala ta fito ta idar kenan ta ji sallamar Shatu ta ɗago ta kalleta Shatu ta ce
"Ba dai kin mance fitan da zamu yi ba?"
Sauke numfashi Hamrah ta yi ta ce
Na manta fa amma a shirye nake zamu iya tafiya.
Daman ta gaji da kwanciyar suka fito ta shige ɗakin Ammie ta shaida mata zata siyayya bata ce da ita komai ba ta fice jiki a sanyaye, a daidai layin unguwar su suka tadda ɗan sahu, suka hau ya kai su GUMALTI nan suka kammala shopping sun fito da lader niƙi² a hannu sai suka ji ance
"Hamrah"
A lokaci guda suka juyo cike da mamaki Hamrah ke binshi da kallo mutumin nan ne da ya taɓa tambayar ta a layin unguwar su, cikin sakin fuska ta ce
Barka da yamma ci.
"Yauwa barka dai ranki shidaɗe da fatan dai baki bance fuska ta ba?"
Murmushi ta yi amma bata mance fuskar ma sai dai sunan shi da ba zata iya tunawa ba....
"Alhaji Sama'ila"
Murmushi tayi, Shatu ta ce
"Bari na nemi ɗan sahu kamin nan sai ku gaisa"
"Sannun ki"
Ya ce da Shatu.
Ta amsa da
"Yauwa sannunka kaima"
Ya yi murmushi ya ce
Ba sai kin nemi ɗan sahu ba nima arean ku zan bi sai nayi dropping na ku ko"
A'a ba komai Alhaji zamu ƙarasa ai.
Cewar Hamrah, amma ya dage sai da yasa drivern shi ya shigar musu da kayayyakin su sannan ya buɗewa Hamrah gidan baya, ta juya ta kalli Shatu ta yi mata alamun ki shiga, sannan ta shiga itama Shatu ta shiga ta zauna a mazaunin gaba ita da driver, Hamrah da Alhaji Sama'ila a bayan mota suka ɗau hanyar dawowa gida.
Comments and share
*MUJARRABI*
By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA
09021706569
PG 17 & 18
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_________ Ajiyar zuciya ya sauke da ƙarfi, idanuwan shi sun sauya kala, duk duniya ya tsani ganin yayar shi cikin tashin hankali ko cikin damuwa baya son ganin ɓacin rainta, shiyasa ya ɗau wa kanshi alkawarin samo mata farin ciki, ita ma taji daɗin rayuwa kamar yadda kowa keyi ta daina zubda ƙwalla, shi dai kawai hankalin shi bai kwanta da wannan mutumin ba, amma zai yi zurfi bincike akanshi, a hankali ya ɗago yana kallon ta ganin duk hankalin ta a tashe ya ce
"I'm sorry"
Ta sauke numfashi jikin ta ya yi sanyi ganin lokaci guda kuma ya dawo cikin hayyacin sa ta ce
Bana so, kada ka sake yi min haka, sannan ko ba komai shi babban mutum ne ya kamata ka girmama shi.
"Ina yin hakanne don farin cikin ki, bana so ki aure shi dan farin cikin Ammie na fi son ki yi aure cikin so da kuma ƙauna"
Ta sauke numfashi, na ji kuma na gode amma kasani dan kaina zan yi ba dan Ammie ba, dan haka ka maida hankali ga shirye shiryen tafiyan ka.
Ya sauke numfashi ya ce
"To shikenan"
Ta fice ta fito compound na gidan ta tadda Alhaji Sama'ila har ya shige cikin mota, ta iso ya buɗe mata ta ciki ta shiga, a hankali ya tada motar sbd shi kaɗai yazo, shuru ya ratsa har suka fito daga layin unguwar su, mamaki ta ke irin na mujiyar da ƴan layinsu suka zubawa motar har suka ɓace. Sauke numfashi Alheri Sama'ila ya yi tare da cewa
"A wacce Hospital ki ke aiki?"
AL'UMMA SPECIALIST HOSPITAL.
"Ok, kin san ba wani sanin kan garin na yi ba, sai kin taimakamin da kwatance"
Suna tafe tana nuna mishi hanyar da zai bi, har suka iso nan ya sauke ta cikin girmamawa ta mai godiya ta shige ciki. Office ta sanyawa key ta buɗe ta shige a nutse ta shirya komanta kamar yadda ta saba. Turo ƙofar Dr Mahmoud ya yi ya shigo tare da sallama, ta amsa ya zauna tare da cewa
"Yau kam kin makara, in ce dai lafiya?"
Alhamdulillah.
Kawai ta ce, ta ɗauko white eyes glass nata ta saka tare da buɗe system nata tana duddubawa, ya yi murmushi ya ce
"Can we be friends?"
Ɗagowa tayi ta kalle shi tare da girgiza kanta ta ce
Friend's, how was that be possible, ni fa mace ce kai kuma na miji ta ya ya za muyi abota.
Ya yi murmushi ya ce
"Ana yi ai, shi ya fi komai sauki"
Uhmm, ni bana yi.
Ya yi murmushi ya fice sbd ƙiran sallah da ake yi. Ta sauke numfashi ta miƙe ta shige toilet ta ɗauro alwala ta idar sannan ta fito ta wuce general ward, ta jima a cen sannan ta dawo. Tana zaune ita kaɗai ta ji wayar ta na ringing ta duba Abuja ne suka gaisa nan suka taɓa fira sannan sukayi sallama. Sai ƙiran OG ya shigo ta ɗauka cikin girmamawa ta ce
Barka da hutawa OG.
"Yauwa barka dai Dr Hamrah, ya ƙoƙari?"
Alhamdulillah.
Yauwa haɗamin file ɗin da ki ke haɗamin da sauran document ɗin zan shigo on Monday around 10:00am akwai abubuwan da zan yi"
In shaa Allahu, zan haɗa su OG Allah ya nuna mana jibin.
"Good, ameen"
Su kayi sallama.
Ta miƙe ta fara haɗa su, daman haka ta keyi duk record yana office nata, shiyasa ido yake kanta, kuma akwai sirri a sskaninta da OG shiyasa yake ɗaura ta kan ragamar komai, bata da yawan magana, kuma bata wasa da aikinta, ta kammala haɗasu ta ajiye su cikin loker ta sanya key, sannan ta kwanta. WASHEGARI a nutse ta haɗa kayanta ta fito babu mutane da yawa sbd Sunday ne yawan ci ƴan visiting ne a farfajiyar Hospital ɗin ta fito ta tari ɗan sahu ta dawo gida, a filin gida ta tadda Daddyn su ta iso gareshi, cikin girmamawa ta duka ƙasa ta gaida shi
Barka da safiya Daddy
Ya ɗago daga danna wayar shi da ya keyi da alama sako yake son turawa ya ce
"Likita barka dai, kin dawo?"
Eh Daddy na dawo.
"To madalla a huta gajiya"
Na gode Daddy.
"Yauwa likita Ammie ta faɗa min da akwai wanda yazo jiya kuma yana son ya turo magabatan shi, to anjima da daddare ki sameni sai mu yi magana"
Jikin Hamrah ya yi sanyi, anya Ammie bata yi saurin sanar da Daddy ba, da ta bari sun ɗan fahimci juna dashi, amma daga zuwan farko. Ta sauke numfashi tare da cewa
To Daddy Allah ya kai mu.
"Ameen"
Ta miƙe ta shigo ta wuce side na Ammie ta taddata kwance nan ta gaidata ta amsa
"Lafiya"
Har zata miƙe kuma ta ji muryar ta
"Nayi magana da Daddyn ku ya ce za ki iya ce masa ya turo magabatan shi"
To.
Shine abin da ta ce sannan ta fito ta tadda Ammar yana shirin fitowa cikin sanyin jiki ya kalleta tare da cewa
"Kin dawo?"
Eh na dawo, fita za kayi?"
"Uhm magana Daddy ke son yi dani akan tafiyar mu, an matso dashi nan da satin sama zamu tafi"
Ta ɗan yi murmushi ganin yana magana yana kallon gefe ta ce
Ina so zamu yi magana anjima ni da kai.
Ya sauke numfashi tare da cewa
To.
Ya fice ta dawo ɗakinta duk jikinta a mace ta watsa ruwa ta sanya riga da wondo na material sannan ta hau kan bed nata ta kwanta, bata jima ba bacci ya ɗauke ta, ta jima tana bacci ta ji alamun an taɓata buɗe idanuwan da tayi ne ta sauke su kan namecynta ta sakar mata da murmushi tare da miƙa mata hannu, ta riƙe ta janyota kan bed suka kwanta, Little Hamrah ta ce
"Good morning"
Hamrah ta shafa kanta tare da cewa
Morning cutie, da Mom ki kazo?.
Ta gyaɗa kai alamun eh.
Suka ji sallaman su Nazeer suka shigo suna gaidata ta amsa musu nan ta hau raba musu choculate daman bata rabuwa dashi, suna murna suka fita itama ta fito ta dawo ɗakin da suke sauka, tana shiga ko duk suna nan, ta zauna Maryama na ganin ta shigo ta fice Zeenat ce ta ce
"Yaya Hamrah duk da ina fushi dake amma bazan ƙi gaida ki ba, ina kwana"
Murmushi Hamrah ta yi ta ce
Amin afuwa duk da bansan laifin da na yi ba, lafiya ta kalau.
"Kin ƙini baƙi ɗaya, ko ƙira ballantana ziyara gani da tsohon ciki ƙafata ɗaya a duniya ɗaya a lahira"
Oh sorry Zeenatu na, kin san Allah kina raina tun last week na ke son biya ta gidan ki amma Allah bai nufah ba, ya kuke ina uwar gidan ki?.
"Ni dai bazan hakura ba har sai kin je min, uwar gida tana nan fah, sai abin da ya ƙaru a halinta yau ma nazo ki bani shawara"
Hamrah ta sauke numfashi tare da cewa
Ikon Allah, ita bata sanin ta girma, to Allah shi kyauta.
Ameen.
Ayshe ta ce
"Zeenat ki yi wa Yaya Hamrah uzuri ko dan irin aikin ta, Yaya Hamrah barka da safiya?. Bata ma bari mun gaisa ba"
Lafiya ta lau uwar gida, ya shirye shirye?.
"Alhamdulillah suna yi, dan ni ko kallo basu isheni ba"
Hamrah ta yi murmushi kishi ya motsa ta ce
Kuna yi dai ba suna yi ba.
"Uhm ke dai bari ashe haka ake ji in za ayi wa mutum kishiya kai abin sai an daure, fisabilillahi duk yadda muke da ƴan uwan shi amma suka juya min baya suka koma gindin Amaryar tun basu shigo ba"
Ayshe ki nutsu ki kwantar da hankalin duk wannan ɗokin na wani lokaci ne amma da kansu zasu dawo gare ki.
"Kai ki bari a wannan satin kam sai na durza bakin ƙanwarshe fiddausi"
Ayshe har yanzu hakuri zan baki, ina nan ina kan shiri nan da kwana biyu zan je na zauna miki in ba danna ƙirji nayi miki ba abin ba zayyi kyau ba.
Zeenat ta ce
"Gaskiya kin kyauta ki je cen ɗin yanzu ma da na biya ta gidan ta ƙadan ta mari Yayar shi, muna zaune ta shigo wai ko anƙi ko anso sai ankawo Amaryar mubi duk bokan da muka daman bi, tamu ba ta Allah ba"
Uhm gwada da baku tanka musu ba, ina yaran ne?.
Ayshe ta sauke numfashi tare da cewa
"Sunbi Yaya Ammar zuwa waje, ni fah nazo da Abinci ko ci ban nutsu nayi ba muje ɗakin ki Yaya Hamrah mu ci na kwanta ko naji sanyi"
A tare suka fito zuwa ɗakin Hamrah, suna shiga suka mimmiƙe Hamrah ta fito zuwa kitchen anan aka ajiye abincin, ta tadda Maryama tana zuba abinci Hamrah ta soma zuba nasu a babban trey jollof rice ne wacce ta ji kayan spices, sai dandarun jan nama, ganin irin rainin dake kan Maryama yasa ta ce
Maryama, kina bani mamaki ta yadda rayuwar duniya ke rud'an ki, wannan halin da kika ɗaurawa kanki wallahi babu inda zai kai ki, bansan meyake sanya ki fuzgar kai ba, amma ina mai baki shawara ki bi duniya a sannu.
Turo baki da kuma ɗaga hanci tayi ta ce
"Ai kinfi kowa sanin dalilin da yasa nake haka in kema baki sauya daga ƙiyayyar da ki ke nunawa habibina nima bazan daina abin da na keyi ba, kin nuna banbanci sakanina da Zeenat bacci ni dake mun fi kusanci....
Ya isa, Maryama kada kiga ina biye miki ki ɗauka tsoron ki nake ji, a'a tausayi ki ke bani sbd kin ɗauki dala ba gamo ne, shi Alay Shatteema ne ya ce dake bana son shi ko kuma ke ce ki ke ganin hakan? To ki sani shi rashin mutunci riga ce kowa ma yana iya arota ya sanya ta kuma ya yi, amma kuma ganin rigar ba mai kyau bace shiyasa ake gudun sanya ta, amma in ba haka ba Maryama kin yi kaɗan kimin na ɗauka.
"Ai ko shi Alay Shatteema bai faɗa ba ni ai kin min na gani, kina ɗaya daga cikin waɗanda basu son aurena dashi ko kin manta ne da abin da ya faru a wancan lokacin, sannan haka still ya sake faruwa a ranar sunan Waleed, dan haka duk wanda ya ce baya son mijina to nima bazan yi dashi ba"
Murmushi Hamrah ta yi su sai ta ce
Au sai yanzu na fahimta wato dai kin fi son mijin ki da danginki to ya yi amma ki sani