Showing 63001 words to 66000 words out of 74305 words

Chapter 22 - MUJARRABI BOOK ONE BY SAYYADA BARRISTER.txt

18 Jan 2025

4617

ta shiga ciki ta jima a cikin sai da taji ta ɗan dama² sannan ta ɗaura alwala ta fito ta sanya kayanta na lace da ke jikinta jiya ta yafa mayafin ta gabatar da sallah. Ma'aikaciyar ta fice dan haka tana sallame wa ta dawo kan bed ɗin ta zauna ganin message ya shigo ne ta duba kuɗi ne daga Alhaji Sama'ila Naira miliyan 10, sai da ta sake dubawa da kyau ta kula ashe tun safe ya tura mata. Tayi saurin kiran layinshi kuma a kashe, ta sauke numfashi ta kira number Ayshe kira na farko ta ɗauka tare da cewa


"Amarya ran gida tun jiya nake ta kewar ki aure ya rabamu, amma meyasa ake ta kiran number ki baki ɗaukawa duk hankalin mu ya tashi musamman ma Daddy tun jiya ya kasa cin abinci, haka ma yaya Ammar"


Sauke numfashi hamrah tayi ta haɗiye abu mai zafi cikin ranta tare da haɗiye kukanta ta ce


Ayshe bacci ne ya kwashe mu, bayan na farka kuma na koma sai yanzu na tashi, ina Ammie?"


Dariya Ayshe tayi ta ce


"Madallah yaya Hamrah kin shiga system ɗin, ai daga yanzu ko zaki fara rama bacci. Ammie tana nan, tun safe duk ta damu ƴan rakiyar ki sun shirya amma kuma shuru ba a ji komai daga gareku ba"


Daram ƙirjinta ya buga, wai tashin hankali yanzu ya za tayi kuma ta san dole sai ƴan rakiyar nan sun rakata hasbunallahu wa ni'imal waƙil, Allah yakawu mata mafita shine abin da take faɗi cikin ranta, a hankali ta ce


Ki hau online muyi video call.


"To yaya Hamrah yanzu ma ko"


Dukkanin su suka hau online Hamrah sosai ta ɓoye damuwarta ta kirkiro murmushi amma ana iya hango damuwa ƙarara kan fuskar da dakuma idanuwanta, cewa Ayshe tayi ta dinga yawo da wayar tana son ganin mutan gida, Ayshe ko ta dinga yawo dashi gida ko cike yake maƙil da mutane, sai kaiwa da komowa suke, wasu a zaune wasu kuma a kwance ana ta fira ana raha ta iso inda Ammie take tana tsaye tana haɗa kayan Hamrah wanda za a tafi dasu ta mota katse video call ɗin tayi ta fashe da kuka, sosai taci kuka jin ringing da wayarta keyi ne yasa ta share hawayenta ta ɗauka ganin sunan Zeenat ta kara a kunne tare da sallama Zeenat ta amsa ta ce


"Yaya Hamrah barka da rana, yanzu Ayshe ke sanar dani kunyi waya na ce bari na kiraki mu gaisa"


Da ƙyar Hamrah ta ita iya yin magana


Eh hakane inna shirin kiranki ma kika kira ya gajiyanku?.


"Sai godiya, amma ya kamar kina kuka?"


Uhm a'a Zeenat ba kuka nake yi ba.


"Kai yaya Hamrah gashi naji har muryarki ta dishe, kada ki damu kaɗaici ne ke damunki kuma zai wuce kewace muma duk munyi irinta kina kaiwa sati ɗaya za ki saba da rashinmu"


Haka ne Zeenat thank you.


"Yauwa ga Ammie nan ku gaisa tana ma son magana dake"


Ta sauke numfashi ta ce


To ki bata.


Ta mikawa Ammie cikin masifa Ammie ta ce


"Haba Hamrah abin da ki kayi bai dace ba yaya za ku shanya mutane tun safe suna jiran ku a ɗau hanya amma sai ku sharesu haka ake yi ne, wallahi banji daɗin hakan ba, yanzu ya za ayi ne goben ne tafiya tun da yau an ɗaga ko kuma kun tafi ne?"


Wani kuka ne ya zuwa Hamrah kamar ta ɗaura hannu a kai ta saka ihu amma ta jure ta danne ta ce


"Ammie ya gajiya eh tafiyan sai gobe in Allah ya kaimu da man sunyi magana da wasu ne akan ɗiban kayayyakin to ban san ya abin zai kasance ba, bari muga goben.


"To ki kira ki sanar dani da wuri dan ko da ƙyar na tsaida babanninki wai zasu tafi, to in kinga tafiya ba ta gobe bace sai su tafi kada mu ɓata musu lokaci ba"


To Ammie.


Shine abin da Hamrah ta iya furtawa. Ammie ta kashe wayar nan Hamrah ta rushe da kuka kamar ranta zai fita ta soma furta kalmar


Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Ya Allah ka kawo min ɗauki Allah na tuba ka yafe mini, Allah ina cikin tashin hankali na rasa mafita Ubangiji kai dayane zaka taimakeni Allah ka dubi lamurana ka rufa min asiri ka taimaka min taimako ka kaɗai nake nema.


Sosai take kuka, har lokacin da Hadiza Aliyu ma'aikaciyar hotel ɗin ta shigo ta taddata tare da Manager suka shigo, nan ta dinga rarrashinta tare da ban baki da ƙyar Hamrah tayi shiru sannan manager yayi magana


"Ba abin da zan iya cewa akan wannan abin da ya faru ya riga da ya faru sai dai na baki hakuri, ki ɗauki hakan a matsayin kaddararki Allah shine MUJARRABI yana jarabtan bawansa ta ko wacce siga musamman irin sigar da bawan ke yaƙi da ita yaga ko in abin ya samesa zai jure ne kamar yadda yake son wasu su jure to ban sani ba ko kina ɗaya daga cikin su. Yanzu dai duba da halin da ki ke ciki yasa na dauke miki kwana ɗaya zuwa biyu a nan dakin sbd wanda yake da niyyar kamawan ma na sauya masa da wani dan haka zaki iya zama nan da zuwa jibi in kin sami lafiya da kuma nutsuwa sai ki koma gida ki sanar dasu halin da ki ke ciki"


Hamrah dai kanta a ƙasa ta rasa bakin magana sai zubda ƙwalla take tabbas maganar wannan manager abin dubawa ne tayu sbd da tana wayar da kan wasu akan kada su kaucewa tsarin musulunci su jure wa duk wani halin da suka sinci kansu a ciki shine Ubangiji ya jarrabe ta yaga ko ya ita za tayi a hankali ta furta


Astagfirullah.


Manager da Hadiza Aliyu ma'aikaciyar hotel ɗin suka fita basu jima da fita ba ta shigowa Hamra da abin da zata sanya a cikin ta, ta ajiye wa Hamrah ganin ko kallon abinci batayi ba yasa ta haɗa mata tea mai kauri ta bata tasha, kaɗan ta sha ta ajiye ta kwanta. Har dare tana kwance ta rasa mafita tayi tunanin duniyar nan ta rasa mafita ta rasa wanda zata kira suyi shawara ya taimaka mata cen sai wata zuciyar ta ce AMMAR nan ko sai hankalinta ya kwanta da ta tuna dashi a hankali ta ɗauki wayar kira ɗaya ya ɗauka tare da cewa


"Ni har nayi fushi dan kinyi aure shine har kika manta dani na kira baki ɗauka ba na ce to su amarsu"


Uhm Ammar, ai ban isa na manta da kai ba, bana jin daɗin jikina ne yasa na kasa amsar wayar.


"Subhanallahi, meke damunki, ya naji muryar ki haka ince dai lafiya?"


A hankali ta ce


Zan tura maka address na hotel ɗin da nake Please be hurry ina jiranka.


"Hamrah is something wrong, are you alright?"


Uhm just come now Ammar.


Ta kashe wayar. Ta tura masa address na hotel ɗin da take ta kuma faɗa masa room number da kuma sunan wacce zai je wajenta Hadiza Aliyu tayi masa jagora zuwa inda take. Ta miƙe ta daura alwala ta idar da sallah ishai tana kan dardumar sallah taji turowar kofar ta shafa addu'ar da take yi ta juyo ta kalli bakin kofar Ammar ta gani a tsaye yana karewa ɗakin kallo idanuwansa suka sauka kan roban drip ɗin dake bedside da kuma tulin magungunan dake wajen, ya sake juyowa ya kalleta cikin sanyin jiki ya ƙaraso inda take kallo ɗaya yayi mata ya fahimci akwai matsala ya rage tsawonsa ya zuba mata idanuwan shi yana sake karantar yanayi ta, a hankali yayi magana


"Kada ki ɓoyemin komai Hamrah idanuwanki sun nuna min akwai abin da ya faru, kuma yanayin ki ma ya nuna? Ina Alhaji Sama'ila?"


A hankali hawaye ya zubo mata ganin Ammar yasa ta danji sanyi a hankali ta ce


Nima ban san inda yake ba.


A take numfashi sa ya soma hawa yana kallon ta irin kallon nan na me ki ke nufi, bakin ta na rawa ta ce


Tun da na farka da safe ban sake ganin shi ba har yanzu.


"Ah bangane ba ina ya tafi baki kira number shi ba ne?"


Na kira baya shiga, amma manager hotel ɗin ya ce wai tun safe ya sake ɗakin ya basu key ya fice.


A take idanuwan Ammar suka kaɗa su kayi jajir numfashin sa ma na sizin, ya ce


"Ya sake ɗakin ya tafi gidan ubanwa ya tafi ya barki me yake nufi da mu ne?. Yaudarar mu zayyi ko kuma yaya.


Ita dai sai hawaye ta rasa abin cewa ta nuna mashi wasikun da ya bari da hannu, ya miƙe ya iso wajen ya buɗe karamar nan take jikinsa ya soma rawa shatin jijiyoyin jikinsa suka bayyaa tun daga kansa zuwa hannayen sa ya dunkula hannu ya daki jikin garu take hannunsa ya fidda jini yana fuzgar da iska ya ce


"What?. Mu za a yaudara, to in ya saba yiwa wasu mu ba zayyi mana mu kyaleshi ba, yana nufin taron da mu kayi ya tashi a banza ya maida mu shashashu kenan taron iska mu kayi, to bai isa ba yayi kaɗan kuma sai ya gane kurensa yayi kuskure da yayi AUREN HARAMCI dake.........
_________________________
Alhamdulillah ala kulli halin. Masu min addu'oi ina godiya matukar. Akwai masu cewa labarin ya sauya ban sauya labarin ba asali ma PG kafin wannan shine PG 1 wannan kuma PG 2 to duba da yadda nake son sakon ya isa kafin abin da ya sami ita Hamrah ta cikin labarin shine na kawo labaran wadanda suke dauke da jarrabawa daban daban SBD in tata jarrabawar tazo a fahimci abin.


Ayi hakuri da typing errors.


Akwai waɗanda suka tura min kyauta ina godiya Allah ya saka da alheri, nayi farin ciki kuma ban sanmaci zan sami haka ba a wannan littafin. Nayi Updating WhatsApp ɗina ɗan Allah su min magana in har sunyi arɓa da wannan PG ɗin su min magana ta pc dan basa ɗaya daga cikin group nawa.


Akwai wata kuma Fa'izi something dai please su min magana kada kuga nayi shuru kamar ko girman kai ne.












Comments and share




*MUJARRABI*




By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA


09021706569


PG 45 & 46




*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*




________ zuciyar shi nayi masa tsuya da raɗaɗi, ji yake tamakar zata tsago ta fito sabar tashin hankali da kaɗuwar da yayi sbd jin abin da Hamrah ta sanar dashi da kuma ganin wannan wasikar da Alhaji Sama'ila na Abuja ya rubuta ya bari. Kaiwa da komowa yake yi yana safa da kuma marwa, jikinsa naci gaba ɗa ɓari ji yake ina ma gashi ga Alhaji Sama'ila na Abuja da ko sai ya yabawa aya zaƙinta. Isowa yayi gaban window ɗakin ya ɗan yaye labulen yana ya ƙurawa fitulun dake haske wajen, kallon farfajiyar hotel ɗin yake yi yana kaɗa ƙafarsa ɗaya yana kallon shige da ficen da mutane ke yi. A hankali kuma ya sauke numfashi tare da juyowa yana kallon Hamrah dake kuka a zaune wuni guda duk ta fita hayyacinta ta faɗa sosai ta rame duk ta kuma yi sanyi. Ya maida idanuwansa kan tulin magungunan dake kan bedside yasa hannu ya ɗauko su tare da roban drip ɗin ya zube su gabanta ya duka har ƙasa ya zuba mata jajayen idanuwansa yana fitar da iska ya ce


"Yayi miki wani abun ne da yasa aka sanya miki ruwa ko kuma sabar kiɗimewa ce da abin da ya aikata miki?"


Jin wannan tambayar da Ammar yayi mata ne yasa gabanta faɗuwa ta sake ruɗewa, tabbas Alhaji Sama'ila ya cuceta ya rabata da budurcinta ya saka kafa ya sallaketa yayi tafiyarsa abinsa bai damu da ita ba ko ta mutu ko ta rayuwa. A hankali ta ɗago ta kallesa ganin yanayin sa da kuma yadda idanuwansa suka sauya launi zuwa ja hatta farar fuskar sa sai da ta koma ja sabar baƙin ciki da takaici, tana ganin yadda faffaɗan ƙirji kai sheking kamar ana jijjiga shi. Kasa ci gaba da kallon sa tayi ta maida idanuwanta kan tulin magungunan da ya kwaso ya zube su gabanta. Tunowa da abin da ya faru tsakaninta da Alhaji Sama'ila ya dawo mata kunya ce kuma ta lulluɓe ta me Ammar yake nufi da wannan tambayar ta yaya kuma zata iya faɗa masa alhalin tana yarsa yana ƙaninta ai hakan bai dace ba a hankali tayi magana da ƙyar ma ta iya furtawa


Uhmmm daman suma nayi ne shiyasa aka sanya min drip.


Ya sauke numfashi da karfi har sai da tayi saurin ɗagowa ta kallesa, kai tsaye ya ce


Ya kwanta dake ne?.


Kirjinta ya bada rasss....


Eh.


Ta furta a kunya ce to bata san me zata ce ba sai kawai taga ya miƙe ya daki jikin garu ya kuma ɗauko light dake kan wani madaidaicin stool ya makesa da ƙasa yana huci a tsorace ta miƙe ta sa hannu ta rikesa tare da rike hannunsa sa dake zubda jini jikinta na rawa ta zaunar dashi da ƙyar ya dago da jajayen idanuwansa yana kallon ta itama shi take kallo, lallai yau zuciyar su UMAR Soja ta tashi a hankali ta ce


Please Ammar calm down, kana ji wa kanka ciwo.


Sauke numfashi yayi tare da kau da kansa gefe ya fuzgar da iska ya ce


"Me yasa kika amince masa bayan kinsan cewa mayaudarine, meyasa baki kirani tun a daren jiya kin sanar dani ba, ai sai daga baya nake jin wai a hotel zaku kwana to dan ubansa ce masa akayi saboda wannan dalilin ne aka basa ke. Yayi kaɗan ya raina mana hankali sai na tabbatar masa cewa ke macece wacce ba dare ɗaya ake bukatar ta ba, har abada ake sonta kuma ake so ayi rayuwa da ita kuma a zauna da ita"


Ita kunya ma duk ya rufe ta, da jin abin da Ammar ke cewa, batayi auni ba taji ya miƙe cikin ɓacin rai ya sake make jerarrun pot flower's da akayi decorating dasu daga gefe ji kake rassss suka faɗo ƙasa warwas. Saurin boɗe kofa akayi wani maaikaci ne yashigo sanye da uniform na ma'aikatan cikin hotel ɗin yayi magana ciki ɓacin rai


"Kai baka da hankali ne ya zaka shigo mana hotel ka lalata mana ɗaki, to wallahi kaji na rantse sai ka biya mu zaka nunawa zuciya...


Aiko bai kai ga rufe mouth nashi ba yaji saukar naushi, Ammar ya shaƙo sa daman me neman kukane aka jefesa da kashin shanu aiko ya haɗesa da jikin garu har sai da idanunsa suka fito waje. Ammar yayi magana cikin ɗaga murya kamar ya haɗiyesa ya huta ya ce


"Kayanku na banza na wofi, da asarar su da su da babu duk ɗaya suke, an farfasa su kaima kanka sai nayi gunduwa gunduwa da part na jikinka kayi wasa, kun gina waje kun baiwa katti daman cin zarafin mata shine har kake alfahari da wajen kana na fasa muku kaya to an fasa baza a biya ba kada ma kasa na rushe hotel ɗin baki ɗayansa"


Da ƙyar Hamrah ta kwace wannan ma'aikacin daga shaƙan da Ammar yayi masa, aiko ya ari ma kare ya fice a guje dan shi bai yarda kan Ammar ɗin daya bane duk a tunanin sa Ammar dukan Hamrah yake sbd yasha jin ana hakan. Hamrah ta zaunar da Ammar bakin bed ta zauna kusa dashi ta juyo da fuskarsa suna facing juna ta ce


Ammar bai dace kayi hakan ba, nima da akayi min na jure na danne balle kai, kayi hakuri muna cikin Hotel ne kada ka tara mana mutane, please.


Maida idanuwansa yayi ya rufe a daidai lokacin manager ya shigo ganin Ammar da baisan da shigowar sa ba da kuma ganin yadda aka farfasa musu kayayyakin da sukaiwa ɗakin ado yasa yayi magana


"Haba bawan Allah ya zaka shigo cikin Hotel kana mana hayaniyar bayan kasan nan wajen hutawa ne da mutane a ciki, sannan kuma wa yace ka fasa mana kaya kasan nawa aka siyesu"


Ammar ya zabura zai tashi Hamrah ta riƙe shi ta hanashi tashi ta juyo tayi magana


Haba manager ka dubi halin da muke ciki dan Allah abar maganar na ɗauki nawin biyan duk abinda ya fasa yaro ne kada ka maida hankali irin nasa ka rike girmanka.


"Manager kake ko waye, sai na kai karanta court da duk wanda yake da hannu cikin buɗe wannan hotel ɗin sai kun yi bayani, tunda daman ba wajen Allah da Annabi bane kun tara katti suna sheƙe ayarsu kuce ana hutawa"


Please Ammar kayi shuru dan Allah.


Da ƙyar ta fidda manager dan cewa yayi ya sauke kwanan da ya bata a ɗakin gwanma ya bata kuɗi taje ta kama wani hotel ɗin, Ammar kam ko kaɗan hakan bai damesa ba shi haushin ma bai samu ya shaƙo manager bane yake jin zafi. Bayan fitan manager ne ta dawo rarrashi ita da zai bawa baki ta ya dawo ita ke bashi ba ki da ƙyar ya sauko ya ciro wayarsa yana ƙoƙarin kira tayi saurin rike wayar tare da cewa


Wa zaka kira?


Ya tsareta da idanuwan sa ya ce


"Daddyn zan kira, yasan halin da muke ciki sai mu koma gida tare, ba zan bari ki kara koda minti ɗaya ne cikin wannan hotel ɗin ba"


Dan Allah kada ka sanar da kowa halin da nake ciki wannan dalilin ne ma yasa na kirata mu tattauna akai.


"Ban gane ba, me kike nufi bazaki koma gida ba, a ina zaki zauna anan hotel ɗin ki keso ki zauna hakan ba zayyu ba mu koma gida asan irin matakin da za a ɗauka"


A hankali ta sauke numfashi, hawaye suka biyu kuncinta ganin haka yasa jikin Ammar sanyi ya ɗan sassauta murya ya yi magana


"To Hamrah ya ki ke so ayi baki son na faɗawa Daddy to akan wane dalili?"


Ammar farin cikin iyayenmu shine suga nayi aure, kuma gashi hakan ya faru anyi bikin nawa, na sani daga jiya zuwa yau suna cikin farin cikin sosai saboda nayi aure kuma suna da burin na zauna lafiya a gidana, kada ka manta irin abubuwan da nayi facing a gida akan rashin aure ba irin kuka, damuwa, rashin hankalin da ban gani ba, kafini sannin irin zaman da nake yi a gida, to yanzu kwasam sai na ce dasu AUREN HARAMCI Alhaji Sama'ila yayi dani ba na halak ba, ta yaya zasu ɗauki abin nasan dole hankalin su ya tashi, sannan ga mutane nan cike da gida duk kuma sbd wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login