Showing 69001 words to 72000 words out of 74305 words

Chapter 24 - MUJARRABI BOOK ONE BY SAYYADA BARRISTER.txt

18 Jan 2025

4632

da plan naki dole ki amshi motar kiyi amfani da ita har zuwa lokacin da zaki sanar dasu Daddy komai"


Ta sauke numfashi tasa hannu ta amshi key ɗin motar tare da cewa


Ya mutan gida?.


"Yau duk yawanci sun tafi ina ji zuwa gobe zuwa jibi za a ma watse"


Alhamdulillah, kaga komai yana tafi kan tsari. Allah ya kaisu lafiya.


"Ameen"


Sun jima suna fira kusan magrib ya fice, sai 8:00pm ya dawo ya kawo mata abin taɓawa ta ci suna fira ta shige ciki ta kwanta dan shi yace ba zai tafi gida ya barta ita kaɗai ba. Haka rayuwar Hamrah ta kasance har tsawo sati biyu, sai dai zuwa wannan lokacin ba kullum bane Ammar ke kwana a gidanta, sbd kada Daddy ya fahimci wani abin. Hankalin Hamrah ya fara dawowa jikinta ta ɗan sami nutsuwa Zeenat da Ayshe suna kawo mata wuni su koma bata taɓa barin sun fahimci komai ba, haka bestie nta Shatu ita ma tana kawo mata wuni su sha firar su da ƙyar suke rabuwa.


_After 1month_


Cikin sauri ta fito ta faɗa cikin motar ta tadata ta fito tayi parking a waje ta koma ta rufe gate ɗin dan har zuwa wannan lokacin basu nemi gateman ba tun bayan sallamar wanda suka tadda yana gadin wajen, sunyi hakanne sbd kada sirrin abin da suke ɓoyewa ya tonu, ta shige motar ta figeta cikin gudu ta hau titi kai tsaye sai Na kowa hospital tayi parking a farfajiyar Hospital ɗin ta shige ciki bata ma ganin gabanta duk ta fita hayyacinta. Tana isowa ta shige cikin office ɗin da zata gamu da ko wacce iriyar likitace, tana shiga ta tadda Doctor da ta duba ta a hotel na washegarin aurenta cikin sauke numfashi ta iso kusa da ita suka gaisa bata shaida Hamrah ba sai da Hamrah tayi mata kwatankwacin wancan ranar ta ganeta cikin sanyin murya ta ce da Hamrah


"Kina bukatar wani abu ne?"


Ganin office ɗin da mutane ta ce


Eh likita amma a sirrance.


Ta sauke numfashi suka shige wani karamin room dake cikin office ɗin, Hamrah cikin kuka ta ce


Nayi farin ciki da yasa dake na haɗu a yau kuma nasan kin san duk abin da ya faru dani a hotel kwanakin baya, to yanzun ma kusan matsalar tare suke, likita a takaice dai ina ɗauke da ciki sakamakon abin da ya faru, bana son cikin wallahi bana so ba haife shege ko shegiya dan Allah ki rabani dashi.


Sosai Hamrah ke kuka kamar ranta zai fita, da ƙyar likitar ta iya rarrashinta ta, ta ce


"Abin da ki ke shirin aiwatar wa babu kyau shawarar dan zan baki ita ce ki yi hakuri ki amshi babyn maybe alkhairi ne amma zubda cikin hatsari ne ga rayuwar ki kuma zaki aikata laifi, sannan menene laifin abin da ke cikin shi bai san komai ba kada ki sanya shi cikin abin da ubansa ya aikata miki"


Har kasa Hamrah ta duka tana kuka ta haɗe hannayenta biyu ta ce


Ni da ki ke gani nima likitace kuma kwararriya nasan illar yin hakan amma kuma hakan shine hanya mafi sauki daga gareni ki taimaka ki zubar barin shi tamkar ruguza rayuwata ce, yau nake fatan komawa gida na sanar dasu abin da ya sameni a ranar bikina na, daga kuma rana irinta yau na sage gina sabon rayuwa sai kuma wannan abin ya sameni dan Allah likita ki zubar min shi.....


Kuka take yi kanta na ƙasa, jin shuru da likita tayi ne yasa ta ɗago tana hawaye idanuwanta suka sauka kan Ammar dake zaune a gabanta ya kura mata idanuwansa da suka kaɗa su kayi jajir, baya tayi cikin sauri tana mamakin yaushe ya iso nan ɗin kuma ya akayi yasan tayo nan ɗin?.


"Ba zaki zubar da cikin ba Hamrah yin hakan kuskure ne ya zama dole ki haifeshi, the baby was innocent bai san komai ba"


Miƙewa tsaye tayi ta nuna shi da yatsa kamar wata zararriya ta ce


Bai zama min dole na haifi cikin shege ba Ammar dole ne a fidda min shi ko ana so ko ba aso bazan taɓa haɗa jini da azzalumi ba kuma fasuki ba, in kuma aka dage sai na haifeshi to zan kashe kaina kowa ma ya huta.


Hankalin Ammar ya matukar tashi tunda suka taso shi da ita bai taɓa ganin ta shiga cikin ɓacin rai ba irin wannan, duk da yasani da ciwo to amma ba zai bari ta zubda ba. Ya miƙe tsaye shima tare da kai hannu zai riƙe ta sbd ganin kamar nema take ta faɗi ƙasa tasa hannu ta bugesa. Ajiyar zuciya yayi ya ce


"Hamrah everything is a matter of time, we should be more patient. If Allah wills, everything will be right. All things must come to an end. Kamar yadda ki ka jure zama da agida na wani lokaci ki kayi hukuri ki ka kau da kai har Allah ya nufa ki kayi aure washegarin bikinki mijinki ya gudu ya barki kika jure hakan to haka ma wannan karon hakuri za kiyi ki kuma jure ki amshi kyautar da Ubangiji ya baki da hannu bibbiyu, dayawa na neman hakan basu samu ba. Kuma bamu sani ba ko da wane irin alkhairi wannan babyn zai zo mana so, Please Hamrah accept it as your destiny"


A hankali ta sulale kasa ta zauna kamar wacce aka cirewa laka, hawaye na ci gaba da zubo mata, ta rumtse idanuwanta a hankali take furta kalmar


innalillahi wa inna ilaihi rajiun.


Abin ya fara fin karfinta, kuma ya wuce tunaninta tabbas Allah ne mai iyawa bawa ba ya iyawa sai da iyawar Ubangiji, a tunaninta a yau ranar farin ciki ne dan tana murna zata koma gida gaban iyayenta bayan rabuwa da tayi dasu na tsawon wata ɗaya a matsayin tana gidan mijinta ashe abin ba haka bane, kana naka Allah na nashi nasa ne kuma shine dai-dai. To yanzu ya za tayi?.


Sunkuyowa Ammar yayi tare da share mata hawayen dake fuskarta cikin tausayawa ya tausasa murya ya ce


Tashi mu koma gida.


Rike hannunta yayi suka fito a tare har cikin motarta ya sakata ya zaunar da ita a mazaunin gaba, ya koma ya sanyawa motarsa key a inda ya bakata sannan ya dawo shige cikin motarta ya zauna a mazaunin driver yaja ya fice daga cikin Hospital ɗin suka dawo gida yayi parking ya taimaka mata suka fito, ya zaunar da ita a palour. Ita kam ta koma mutum butumi sai ido babu bakin magana ji take sam kamar ba ita bace. Ammar ya fice babu jimawa ya dawo da alamun ba da motarta ya fita ba amma jin shigowar motar yasa ta tabbatar da cewa Hospital ya koma ya ɗauko tasa motar. Shigowa cikin palourn yayi yanda ya barta zaune haka ya taddata, hawaye da bin gefen fuskar ya zauna kusa da ita cikin kulawa ya ce


"Ko kina ganin yau mu sanar dasu Daddy abin da ke faruwa in yaso musan irin matakin da zasu ɗauka"


A'a.


Kawai abin da ta ce. Ya sauke numfashi ganin yanayin da take ciki yasa ya kyaleta ya koma kan 3setter ya kwanta tare da lumshe idanuwansa.


Ya akayi kasan Hospital na tafi?.


A hankali ya buɗe idanuwansa ya juyo ya kalleta ya ce


Nazo ne da niyyar ɗaukanki na kaiki gida kamar yadda mu kayi sbd sanar da iyayenmu gaskiya akan aurenki da Alhaji Sama'ila shine naga kin figi motar kin fice daga layin a daidai lokacin kuma ni ina ƙoƙarin shigowa nayi mamaki ma da baki ganni ba, ganin haka yasa na fahimci ba lafiya ba nabi bayanki sai dai abin da ya bani mamaki shine shigar ki cikin Hospital ɗin me ya kawo ki, kawai nayi parking na biyo ki ciki shine na tadda abinda ki ke sanar da likitar"


Ajiyar zuciya tayi a hankali ta sake cewa


To ya zanyi da abin da ke cikina shin bayan na haifeshi ina zan kaishi rikesa zanyi ko kuma zan nemo ubansa?.


Tashi yayi ya zauna ya kura mata idanuwa na wasu lokuta, sauke numfashi yayi a hankali ya ce


"Ai ba zamu baiwa Alhaji Sama'ila abin da zaki haifan ba ya zama namu mu zamu rikesa ko riketa har zuwa lokacin da Ubangiji ya kayyade mana, kuma nasan iyayenmu zasu amshi abin da ƴarsu ta haifa.....


Ni bani son abin da zan haifa, dole ne in na haihu a kaiwa ubansa.


"A ina kenan?"


Abuja.


Murmushi mai ciwo Ammar yayi ya ce


"Kina da tabbacin a Abujan yake ina da tantama ma bashi da asali. Ni na amince in kin haifa ki bani babyn zan zame masa uwa da uba in kuma lokacin Allah ya ƙaddara nayi aure sai na tafi da babyn gidana mu renesa"


A hankali ta ɗago ta kallesa da jajayen idanuwanta ta ce


Na mallaka maka tun yanzu ko na mutu ko kuma ina raye na baka babyn ni kuma bayan na haihu, I'll to go far na fara sabon rayuwa.


















Comments and share*MUJARRABI*


By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA


09021706569


PG 49 & 50 _end of book 1_




*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*


_MIKIYA mai hangen nesa, mai kuma farin jini wajen al'umma, mai ɗauke da tarin marubuta hazikai kuma fasahai. Kungiyar masu haɗin kai da fahimtar juna. Godiya ban girma ga shuwagabannin kungiyar da kuma members ɗin ta kun nuna min kauna wajen sharing, shawara da kuma ƙwarin gwiwa, i dey with you till.....🤣 You showed me love 💕😘. Much love for you._


_Bana taɓa mantawa dake habibty Bilkisu S fari. Much love for you 😘_




__________ Laulayi sosai cikin ya sanya mata bata iya cin koma sai amai da tofar da yawu duk ta fita hayyacinta, ta rame ga yawan tunani da take yi, bata iya komai daga kwanciya sai zama duk ayyukan gidan Ammar ke yinsa. Kwance take a wannan lokacin ma idanuwanta biyu tana kallon jikin garu kamar me nazarin painting dake jikin mai ɗauke da kyalli² lokaci zuwa lokaci take sauke numfashi. A hankali ya turo kofar ɗakin ya shigo ya zauna kusa da ita ya kura mata idanuwa cikin tausayawa yayi mata magana


"Hamrah ki tashi ki sanya abu a cikin ki rashin cin abinci zai haifar miki matsala tare da abinda ke cikin ki, ko bakyaso ki daure ki ci Please"


Kamar zayyi kuka yake rarrashinta, a hankali ta yunƙura ta tashi ta zauna da ƙyar ta kallesa kuma sai ta kau da kai gefe, saukowa tayi ta nufi toilet tana shiga kuma sai kwara amai tun tana iya yinsa har ta gagara sbd babu komai cikin cikinta daman ruwa ne gashi kuma ta amayar, nan take ta faɗi sumammiya. Cikin hanzari Ammar ya iso cikin toilet ɗin sbd jin karan faduwar da tayi yasa ya taso dan ganin abin da ke faruwa. Ganin ta kwance a ƙasa yasa ya dinga jijjigata yana tashin ta amma ko motsi bata yi ba yasa ya ɗauke ta chak kamar wata jiririya yayi waje da ita ya sanyata cikin mota ya kwantar da ita a sit na baya, sannan ya wuce ya buɗe gate ya dawo ya shiga ya tada motar ya tukata zuwa kofa yayi parking daga gefe ya fito ya rufe gate ɗin sannan ya koma cikin motar ya tada ta kai tsaye sai Hospital. Da taimakon Allah dana likitoci Hamrah ta farfaɗo aka sanya mata drip bata san inda take ba sai da ta kai kwanaki uku a hospital, ta farka taga ƴan gidansu a kanta binsu take da kallo su kuma suna mata ya jiki, da kai take iya amsa musu, jikin dai tana jin sa da sauke da taimakon karin ruwan da akayi mata. Sai da tayi 1week a hospital sannan aka bata sallama sai dai wannan karon Ammar sam yaki goya mata baya akan ta koma gidanta duk da bai sanar dasu komai ba amma ya ce mijinta baya nan dan haka a tafi da ita main house ta ɗan huta. Haka ko akayi gida aka tafi da ita sai da tayi 3 weeks sannan ta dawo gidanta. Zuwa wannan lokacin kam jikin dama² dan tana iya komai da kanta Ammar ma ya fara fita office nashi na soja sbd kwazonsa tashi guda aka basa matsayi, yakan zuwa da safe sai ya fice sai kuma dare yazo ya ganta wani lokacin ya kwana wani lokacin kuma ya tafi.




************************
Cikin sauri akayi labour room da ita duk hankalin su a tashe sbd bleeding ɗin da take yi, ganin haihuwa ce ta kamata kadan² yasa likitoci mai da hankali akanta sai da aka dau 1hour 30munute sannan ta haifu baby girl nan ko murna da farin ciki a gun ƴan'uwanta ba a magana, ita dai tun da taji babyn ta faɗo ta kama bacci bata san wainar da ake toyawa sai da ta farka ta ganta a side room an shiryata saf kamar ba mai jego ba, ita kaɗai a ɗakin shuru babu motsin kowa. Jin motsin turo ƙofar ne yasa ta ɗan juya ta kalli ƙofar. Amma ta gani a tsaye hannunsa rike da handle door kamar bazai ƙaraso ba a tunanin sa bacci take, ganin idanunta biyu yasa ya ƙaraso ya zauna kan kujerar dake kusa da bed ɗin ya sakar mata da murmushi a hankali yana ci gaba da kallonta sauke numfashi tayi a hankali ta ce


Did you tell them the secret?.


Kai ya girgiza mata alamun a'a, sannan ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce


"No. I won't, until you agree"


Sauke numfashi tayi ta maida idanuwanta ta rufe....


"The baby is pretty like you"


A hankali ta buɗe idanuwanta ta kallesa, sai kuma ƙirjinta ya bada rasss, to yanzu kuma ta haihu ko wacce iriyar rayuwa zata sake sintar kanta cikin ta dan wannan karon ba zata iya ɓoye komai ba zata bayyanawa iyayenta komai sbd itama ta samu taji sanyi cikin ranta ta rabu da fargaba, bata ce dashi komai ba shima ganin bata son yin magana yasa yayi shuru har Ammie ta shigo da babyn tana cewa


"Lah ashe uwar taki ma ta farka, to taho meje ta baki mamman naki kisha"


Hamrah dake kwance ta kalli Ammie dake ƙoƙarin ƙarasowa da babyn, ta sauke numfashi tare da tashi ta ɗan kishingiɗe da jikin bed ɗin, Ammie ta mika mata babyn tana


"ki bata tasha yunwa sai addabar take tun da ta taho duniya bata sha nono na sai ruwan zamzam da dabino"


Sudda kai ƙasa tayi tasa hannu ta amshi yarinyar ta kura mata idanuwa tana kallon yadda ta sanya babban yatsar ta cikin bakinta tana sosa alamun yunwa take ji, fara ce kal wanke hannu ka taɓa duk da jaririya ce kyawunta bai buya ba wasu kwantantun gashi ne saman goshinta, idanuwanta farare tas da su roung face gareta hanci ɗil dashi da ɗan ƙaramin bakinta mai ɗauke da jan laɓɓe, sai wusili wusili take da idanu. A hankali Hamrah ta sauke numfashi tana jin tausayin yarinyar na shigar ta sosai tana jin ƙaunarta...


"Oh ni yaran zamani, ki bata tasha shine ki ka zuba mata idanu yunwa fa take ji"


Cike da kunya Hamrah ta buɗe rigarta ta fidda nono ta sanyawa yarinyar a baki nan da nan ta kama sosa tana sha, a hankali ta ɗaura hannunta saman kan yarinyar tana shafa gashin kanta mai laushi da tsantsi baki wuluk dashi. Jin ajiyar zuciya da Ammar yayi ne yasa ta ɗago ta kallesa kura musu idanuwana yayi yana kallon su ko kiftasu baya yi, sun matukar burgesa mamaki yake Hamrah na feeding baby lallai rayuwa kenen. Harararsa tayi da ya sanya ya saki murmushin da ya fito da boyayyun dimples nasa fararen hakwaransa suka bayyana ya girgiza kansa ya miƙe tare da yiwa Ammie sai anjima ya fice. Baby kam daga shan nono tayi baccinta nan Hamrah ta kwantar da ita a daidai lokacin kuma ƙannenta suka shigo Ayshe, Zeenat da Maryama suna mata sannu tana amsawa. Anan suke wuni da yamma su tafi har aka sallameta suka dawo gidan Hamrah saboda shirye shiryen bikin suna. Shirye shiryen bikin suna ake yi babu kakkautawa Daddy kam kamar akan Hamrah ya fara samun jika sai hidima yake musu musamman da yaji cewa Alhaji Sama'ila na cen Umrah yana ibada Daddy yace ko yana nan ko bayanan hidima sai anyi nan Hamrah ta kwantar da hankalinta suka sha suna bidia kala kala, gift kam ba a magana kowa yazo taron sunan nan zai koma da goma ta arziki anyi wasan Naira yarinya taci sunan kakarta Fateematul Batula wato Ammie aiko ranar Ammie wuni tayi tana washe hakwara. Washegarin suna ne Ammie ta ce za a tafi wankan jego babu musu suka tafi dan Hamrah cewa ma tayi Alhaji Sama'ila ya amince ya ce ta zauna a gida har sai ya dawo.


Satin Hamrah 3 da haihuwa jikinta yayi sumul kamar ba ita ba, sai dai kuma yawan shuru da take yi ne da kuma yawan keɓance kanta ke sanya Ammie mamaki kamar ba Hamrah ba duk da daman bata da yawan hayani amma wannan karon shurun yayi yawa. Ammie ta shigo ɗakin Hamrah ta taddata tana nan zaune tana aikin tunani ta zauna kusa da ita sosai take kallonta cikin kulawa ta kira sunanta


"Hamrah"


A hankali ta ɗago ganin Ammie yasa ta gyara zama tare da cewa


Na'am Ammie, yaushe ki ka shigo?.


"Ai baza ki sani ba tun da ki zaɓi ki dinga zama ke kaɗai kina tunani, wai meke faruwa dake ne shin gidanki da matsala ne ko kuma akwai abin da ke faruwa sakaninki da mijinki ne?"


Jikin Hamrah yayi sanyi tayi ajiyar zuciya a hankali ta ce


A'a Ammie babu komai fah kawai babu ƴan tayani firane shiyasa.


Sauke numfashi Ammie tayi ta tsurawa Hamrah idanu tabbas akwai abin da ke damunta, a hankali ta ce


"Hamrah akwai abin da ke faruwa sakaninki da mijinki dan na kula tun ranar da kika haihu har zuwa yau baki sake yin maganar da ta danganta dashi ba sannan ko waya ma bana ji ko ganin kuna yi. In dai da matsala ki faɗeta tun kan ya dawo mu sami bakin zaren mu warware ki koma ɗakinki lafiya"


Ƙirjin Hamrah ya bada rasss, tab ai abin da ke faruwa ya wuce matsala ai da zata sanar da Ammie dako tafi kowa shiga tashin hankali, sauke numfashi tayi tare da ƙirƙiro murmushi ta ce


Lah Ammie ba komai yawancin wayar dare muke yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login