Showing 9001 words to 12000 words out of 74305 words
na rintse su sosai ina jin zuciya ta tana min zafi, kuma wannan yana da nasaba da irin kishin da Allah ya halicce mu dashi mu mata, na sauke numfashi sannan na buɗe su tare da zuba masa su, ina son Alay BUKAR ba wai auren da zayyi bane bani so, tsoro na ɗaya shine kada wacce zai auro ta shigo ta wargaza min farin cikin gidana, amma ba komi zan na barwa Allah...
A hankali na ji saukar hannun shi kan fuskata yana ci gaba da rarrashina har bacci yayi awun gaba damu, washegari bayan mun tashi mun karya ya ce zai je ya dawo. Fitar shi bada jimawa ba ya dawo tare da miƙamin key motar, cike da mamaki nake kallon shi, ya rike hannuna muka fito compound na gidan nan nayi tozali da sabuwar mota, ya ce mani ya siyowa, cikin murna da farin ciki na karɓi key ɗin ina godiya.
Da yamma lis ina zaune a palour na ji ana nocking, na miƙe na iso na buɗe sai ganin Sulaiman furniture na yi a tsaye, a lokacin ne ma na tuna da cewa mun yi waya a kan zai zo ganin set na kujeru na, sai muyi magana. Bayan mun gaisa ne ya shigo a lokacin shima Alay BUKAR ya dawo nan ne ya ke tambayar meke faruwa ne?. A nan nayi mishi bayani ya ce kada na damu za suyi magana, to shine fa daga wannan maganar washegari da safe, yau kenan nake nufi aka shigo min da kujeru da tv da kuma show glass, aka ajiye su a ma'ajiyar su, shine ya ce gobe za a kamin set na kayan ɗakina.
Sauke numfashi Hamra ta yi cikin farin ciki, ta furta
Alhamdulillah, kin ga abin da nake nuna miki ba, da yanzu kin biyewa zuciyar ki da shikenan ta kai ki ta baro ki, hakuri za kiyi, da kuma ki dage da addu'a Allah ya ka miki sauki cikin wannan al'amarin.
"Haka ne yaya HAMRA na gode, in shaa Allahu zan ci gaba da hakuri da kuma addu'a"
Sun jima suna tattaunawa sannan Hamra ta yi musu sallama ta dawo gida, kasancewar dare ya soma yi ko kuma dare yayi dan a lokacin to 9:00pm unguwar su cike take da majalisar mata sa da kuma ta dattawa, a hankali take takowa saboda ɗan sahu a bakin layin unguwar su ya ajiye ta, har tazo giftawa ta ce ɗaya daga cikin waɗanda suke zaune a majalisar dattawa ya ce
"Kai ina mamakin rayuwar yanzu, ka duba fa wannan yarinyar tana iskanci ƙarara ubanta na gani, yanzu fisabilillahi a wannan lokacin ya dace a ce ƴa mace na waje, kai da wannan ɗiyata ce wlh ko sadaka zan bada ita"
Ci gaba da tafiyarta ta ke, kasancewar bata da saurin tafiya shi ya sa ta ke jiyo abin da suke faɗa, murmushi ta yi tare da girgiza kanta a ranta ta ce shi fa zato zunubi ne, yanzu basu san daga inda ta ke ba suka ƙaƙaba mata sharri in ta ce bata yafe ba ma ya zauna amma ba komi ta barsu da halin su.
Ɗaya daga cikin su ya tari numfashin wanda ya yi magana ya ce
"Ka taɓo min in da yake min ciwo, abin takaici ma wai akin asibiti ta ke, a ce ƴa budurwa tana aikin asibiti kuma wai har da wani night duty, kai kaji shashanci Bature wato su suna night a na kuma night dasu"
Suka kwashe da dariya, ita abin da ya bata haushi ma shine sa'annin mahaifinta ne amma suke faɗin haka akanta, ta ji saukar muryar mutum na uku ya na cewa
"Ai ni ban ga laifin ta ba, na ubanta nake gani, shi fa ko a jikin shi tana sheke ayar ta a gaban sa amma bai iya cewa kala, irin waɗannan ai auren dole ya dace ayi musu dan in dai ta su ne su shekara saba'in babu aure"
Tayi sauri ta wuce su, ranta bai ɓaci ba tausayin su ma ta ke saboda yi da mutum haramun ne, ta turo kofar gida ta shige, har ta iso kofar shiga palour ta ji muryar AMMAR na cewa
"Likita"
A hankali ta jiyo ta kalle shi ta ce
Ammar, kaima shigowar ka ko?.
"A'a tun ɗazu na dawo jin baki gidan ya sa na ji babu daɗi kuma na kira ki baya shiga"
Ta sauke numfashi ta ce
Ji ka sai ka ce dan yaye, dan bana nan shine ka ke jin babu daɗi to ina kuma ga nayi aure, sai kuma ka yi yaya.
Murmushi ya yi sosai ganin yadda ta ke wani zazzare idanuwan ta na faɗa, Hamra kenan akwai hakuri da saurin hawa ta ce
"To me a ciki ba sai na biki cen gidan ki ba, mu tare a bani ɗaki, ko ya ki ke gani babbar yaya"
Ya faɗa yana dariya, ta hararesa ta juyo tare da buɗe kofar ta shigo ya bi bayanta, ɗakin Ammie ta nufa, ganin haka ya sa AMMAR wucewa ɗakin sa. Ta shiga tare da sallama, Ammie na zaune tana kallo a ɗan karamin tv ta, ta amsa mata, HAMRA ta zauna tare da cewa
Ammie na dawo, jikokanki suna gaida ki, Ayshe ma ta ce na miƙa mata sakon gaisuwa.
Sauke numfashi Ammie ta ɗago sosai tana kallon Hamra, ganin haka yasa ta yi saurin sudda kai kasa, Ammie ta ce
"Da fatan baki mance da abin da na faɗa miki ba, akan cewa na baki nan da ƙarshen wata ki fidda miji?"
Jikin Hamra ya yi matukar sanyi ta ce
Eh Ammie ban mance ba, sai dai Ammie har zuwa wannan lokacin bani da sayayye.....
"Na gama magana ta, shawara ta rage gareki, bazan zuba idanu ina kallon ki ba, sannan ki sani kasancewar ba ki da aure ba zayyu ki dinga zuwa gidan ƙannenki ba, yin hakan ba tsari bane, kema ki yi ƙokari ki mallaki na ki gidan"
Sauke numfashi Hamra ta yi ba abin ta yi kuka ba, da yau ko mahaukaci ne ya fito neman aurenta zata amince ayi in dai hakan shine farin cikin Ammie, jiki a sanyaye ta ce
In shaa Allahu.
Ta mike ta iso ɗakinta, zama ta yi bakin bed tare da riƙe kanta sosai tana ji yana tsara mata, ita kanta zamanta babu aure yana damun ta amma ya za tayi, dole tayi hakuri zuwa lokacin da Allah ya yi za ta yi auren....
"Kuka ki ke yi?"
Saurin ɗagowa ta yi ta kalli Ammar dake zaune kan carpet ya tsura mata idanu, bata ma ji shigowar shi ba, girgiza kai ta yi ta ce
Shikenan bani da abin yi sai kuka.
Murmushi ya yi ya miƙe ya kunna tv tare da kaiwa channel na MBC ACTION, ya dawo ya zauna ya ce
"Ba haka na ke nufi ba, na san kin shiga ɗakin Ammie kuma na san da zaran kin fito ki ke kuka, sbd ba ta son kulaki"
Ta sauke numfashi a hankali ta ce
Mun yi magana da ita yau.
Cike da mamaki ya ce
"Abu ya fara yin kyau, to me ta ce da ke?"
Hamra bata ɓoyewa Ammar damuwarta wani abin ma sai su yi shawara tari kuma ta sami mafita ba tare da kowa ya sani ba ta ce
Ammie ta ba ni nan da end of the month na cire mijin aure.
Jikin sa ya yi sanyi ya ce
"To in ba abin Ammie ba, menene abin gaggawa har da yanke lokaci, kuma ma abin damuwar shine babu tsayayyo balle ki zaɓa, amma ba komai zan yi magana da Daddy.....
A'a Ammar mafita zamu nema ba wai sanar da Daddy ba, faɗa masa ba abin da zai haifar sai rashin hankali dan tunkarar Ammie zayyi da maganar kuma kasan baya son wannan magana, mu dai nemo wata hanyar.
"Okay, ba damuwa ban nan da zuwa gobe zan samo mafita"
Sun jima suna fira sannan ya tashi ya fice zuwa ɗakin shi, ta miƙe ta faɗa toilet ta watsa ruwa ta yi shirin kwanciya sbd fita aikin safe, bayan ta kammala addu'ar bacci ta shafe dukkanin jikinta, ta kwanta.
WASHEGARI ____ A nutse ta kammala shirin tafiya wajen aiki, bayan ta gaida Ammie kuma ta sanar da ita zata wajen aiki ta fito, ɗan sahu ta hau dan Ammar na bacci, tana isowa ƴan night na shirin tafiya, ta shigo office na ta, ta ciro duk abin da za ta buƙace shi anjima ta ajjiye kan teburin, sannan ta kunna system ɗinta, sai jin ƙarar abu kamar ya faɗo daga waje, da kuma hayaniyar tafiyan ƙafafuwan mutane, ikon Allah duk da bata da shiga abin da bai shafe ta ba, amma sai ta tsinci kanta da son ganin meyasa ake wannan sintirin, a hankali ta buɗe ƙofar ganin ana fidda kaya daga cikin office na Dr Aliyu yasa ta yi mamakin hakan, me hakan yake nufi Dr Aliyu zai bar office ɗin,......
"Dr Hamrah"
Ta juyo ta kalli nurse Laraba iyayen gulsy, ta ce
Ya aiki.
Nurse Laraba ta ce
"Sai godiya woo, yau mun tashi da wani lamari mara daɗi, kin ga wai Dr Aliyu za ayi wa transfer"
Cike da mamaki Hamra ta ɗago ta kalli Laraba tare da cewa
Transfer kuma?.
"Eh haka na ji MD ke faɗi"
Sauke numfashi Hamra ta yi, wato ta wannan hanyar MD ya ɓullo amma ba damuwa, she knows what to do.........
Comments and share
[1/10, 19:31] SAYYADA ✍️ Barrister: *MUJARRABI*
By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA
09021706569
PG 5 & 6
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_______ Buɗe idanuwanta tayi a hankali a daidai lokacin da ake kiran assalatu ta asubar farko a nan masallacin dake layin unguwar su, da ƙyar ta sauko daga kan bed duk tsawon baccin da tayi amma ji take bai isheta ba duk jikinta yana mata ciwo, sbd gajiyar tafiya da dawowa ta wajen aiki da take yi. Tana shiga cikin toilet ta watsa ruwa bayan ta yi brush ta ɗauro alwala ta fito ta sanya doguwar riga da dogon hijabi ta idar da raka'a biyu na nafila sannan tayi raka'a biyu na farillah, ta jima tana miƙa kukanta ga Ubangiji sannan tayi azkhar na safe ta ɗan taɓa karatun Alkur'ani sannan ta shigo kitchen, ta tadda Ammie na kitchen tana haɗa karin kumallo hakan ya tabbatar mata cewa Daddyn su zai yi fitan safe saboda a duk lokacin da Ammie in dai da kanta ta shigo kitchen to hakan na tabbatar wa da breakfast zata haɗawa Daddyn su dan shi in ba dole ba baya cin abinci masu aiki sai dai ko su yaran su dafa shima sama² yake ci, HAMRA na taimakon amma tun ranar da wannan al'amarin ya faru a sakanin su Ammie ta dakatar da ita daga duk abin da take yi, HAMRA na da gudun ɓacin ran Ammie shiyasa ta ke taka tsantsan da abin da zai jawo ta bata mata rai. Ƙarasowa ta yi kusa da ita cikin girmamawa ta ce
Ammie, ina kwana?.
"Alhamdulillah"
Kawai abin da ta faɗa ta ci gaba da haɗa souce ɗin kayan ciki, hamrah jiki a sanyaye ta wuce cikin store dan dubo ko da akwai abin da zata girka cikin sauki, mutum ta tayi tozali da shi jirge a gefe guda a store ɗin da alamu jiya da daddare mai kawowa Daddyn ya kawo musu, kai fitanta aiki yasa bata sanin wasu abubuwan saɓanin a da ita ke duba ƙarewar abin store ta sanar, ɗauko ɗaya ta yi ta maida hankali ta fere doyar ta sannan tafasa shi ta soya da kwai ba tare da tayi souce ba ta zuba yaji akan plate ɗin da ta zuba soyayyar doyar ta fito, dan tasan bata isa ta taɓa wanda Ammie ta girka ba, to ina ma fuskar balle ta taɓa haka ta tattaro ta dawo ɗakinta ta haɗa black tea ta sha tare da cin doyar sannan ta shirya ta fito tafiya kada ta makara. Ta shige ɗakin Ammie ta tadda Daddyn su ya shirya yana breakfast da alamu fita zayyi da ya kammala ta gaida shi ya amsa cikin kulawa
Good morning Daddy.
"Morning likita, har an fito, to Allah ya taimaka"
Ameen Daddy, eh na fito ina sauri ma kada na makara.
"Gaskiya kam yanzu lokacin gudu yake kan ka ankare ka makara"
Eh fah Daddy,
Ammie anjima da na tashi zan wuce gidan Ayshe.
"To"
Kawai Ammie ta ce, taci gaba da cin abincinta, Daddy ne ma ya ce
"Ah madallah ki gaida min da jikokai na, ko zaki jira na sauke ki ne?"
Zasu ji, a'a Daddy zan wuce ...
Ammar ne ya shigo tare da sallama bayan ya gaida Daddy da Ammie ya ce
"Ah na manta ashe kin koma morning, to tashi na sauke ki, nima fita zan yi"
HAMRA ta sauke numfashi SBD rashin sakin fuskar da Ammie ba tayi mata ba, kuma amsawar da ta yi shima saboda Daddyn su dake wajen ne a hankali ta kalli AMMAR ta ce
To tashi mu tafi kada na makara.
A tare suka fito, sun ɗanyi tafiya jim kaɗan ya ce
"Afwan bari na kira a amshi sako minti biyu Please"
HAMRAH ta soke fuska ta ja numfashi ta sauke ta ce
Kaga irinta ko, ni dama bari na kayi na hau ɗan sahu hankali na kwance, amma kawai kasa mutum ya makara.
Murmushi yayi ya ɗau waya ya yi ƙira, ya sanar da mai shi ya iso. ya juyo ya ce
"Ayi hakuri likita, ban yi bayani ba tun farko"
Bata ce komai ba ta maida kallon ga bakin titi tana kallon yadda mutane ke sintiri.
Suna nan zaune cikin motar Hamrah taji muryar mace tana
"Young Roheet how fah"
Ta ɗago ta kalleta, fara ce sol ƙirar Yaruba, tana ganin HAMRA ta ce
"Is she your sister, kuna kama sosai, hey barka da safiya?"
Hamra ta sake fuskantar ta amsa da
Yauwa, barka dai.
Ammar ya ce
"Yeah, uhm Furera ga sakon ki, tun jiya fa nake son kawo miki amma abubuwa sun sha min kaina. Ya mika mata ta karɓa tayi masa sai anjima ta tafi ya tada motar su kayo hanyar Hospital, Hamra ta ce
Young Roheet, yaushe kayi sabon suna?.
Murmushi ya yi ya ce
"Tun sunan da suka saka min jss, shine har ya bini"
To, ikon Allah wato kai fans na Roheet ne na India shine suke kiran ka da sunan shi.
"Uhm wai muna kama suke cewa"
Ta taɓe baki ta ce
Uhm ya yi kyau. To AMMAR da alamu bikin Yaruba zamu yi kenan?.
Ya sauke numfashi a daidai lokacin da yayi parking bakin gate na Hospital ɗin ya ce
"Ni bani da wata budurwa wannan itama tana cikin waɗanda zamu tafi training ne kuma tare muka kammala secondary skul namu"
Uhm to waya san muku yaran yanzu.
Murmushi yayi ya ce
"To babbar yaya sai kin dawo"
Thanks.
Ta faɗa ta shige ciki a daidai lokacin da MD shima yake parking. Kai tsaye office nata ta nufa ta buɗe ta shirya duk abin da zata buƙata sannan ta sanya white coat ta fito, taci karo da Nurse Laraba cikin sauri ta iso kusa da ita ta ce
"Dr HAMRAH, yau kina morning kenan?"
Kallon ta HAMRAH tayi sam bata son shishigi da kwainene irin da abokan aikinta to in ma ba abin Laraba ba, da bata morning duty ai ba zata ganta ba, ta ce
Eh Laraba, da akwai wani abu ne?.
"No, ba wani abu bane, daman tun jiya nake son yi miki magana ashe kina night duty shine na bari yanzu kuma na ga hango ki shine na ce bari mu gaisa kuma naji ana cewa kun sami matsala da MD wai akan ya ce.....
Sauke numfashi HAMRA ta yi cikin takaici ta ce
Laraba, mind your business. Wannan ba hali bane to menene naki a ciki in ma ya faru ai sakanina da shine.
Tana faɗin haka ta shige cikin general ward, tana mamakin gulmar ma'aikatan wannan Hospital ɗin musamman ita wannan Nurse mai suna Laraba akwai kai kawo sakanin ma'aikata. A nutse take gaisawa da patients ɗin ta jima a wajen su, sannan ta dawo office nata, Dr Aliyu ya shigo tare da sallama yana
"Good morning special Doctor"
Cikin sakin fuska ta ce
Morning doctor Aliyu, ya ƙoƙari?.
"Sai godiya kam"
Da akwai abin da kake buƙata ne?.
"Eh Dr Hamrah akwai patients nawa taƙi na duba ta shine na ce ko zaki duɓa min ita, kin san yawanci mata in ba a dole ba ba sa son maza su duba su, ita ma wannan haka taƙi"
A hankali ta katse abin da take yi a system nata ta ɗago, ta ce
A wane ward take?.
"Tana vip 3"
Ok ba matsala a tare suka fito, Dr Mahmoud yana daga bakin ƙofar office na shi ya kura musu idanu ganin su tare kuma su biyu yasa ya haɗe rai har suka ɓace wa ganin sa. Dr Hamrah ta wuce vip shi kuma ya wuce wani bangaren, tana shiga ta tadda patient ɗin ta dubata sannan ta fito ta iso office nata. Dr Mahmoud da kuma MD suna tsaye suna tattaunawa har ta iso ba tare da tayi magana ba ta buɗe office ta shige ta zauna, ta kunna system nata ta ci gaba da aikin ta. Taji an turo kofar a hankali ta ɗago MD ne ya ƙaraso ya tsaya yana karewa cikin office ɗin kallo cike da mamaki ta kallon shi mutum ko sallama ba zayyi ba da girmansa....
"Hamrah who are you?"
Ta sauke numfashi, bata yi mamakin wannan tambayar ba dan indai bak'ar magana ce ya iya yinta kuma duk yanda yaso haka yake yinta ta ce
I'm human like everyone.
"Saboda jiya nayi miki magana shine kika ɗau gaba dani?"
Ta sake kashe system nata ta ce
Subhanallah gaba kuma MD, a'a ni bana riƙe kowa a raina kuma mema zai sa na yi gaba da kai?.
Eh wato duk iya shegen sa akwai wacce ta fi shi, murmushi yayi har jajayen hakwaransa suka bayyana ya cire glass na idon shi ya ce
"To me yasa da kika ganni da Dr Mahmoud ki ka wuce ko gaishe ni bakiyi ba?"
Ta sauke numfashi ta ce
Oh i got it, nayi tunanin kuna tattaunawa ne shiyasa bana son katse ku.
Nan ma ya ce
"Hamrah i need to know more about you"
This time murmushi ta yi ta ce
I'm nobody but I'm somebody.
"What that means"
Uhm sir, nothing.
Mamaki yake yi tabbas akwai abin da take takama da shi, koma menene zai bincika ya gani sannan kuma nan da kwanaki biyu zata gane kuren ta.
Ya juyo ya fice ta ci gaba da aikin ta. Ita sam taki jinin yawan magana