Showing 54001 words to 57000 words out of 74305 words
Chapter 19 - MUJARRABI BOOK ONE BY SAYYADA BARRISTER.txt
ga faɗawa cikin wannan yanayin. Amma bazata nuna mata cewa tana tausayin ta ba yin hakan zai sake jefa rayuwar ta cikin son ci gaba da wannan harkan kuma ita gani take tana kan daidai bata da laifi yana yi ne ya jefa ta cika. Tabbas akwai yanayin da yakan zo wa mutum yarasa mafita ya rasa masu goya masa baya wajen janyo sa jiki dan a gano matsala a taimake sa wajen bashi shawara da kuma kwantar masa da hankali amma anzo zamanin ko in kula kowa kansa ya sani babu ruwan wani da wani babu taimakekeniya a sakaninsu....
"Amma pretty kinsan su mallamai ma suna faɗin gaskiya kuma cewa da akayi bakin aljani ya aureni gaskiya ne ina kallon shi cikin bacci na kuma muna mu'amala kamar mata da miji sannan kuma gashi na kasa auruwa to kinga maganar su gaskiya ce. Allah shine ya halicci mallamai kuma ya basu sani shine suke taimakon ire-iren mu matsu matsala. Mu da kike gani irin tamu kaddarar ce da man tun farko a rubuce yake sai munyi irin wannan rayuwar dan haka ki daina ɗaura mana laifi"
Ajiyar zuciya ta sauke ta sake gyara zamanta ta kalli ƴar gold sosai na wani lokaci sannan ta ce
Ƴar gold ki dawo cikin hayyacinki, tabbas faɗin bakin aljani ko bakin iska gaskiya ne, amma cewa da mallamanki su kayi akan cewa ba zaki taɓa auruwa shine kuskure sun shiga lamarin Ubangiji sun yanke hukunci, shine kaɗai yasan da cewa zaki auro ko bazaki auruba, duk tsanani yana tare da sauki duk mai hakuri yana tare da nasara. Tabbas tun kafin a haifi kowa wane bawa an rubuta kaddarar sa amma ki sani Allah na duba zukatanmu taka niyyar mu kuma ya kawo mana sauki, da bakiyi garajen yarda da abin da su Mallam suka faɗa miki ba da duk hakan bai faru ba sannan kuma ƴar gold akwai ƙarancin addu'a a tare dake da kuma tawakkali, da kin je Islamic medicine kinyi musu bayani ba zasu ce sai sunyi duba ba kawai zasu haɗa miki magunguna na ko wanne fanne kiyi amfani dashi kuma ki dace, bance na gargajiya haramun bane amma da yawa daga cikin su na kai mutum halaka kamar yadda kema yanzu kina cikin halaka, sannan ma indai har kina da wannan laruri na bakin iska hakan na nufin babu wani ɗa namiji da zai kusance ki to ya akayi su na bariki suke taraiya dake mesa bai hana su ba, kinga da ayar tambaya anan so, Please don't ever believe on that......
"Pretty kenan baza ki taɓa fahimtar hakan ba sbd baki fama da larurar ce amma ba komai bari na kawo muku abinci yanzu kam Laure ta kammala"
Murmushi Hamrah tayi ta ce
Uhm Hauwa'u ai nima ina da wannan matsalar ta jinkirin aure amma kuma rashin bibiyar diddigi da banyi ba Alhamdulillah I'm safe daga rabamin kai da za a dinga yi. To ba damuwa ina Shatun ne?.
Shatu na cen kasa tana ta kaiwa da komowa duk gidan ya gundureta tana mamakin yadda mutanen yanzu sun manta da mutuwa da kuma gamuwarsu da Ubangiji da yawa sun manta cewa akwai tsayuwar kiyama....
Shatu ki hau mana tun ɗazu nake raba ido ko zan ganki ashe kina nan kasa.
"Kun gamane mu tafi, hankalina na gida"
Murmushi Hamrah tayi ta ce
Ƙaraso mana Bestie.
Shatu ta hauro ba dan taso ba suka haura sama suka zauna a palour ta kalli Hamrah ta ce
"Da fatan an dace?"
Uhm tukuna.
"Na faɗa miki ai sunyi nesa babu wanda ya isa ya kira su waigo ɓata lokacin mu kawai mu keyi"
Bestie babu abin da tafi ƙarfin addu'a da kuma nasiha yau da gobe tafi ƙarfin wasa, kyamatarsu da zamuyi sake tunkuɗasu cikin halaka ne zamu yi, na faɗa miki ki barmin komai a hannu na. I'll handle it.
Ƴar gold, Rahama da Zee suka fito tare da ɗauke da niƙe niƙen food flask na abinci suka ajiye akan Dining area sukayi musu su taso su ci Hamrah ce ta miƙe ta iso wajen amma Shatu ko kallo basu isheta ba, Hamrah tayi hakan ne dan su saki jiki da ita, juice kawai ta shafa sannan su masu aikata irin wannan abin ba najasa bane su kawai ɓatan kai ne ya samesu da kuma rashin neman sani.
Wunin ranar a gidan Hauwa'u Jibrin su kayi ta, Hamrah ta miƙe ta shige kitchen tana kallon yadda tsarin kitchen ɗin yayi matukar kyau sai ga Rahman ta shigo ɗauke da tea cups wanda su kayi amfani dasu shine ta kawo ganin Hamrah a tsaye ta ce
"Pretty ashe kina nan, da akwai abin da ki ke so ne?"
Sauke numfashi Hamrah tayi ta ce
A'a Rahama, amma nayi mamaki da akace kina da aure kuma kina cikin wannan harkar abin da ɗaure kai to menene amfanin aurenki in dai kina son wannan harkar kamata yayi ki sauke nawin auren da kuma darajar sai ki shigo amma yin hakan kuskure ne babba.
Murmushi sosai Rahama tayi ta ƙurawa Hamrah manya manyan idanunta ta ce
"Uhm da aurena gwamma babu shi, babu macen da bazata so zama a ɗakin aurenta, rufin asirinmu mu mata shine ɗakin mazajen mu to amma kuma wani lokacin sune ke sanya mu muke aikata wasu abubuwan duk canji da za ki gani daga mace to babu tantama miji ne ya sauyata, wasu mazan suke rugurguzawa mata rayuwar su. Pretty na tsani rayuwar aure babu komai cikin sa sai tashin hankali da kuka da takaici.....
Subhanallah! Bai kamata ki faɗi hakan ba sbd aure ba abin wasa bane ta hanyar aure ne hanya mafi sauki samun shiga aljannar mace, sannan duk abin da ki kaci karo dashi a gidan aurenki jarrabawa ce da kinyi hakuri kin jure sai kiga daga karshe kece da riba amma batun munanan kalamai ga aure kuskure ne sbd aure turɓane ta bautar Ubangiji. Amma menene dalilinki na faɗin haka meyasa ki ka zaɓi wannan hanyar baki nemi wata ba shin ina mijinki da kuma ƴaƴanki?.
Jan ɗaya daga cikin kujerun dining table dake kitchen Rahama tayi ta zauna tare da cewa
"Have a sit pretty, amma kuwa kinsan yadda ki ke da kyau su ƴar gold naji suna faɗi sai da nagani kuma naga ya wuce tunani na, kai gaskiya Masha Allah"
Murmushi Hamrah tayi ta ce
Rahama bani amshoshin tambayoyi na.
Sauke numfashi Rahama tayi ta ce
"Ni haifaffiyar Kaduna state ce, ban taɓa zuwa Maiduguri ba ban san ya take ba aure ne ya kawo ni zan iya cewa sanadiyyar aure ce na san Maiduguri. Soyayya ce mai karfi sakanina da Ahmad yana matukar kaunata sai dai a lokacin bashi da sana'a tsayayya a shogon wani yake ma'ana a karkashin wani yake aiki, haɗuwarmu a sali a facebook ce kuma karon farko da soyayya ya tunkare ni kamar da wasa yaje garin Kaduna muka haɗu, to tun daga lokacin muka sake kulla dankon soyyayya mai karfi, sai kuma maganar aure ta taso amma iyayena suka ce ba zayyu na aure shi ba nayi nesa da gida sunyi sunyi su rabamu abin yaƙi. Daga karshe dai suka amince amma da sukaji a karkashin wani yake suka sake cewa ba zayyu ba, ina ƴar gidan masu kuɗi na auri talaka kuma wanda bashi da tsayayyen sana'a dan haka ya ƙara gaba. Kuka na dinga yi musu har suka amince aka ɗaura aure da ƙyar aka samu aka kawo ni dakina shima ni na biya kuɗin kawowa dan na rufa masa asiri, ɗaki ɗaya ya kamamin sauran kayana aka koma dasu dan sun fi karfin gidan, ban damu ba haka na hakura har na haihu diyata ta fari ni nayi suna to haihuwa mai albarka albarkacin haihuwa ya samu shima ya buɗe shago a kasuwa ya dogara da kansa har ya kaiga muka samu muka tashi daga wannan daki dayan muka koma ciki da palour ya samu ya canja min kaya, muna lallaɓa rayuwar mu har muka sami ƴaƴa hudu. Alhamdulillah hankalina ya kwanta zuwa wancan lokacin aka daina goranta min. Kasuwarsa ta sake habbaka har ya gina mana dankareren gida flat, a lokacin da muka koma na haifi ɗiyata ta biyar. Daga nan rayuwa ta sauya na daina gane kan Ahmad kwata kwata baya son ganina na sha matukar wahala wajen hakuri da kuma janyo hankalinsa kaina, da ƙyar na samu nayi hakan.
Sauke numfashi Rahama tayi tare da zubda ƙwalla a lokacin da ta tuno da tashin hankalin da ya faru da ita ta ce
"Watarana da yammaci ya shigo min da luggage riƙe a hannunsa na miƙe cikin girmamawa na karɓa ina ƙoƙarin shigewa dashi ciki sai nayi la'akari da wacce ke shigowa ta ƙaraso tare da gaidani na amsa tare da cewa bakuwa mu kayi, ya ce eh "bakuwa ce" nayi mata isowa ciki na bata ruwan sha ta sha ya bata ɗakin da yake bama amfani dashi, sai cikin dare yake sanar dani cewa ƴar baffansa ce sunyi hutun skul tana karatu a unimaid za tayi kwana biyu sai ta wuce Ummah sa ta sani. Nan na hau hidima da ita har tsawon 1week to ganin yadda take sakin jiki dani yasa nima na saki raina tana taimaka min sosai. To bayan kwanaki biyu sai naga Ahmad na yawan tashi daga bacci cikin dare ya fice tun hakan bai damuna har ya fara kwasam rannan sai nace zanga me yake yi, yana fita na tashi nabi bayan shi abin da ya bani mamaki shine ganin ya doshi ɗakin wannan yarinyar da ake kira da Fateemah, kamar zan bi bayan sa kuma na fasa na dawo ɗakina na kwanta cike da mamakin me ya kaishi ɗakinta ina cikin tunanin naji ya shigo a lokacin awansa 1 da rabi, kamar zan tambaye sa amma nayi shuru. Gari ya waye na fara observing nasu sai kuma nake fahimtar wani abu na daban yana yawan kallonta su sakarwa juna murmushi, a daren ranar na ce kai sai naga me suke nufi ne kuma me suke ƙullawa na, yana fita da 10 minute's nabi bayansu. A hankali na tura kofar abin da naci karo dashi ne ya gigitani kusan 5 minutes brain nawa ya daina aiki jikina da a lokacin za a saga dako ba za a sami ko da ɗigon jinine na matukar kaɗuwa, ina karanta kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun, sannan na fara dawowa daidai. Mijina kwance kan ruwan cikin Fateemah suna aikata zina a gidana a kuma ɗakina da kuma gadona, wata zuciyar ta ce na watsa musu ruwan zafi. Wata kuma ta ce na kashe su na huta, amma kuma da ikon Allah na sake daurewa na fito cikin tashin hankali na komo ɗakina ina ta sake² cikin raina na irin matakin da zan ɗauka, sai kuma wani tunani ya faɗo min na cewa in kuma sun san nasan me suke aikatawa suka kasheni fah suke ɓarayi ne suka shigo, to in dai Ahmad zai shigo da dadironsa cikin gidana babu abin da zai hanashi kasheni...
Ina cikin wannan tunanin ne ya shigo ya wuce toilet ya watsa ruwa ya shirya ya dawo ya kwanta ganin idanuwana biyu yake tambaya ta me ya hanani bacci kamar na shake sa ya mutu amma na daure na bashi amsa da eh. Washegari na shirya na ce ta rakani muje gidan iyayensa amma fir ya ce bazata je ba sai dai ni kaɗai na tafi, nan na gama fahimtar komai sai na shiryawa mahaifiyarsa da ƙannensa waleema na ce suzo ba tare da ya sani ba, kawai kwasam sai yaga sun diro cikin gidan ......
"Hamrah magrib ya kawo kai ya kamata mu tafi"
Cewar Shatu ta katse Rahama da labarin da take baiwa Hamrah wacce tayi suman zaune da jin wannan labari, ta sauke numfashi cikin sanyin jiki ta kalli Shatu ta ce
Gani fitowa.
Shafu ta koma Hamrah ta ce da Rahama
Zan dawo nan da kwanaki biyu sai ki ƙarashe min.
"Ba komai a gaida gida"
Hamrah ta amsa sannan ta fice zuwa palour. Nan su kayi musu sallama suka fice akan sai zuwa nan da kwana biyu zasu dawo Hamrah suka dawo Shatu ta wuce gida.
_Bayan kwanaki biyu_
Hamrah ce tsaye bakin titi tana jiran ɗan sahu zata shopping na mayyukan gashin kanta, daman sunyi waya da Shatu akan zata biya mata su wuce, har ta tari ɗan sahu kuma sai ga kiran Abuja ya shigo tayiwa mai a daidai yayi hakuri ya tafi da hannu tayi masa alama, ta koma gefen hanya ta ɗauka tare da sallama ya amsa ya ce gashi zuwa gidansu ta sanar dashi tana hanyar tafiya shopping ya ce ta jirashi nan ta sake sanar dashi ya bari zuwa gobe zata wuce gidan ƙawarta Shatu amma ya nace sai yazo haka ta hakura yazo ya ɗauke ta suka wuce gidan su Shatu, ta kallesa ta ce
Bari na shiga sai mu fito ko?.
Kai ya gyaɗa mata alamun to. Ta shige ciki suka fito da Shatu cikin girmamawa shatun ta gaida shi ya amsa cikin fara'a tare da cewa
"Yauwa yau na haɗu da kawar matata wacce zamu dinga shawara game da bikin"
Murmushi Hamrah da Shatu suka yi shatun ta ce
"Aiko nima nayi farin cikin haɗuwa da mijin bestie nah"
Suka shige motar ya tada ta yake tambayar su wane shop suke son zuwa nan Shatu ta sanar dashi amma kuma sai ya kaisu wani babban shop a tare suka shigo sukai siyayya ya dinga jido musu kaya kamar babu gobe, suka fito bayan ya biya ya riga su fitowa tare da wani ma'aikacin wajen ya taimaka masa ya fito musu da sauran kayayyakin. Shatu da Hamrah na ƙoƙarin fitowa sai su kayi kicibus da su yar gold, cike da mamaki Zee ta ce
"Aminai an fito siyayya kenan?"
"Uhm fah Zee kuma ku kayi balle kuma mu"
Bata fahimci abinda Shatu ke nufi ba Hamrah ta ce
Da mutum muke tafe kada ya jiramu yaga mun daɗe.
Juyowa suka yi lokaci guda, suna kallon motar cike da mamaki ƴar gold ta ce
Kamar nasan wannan motar............
Comments and share
*MUJARRABI*
By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA
09021706569
PG 41 & 42
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_________ Kallonta Hamrah keyi tun da ta shigo ta ganta ta soma bala'i bata ce komai ba sai dai tayi mamaki a ina taji zancen za tayi aure ita Hamrah ba wasu kawaye ne da ita ba ballantana zancen aure ya bayyana kuma ba wasu ƙannene da ita ba waɗanda za a ce su suka yaɗa sbd yarinta, ƙannenta duk sunyi aure kuma ba masu yawan yawace² bane. Bata so ƴar gold ta san da zancen aurenta ba tafi son ayi sa cikin sirri har ta kammala abin da take so cikin kwanaki kaɗan amma ba komai ko a hakan ma tasan za tayi nasa ko bajima ba zasu gano gaskiya su dawo kan turɓa madaidaiciya. Ta sauke numfashi a daidai lokacin da ƴar gold ta ƙaraso ta zauna ta tsareta da idanuwanta ita a dole anci amanar ta, murmushi Hamrah tayi ta ce
Ƴar gold, sannun ki da gajiya ban ma jima ba da shigowa, Rahama ke faɗa min kina hanya....
"Dakata Hamrah ki fara bani amsar tambaya ta wai shin da gaske this week za a Daura aurenki?"
Sauke numfashi Hamrah tayi ta ce
Eh Hauwa'u abin da ma ya kawo ni kenan...
"Ba wani pretty daman cen da wata manufa a ƙasa, yaudarar mu ki ke son yi, in ma ita ce to ki sani ko da aurenkinne ma za ki ci gaba da wannan harkar"
Uhm.
Cewar Hamrah, Zee ta ce
"To ai daman tasan da hakan kawai dai auren da za tayi a matsayin kariya ce daga idon al'umma"
Rahama zaune duk jikin ta yayi mata sanyi da abinda Hamrah ta faɗi mata, a hankali ta ce
"Ai aure ba matsala bane muma ai yana kanmu kuma muke harkar, zata iya fitowa ayi da ita kawai a bata sati kan cin amanar ci tana gamawa sai ta fito"
"To na ji wannan shawarar amma tunda taji sirrin mu ya zama dole ta zauna ayi harkar tare amma cewa zata bari bazata ga daidai ba"
Cewar Hauwa'u Jibrin, ita dai Hamrah bata ce komai ba, bata jima ba ta fito ta dawo gida, a ƙofar gida ta tadda Alhaji Sama'ila a tsaye a kofar gida yana gingine cike da mamaki ta iso inda yake yana ganinta ya sauke numfashi cikin sanyin murya ya ce
"Wayar ki bata shiga duk na damu, tun ɗazu nake nan na rasa wanda zan aika shi cikin gidan ya kiramin ke"
Ajiyar zuciya Hamrah ta sauke tare da ciro wayar ganin network ne ya ɗauke ta ce
Wayar a kunne take service ne ya ɗauke.
"Ok shigo mota"
Ta zagaya ta shiga suka zauna jikinta duk yayi sanyi ta zauna cikin sanyin murya ta ce
Amma lafiya ko?.
Ya juyo sosai yana kallon ta na wani lokaci sannan ya ce
"Em nazo ne na baki kuɗaɗen da zasu isheki, sannan kuma kinsan ba a garin nan zamu zauna ba a cen Abuja ne, dan haka bana son ƴan rakiya dake kaɗai zamu tafi kuma bana son tarkacen kaya ina da komai cikin gidana"
Ta sauke numfashi cikin sanyin murya ta ce
To zanje muyi shawara da yan'uwana duk yadda mu kayi sai na sanar maka....
"A'a Hamrah bana son hakan shiyasa tun farko na faɗawa maneman auren cewa bana bukatar komai daga wajenku sbd bana son yawan magana ne kawai muyi maganar nan a sakanin mu, ke ba yarinya bace da zamu tsaya muna cece kuce kawai maganar ta zauna a haka"
Sauke numfashi Hamrah tayi ta ce
Gaskiya, maganar gaskiya wannan ba al'adar Maiduguri bace kamar yaya zan yanke hukunci da kaina, bayan bani ce zan aurar da kaina ba, zancen akaini babu kayama bai taso ba dole sai amin duk abinda ake yiwa ko wacce amarya. In yaso ko daga baya ne sai akai min cen ɗin. Amma menene dalilinka na son na tafi babu kaya kuma babu ƴan rakiya?.
Ganin ranta ya tsoma ɓaci yasa ya rage murya ya ce
"Shikenan ayi miki kayan, amma daga baya sai a kawo miki, bani account number ki sai na tura miki kuɗi"
To.
Ta faɗa ta bashi sannan ta shigo cikin gida bayan sunyi sallama, mai Alhaji Sama'ila ke nufi ne. Har ta shigo cikin nan ta tadda Ammie a palour tana zaune tana ta shirya kayayyakin da tasa a kawo. Zama Hamrah tayi cikin