Showing 3001 words to 6000 words out of 74305 words

Chapter 2 - MUJARRABI BOOK ONE BY SAYYADA BARRISTER.txt

18 Jan 2025

4616

ya zauna kusa da ita yana kallon ta


"Har kin kammala duba patients ɗin ne?"


Shine a bin da ya faɗa, a hankali ta buɗe idanuwanta da su kayi mata nawi ta kallesa shima ita yake kallo, sauke numfashi tayi ta ce


Dr Mahmoud are you not a Muslim, da za ka shigo babu sallama?


Murmushi ya yi ya kurawa ƙirjinta idanu yana wani zazzare su yana jan numfashi. Ta haɗe rai matuka, ta tashi ta gyara zaman ta, ya sosa keyarsa ya ce


"I did but maybe you didn't hear it amma Assalamu alaikum"


Bata amsa ba ta jefa masa tambaya


Do you need something?.


Kai tsaye ya ce


"Of course, i need you?"


Tayi shock dajin maganar amma ta dake kamar bata san me ya ce ba. Ganin haka ya taso ya kai hannunsa zai rike nata ta yi saurin tashi tsaye ta ce


Baka da hankali ne, meya haka kuma?.


Kurawa coca cola shape nata idanu yayi ya sauke numfashi ya ce


"Eh a yanzun bani da hankali amma in kin bani abin da nake nema zan dawo cikin hankalina"


Galala take kallon shi babu kunya babu tsoron Allah yake magana idanun nan a bushe suke, ta miƙe da niyyar ficewa ya yi sauri ya kai hannun ya riƙo ta ya janyo ta tare da haɗe ta da jikin garu tayi saurin hankaɗesa tare da ɗauke sa da wani gigitaccen mari cikin ɓacin rai da tashin hankali ta ce


Dr Mahmoud, ina maka kallon mutumin arziki sbd wannan gemun da ka ajiye shi a she dai na banza ne, to kasani in kana cin ƙasa ka kiyayi tashuri, get out.


Ko ɗar bayi ba ya kafe ta da jajayen idanuwan sa yana sauke numfashi ya ce


"Ni zan baki kulawa fiye da wanda Dr Aliyu yake baki, in dai iya tsarrafa mace ne na iya kuma zakiji daɗin wannan harkar"


Zuwa wannan lokacin abin ya fara bata soro what?. He thinks that, she slept with Dr Aliyu, ta ɗago da idanuwan ta da suka sauya kala sbd ɓacin rai ta ce


Think whatever you want, and God forbid na haɗa jiki da kai, ƙazami mai ƙamamin rayuwa.


Tana faɗin hakan ta ɗau wayarta, ta fice ta yi harabar Hospital ɗin tana huci, ta jima da son ajiye wannan aikin amma yau ya fi ko wacce rana fita cikin ranta, kenan zuwan da Dr Aliyu yake yi neman taimakon ta wajen sake wayar masa da kai ta wasu fannin aikin su, shine Dr Mahmoud yake tunanin ƙazamar alaka ce a sakanin su, tana nan tsaye yazo ya gifta ya wuce ko ajikin sa, ta dawo officer ta sanya key ta rufe ta koma kan resting chair ta kwanta, tana jin duk rayuwar ta fice daga ranta, bacci ya ɗauke ta.


Washegari tunda ta tashi da matsanancin ciwon kai ta tashi, tun asuba take fama dashi, haɗa kayayyakin ta tayi ta fito har ƴan morning duty sun iso suka gaisa sannan ta fito, ta dawo gida, ganin motar Daddyn ta ya tabbatar mata da yana gida, ta shigo gidan sittt babu motsin kowa, daman ita da AMMAR ne a gidan shiyasa gidan ya ke da shuru dayawa, a hankali ta tako ta iso kofar ɗakin ta har zata murɗa handle door muryar Ammie taji ta kira sunan ta


"HAMRA"


Jiki a sanyaye ta juyo tare da cewa ina kwana Ammie.


Bata amsa ba ta ce


"Yanzu wannan rayuwar kika zaɓarwa kanki, to ki sani kiji tsoron Allah ki fidda miji kiyi aure in kina so mu shirya a cikin wannan gidan, dubi kannenki duk sun yi aure sun rufawa kansu asiri amma ke kin tona wa kanbki da kuma mu asiri kina duk abinda ki kaga dama, to ki sani ba zan zuba ido naga kina yin haka ba, na baki nan da karshen wata ki fidda miji in kuma ba haka ba daga ni har ke ba zamu ji daɗin abin da zai faru ba, kin sa sai zancen ki a keyi a family da kuma unguwa kin tsaya zaɓe SBD kyawunki na ruɗan ki to ni ba zan lamun ta ba"


Numfashin HAMRA sama² ya keyi hankalin ta ya matukar tashi dajin waɗannan kalaman daga bakin mahaifiyar ta, daman shine dalilin da ya sa take fushi da ita....


"Hajjiya BATULA ba na hana a dinga wa HAMRA irin wannan zancen ba, ina mun riga da munyi magana akan hakan, mesa kuma yau ki ke tada zancen, lokaci ne bayyi ba in yayi za ayi shi kamar yadda a kayi na sauran"


Cewan Daddyn su, ya ƙaraso wajen tare da isowa wajen HAMRA cikin kulawa ya ce


"HAMRA ki shige ciki ki huta, nasan kin kwana aiki duk kin gaji Allah ya bada ladan taimakon da ki ke badawa"


Ameen.


Ta ce, ya juya ya fice, Ammie ma ta shige ciki, HAMRA ta juyo tana hawaye zata shige ciki sai ganin AMMAR tayi yana tsaye cikin damuwa yana kallonta da alamu ya ɗan jima a tsaye saurin buɗe ɗakinta tayi ta shige, a hankali ta ajiye kayan hannunta, ta fashe da matsanancin kukan da bata taɓa yin irin saba, daga jiya zuwa yau ta shiga tsananin tashin hankali sbd abinda taji kuma ta gani, fushin Ammie da kuma kalaman ta sun fi ɗaga mata hankali ina zata waiga taji sanyi ne, mahaifiyar ta ma ta juya mata baya.....




Alhamdulillah ala kulli halin.


Ina godiya ga Ubangiji da ya sake bani damar sake rubuta wani littafin, ina rokon shi kamar yadda na fara ya bani ikon kammalawa lfy.


Tafiyar wannan littafin mai rai ce, kuma ba za kuyi nadamar karanta shi ba. Ƙunshe yake da darussa da dama, kuma zaku ƙaru da su.


Zan dinga skipping rana ɗaya na posting sbd na sami nutsuwar typing.






Comments and share[1/10, 19:31] SAYYADA ✍️ Barrister: *MUJARRABI*



By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA


09021706569




PG 3 & 4


*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*




_______Ƙirjinta yana mata raɗaɗi da zugi kamar zai fito, a hankali take sauke numfashi tana zubda hawaye, tana tuna irin rayuwa ta farin ciki da gata da ta ta yi tare da Iyayenta da ƴan uwa ta. Taso cikin gata da kulawa bata taɓa sammanin zata riski irin wannan rayuwar ba, ta ƙunci da tashin hankali. Basu taɓa ganin iyayen su sun sami saɓani da juna ba sai akanta, kuma wannan duk yana faruwa ne saboda rashin auren da batayi ba, da farko anyi ribibin fitowa neman aurenta amma sai kuma daga baya shuru babu wanda ya ce yana ma sonta balle kuma a je ga zancen aure, har aka aurar da ƙannenta....


"HAMRA"


A hankali ta ɗago ta kalle shi, damuwa ce kan fuskar shi sosai kamar zai taya ta kuka, yana mai jin tausayin ta sosai kuma baya son ganin ta tana cikin damuwa, shi ya zame mata abokin kukan ta kuma abokin shawaranta, ganin tana kallon sa kuma tana zubda kwallah yasa ya miƙa mata roban swan water tare da glass cup, ta karɓa ta siyaya ruwan ta sha, sannan tayi ajiyar zuciya a hankali furta


Thanks.


Sauke numfashi yayi ya ce


"Kuka baya miki kyau, kin san me ki ke komawa in kina kuka?"


Ba tayi magana ba tayi shuru tana kallon sa ya ce


"Kamar shrunk"


Murmushi tayi ta share hawayenta daman abin da yake son gani kenan, ta ce


Baka fita bane?.


"Uhm sai zuwa anjima, shima saboda ana neman mu ne zamu yi meeting akan tafiya training na sojojin da muka sa gaba"


Ta sauke numfashi tare da sake zuba ruwan ta sha sannan ta sake cewa


Wacce ƙasar ma zaku je?

"ABGANISTAN"


ya faɗa yana kallon ta tare da murmushi akan fuskar sa.


Uhm ya yi kyau, Allah ya taimake ku. Ta faɗa tana ajiye roban swan water da kuma glass cup ɗin


"Ameen"


Sosai ya juyo yana kallon ta ya ce


"HAMRA, ke ki ke cewa mu koyi jure wa ko wacce irin damuwa, mu rufe idanuwan mu kamar bamu gani ba sannan mu toshe kunnuwan mu kamar ba muji ba, amma mesa ke ki ka kasa yin haka, though a baya ki nayi but this time around kuma kin saduda, kin manta cewa duk tsanani yana tare da sauki, in shaa Allahu nan bada jimawa ba komai zai zama tarihi, za ki yi rayuwar farin ciki kamar yanda kowa ke yi, Please kada ki damu da yanayin da Ammie ke nuna miki ita ma zuwa wani lokaci za ta daina"


Ta sauke numfashi a hankali ta sake cewa


Thank you AMMAR.


Ya miƙe ya fice, ita kuma ta tashi ta shige toilet ta watsa ruwa sannan ta fito ta shirya cikin doguwar riga mara nawi, ta hau kan bed tana jin yunwa ga kuma bacci da ciwon kai da take ji...


Da sallama ya shigo ya ajiye basket dake hannun shi ya ce


"Tashi ki yi breakfast, nasan ba abinda kika ci".


A hankali ta sauko tare da cewa


Kamar kasan yunwa nake ji, shiyasa nake kara son ka ɗan KANINA.


Murmushi yayi ya ce


"A'a ya kamata zuwa wannan lokacin ki barmin girman nan daman cewa a ke yi ke ƙanwarta ce"


Murmushi tayi ta ce


Ai koda girgiza kurna tafi magarya girma.


Yayi murmushi ya ce


"Ba haka karin maganar take ba, cewa a ke yi ko da girgiza magarya tafi kurna zaƙi"


Uhm nawa ne daidai.


Suna fira tana cin indomie da kwai da ya soya mata, har ta kammala sannan ya mata sai anjima ya fice, ta ɗan zauna jim kaɗan sannan ta kwanta bacci sai azahar ta farka bayan ta idar ta sake komawa bacci sai bayan la'asar ta tashi ta idar sannan ta wuce kitchen tare da duba menene akwai, gannin Uwale ta kammala haɗa stew yasa ta fere doya ta dafa sa fari sannan ta zuba a plate tare da zuba stew akai ta dawo ɗakin ta, nan ta ci tare da haɗa tea na ruwan zafi ta sha sannan ta tashi ta shirya ta fito. Ɗakin Ammie ta shige tayi mata sai da safe amma bata kulata ba, hakan yasa ta fito cikin sanyin jiki, ta tadda Daddyn su na zaune a farfajiyar gida ta iso cikin girmamawa ta ce


Daddy zan wuce wajen aiki.


Cikin kulawa ya ce


"Likita Allah ya taimaka sai kin dawo, ayi ta hakuri da sha'anin rayuwa"


To Daddy in shaa Allahu, nagode.


Nan ta fito, ta tari ɗan sahu ta wuce wajen aiki.


Tana shiga cikin Hospital ɗin ta wuce office nata, ta kimtsa duk abin da zata buƙata anjima da daddare sai ga Dr Aliyu ya shigo cikin sallama, ta amsa ya ce da ita


"Special Doctor an fito ko?"


Tayi murmushi tare da cewa


Yau kuma harda zolaya?


"Ai gaskiya ce kuma kowa ya shaida ke ƙwararriya ce ta fannin aikin ki"


Uhm to ina godiya.


Ta faɗa idonta a kan system nata, ya ce


"MD ya ce akwai zaman ku dashi bayan magrib"


Ta sauke numfashi tare da ɗagowa ta kallesa ta ce


Badamuwa Allah ya kaimu.


Matukar burge shi take SBD jarumtarta duk cikin Hospital ɗin nan tsoron MD ake amma ban da ita, ya sake cewa


"Amma bakya tunanin ko abin ya shafe abin da ya ce kiyi jiya da daddare kuma...


Dr Aliyu ni in dai a kan gaskiya ta ce ko ina a kaini, meyasa kuke tsoron sa shifa ɗan Adam ne kamar kowa sannan kuma kowa yana da right na kare kan shi so, banga wani abin tada hankali ba, I'm waiting for the hours.


Ya sauke numfashi ya ce


"Well don special Doctor till we meet later, an fara kiran sallah sai zuwa anjima"


Ya miƙe ya fice, ta sauke numfashi tana mamaki sauran likitoci da suke neman gindin zama a wajen MD shi da ba wani aiki yakeyi ba kawai dai yana zagoyowa ne yana taking information akan wasu abubuwan amma duk da haka suke ɓata ta a wajen sa a cen baya tayi tunanin Dr Aliyu ne amma da tayi bincike ta tabbatar likitoci mata ne ke kai masa gulmanta shiyasa ta share su baki ɗaya indai ba sha'anin aiki bane ya haɗasu to bata shiga tsabgarsu, jin ana kiran sallah yasa ta miƙe ta shige toilet ta ɗaura alwala ta fito ta idar sannan ta wuce office na MD tana isowa ta tadda sa yana waya a waje ta shige ciki ta zauna har ya kammala ya shigo cikin girmamawa ta ce


Afternoon sir, an ce kana nemana.


Ya cire white eyes glass dake idonsa ya ajiye sa kan tebur dake gaban sa ya kuramata jajayen idanuwan sa na wani lokaci sannan ya ce


"Jiya saƙo na ya iso ki ko bai riske ki ba"


Kai tsaye ta ce ya riskeni.


Ya sauke numfashi ya ce


"Kinyi yadda na ce ko kuma kinyi abin gaban ki?"


Ta sauke numfashi tasan yaji labarin komai kawai yana so ta tabbatar masa ne ita kuma baza ta yi ƙarya dan ta kare kanta ba ta ce


Ina da patients waɗanda na ke kulawa dasu, kuma na yi musu alkawarin cewa zan basu kulawa har su sami lfy, shiyasa na fara duba su sannan na duba.....


"Who the hell you are da zakiyi abin da ki ka ga dama dake da patients ɗin ai duk a karkashina kuke, daga yau muddin na ce ayi abu kika sauya to ki sani dole ki bar wannan Hospital ɗin, kina ganin tafiyar ki zai sauya komai ne, we'll work even without you, sai me dan kinga OG yana yabon ki shine ki ke wani ganin kan ki kin fi kowa, to ki sani banga wanda ya isa na saka doka ya karya ta ba a duk faɗin duniyar nan"


Sosai ta rumtse idanuwanta SBD tsawar da ya daka mata, ta tsani ayi shouting mata akai, nan take take gigicewa, hankalinta ya tashi kuma ranta ya ɓace bata san lokacin da ta miƙe tsaye ta nunasa da yatsa ba ta ce


I'm not a young girl, kada ka sake min ihu, a kan wane dalili kake faɗa min waɗannan maganganun? da kake cewa zaka koreni ɗin ai ba kai ka bani wannan aikin ba sai dai OG ya koreni ko da kuwa zan bar wanna aikin, to ka sani ba ta dalilin ka ba, kai kan ka kasan abin da kayi bai dace ma, ta yaya muna aiki domin ceto rayukan al'umma zaka ce a barsu su sha wahala kai a duba naka, wannan ba adalci bane.


Tana kaiwa nan ta fito tabarsa baki sake yana mamakin ta, lallai HAMRA bata san waye shi ba, tana dai jin labarin shi ne, amma soon za ta sani. Tana shiga office kanta ya soma tsara mata saboda ihun da yayi mata, maisa MD bashi da imani ne, kowa yana complain na shi a bayan idon sa akan irin zaluntar mutane da yakeyi. Ta sauke numfashi ta shige toilet ta ɗaura alwala ta idar da sallah ishai sannan ta wuce duba marasa lafiya yau kam ta daɗe a wajen su, mutanen MD kuma Dr zalihat ce ta duba su, HAMRA sai kusan 1:00am ta dawo office ta saka key ta rufe kofar sannan ta kwanta.


Da safe ta tashi a makare ta gaggauta isar da sallah ta ɗau jakarta ta fito har ƴan morning duty sun iso, bayan sun gaisa ne ta fice kasancewar safiya ce ana wahalar abin hawa saboda kai yara makaranta, hakan yasa HAMRA takowa zuwa bakin titi, tana tsaye tana jiran abin hawa amma duk wanda yazo wuce wa sai taga cike yake da mutane. Har ta gaji da tsayuwa ta yanke shawarar ko ta sake yin gaba ne sai taga wata bak'ar mota jeeb mai liƙe da bakin glass ta tsaya kusa da ita, kau da kai gefe tayi kuma take shirin barin wajen taji an ce


"Wa nake gani haka kamar HAMRA pretty kece?"


Jin muryar mace ce yasa ta tsaya tare da juyowa ta kalle ta cike da mamaki ita ma ta ce


Hauwa'u Jibrin! Kina wannan duniyan?.


Aiko ba shiri ta fito daga cikin motar ta tana cewa


"Wata sabon gani inji Hausa people, HAMRA pretty ashe zan sake ganin ki, rabo na da saki cikin idanu na tun a secondary School fa, from where?"


Uhm Hauwa'u daga wajen aiki nake.


"What?.


Ta faɗa tana koƙarin gyara parking na motar ta fito sannan ta ci gaba da cewa


"Aiki daman ana aiki ne a wannan zamanin ai zuwa aiki ɓata lokaci ne, yanzu da wannan kyawun naki ki ke aiki"


Uhm kina nan kamar yanda na sanki, daman an ce in dai ka jima baka haɗu da mutum ba to kada ka tambayi halinsa saboda hali zanen dutse ne baya taɓa kanza wa, to in ba abin ki ba Hauwa'u in dai banyi aiki ba me kike so nayi?"


"Shigo cikin mota na ƙarasa dake gida sai mu ƙarasa gaisawa".


A tare suka shige cikin mota da mamaki HAMRA ke kallon ta, ganin ita kaɗai ce a cikin motar yasa ta ce


Kin kai kids naki skul ne?.


Dariya Hauwa'u tayi sosai tana tuki ta ce


"Ki jiki wai na kai yara makaranta, ni da ko auren ban yi ba, ina na ga yaran?"


Cike da mamaki da kuma tausayawa HAMRA take kallon ta ce


Ayya ki ce duk jirgi ɗaya muke.


"Don't tell me HAMRA pretty wai da gaske ba kiyi aure ba duk da wannan kyaun naki, to ina ga mu kuma munana"


Uhm Hauwa'u ai shi aure ba wai kyau ko rashin sa yake dubawa ba lokaci ne, abin da yasa na tambaye ki ko yara ki ka kai skul shine ganin ki da nayi da wannan motar.


Murmushi Hauwa'u tayi sosai ta ce


"Har yanzu a gidan ku na da ku ke?"


Eh a nan ne.


Cewar HAMRA tana kare mata kallo, sanye take da doguwar riga ta habaya baƙa ta yane gashin kanta da gyallen duk da ma tulin kitson Attachment da tayi duk ya baje mata a baya hakan yasa gyallen habayar kasa rufe kanta, farcen yatsun hannayen ta sun sha janfarce, da kuma zobe, ga kuma bleaching da tayi sosai duk fuskar ta fita hayyacinta. Sauke numfashi HAMRA tayi a daidai lokacin da suka shigo layin su Hauwa'u ta ce


"Ni ina Shatu, What i mean Aishatu Muktar?"


HAMRA ta buɗe kofar motan ta fito saboda parking ɗin da Hauwa'u tayi a daidai kofan gidan su ta ce


Shatu tana nan fah amma yanzun tayi tafiya.


"Ikon God kai rayuwa! SUCH IS Life, did she get married?"


No, ita ma har yanzu like us.


Kurawa HAMRA idanu Hauwa'u tayi na wani lokaci sannan ta ce


"To a zaman ki yanzu haka me kike yi ne bayan aikin nan, i mean kina da wanda yake ɗebe miki kewa ne ko kuma in ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login