Showing 51001 words to 54000 words out of 74305 words

Chapter 18 - MUJARRABI BOOK ONE BY SAYYADA BARRISTER.txt

18 Jan 2025

4624

zan wuce wajen aiki.


"To wannan sai kin dawo sai mu cigaba da lissafin abubuwan da za a siyo to in ba abin surkin nawa ba yaushe zamu ɗauki yarinya mu bada babu kayan ɗaki ai ba zayyu ba sai munyi"


Galala take kallon Ammie rabonta da taga tana fara'a yau kusan 2yrs kenan...........








Comments and share






*MUJARRABI*




By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA


09021706569


PG 35 & 36




*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*




_________Sauke ajiyar zuciya Hamrah tayi tare da gyara zamanta ta kalli Ammie wacce ke cikin farin ciki kamar wacce akayiwa bushara da gidan Aljanna, mamaki take ganin lokaci guda ta sauko daga fushin da take yi da ita, daman rashin mijin aure ne tunda ko ta samu komai ya wuce. Ta dau alkawarin zama a ɗakinta koman yaya ta tadda zata jurewa duk rayuwar da zata sinci kanta a gidanta indai hakan zaisa Ammie farin ciki, a hankali ta ce


Ammie ba sai mun zauna munyi list na komai tare ba kiyi duk abinda ya dace nima yamin.


"A'a jeki wajen aiki kin tunda da yamma zaki dawo in yaso zuwa dare sai muyi magana, ai wani abin sai anji ra'ayinki kowa da irin zaɓin sa ballantana ku ƴan zamani da son kyalele ai sai ku kuka san abinku"


Sauke numfashi Hamrah tayi ta ce


To Ammie sai na dawon sai mu tattauna.


"A dawo lafiya"


Hamrah ta miƙe ta fito, tunowa da tayi da ta manta da snacks ɗin da zata kai wajen aikinsu na sanya ranan bikinta yasa ta koma ɗakinta ta ɗauko su kamar yadda ta kulle na kowanne su cikin lada. Ta iso kamar yadda ta saba batayi late ba yasa ta wuce cikin office nata ta ajiye jakarta ta ɗauko white coat nata ta sanya sannan ta ɗau wayarta da kuma ledan snacks ɗin ta fito ta riski Nurse ta bata nata ta faɗa mata an sanya ranar bikinta, aiko da jin haka ta karɓa ta dinga bin office by office tana rabawa nan da nan zancen sanya auren Hamrah ya karaɗa Hospital masu mata fatan alkhairi nayi masu zancen ƙasa² ma nayi, tana zaune a office nata Dr zalihat ta shigo ta tadda ta zaune tana danne dannen wayarta ta ɗago sbd sallaman da tayi ta amsa tare da sakar mata murmushi ta ce


Dr zalihat ke da kanki sannunki da zuwa.


Murmushi tayi ta ce


"Eh fah na ce wannan abin farin cikin yakamata na taho takanas ta Kano nazo na sanya alkhairi. Na tayaki murna Allah ya nuna mana lokacin"


Murmushi Hamrah tayi ta ce


Nagode sosai Dr zalihat.


"Ba komai, amma dai da fatan bazaki bar aiki anan ba ko da bayan kinyi aure"


Murmushi Hamrah ta sake yi ta ce


Yanzu dai bana ce komai ba, dan babu tabbacin anan garin Maiduguri zan zauna amma da zan ci gaba da aikina da yafi amma sai yanda yayu.


"To masha Allah, Ubangiji yayi maki zaɓi na gari, muma da zaki zauna da munyi farin ciki"


Sun jima suna fira sannan ta tafi, Dr Hamrah na zaune Dr Aliyu ya turo kofar ya shigo cikin farin ciki ya ce


"Special Doctor sai naji labari mai daɗi, kai na tayaki murna sai ko gashi dani dake duk a sanya lokacin bikinmu"


Murmushi tayi ta ce


Eh fah haka Allah yake al'amuran sa nima lokaci yayi.


"To Allah ya sanya alkhairi, ya nuna mana lokacin"


Amen.


Sun ɗan tattauna akan aikinsu da zasu gudanar a ranar sannan ya fice. Yamma nayi Hamrah ta soma shirin tafiya gida amma kuma sai tunani ya faɗo mata zata biya gidan Zeenat ta dubata sannan ta wuce gida. Turo ƙofar Dr Mahmoud yayi ya shigo cikin sanyin jiki yayi sallama ta amsa ba tare da ta juyo ba tana ƙimsa files ɗin da suke kan teburin taji ya ce


"Da gaske ne abin da naji ake cewa akan an sanya ranar bikinki?"


Barin abin da take yi tayi ta juyo tana kallonsa yadda yayi maganar cikin sanyin murya kamar ba shi ba ganin duk tashin hankali ya bayyana akan fuskar yasa tayi mamaki ta ce


Dr Mahmoud, nurse Laraba bata baka snacks ɗin bane?.


Takowa yayi dab da ita ya zuba mata jajayen idanuwansa yana kallon fararen idanuwanta yana sauke numfashi akai akai ya ce


"Ba abin da nake son ji ba amsa kawai zaki bani eh ko a'a?"


Eh.


"Dan meyasa sbd kinga an sanya ranar Dr Aliyu shine ke ma ki kayi hakan sbd ki huce haushin cin amanar ki da yayi ko ko yaya?"


Murmushi tayi sosai tana kare masa kallo anya Dr Mahmoud yana kalau kuwa, ta sauke numfashi ta ce


Dr Mahmoud ba zaka taɓa ƙanzawa ba, sannan ni banga dalilin da zan tsaya inayi maka bayani ba sbd ba zaka taɓa fahimtar komai ba, kawai abin da zan iya cewa think whatever you want.


Ta ɗau jakarta tana ƙoƙarin fitowa yayi saurin tare ta ya tsaya yana huci ya ce


"Dr Hamrah amma kinsan ina sonki kuma ina son na aureki kawai ina so na baki time ne zuwa wani lokaci na faɗa miki, amma ban san kina son kiyi aure yanzu ba da na fito cikin manema ki"


Uhm Dr Mahmoud, i need to go Please mu bar wannan maganar bata da amfani yanzu.


"Dr Hamrah please don't leave me, i really love you"


Ganin Dr Mahmoud da gaske yake kuma ya dage sai ta fahimce shi yasa ta ajiye jakarta akan resting chair ta ɗago tana kallon sa, duk da bata san so ba, bata san raɗaɗinsa ba amma kuma ganin yanayin da Dr Mahmoud ke ciki ta tabbatar yana sonta, a hankali tayi magana cikin rage muryar ta ce


Dr Mahmoud ai ban san kana so na ba kuma kaima kayi jinkirin sanar dani kuma kaga babu an sanya ranar bikina kuma kasan nema cikin nema haramun ne, dan haka inayi maka fatan ka sami wata kaima kayi aure.


Kamar zayyi kuka, idanuwan sa sunyi ja dasu, shi kanshi bai tashi sannin soyyayyar ta tayi nesa cikin zuciyar sa ba sai cikin kwanakin nan yana jin sha'awar ta ne a cen baya amma bai taɓa tunanin zai faɗa a tarkon sonta ba, to yanzu ya zayyi dole ya hakura amma yasan zaiji jiki.....


Dr Mahmoud bye, till tomorrow morning.


Ta fice ta barshi nan tsaye ta tsaya a ƙofar office ɗin ya jima sannan ya fito ya wuce office nashi ta rufe office nata har zata juya sai taji muryar MD yana kiranta. Ta iso cikin office nashi cikin girmamawa ta ce


Evening sir.


Ya sauke numfashi ya ƙarashe tauna ragowar goron dake bakinsa ya ce


"I heard you are going to be a Bride, what was the month"


Uhm, yes sir at the end of this month.


"Uhmm so good, amma dai ba irin na wankan karon za ayi ba a taramu kuma a watse ba tare da an ɗaura ba, ki sake dawowa bakin aiki bayan kinyi sallama da kowa"


Ɗagowa tayi ta kallesa bata ce komai ba, ya cigaba da cewa


"Za ki cigaba da aikin ne bayan kin yi auren ko kuma za ki sauya wani aikin?"


I don't know.


Ta bashi amsa a takaice ta ɗaura da cewa


Zan wuce.


"Okay"


Ta fito tana mamakin MD da son abin duniya ya kwallafa rai akan wannan aikin kamar ba zai mutu ba. Tana fita ta iso gidan Zeenat cikin murna ta tare ta suka gaisa ita kaɗai ce a gidan ta kawo mata baby ta bata suna ta fira sai da aka kira magrib sannan ta miƙe ta shirya ta ce zata tafi gida. Kallon Zeenat tayi cikin sanyin jiki ta ce


Zeenat tambayar ki nake son yi?.


"Yaya Hamrah ina jinki"


Sauke numfashi tayi ta ce


Wacece baaba Hajara?"


Cikin sauri Zeenat ta dago tana kallon Hamrah bakin ta na rawa ta maimaita


"Baaba Hajara?"


Eh ita, shin kinsan inda zan sameta ne?.


"Uhm amma meyasa ki ke son saninta, kuma ina ki kaji ana ambaton sunanta?"


Zeenat tayi mata tambayar da Daddynta yayi mata to hakan na nufin Zeenat tasan wacece Baaba Hajara dan haka ta ce


Zeenat kada ki ɓoyemin komai tare muka taso cikin gida ɗaya kinsanni na sanki kinsan bazanyi abinda ba zai zamo daidai ba Please tell me ina zan ganta?.


"Uhmm yaya Hamrah baaba Hajara ta jima da rasuwa nima a bakin Aunty maimuna naji suna firar amma maganar gaskiya basan dangantakar da take da ita damu ba amma kuma yadda naji suna firar ta na tabba tana da mahimmanci cikin wannan familyn"


Sauke numfashi Hamrah tayi tana jinjina lamarin to baaba Hajara ta rasu to meyasa da ta ambaci sunan ta gaban Daddy hankalinsa ya tashi kuma meyasa bai sanar da ita ta rasun ba, ta kalli Zeenat ta ce


Please do me a favor, i need to know more about her.


Ta sauke numfashi ta jinjinawa Hamrah kai alamun to. Sukai sallama Hamrah ta fito ta dawo gida ta shiga ta tadda Ammie na sallah ishai ta wuce ɗakinta sai bayan ta idar da sallah ta fito ta wuce ɗakin Ammie ta tadda tana cin abinci nan ko Ammie ta sata saida ta ci suna fira suna ci sai da suka kammala sannan ta dawo ɗakinta tana jinta wasai cikin farin ciki, a hankali ta furta


Alhamdulillah.


Bacci yayi awun gaba da ita cikin farin ciki komai ya kusa zamowa karshe, itama tayi aure ta zauna a ɗakinta kamar yadda sauran yan'uwanta suke.


_After 1week_


Auren Hamrah saura 3 weeks, sai shirye shirye ake yi su Ayshe da Zeenat kam ba zama duk rabi da kwatan siyayya su sukai mata su ce ta sayi abu kaza yana da kyau ita dai sai dai ta basu ATM nata suyi duk abin da ya kamata, tana fita aiki kamar yadda take yi Alhaji Sama'ila ma na zuwa zance ya koma.


Kasancewar yau weekend ne ta shirya cikin doguwar riga ta habaya ƴar Dubai ta matukar yin kyau a cikin ta, royal blue ne ta fito bayan tayi sallama da Ammie ta wuce gidan su Shatu inda suke da zama ahalin yanzu daga nan suka wuce address ɗin da ƴar gold ta basu. Suna isowa suka kirata a waya ta ce su shigo aiko baki da hanci suka sake suna kallon cikin gidan a lokacin da gate man ya buɗe musu karamar kofa ta shigowa. Wannan shine aljannar duniya, danƙararren benine mai hawa uku wanda yaji ginin zamani, faɗi tsarin gidan da kuma kyaun sa ɓata lokaci wata ce ta fito cikin shiga ta mini skirt tayi musu jagora ciki, jikin Hamrah yayi sanya tun kafin ta ƙarasa ciki ta tabbatar wa kanta cewa faɗa da aljani baya sauki, lallai sai ta dage sannan ta samu ta showa kansu dan kam sunyi nesan da baza suji kiraba giyar kuɗi ta gama mamaye jinin jikinsu....


"Pretty barkanku da isowa bismillah ku ƙaraso cike"


Cewar Hauwa'u Jibrin, sauke numfashi Hamrah tayi daga zurfin tunanin da ta shiga, suka hau makalan da Hauwa'u ta bi suka yi tattaki har zuwa babban palour dake sama, suka zauna Zainab ta fito cikin farin ciki ta rungumi Hamrah zata rungumi Shatu amma ta ƙi ko kallon ta Shatu ba tayi mai kyau ba ta ɗauke idanuwan ta, ita ko Zee ko ajikinta ta zauna nan ta bada umurnin akawo musu abin taɓawa. Rahma ma ta fito suka gaisa ta zauna nan suka taɓa fira suna basu labarin yadda kungiyar su ta sami ci gaba, daga bisani ko wacce tayi ciki ya rage daga Hamrah sai Shatu da kuma Hauwa'u Jibrin, Shatu ta miƙe ta sauko sbd ta baiwa Hamrah damar shawo kan ƴar gold, sai ke numfashi Hamrah tayi ta ce


Ƴar gold wannan arziki haka na innalillahi wa inna ilaihi rajiun, daga ina ki ka samu sa kuma gidan nan na waye ne?.


Murmushi ƴar gold tayi tare da tashi daga inda take zaune ta zauna kusa da Hamrah ta ce


Ai wannan ƙaramin gidane daga cikin gidajena na nan Maiduguri ina dasu sunfi biyar sai kuma waɗanda nake dasu a wasu garuruwan, a jinki kuɗin da nake samu almubazzaranci nakeyi dashi a'a kadara nake ajiyewa sbd tsaro basan me zai faru nan gaba ba"


Murmushi Hamrah tayi ta sake cewa


To Hauwa'u batun aure fah?.


"Uhm aure ai na wuce age na aure wa zai aureni kawai cigaba da harkan nan zan yi zuwa wani lokaci naga ya hali zayyi"


A hankali Hamrah ta ɗaura hannunta kan na hauwa'u ta ce


Hauwa'u Jibrin aure baya taɓa wucewa kuma bai kamata ki cire rai ga aure ba domin shi lokaci ne da lokacin yayi za ayi amma batun shekaru age is just a number, ko kin kai shekaru 50 za ki iya aura indai lokacin sa yayi, amma kuma menene dalilin ki na buɗe wannan kungiyar kuma nasan kina da tabbacin cewa abinda ki ke aikatawa kuskure ne....


"Hamrah kin zo muyi harkan nan tare ne ko kuma kinzo bincike"


Murmushi Hamrah tayi cikin kulawa ta ce


I need to know more about the ƙungiyar sbd nasan ta yadda zan fara.


"Uhm yanzu naji batu. First and foremost, i came from the poor background family, we don't have anything, infact sometimes or somedays zan iya cewa muna wuni bamu ci abinci ba, ke ma shaidace sai nayi sati ina zuwa skul ba tare da na kashe ko 5naira ne ku ne ma kuke taimaka min na ɗan saka wani abin a bakina, muna cikin wannan rayuwar ce muka zana jarabawa ta zuwa senior set, da ƙyar na na wuce kuma a lokacin ne mahaifiya ta rasu, na sake sintar kaina cikin tashin hankali ga ƙannena mata har su uku kuma dukkanninmu mata ne, kawai sai Abbanmu ya ƙara aure, da farko muna zaman lafiya har na kammala secondary School nawa a lokacin ƙannena duka uku suka sami mijin aure, ya saura ni kaɗai na rage nan fah babu mashinshini gashi bani da kuɗin da zan ci gaba da karatuna, nan fah nake fuskar fitina kala daban daban na matar ubana har ta kaiga ta shiga sakanina da mahaifina tsam ya tsaneni, damuwa tamin yawa na nemi shawarar wata ƙawata da muke kawanci irin na unguwa haka tana da aure an unguwar tamu, shine ta bani shawara muje wajen mallamin da yayi mata aiki har ta sami mijin aure. To zuwanmu karon farko yace bakin iska gareni kuma ya aureni bazai bari nayi aure ba dan haka ni da aure har abada. Da farko na karaya amma kuma daga baya na sake ce mata inda wani takaini shine ta kaini wajen wani shi kuma ya ce matar ubana ne ta tura min iskar, kuma ya ce zan auro amma ba nan kusa ba. Na hakura na zauna na zubawa sarautar Allah ido, ga tashin hankali da nake fuskata a gidanmu ta wajen Abban da kuma matarsa har ta kaiga bata bani abinci gashi ba wata kwakkwaran sana'a ce dani ba, na lalace kamar wacce tayi jinya ta shekaru 2 haka dai na dinga lallaɓa rayuwa ta kwasam watarana da bazan manta da ita ba, ina zaune a gida akace ana sallama dani, na fito sai ganin wani mutum ne a tsaye muka gaisa nan take sanar dani yana so ne nayi masa hanya na haɗashi da wata ƙawata da take gaba da layinmu to ban san komai ba a tunanina neman aurenta yake nayi mishi hanya suka fara soyyayya kawai tashin farko ya bani kyautar 100k na kiɗime sbd ganin kuɗin, na boyesu ban nunawa kowa ba na dinga amfani dashi a hankali ina cefanena wasa² sai ko abin ya fara girma sai sumin magana da abokan sa ni kuma na haɗasu suna bani kuɗi daganan abin ya koma sana'a lokaci guda nayi kuɗi ni ke juya gidan da Abbana da matarsa suka koma yimin biyayya nan na sake musu bakin aljuhu daga nan kuma sai ko na daina zama a gida ni ma na faɗa a harkar sbd shi wannan mutumin ne ya fara lalata min rayuwa ya buɗe min ido nasan me duniya take cike, to daga lokacin na fara fita outside anan na haɗu da Zee muka sake kulla abotar da muka fara a secondary School shine muka buɗe wannan kungiyar ta taimakon mata da suke fama da irin tamu matsar minti nesa cikin wannan harkar sannan muka haɗu da Rahama muka sake habbaka abin amma ita Rahama matar aure ce"


Shuru Hamrah tayi tana kallo da kuma saurari abin da ƴar gold ke faɗi, itama Hamrah take kallo ganin ta zuba uban ta gumi ta cire tare da cewa


"A wannan yanayin ki ke tunanin zan sami mijin aure tab da wuya shiyasa ban taɓa tunani ba balle kuma na saka yuwar hakan cikin raina"


Sauke numfashi Hamrah tayi tare da ɗaura hannunta kan na Hauwa'u ta ce


Hauwa'u waye ne ya halicce ki?.


Cike da mamaki ta ce


" Allah mana"


To waye kuma ya halicci su mallamai ko ince bokayen da ki kabi suka ɓatar dake, dole nace bokaye mallamai magadar annabawa ba zasu taɓa faɗin hakan ba sai dai su dauraki kan hanya mai kyau ta yadda zaki bi har ki rabo da dukkanin cutar da take damunki amma ace ba zaki taɓa aure ba har abada bacin akwai aya cikin Alqur'ani da take cewa Allah bai saukar da cuta ba sai da ya saukar da maganin ta. Babu cutar da bata da magani, ɗaukan su waɗannan bokayen da ki kayi a matsayin kin yarda da su shine ki ke ganin ba daidai ba sbd Allah baya ɗaurawa bawansa abin da ba zai iya ba da kin jure kin miƙa al'amuran ki gareshi da kinga kyakkyawar ƙarshen KADDARAR ki...........




________________________
Ina matukar godiya da addu'oin ku. Kada ku manta har yanzu muna cikin shimfiɗa ne na wannan littafin mai suna MUJARRABI (Age is just a number) asalin labarin na gaba ku dai ku biyoni dan jin abubuwan da ya kunsa. Littafin book 1&2 ne muna dab da ƙarashe book 1 in shaa Allahu.


A dinga hakuri da typing errors, bana samun time na gyarawa.


Comments and share






*MUJARRABI*


By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA


09021706569


PG 37 & 38




*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*




__________ sauke numfashi Hamrah tayi ta kalli Hauwa'u cikin damuwa da kuma tausayawa labarin rayuwar ta itama shaidace na ganin irin rayuwar wahala da kuma tashin hankali da Hauwa'u ta fuskanta a lokacin da suke secondary School, duk da a makarantar kuɗi suke wato private skul dan a lokacin marigayiya ummanta ke biyan kuɗin makarantar, tana da tabbacin bayan mutuwar uwar ne ta faɗa cikin ƙuncin rayuwa mai tsanani har ya kaita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login