Showing 30001 words to 33000 words out of 74305 words

Chapter 11 - MUJARRABI BOOK ONE BY SAYYADA BARRISTER.txt

18 Jan 2025

4628

dawo sai ya bata mamaki, itako ko a jikin ta tayi addu'ar bacci ta kwanta tana mamaki yanda yara maza ke aure a wannan zamanin.


_After 2days_


Zaune ta ke a office ɗinta tana ƴan rubuce-rubuce, sbd so ta ke ta yi arranging komai kamin ta tafi huta da zata yi na 2 days kasancewar daren Thursday night duty ne da ita, ta samu ta kammala ta miƙe ta sanya su cikin loker ta rufe sannan ta ƙimsa kan teburin. Turo ƙofar Dr Mahmoud ya yi ya iso tare da sallama ta amsa ba tare da ta kalleshi ba ya matso inda ta ke zaune ya zauna kusa da ita har tana iya jiyo bugun zuciyar shi, cike da mamaki ta ɗago ta dubeshi ya zuba mata ƙananun idanuwan shi da suka sauya kala, ta ce


What these means, ka sakani gaba kana kare min kallo?.


Ya sauke numfashi tare da damƙo hannunta ya riƙe shi gam cikin nashi yana fidda numfashi on on ya ce


"Bazan iya jure sha'awar da na ke ji a kanki ba, ina son kasancewa dake kuma a daren yau kuma ya zama dole ki bani haɗin kai"


Zuciyarta ta buga cike da tashin hankali ta ke kallon shi, tana tantama abu yasha baya cikin hayyacin shi, tayi saurin ƙwace hannun ta amma ya haɗa duka biyu ya damƙe su cikin hannu ɗaya, ta yadda bazata iya kwacewa ba, hannu ɗayan kuma ya kai ƙan botton na rigar da ya soma cirewa, zara idanuwana ta yi a lokacin da taga ya ɓalle bottonan idanuwan shi sun yi jajir dasu jikin shi ya soma rawa cikin rawar murya ya ce


"Ke kaɗai na ke muraɗi, kuma ke ce wacce zata kashe min ƙishirwar da nake ji yanzu, please kada kimin gaddama nasan kin san komai kawai ni ne ba ki so amma ina mai tabbatar miki cewa sauran samarinki suna suka tara da ƙin ji salona zaki......


Jikin Hamrah na rawa tsoro ya rufe ta sbd bata taɓa kasancewa da namiji ba cikin wannan yanayin, da ƙyar ta tattaro karfinta ta hankaɗe shi ta miƙe tare da nufo ƙofar hannunta na rawa tana ƙoƙarin buɗewa ya yi saurin isowa ya rike ta tare da janyo ta ya haɗata da jikin garu yana sauke numfashi ya ce


"You do like baki san na miji ba alhalin kin san komai kuma....


Tasssss, ta wanke shi da mari da ya sanya shi saurin dafe wajen ta nuna shi da yatsa ta ce


Kayi kaɗan Mahmoud, kuma ka yi ƙarya ɗan iska ka kawai mara mutunci, think whatever you want amma ba zaka taɓa samuna ba.


Duk da jakircewar ta ya tsorata ta, ta dau wayar ta tayi sauri zata bar wajen ya biyota zai chapke ta aka turo ƙofar cikin sauri ta yi hanyar fita Dr Aliyu ganin hakan yasa ya matsa mata ta fice Mahmoud kuma ya tsaya suna kallon juna yana sauke numfashi, cike da mamaki Dr Aliyu ke kallon shi ya jefa nashi da tambayar


"Me ka ke shirin aikatawa?. Are you out of your mind, fyaɗe za ka yi mata"


Dariya Dr Mahmoud ya ce


"Rape, with who?. Bayan kuna sheƙe ayar ku tare shine za kace zan yi mata fyaɗe, gwada sa a ta naƙe"


Hankali Dr Aliyu ya matukar tashi ya ce


"Gwada sa'ah, hakan yana nufin ƙarya kamin ranan da ka ke cewa kasanta, kenan sharri kayi mata?"


Ya isa. Ku fice min daga cikin office, kada ku ƙara shigo min.


Cewar Hamrah tana tsaye daga bakin ƙofar, saka botton na rigar shi ya yi cikin sanyi jiki ya fice, ta sauke numfashi tare da dafe kanta bayan ta zauna


Special Doctor, ki yi hakuri da abin da na faɗa miki ranan nan, ban san cewa sharri ya yi miki ba.....


Please Dr Aliyu ka tashi ka fice, bana son jin komai da kai dashi duk halinku daya ne, tunda kunyi tunani iri ɗaya a kaina.


"A'a Dr Hamrah kada ki haɗani da wancan fasukin, na yi miki hakanne a rashin sani ki ya fe min"


Ta sauke numfashi tare da cewa


I need to be alone, please go back to your office.


Ya miƙe tare da sauke numfashi ya fice. Hamrah ta girgiza da abin da ya faru sakanin ta da Dr Mahmoud tabbas yana cikin maye ne amma za tayi maganin shi da zaran ya dawo hayyacin shi, har ta kwanta bacci ya ɗauke ta. Gari na wayewa ta shirya ta fito sbd da tafiya ta rufe office nata ta wuce office na Dr Aliyu wanda MD ya kwace kuma ya maida mashi abin shi, ta turo ƙofar ta shige ta tadda shi zaune shima ya kammala shirin tafiya ganinta yasa ta muƙe tare da cewa


"Barka da safiya?"


Barka dai, zan tafi sai Monday zan shigo.


"To likita Allah ya nuna mana, amma lafiya ko?"


Lafiya.


Kawai ta faɗa tare da ajiye mashi wasu document ɗin ta fice. Kai tsaye ta dawo gida ta shige ɗakin Ammie ta gaidata a lokacin ma Daddy ya shigo suka gaida ya ke ce mata


"Likita yau za ki tafi gidan Ayshe ko, to ayi ta hakuri fa kada kuyi abin da za ayi ta magana akai, Allah ya yi albarka"


Amen Daddyn, mun gode.


Ta miƙe ta dawo ɗakinta ta faɗa toilet ta shirya sannan ta fito daman kayanta a haɗe ta ɗauko tana ƙoƙarin fitowa Ammar ya shigo ganin haka yasa ya ce


"Zuwa ina kuma naga ko hutawa ba kiyi ba?"


Ta sauke numfashi tare da cewa


Yauwa taimaka ka fitar min, sai ka nema min ɗan sahu ina sauri jirana suke.


Kallonta ya yi sbd ganin yadda ta ke magana kamar da ɗan 15 yrs wai ya je ya kira mata ɗan sahu, ya ɗauki kayan ya fita dashi ta bi bayan shi sai gani ta yi ya sanya cikin motar shi, ta ce


Kai ni za kayi da ka kiramin dan ɗan sahu, kai kam Allah ya shirya kana na miji baka son wahala.


Bai ce komai ba ya koma ya dauko kayan dake ɗakin Ammie daman ta ce zai kai anjima kawai zai haɗa su tafi tare. Ya fito ya tada motar ya kalleta tare da girgiza kai ta ce


Me kuma?.


"Ba komai, nima daman ina son zuwa gidan Ayshe"


To sai muje ai.


Ya ɗan juyo ya kalleta itama ta ɗago ta kalleshi ya sakar mata da murmushi ya ce


"Kamar kina cikin damuwa, akwai abin da ya faru ne a wajen aiki?"


Daram ƙirjinta ya buga da ta tuna da abin da ya faru da ita daren jiya. Bazata sanar dashi ba dan kuwa zai aikata mashi abin da ya taɓa aikatawa shekarun baya dan haka ta ce


Ba komai, ciwon kai ne.


Ya sauke numfashi ya ce


Ciwon kai, ciwon kai always shine amsa, anyway bakomi.


Sai da suka biya suka yi wa yaran siyayya sannan kai tsaye suka wuce gidan Ayshe.......














Comments and share








*MUJARRABI*






By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA




09021706569


PG 19 & 20




*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*




__________ Da ƙyar ta ke iya fidda numfashi tana sauke ajiyar zuciya on on zuciyarta na yi mata zafi sai gumi ta ke haɗawa, tana jin kanta na tsara mata zazzaɓi na neman rufe ta cikin ƙanƙanin lokaci. Ta juya tare da jan blanket ta rufe jikin ta tare da rumtse idanuwanta waɗanda suka kasa fidda kwallah sbd damuwa, a kullum sai tayi tunanin meyasa hakan ke faruwa cikin rayuwarta, yaushe zata ji ta cikin farin ciki kamar yanda kowa ke ji, yaushe iyayenta zasu daina faɗa a kanta, yaushe za a koma cikin farin ciki irin na rayuwar baya, yaushe, yaushe, yaushe?. Amma da ta tuna cewa ko wane bawa da irin ta sa jarrabawar sai taji sanyi cikin ranta, duk abin da ya yi farko yana da ƙarshe kuma duk tsanani yana tare da sauki kamar yadda bata taɓa zaton zata riski wannan lokacin ba haka bazata cire sammanin samun sauki nan gaba ba.


"Hamrah"


A hankali ta buɗe idanuwanta sbd jin muryar Ammar da ya ƙira sunanta, ta haɗiye damuwar ta tare da sauke numfashi ta fito da fuskar ta tare da ɗan kishingiɗe jikin bed ta ce


Ammar, na yi tunanin ka kwanta ai, shiyasa nima na kwanta sbd gobe Monday kuma morning duty gareni.


Ya sauke numfashi sosai ya ke kallonta, duk da tana ɓoye damuwarta kada ya gane amma tun shigowan shi ya riga da ya gane sannan yaji abin da iyayensu suke cewa, ko shi kanshi baya son irin yadda su keyi, sun daina jituwa da juna zaman lafiyar ma yanzu ba sosai suke yin ta ba, abin damuwar ma shine yanda Ammie ta ke ɗauka hot akan maganar, babban tashin hankalin shi shine tafiyar da zayyi ya bar Hamrah, yasan za tayi ta shiga damuwa gashi kuma zayyi nesa da ita babu mai kwantar mata da hankali. Ya sauke numfashi a hankali ya ce


"Ban kwanta ba ina chatting ne muna online meeting, muna gamawa ne na ce bari nazo sbd ɗazu kin ce kina son magana dani"


Ta kwakulo murmushi dole tare da cewa


Ammar, shin menene laifina akan zaɓar Alhaji Sama'ila da nayi, meyasa ka ke ganin bai dace na zaɓe shi ba, shin akwai abin da ya faɗa maka ne?.


Ajiyar zuciya ya sauke tare da kura mata idanuwa na wani lokaci yana jin tausayinta yasan tana yin wannan ne saboda ta sami kulawar Ammie ta samu ta sauko su koma daidai kamar yadda suke a cen baya har ake ƙiransu da ba a shiga sskaninsu sbd yadda suke shawara da juna koman Ammie Hamrah. Sai dai ya fi sha'awan ta aure saurayi ko da wanda ya ja shekaru ne amma Alhaji Sama'ila girma ya gama bayyana a gareshi yasan dududu ba zai ƙara shekaru goma kan nashi ba a duniya, a hankali ya yi magana cikin sanyin jiki


"Hamrah, farin cikin mu shine kiyi aure, kema ki sami farin ciki kamar kowa, ba wai bamu son Alhaji Sama'ila bane a'a ba haka bane, kamar yadda Daddyn ya ce babu wanda yasan asalin shi, sannan ba a san sana'ar shi ba, ba zayyu a dauke ki a bashi ke ba, ba tare da anyi bincike akan shi ba, bai ce min komai ba sannan bai bani amsar tambayoyin da na yi mashi ba kawai ya girgiza kai ne wanda i don't know what that means shine na ji shakku akan shi, amma kuma in dai zai aure ki ya baki farin ciki muna maraba dashi"


Ta sauke numfashi tare da tashi ta zauna ta naɗe ƙafafuwanta ta ce


Ga dukkan alamu mutumin kirƙi ne, sannan in kayi duba da lokaci guda ya ce yana so na da aure hakan ya nuna kamilalle ne, sannan next time idan ya zo zan tambaye shi labarin shi kaga zamu sami duk amshoshin mu.


Ya sauke numfashi ya ce


"Allah shi kyauta, me ki ke so na kawo miki zan fita bakin hanya na dawo"


Ta fahimci baya son maganar ne shine ya sauyata, ta ce


Ni bana ma sha'awar komi duk abin da ka siyo ka kawo ina so sai dai amma abin ya zamto mara nawi.


"To shikenan sai na dawo"


Ya miƙe ya fice, ta sauke numfashi ta shiga zancen zuci daman haka sha'anin aure yake da zaran an fara zancen yin sa sai an sami tangarɗa amma baza ta bari wannan damar ta wuce ta ba ta ɗau tsawon shekaru tana jiran irinta, ai kuma duk wanda ya ce yana son ka kuma yana son haɗa zuri'a da kai to ya fi wanda zai ce ba ya son ka..... Ringing wayar ta tayi tana duba ba sai ganin Abuja ta yi yana ƙira ta ɗauka tare da sallama ya amsa tare da cewa


"Likita bokan turai in ban nemeki ba ke baza ki neme ni ba, shariyar ta yi yawa"


Ta yi murmushi ta ce


Yau na wuni da ɓaki shiyasa ban samu sukuni ba sai yanzu shi ɗin ma kwanciya na yi sbd na samu na miƙe.


Ya sauke numfashi ya ce


"Ni dai nasan har yanzu ban sami gurɓi cikin zuciyar ki ba"


Murmushi tayi ta ce


A'a ba haka bane, na faɗa maka uzuri na.


"To shikenan ranki shidaɗe, da fatan kina lafiya?"


Alhamdulillah.


Suna fira Ammar ya shigo jin da Alhaji Sama'ila ta ke wayar yasa ya ajiye mata ledar bai ko waiwayo ya sake kallon inda ta ke ba ya fice abinshi, ta yi murmushi tare da girgiza kanta suka ci gaba da firar su, yake sanar da ita gobe zai wuce Abuja zayyi kwana biyu kafin nan ya dawo ta ce dashi Allah ya kiyaye hanya su kayi sallama ta buɗe ledar ta ci gashashiyar kazar da ya siyo da fresh milk sannan ta kwanta.


Tun da ta farka sallah asubah bata koma ba ta hau shirin tafiya wajen aiki tea da bread tasha ta ɗau jakarta ta fito ɗakin Ammar ta yi nocking jin shuru yasa ta turo kofar ta shiga sai ganin shi ta yi yana Sallah ta duba a gogo a lokacin 7:00am, ya sallame tare da juyowa ya kalleta tana zaune bakin bed ya ƙarashe addu'o'in shi sannan ya ce


"Good morning likita?"


Ta sauke numfashi ta ce


Ammar yaushe ka daina sallah asubah kasan kuwa karfe nawa yanzu?.


Ya sauke numfashi tare da cewa


"Makara na yi jiya ban kwanta da wuri ba"


Ammar ai ya kamata ka sanya Alarm, Kai ba yaro bane da za kayi ta bacci sai lokacin da kaga dama ka tashi ka idar, sannan ko yaro ma an fi son ya dinga yinta har ta shige jikin shi amma gaskiya ka gyara hakan ba daidai bane.


Ya sauke numfashi ya tashi ya iso kusa da ita ya zauna ya ce


"Na gaidake baki amsa ba"


Lafiya ta kalau, Please ka dinga tashi da asubah kana sallah akan lokaci.


"Na faɗa miki makara nayi amma zan gyara"


Wannan ba hujja ba ce kace ka makara amma tunda kace zaka gyara that's good. Sallar asubah itace mafi alkhairi fiye da Bacci, ka rage bacci don ka ribanta da goben ka.


Bacci amsawar zuciya ne ita Kuwa sallah amsawar kiran Ubangiji ne.


Shi bacci mutuwa ne ita kuwa sallah rayuwa ce.


Shi bacci hutu ne na gangar jiki sallah kuwa hutu ne na ruhi.


Bacci da mumini da kafiri duk suna yinsa ita kuwa sallah musulman kwarai sune kadai ke yinta.


Masu tashi lokacin ketowar alfijiri sun rabauta, fuskarsu kuma ta haskaka, goshinsu kuma yayi Haske da Kyalli, lokacinsu kuma yayi albarka, idan kana cikinsu toh Ka godewa ALLAH da Ya Fifita ka, Idan Kuwa baka cikinsu toh Ka roki ALLAH Ya saka Cikin su.


Farillarsa {Sallar Asuba} zata Saka ka Acikin Kulawar Ubangiji


Sunnarsa (Rak'ataanil fajr) tafi Duniya da abinda ke cikin ta.


Ita sallar asubah da Mala'iku masu aikin dare da Mala'iku masu aikin safe duka suna halartar ta, kasani duk wanda ya rayu akan wani aiki toh akansa zai mutu, wanda ya Mutu kan wani aiki kuma akansa za'a tashe shi.


Jikin Ammar ya yi matukar sanyi, ko shi bai ji daɗi ba da ya tashi a makare amma ba ɗabi'ar shi bace ya ce


"Na gode da tunatar dani da ki kayi, har kin shirya ko?"


Eh bari ma na wuce kada na makara.


Ya miƙe tare da yi mata rakiya suka fito, ya koma ita ta wuce ɗakin Ammie ta same su da Daddy suna faisa sannan ta fito ta wuce wajen aiki, baya ta ɗan a daidaita ya sauke ne tashigo ganin yanda ake kai kawo yasa ta tabbatar da sun ji labarin OG zai shigo tayi murmushi a ranta ta ce duniya ba gaskiya ba zasu yi aiki sakanin su da Allah ba sai dai suyi dan mutum, Allah shi kyauta. Ta buɗe office ta shige tare da fito da duk wasu abubuwan da zata buƙata tana cikin hakan ne Dr Mahmoud ya shigo.


Ɗauko white coat nata ta yi tare da sanya white eyes glass ta ɗau wayar ta tare da sanyata cikin aljuhun rigar tana ƙoƙarin fitowa ya yi saurin riƙe ƙofar ya hanata fitowa ya ce


"Amma ai kin ga shigowa ta shine zaki fice wannan bai dace ba"


Ɗagowa ta yi tana kallon shi da fararen idanuwanta ta ɗan waro su ta ce


Dr Mahmoud i think you have nothing to do, so bani hanya na je na duba patients ɗina lokaci na tafiya.


Ya sauke numfashi yana kallon pretty face nata ya ce


"Yaushe zaki daina min wulakanci, sbd kinga na damu a kanki ne ki ke min haka, to ki sani badan MD ya haɗa mu muyi aiki tare ba, ba ki isa ki wulakanta ni ba"


Murmushi Hamrah tayi ta ce


I need to go.


Ya ɗan matsa ta buɗe kofar ta fito tare da ce mashi


Zan kulle ƙofar.


Ya fito ta rufe ta kama hanyar tafiya general ward shi kuma yana biye da ita har suka shigo tare suka duba so ya rigata barin wajen ita kam ta jima sannan ta dawo, zata shige ciki ne taji muryar MD ya kirata ta shigo tare da gaidashi ya amsa ya ce


"OG zai shigo nan da 30 minutes so, you should get ready with the all records, if possible ma i have to see them before ki kai mashi ko ki faɗa min me da me yake buƙatar"


Ta sauke numfashi a ranta ta ce, tasan wannan abin ne ya kai Dr Mahmoud office nata ɗazu ganin basu sami wani kwakkwaran dalili bane yasa ya yi kiranta da kanshi ta ce


Sir, akwai abubuwan da zan sake dubawa bari na tafi.


Ya buɗe jajayen idanuwan shi ya zuba mata ya ce


"In kin kammala ki kawo na gani"


To.


Ta faɗa sannan ta dawo office nata, a nutse ta fiddo su ta shiga dubasu kamar yadda ta keyi nan ta shirya komai ta kammala tsarawa ta ji ana nocking ta bada izinin shigowa Dr Laraba ce ta ke shaida mata OG ya iso an hallara a ɗakin meeting ta fito in ji MD, ta ce da ita tana fitowa.


A nutse ta fito ganin office na Dr Mahmoud da MD a kulle yasa ta sauke numfashi tare da furtawa


Thank God.


Ta iso a lokacin OG ma ya shigo ana gaisawa ta gaida shi, sanye yake da suit baƙi koman shi baki hatta eyes glass dake idanun shi ma baƙi ne, yana da haske ba cen ba ya cire glass ɗin ya ce


"Dr Hamrah lafiya kalau ya kokari"


Alhamdulillah sir.


Ta ajiye mashi komai ta ɗan kalli MD shima ita yake kallo sabar haushi kamar ya shaƙo ta badan OG ne ya ƙirashi ba da ko sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login