Showing 6001 words to 9000 words out of 74305 words
masu ɗebe miki kewa"
HAMRA bata fahimci zancenta ba ta ce,
I didn't get you, what do you mean by that, though zan iya cewa aikina kaɗai yana ɗebe min kewa.
Murmushi Hauwa'u tayi kai tsaye ta ce
"Zaki ce bakya harka da namiji duk tsawon wannan shekarun naki, kina wane ɓoye zancen ai yanzu komai a fili ake yinsa, ba a ɓoyewa saboda abin ya zama ruwan dare gama duniya, kuma rayuwar yanzu kowa nemawa kansa mafita yake, kowa ta kansa yake dan haka feel free muyi magana"
Tsayuwa da kyau HAMRA ta yi tana sake karewa Hauwa'u kallo sai yanzu ta fahimce ta, ta ce
Hauwa'u kenan, wannan kwatakwata baya daga cikin tsarin rayuwata, dan banyi aure ba shine zan zubar da mutuncina, ina har abada ko da zan dauwama a hakan ba zan taɓa zubar da tarbiya ta ba da kuma darajan gidan mu ba kuma bazan saɓawa mahaliccina ba, to ita kanta rayuwar yanzu kayi daidai ma ya ka kare ballantana bakayi ba, kin ganni nan ko saurayi bani dashi.
Dariya sosai Hauwa'u tayi tare da ɗaukan goran faro water ta kai baki ta sha sannan ta ce
"HAMRA pretty kada ki mai da karuwa ƴar iska mana, yanzu zaki ce dani ke VIRGIN ce ina, bazan taɓa yarda ba"
Ran HAMRA zuwa yanzu ya fara ɓaci ta fara tantama kan Hauwa'u Jibrin anya ba ƙazamar rayuwa ta keyi ba da take cewa ita ba cikakkiyar mace ba ce, ta san dai duk macen da zata faɗi hakan akan ƴar uwar ta mace to hakan yana nuni da ita ba mutuniyar kwarai ba ce gani ta ke yi abin da ta keyi ne kowa ma nayi, cike da mamaki HAMRA ta ce
Hauwa'u, ni na yarda da kaina, dan haka bana tsoro ko shakka dan wani zaya min mummunan fahimta kuma naji haushi, to ke kuma fa kina nufin ke ba cikakkiyar mace ba ce?.
Murmushi Hauwa'u tayi ta fito da bunch na dubu ɗari guda biyar ta nunawa HAMRA tare da ce mata
"Ɗazo kin tambaye ni akan wannan motar da nake cikinta, ita dai wannan motar ɗaya ce daga cikin motaci na wanda ALHAJI GONI ya bani, sannan yanzu ma daga wajensa nake a hotel muka kwana shine ya bani wannan 500k ɗin nasha ruwa a hanya bayan ban da wanda ya turamin ta account, ire-iren su suna da yawa ke har outside muna fita tare da shi, kai da duk wanda ya nemi yin hakan ina shanawa ta, duk abinda matar aure take yi nima ina yinsa to naga ai wannan normal ne, damu da matan auren duk ɗaya muke.
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, shine abinda HAMRA ke furtawa cikin tashin hankali ta ce
Amma ko Hauwa'u ba kiyiwa rayuwar ki adalci ba, kin cuci rayuwar ki, babu haɗe sakanin kwaɗan rama da zogale, ko ni nan wahala na fiki sau dubu ballanta kuma matar aure. Kiran da zan miki shine har yanzu da sauran lokaci za ki iya tuba ki dawo cikin rayuwa mai kyau ki tsafta ce zuciyar ki.....
"Heeeee HAMRA pretty, do you mean za ki ce min baki san namiji ba har yanzu, bazan taɓa yarda ba. To ki sani wannan rayuwar da nake yi bata karewa bace haka kurum ina cin duniya ta da tsinke baza ki kamin cikas ba, in kina so hanya buɗe take zan iya haɗaki da irin namijin da kike burin samu a rayuwar ki, haka kurum ba zaki sa nayi 2 zero ba, ni banyi aure ba kuma ban san na miji ba har na mutu kai ba zayyu ba, kinga tafiya ta"
Ta shige mota ta yi tafiyarta, HAMRA sabar kaɗuwa da abinda taji yasa ta juyo cikin tashin hankali ta shigo gida nan tayi kicibis da AMMAR dake shirin fitowa, ta daidaita nutsuwar ta dan kada ya fahimci wani abin tasan da ya sani zai dameta da tambayoyi da SBD ganin tana cikin damuwa, ta kwakulo murmushi ta ce
Ina zuwa da safen nan?.
Yayi murmushi cikin kulawa ya ce
"Kin manta ne ina shirye shiryen barin Nigeria, ko da shike tsufa ya fara kamaki, ba dole ki tuna ba"
Tayi dariya ta ɗan bugesa a kafaɗar sa ta ce
Kai kasani, girma dai na fika, to Allah ya taimake ku, zan shige ciki na huta.
Yayi dariya ya fice yana mai farin cikin ganin ta, cikin farin ciki. HAMRA na shiga ta wuce ɗakin Ammie ta taddata tana breakfast ta duka har ƙasa ta gaidata, amma Ammie ko kallon ta ba tayi ba balle kuma ta amsa mata, HAMRA ta miƙe ta fito sai taji muryar Daddyn su yanawa Ammie magana a lokacin ya fito daga cikin toilet.....
"Zamu sami matsala akan wannan abinda kike son haifarwa a cikin wannan gidan, haba hajjiya Batula sai ka ce ba ɗiyar ki ba ce kike mata haka, ya kike so tayi?.So kike taje ta ce da namiji kazo a ɗaura mana aure ko kuma so kike damuwa ta kashe ta, a wannan lokacin ne take buƙatar kulawar ki amma ki ke nuna mata halin ko in kula"
"Uhm ALHAJI na kula kai kake ɗaurewa HAMRA gindi take duk abin da taga dama shiyasa taki fidda mijin aure....
"Ya isa haka, na ce ya isa haka, kuma bana so ki sake maimaita abin da ki kayi mata yanzu"
Sauri HAMRA tayi ta shige cikin ɗakinta zuciyar ta na harɓawa, ji tayi duniyar ta fice mata a rai, ta saki kuka a hankali, tana tuna abin da Hauwa'u ta faɗa mata da kuma faɗan da iyayen ta sukai akanta, ta jima tana kuka sannan tayi bacci da yunwar da take ji, sai kusan azahar ta tashi ta idar da sallah sannan ta samu ta ci abinci ta koma bacci, har dare tana ɗaki, daman ba inda take zuwa, gidan su Shatu ne take zuwa suyi fira ko kuma ita tazo mata, tunda ta yi tafiya bata fita, daman gidan su kawai take shiga sauran duk ta fisu a shekaru sauran kuma sun yi aure.
Ta miƙe ta shige toilet ta watsa ruwa ta sanya doguwar riga mara nawi ta bacci, ta kunna ɗan ƙaramin TV nta plasma dake maƙale jikin garu daman a NTA News yake ta ci gaba da kallon labaran karfe 9:00pm, nocking akayi ta bada izinin shigowa ya shigo tare da sallama ta amsa, sanye yake da jallabiya ruwan ƙasa ƙirar Dubai, ya zauna kan carpet ya ajiye mata ledar da ya shigo da ita ya ce
"Ke kam akwai ki da son labarai, ki kanza ki kai MBC max yau akwai raceling"
Uhmm kaga Ammar kyale ni na kalli labaran duniya, in kana son kallon wasan dambe koma ɗakin ka, ka kalli duk channel ɗin da kake so, to ba za a zo fada ta ba kuma amin mulki.
Dariya ya yi ya ce
"Fira nazo taya ki fa shine ki ke korata tam akwai gobe. To gashi na siya miki roasted fish da banana juice"
Kai ƙanina kana fa ji dani sosai.
Murmushi yayi tasa hannu ta buɗe ladar ta soma ci ta sake cewa
Ka jima a waje ashe dai wajen siyayya ka wuce.
Ya sauke numfashi yana kallon News ya ce
"A'a daga station nake"
Cikin sauri ta haɗiye ragowar kifin dake bakinta ta ce
Kana nufi police station! Me kuma ya kai ka?.
Kai tsaye ya ce
"Na raka abokina Abdullahi, saboda case na ƙanin shi Sadiq"
A hankali ta kurɓi banana juice ɗin ta ce
Iko sai rabbi, me kuma ya sami Sadik ɗin?.
"Uhm wai budurwa sa ce da iyayenta suka kai ƙarar shi, shine Abdullahi ya ce na kai shi da mota ta"
Budurwa? Yanzu Sadiq har wata budurwa gare shi?. Kai wannan zamanin da abin mamaki yake, in ba karshen zamani ba ina Sadiq da wata soyyayya.
Ya juyo ya kalle ta tana cikin kifin ya ce
"Eh wai ciki gareta kuma ta ce sam na Sadiq ne"..
Aiko kifin da bai wuce mata wuya ba ta ƙware, yayi saurin mika mata robar swan water ta karɓa ta kora sannan ta ɗago ta ce
"AMMAR bana son shashanci yanzu wannan yaron Sadiq ne zayiwa budurwa ciki, kai sai dai ko wani cen ya yi mata zata ƙalla masa sharri.
Murmushi yayi tare da girgiza kansa ya ce
"Shi yayi daga karshe ya amsa, yanzu haka ma sun ce dole sai ya aureta"
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, lallai na tabbata karshen duniya yazo, a ce yaro mai shekaru 20 ya yiwa mace ciki, amma abin da mamaki yake.
Ya sauke numfashi ya ce
"Waye ne mai shekaru 20, Sadiq fa 25yrs gare shi 5yrs muka ba shi, ai wannan ba abin mamaki bane"
Ta kammala cin kifin ta ce
Kai Ammar, kai yanzu za kace 30yrs gareka, haba dai sai dai 25yrs.
Ta miƙe ta shige toilet ta wanke hannunta sannan ta fito, ta zauna tana jinjina al'amarin kai yaran yanzu da karambani suke....
"HAMRAH kina nufin I'm 25yrs to kenan ke 30yrs"
Ta hararesa ta ce
Ka jika I'm 35yrs, kana nufin zaka haɗa kanka dani.
Yayi murmushi yana kallon ta yace
"Shekaru biyar kika bani, kuma suma ai suna ne"
Ammar kenan, girman nan dai na fika, kaga bacci zanyi gobe morning duty nake dashi.
"To babbar yaya a tashi lafiya"
Ya miƙe ya fice ta gyara wajen ta kashe tv sannan ta kwanta saboda kada ta makara wajen tashin safe.
Comments and share
[1/10, 19:31] SAYYADA ✍️ Barrister: *MUJARRABI*
By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA
09021706569
PG 7 & 8
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_________Tun da na baro gida nake ta sake² cikin raina shin nayi amfani da shawarar da ki ka bani ne ko kawai na watsar nayi sha'anin gaba na. Har na iso gida na ban sami mafita ba, na tadda yaran har sun dawo daga gidan kakarsu ta uba, da akwai Uwale wacce ke taya ni aikace aikacen cikin gida, na tadda ta har ta kammala musu abinci dare kasancewar ni yawanci ban cika cin abinci da daddare ba ko da yamma ma sai dai ko da rana ko kuma da safe haka sai na yi full tank. Na yi shigewata ɗaki sai jin raina na yi yana ɓaci sbd tunowa da na yi za amin kishiya, abin da ya fi tada min hankali shine wai a ce BUKAR zai iya kwanciyar aure da wata mace ba ni ba, kai lallai na miji ba ɗan goyo bane, sai kawai na ji bazan iya kyautata mashi ba, ina nan zaune bakin bed har zuwa lokacin ina ta zancen zuci, daga bisani dai na ɗan sauko na miƙe sbd gabatar da sallah magrib, har zuwa ishai ina kan dardumar sallah sannan na fito palour na zauna. Na jima a zaune ko zanji motsin shigowar shi amma har 9:00pm shuru na dawo ɗakina na faɗa toilet na watsa ruwa kamar yadda na keyi a ko da yaushe in dai zan kwanta, sai na ji alamun tsayuwar motar shi, na sauke numfashi tare da duba agogon da ke manne jikin garun dake cikin ɗakin to 10:00pm. Alay BUKAR kamin ya ɓullo da zancen aure ana idar da sallah isha'i ya ke shigowa gida amma kuma tun da ya tsaro da zancen auren nan sai ya kai 10:00pm to 11:00pm kamin ya shigo kuma ko da ya shigo side nasa ya ke wucewa, yana watsa ruwa yake ɗaukar wayar shi ya kafata a kunne yana fira sai ya kai 2:00am sannan ya ke kwanciya. Wannan yana daga cikin abin da yasa na janye jiki daga gare shi. Jin ya turo kofar palour ya shigo sannan ya maida ta ya rufe ya wuce ɗakin shi, ina jin shi ya saka key, cen kuma na sake jin ya fito, hakan ya sa na fito a hankali dan ganin ina kuma zai je, a zaune a palour na hango shi kan 2setter yana waya, na ce to yau za ka gamu da nawa salon ƙissar, to in ba a abin ita wacce ya ke son auren ta ba magidanci na gidan shi da wannan lokacin ki kira shi ko ya kira ki, ki kuma ɗauka kina jin kan ki wai yana son ki to in dai ki ka yi wa wata to kema wataran za a yi miki. Na koma cikin ɗakina ina ta kai kawo, kawai na sake faɗawa toilet na haɗa ruwan wanka da haɗin ruwan turaruka haɗi na musamman na watsa a jikina na fito sai kamshi na ke, na wuce gaban mirror na shafe dukkanin jikina da man da na haɗa ta coconut oil and carrots, na mulke duk jikina musamman ma mazaunaina da suka fi jan hankalin shi, sannan na shafa haɗin culacham da kuma humra, na iso wajen wardrobe na buɗe ina duba wacce iriyar riga ce zan saka ta tafi da imanin shi, cen na hango wata arniyar riga wacce da ita gwanda babu, milk color ce silk da ita hannun vest ta ɗan sauko kasan mazaunaina kaɗan duk cinyoyina a waje, na sake fashe jikina da turare na cire ribon da na tufke gashin kaina dashi na baza gashin na fito na ce bari yau na yi bariki a cikin gidana, abu na halak. Ina isowa cikin palour na sauya salon tafiyata a hankali na ke tafiya tare da dan jijjiga jikina, ƙirjina da mazaunaina na ke motsa su har na iso sakiyar palour na yi kamar bangan shi zaune ba, cikin yanayi kamar na ɗan yi bacci na farka, na iso kofar palour na sa key na rufe kofar ina cewa
Uhm Uwale ko mantawa tayi bata rufe kofar ba yau.
Na wuce inda yake kwance nan ne inda makashin wutar palour yake, cikin irin na ɗan ji tsoron nan na ɗan ja da baya tare da furta
Subhanallah, ashe da mutum a wajen.
Na ɗan wani fari da idanuwana, sannan na juyo cikin sake kanza salon tafiyata na dawo cikin ɗakina, na faɗa kan bed ina sauke numfashi, ina addu'ar Allah yasa wannan tarkon ya kama. Ina cikin wannan tunanin ne naji alamun motsin buɗe ƙofar ɗakin, sai na yi saurin juyawa ƙofar baya na kwanta tare da sake turo da mazaunaina alamun na fara bacci, ya shigo tare da tsuramin idanuwa na wani lokaci a hankali naji ya ce
"Oum Ukhty"
Na taɓe baki wai tab lallai abin ya yi aiki, sai da ya furta kusan sau biyu na ɗan juyo ina wani motsa jiki tare da murza idanuwana ina
Daddyn Ukhty, lafiya da tsohon daren nan?.
Ya sauke wani irin gwauron numfashi ya ce
"Yunwa nake ji, kamar zan jure sai kuma na tuna in na kwana da yunwa ulcer ta za ta iya tashi min cikin dare, shine na ce ko zan sami abin taɓawa"
Kaɗan nayi dariya, kai na miji, Uhmm halin shi sai shi, mutumin da ya kauracewa abincina shine yanzu ya ce wai in baici ba ulcer shi za ta tashi, na ce
To yanzu dai ba abinci a ƙasa sai dai ko na ɗan dafa maka indomie na soya kwai akai da kuma tea.
Jin hakan ya sa ya matso ya zauna bakin bed ɗin ya ce
"Aiko da kin kyauta min beb.
Beb! Na furta cikin raina, lallai Alay BUKAR ba shi da dama, ganin ya zauna bakin bed yasa na miƙe cikin rangwaɗa na wuce shi na fito tare da buɗe kofar na fito har ina jin yadda ya ke sauke numfashi, ina fita na sheƙe da dariya na wuce kitchen ina ni za ayi wa iya shege. Cikin mintina kaɗan na kammala haɗa masa na jero kan trey na wuce da shi ɗakina sai dai kuma baya ciki na ajiye masa, jin shuru ya yi yawa yasa na leko ɗakin shi ko yana nufin cen ɗin zan kai mashi ina shiga ko na tadda ya fito daga wanka, cikin sanyin murya na ce
Na kawo maka nan ne ko na barshi a cen ɗin?.
A hankali ya ke kallona ya ce
"Ki kawo min nan ɗin"
Har na juyo zan fice ya kira sunana
"Ayshe"
Na tsaya ba tare da na juyo ba, ina jin shi har ya iso kusa dani yasa hannun shi ya juyo dani tare da ɗago da fuskata ya kuramin idanuwan shi da suka fara kankancewa ya ce
"Na gode, na hanaki bacci ko?"
Kamar na yi dariya amma na sake haɗe fuska na ce
To ai ba komi.
Saukar hot kiss naji kan goshina, ya sauke numfashi ya ce
"Ki kawo min kin ji"
Kai na gyaɗa na fice, ina mamakin wannan al'amarin, na ɗauko na kawo masa na ajiye mashi cikin sanyin murya na ce
Gashi nan zan wuce na kwanta.
Ya yi saurin isowa ya rike min hannu, ya ce
"Please, stay with me har na kammala"
Na ɗan wani fari da idanuwana tare da zaunawa, shima ya zauna tare da rike hannuna, ɗayan hannun shi kuma yana cin abinci shi yana kuma ƙurban tea, har ya kammala tare da janyoni jikin shi yana shaƙar kamshin jikina ya ce
"Na hana ki bacci ko so sorry beb"
Banyi magana ba, na sunkuyar da kaina ya dago da fuska sai ganin hawaye na bin kuncina a hankali ya share min cikin sanyin murya ya ce
"Ki yi hakuri Ayshe, i don't meant to hot you, kin fi kowa sanin ina son ki, bazan taɓa cutar da ke ba, ke ta daban ce, kin ji ina son ki"
Na sauke numfashi sbd nima na yi kewar shi sosai, sbd Alay BUKAR irin mazan nan ne da suka ƙware wajen iya sarrafa mace. Amma na sake turo baki na miƙe da nufin barin ɗakin ya yi saurin dawo dani ya rungume ni yana sauke numfashi cikin sauri² yana ajiyar zuciya tare da kwantar dani kan bed yana kissing ɗina ta ko ina a jikina, duk ya kiɗime yana
"Wlh billahillaza ke ta daban ce, kwal uba....
Nayi saurin manne baki na da nashi sbd ɗakin yaran na kusa da nashi kada su jiyo mu, cikin salo da dabara na ƙiɗimar dashi, yana samun nutsuwa ya koma gefe ya kwanta yana sauke numfashi, ya ɗau tsawon wasu muntuna sannan ya sake janyo ni jikin shi tare da ɗago da fuskata ya kura min idanuwana na wani lokaci sannan ya ce
"Ki yi hakuri da kin faɗa miki ƙarin auren da ban yi ba, ban san ya zaki ɗauki abin bane shiyasa nake tsoron faɗa miki, zan ƙara auren ne ba dan kin gaza min komai ba kawai zan yi ne saboda hakan yana cikin ƙaddarata, na miki alkawarin bazan cutar dake ba, kin ji beb so sorry Please"
A hankali na lumshe idanuwana