Showing 15001 words to 18000 words out of 74305 words

Chapter 6 - MUJARRABI BOOK ONE BY SAYYADA BARRISTER.txt

18 Jan 2025

4618

motar Ammar ce ke mata horn ya ɗaga mata hannu alamun ta buɗe masa, ta ce


Kai da wannan motar ta ka one door ka ke min mulki, to baza a buɗe ba.


Dariya ya yi sbd yana jin abin da ta ta ce, wani yaro ne da gudu ya yi cikin gida ya boɗe mashi ya shiga ya yi parking ya fito yana


"Likita kada ki damu da zaran na dawo daga ABGANISTAN za ki ga na siyo dan kareriyar mota"


Uhm Ammar kenan ce maka a kayi da ga dawowa za kayi kuɗi ai sai ka ci kwakwa tukuna.


Ya yi murmushi ya ce


"Ai ni da kafar dama na shiga kin san ina da babban kwali kuma certificate biyu gare ni na nan da kuma na out side kada ki yi mamaki na samu genaral"


Dariya ta yi tana nufo kofar palour tana


Su genaral manya.


Ya yi murmushi ya biyo bayan ta yana


"In shaa Allahu, duk abin da aka ce Allah an gama komai"


To Allah ya sa.


"Ameen"




ta wuce ɗakin Ammie, shi kuma ya wuce dakin shi. Tana shiga ta tadda Daddyn su na zaune ta gaida shi yake tambayar ta wajen aikin su ta ce dashi Alhamdulillah, ya ce


"Kamar na ji tsayuwar motar Ammar"


Eh Daddy ya dawo yana ɗakin shi.


To madalla ya yi kyau, shima yanzu fama yake da jama'a kin san kasuwanci sai an jure saboda har ka ce ta mutane amma kuma yana complain a kan su"


Uhm hakane Daddy sai anyi hakuri, to in ma ba abin UMAR ai harkar jama'a sai an yi hakuri balle kuma customers sai da lallaɓa"


Daddyn su ya yi dariya ya ce


"Wa Ammar ne zai lallaɓa customers ai ko cewa ya ke in dai tsari ka zo yi ka sara ko kuma kayi gaba, baya ɗukan nonsense"


Uhm gashi kuma sun kusa tafiya training.


"Eh na kammala haɗa masa duk abin da zai bukata kuɗin shi ma yana account"


Masha Allah Daddyn mun gode.


Ba damuwa ai....


Ammie ce ta shigo ta zauna Hamra ta gaidata ta amsa sannan ta wuce ɗakin ta.


Faɗawa toilet ta yi ta watsa ruwa sannan ta ɗauro alwala ta fito ta shiryar ta gabatar da sallah magrib tana kan dardumar sallah ta na lazimi aka kira ishai ta tashi ta idar yunwa ta ke ji, ta fito ta shige kitchen yau ko ruwan zafin haɗa tea ɗin ma nata dashi tana kan ɗaura ruwan zafi cikin electric cattle ne AMMAR ya shigo, ta juyo tana duba me zata dafa cikin ƴan mintina ta rasa ya ce


"Likita nima yunwa na ke ji a dafa dani"


Ba tare da ta juyo ba ta ce


To ai abin da zan girka ne ma ban sani ba.


"To ki dafa indomie mana"


Kai baya raina, kuma dole ke sa na ci, bari na duba cikin store ko na samu abin da zai kwanta min a rai sai na dafa shi.


Ta shige cikin store ta duba ganin tayi kwana biyu bata ci macaroni ba yasa ta dauko shi ta dawo dashi nan ta soma haɗashi jollof na shi, ta soma pa_boilling nashi ta zuba shi cikin matsiyaya sbd ruwan jikin ya tsami sannan ta soma haɗa souce ya ɗan ji wuta sannan ta zuba kifi da nama a ciki sannan ta juyi macaroni a kai ta yi ta juya shi komai ya haɗe ta kashe gas tana kammala shi ta juye ruwan zafin cikin tea flask ta miƙawa Ammar wanda ke tsaye yana ta santi tun kan ya ci ta abin cikin cikin food flask su ka dawo ɗakin ta, nan ya zauna suka soma ci, yana santi ya ce


"Kai da zayyu da sai ki bini mu tafi ABGANISTAN wlh"


Dariya ta yi ta ce


Kai Ammar naje nayi menene a cen.


"Uhm ki yi ta dafa min irin wannan"


Tayi murmushi, ta ce


Uhm Ammar kenan, yanzu akan abinci sai na bika cen da yake ni ce ƴar fari ko.


Dariya ya yi sosai ya ce


"Yes babbar yaya"


Ya haɗa musu tea suna sha suna fira ya tashi ya kunna tv sai suka ji ana nocking, Ammar ne ya miƙe ya buɗe, ganin ƙawar Hamra yasa shi cewa


"Shatu ki shigo mana"


Ta shigo Hamra na ganinta ta sakar mata da murmushin nayi kewar ki, ta ƙaraso ta zauna nan Ammar ya fice bayan sun gaisa. Hamra ta haɗa mata tea tare da zuba mata abinci tana


Ƙawata saukar yaushe haka, shiru babu labarin ki.


"Yau na dawo, na tambayi Nura mai shago ko yaga giftawar zuwa wajen aiki ya ce eh kin fice, shine na ce sai zuwa dare zan shigo, ji na shuru da kika yi wata ce ta sami matsala shiyasa na rasa number ki"


Ayya Shatu so sorry, ya Mama?.


"Tana nan tare muka dawo ai, da bazan zo ba ma da ƙyar aka shawo kaina"


Subhanallah! Me kuma ya faru?.


"Uhm pretty ke dai bari, abubuwa a kullum sake taɓarɓare min suke, wlh da wannan rayuwar ƙuncin da nake ciki gwamma na mutu, i hate this life, menene daɗin duniyar ma.....


Shatu.


Cewar Hamrah, tare da dafa ta ce


In dai akan jinkirin auren ki ke irin waɗannan kalaman to ki sani wannan babu kyau, kina ja ne da jarrawabar da Ubangiji ya yi miki, kuma ba a so bawa sbd yana cikin tsanani ya dinga furta irin wannan kalaman, sannan irin su ke cire mutum cikin musulunci, musulmi an fiso ya yarda da KADDARAR mai kyau ko mara kyau, sannan Ubangiji yana jarraba bawan shi ne sbd ya gwada imanin shi, amma da addu'a, hakuri da juriya sai ki ga ya yaye mana damuwar mu kamar ba a taɓa yi ba, abin da nake so dake shine ki daure ki ci gaba da addu'a Allah zai kawo mafita.


"Hamrah pretty na gode da karfafa min gwiwa, wlh matsalar da nake cikin ta, tafi ƙarfin kai na, abin ya wuce tunanin mai tunani, in taƙaita miki saura ƙiris na sami matsalar brain, sbd tunani da kuma tashin hankali"


Jikin Hamra ya yi matukar sanyi ta gyara zaman ta cikin sanyin murya ta ce


Shatu kina nufin bayan matsalar da na sani kina fama da ita akwai wacce ta fita?.


"Eh hakana nake nufi akwai wacce ta fita amma kuma kusan ita wancan ɗin ta rashin auren ce ta haifar da wannan ɗin, zan faɗa miki komai amma sai ranar da baki da aikin wuni zan shigo na sanar dake"


Sauke numfashi Hamrah tayi cikin sanyin murya ta ce


To shikenan ƙawata gobe ma night duty gareni, babu inda zan je sai kin shigo.


Sun ɗan taɓa fira sannan Shatu ta tafi, Hamrah ta dawo ta rufe ƙofarta, ta haye kan bed ta yi addu'an bacci sannan ta kwanta.








Ina godiya da addu'oin ku, jina da ku kayi kwana biyu banyi Update ba na shiga rubibi ne amma Alhamdulillah yanzu ina free.














Comments and share
[1/10, 19:31] SAYYADA ✍️ Barrister: *MUJARRABI*




By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA


09021706569


PG 11 & 12






*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*




_WASHEGARI_




_______ Da ƙyar ta iya buɗe idanuwan ta da suka yi mata nawi sbd bacci da kuma gajiya dake tattare da ita, a hankali ta karanta addu'ar farkawa daga bacci, ta yi miƙa ta sauko daga bed ta shige toilet a daidai lokacin ake kiran assalatu ta asubar fari, ta ɗauro alwala ta idar da raka'atainil farjir, raka biyu ta na fila sannan ta idar da ta farillah, ta bima tana addu'oi nta sannan ta yi azkar na safe ta ɗan taɓa karatun Alkur'ani sann ta koma bed ta ci gaba da bacci sbd night duty gareta. Sosai ta sha bacci sai kusan 11:00am ta tashi, ta shige toilet nan ta watsa ruwa ta fito daure da towel ta shafe jikinta da mai da kuma turare sannan ta gyara gashin kanta, ba laifi yau kam har da shafa powder da lipstick ta shirya cikin riga da skart wacce ta sake fito da coca cola shape nata, tayi normal ɗauri sannan ta fito ta wuce ɗakin Ammie, ta tadda tana kwance cikin sanyin murya ta gaida ta, ta amsa tare da ce mata yau bata jin daɗin jikinta, ta taimakawa mai'aikinsu su gyara gidan tare da girki, ta amsa da to Allah ya baki lfy sannan ta fito, ta wuce kitchen ta tadda ta har ta soma aikin nan Hamra ta ce da ita ta bari ita zata girka abinci ta je ta gyara palour, nan ta wuce, Hamrah gwanan son girki ta fara sharyawa musu abinci tam kala biyu zata yi, Daddyn su ya fi cin biski da miyar ganye Mommyn su kuma ta fi cikin cin tuken shinkafa da miyar ganye, sbd girkin na rana ne yasa suke da fa abinci mai nawi ita hamra ba kasafai ta ke ƙaryawa ba shiyasa breakfast bai dame ta ba, ta daura ruwan farar shinkafa sannan ta daura ruwan biski (tsaki) a cikin ruwan ta zuba gishiri da mai ta barshi ya tafaso, sannan ta zuba biskin a hankali har ya haɗe kanshi sannan ta rufe shi, ta komawa ruwan shinkafar ganin ya tafaso yasa ta wanke farar shinkafa ( ɗanya) ta zuba ta rufe ta barshi, ta buɗe fridge ta fito da nama da kayan miya nan ta soma haɗa miyar ganyen ta wacce tasha gyaɗa sannan ta koma ta bude tukunyar shinkafa ta tuƙa shi, ta kashe gas ta dawo wajen biskin ta da yayi warawara sbd mai da ta zuba mashi ta kwashe ta zuba cikin food flask, ganin miyar ta dahu yasa ta juye ta, tare da sauke shinkafar ta mulmulata cikin, leda nan ta kammala.....


"Wow, what a nice delicious!"


Ta juyo ganin Ammar ya sa ta ce


Yauwa zo ka taimaka min ka kaiwa Ammie nata sannan wannan zan kai dining area sbd anjima.


"To na ji kin ce na Ammie da Daddy ina nawa kuma?"


Kashe nan sai ka ɗiba, ai nayi mai wuyan tun da na girka.


"Nasan zayyi daɗi duk ƙamshi ya baje gidan"


To ɗauka dai sojo.


Dariya yayi ya ɗau basket da ta jerawa Ammie duk abin da zata buƙata ya kai mata, ita kuma ta dawo palour ta ajiye, ta koma ta ɗauko nata ta fito dashi, shima Ammar ɗin ya wuce ya ɗauko plate ta zuba mashi tare da ɗauko goran ruwa ya ajiye musu, suna ci suna fira yana santi ya ce


"Kai zan yi missing na girkin ki da na tafi"


Murmushi ta yi ta ce


To ka zauna mana.


"Uhm ai ba zayyu ba, kema rigima ta ki ke nema tafiya babu fashi"


Ah to ashe kana da sense.


Murmushi yayi yana kallonta, ganin ta yi kwalliya ya sa shi cewa


"Unguwa za ki tafi?"


A'a meka gani?.


Naga kinyi kwalliya ne.


To ai sai kace bana kwalliya sai zani unguwa, shikenan na fahimta.


Ya yi murmushi ya ce


"To ai naga baki cika yin shi ba ne shiyasa"


To yau nayi is that okay.


"Uhm Allah baki hakuri"


Wayarta ta yi ringing ganin sunan Ayshe yasa ta ɗauka suka gaisa Ayshe ta ce


"Shuru tun da ki ka baro mu, na so kiranki amma ban samu na kira ki ba, ya mutan gida ina Ya Ammar?"


Uhm uwargida a gidan Alay Bukar, kowa yana lafiya ga nan Ammar ma.


"Umm uwar gidan dole ba an kama an mai dani babba, to na ƙarba ya zan yi, ki baiwa ya Ammar mu gaisa"


Hamrah ta miƙawa Ammar wayar ya karɓa suka gaisa ta ke masa ƙorafin ya ƙi gidan ta yaran ma na tambayar shi, ya sauke numfashi tare da cewa


Ba haka bane Ayshe abubuwan ne sun min yawa, na ji kuna batun uwar gida, ki na nufin Alay Bukar zai ƙara aure?"


"Eh ya Ammar zai ƙara nan da upper Saturday"


"Ok ina gari ma, zan shigo kamin lokacin"


"To Ya Ammar thank you"


Ya miƙawa Hamrah wayar suka ci gaba da firar su, Ayshe ta ce


"Yaya Hamrah ankawo min set na ɗaki fah"


Barakallah na taya ki murna.


"Na gode, jiya aka kawo"


To asufar lafiya.


"Na gode"


Ya su namecy ta?


"Suna nan lafiya, sun tafi skul"


My regards to them.


"Zasu ji"


Sukai sallama.


HAMRA ta sauke numfashi ta kalli Ammar da ya kammala cin abinci shi yana ƙoƙarin tashi ta ce


Har ka kammala sai ina kuma?.


"Eh fah office na Daddy zan je yau akwai waɗanda za suzo su ɗauki kaya"


To ya yi kyau.


Ya fice hamra ta dawo cikin ɗakinta, ta kwanta ɗaya saura amma ta ɗan kwanta zuwa da rabi sai ta tashi. Ta ɗan sami bacci ta farka, ta shige toilet ta ɗauro alwala ta idar da sallah azahar, ta miƙe ta fito ƙarƙashin bishiyar darbejiya ta zauna, sai taji duk gajiyar babu, tana nan zaune ne sai ga Shatu ta shigo, da sallamarta ta ƙaraso ta zauna, daman anan suke wuni su sha firar su sannan ta tafi, ta ce


"Tun ɗazu fa nake ta son na shigo amma kuma aiki ya shige min gaba"


Sai a hankali ƙawata nima sai bacci bai jima ba na farka, kin san akwai gajiya kema haka daga tafiya ki ke sai kin sami hutu na ƴan kwanaki.


"Hakane ƙawata to ni ina naga wani hutu ai hutu ba na irin mu bane"


Murmushi Hamrah ta yi ta ce


Shatu you have to say Alhamdulillah, tun da kina da rai da kuma lafiya kin fi dubi.


"Alhamdulillah ala kulli hali, hakane kam Allah yasa mu dace"


Ameen.


"Na shigo ne akan maganar da na ce zamu yi jiya, ƙawata ina cikin damuwa duk hankalina a tashe"


Sauke numfashi Hamrah ta yi sannan ta ce


Ina jin ki Shatu, Allah ya bamu mafita.


"Ameen ƙawata, to cikin matsalolina wanne da wannene ki ka san su ina yaso na san yadda zan miƙi bayani ki fahimta har ki bani shawara"


Shatu mun jima tare tun muna yara ke mace ce mai juriya da kuma zurfin ciki hakan yasa ba komai ake iya sani naki ba ko a fahimta amma abin da na sani shine, kina fama da matsalar rashin aure da wuri hakan har ya kai ga mijin mahaifiyar ki takure ki, ya kai ga ko ya yi cefanen gida baya so ki taɓa, kai har ya kai ga kwanan gidan ma yana so ya hanaki, wai kina takure shi.


Sauke numfashi Shatu ta yi a hankali hawaye ke zubo mata cikin sanyi murya ta ce


"Ƙawata, duk abin da ki ka faɗa haka ne amma kuma kusan akwai asalin abin da yasa hakan ya ke faruwa, mijin mahaifiya ba mutumin ƙirƙi bane fatsiki ne, kuma so yake ya lala tamin rayuwata ƙin amincewa da hakan ya sa yake takure min ba tare da kowa yasan dalili ba, ake ganin laifina ne sbd ƙin gaishe sa da na keyi kuma bazan taɓa yarda da shi ba a matsayin uba ba har abada ko da hakan zai zame silar rabuwata da mahaifiyata"


Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ya hayyu Ya Qayyum, Shatu me ki ke shirin sanar dani, dan Allah ce min mafarki nake, what Alhaji Yusuf mijin mahaifiyar ki shine ke son lalata miki rayuwa, Shatu Please kada ki ce dani gaskiya ne.


"Uhm kin fi kowa sanin yanda nake son mahaifiyata kuma kin san irin shaƙuwa da kuma soyayyar dake sakanin mu, bayan rasuwar mahaifina kowa ya juya mata baya amma ban dani, sannan kin san irin gwagwarmayar da aka sha kamin ta aure Alhaji Yusuf, to kuwa yakamata ki sani ba zan taɓa yi masa ƙazafi ba, abin da na ke shirin sanar dake gaskiya ne"


Jikin Hamrah ya matukar sanyi, lallai rayuwa ba tabbas kuma duk irin damuwar da ka ke ciki akwai wanda na shi ya fi naka, wai duk irin nata damuwar ga wacce ta dameta....


"Hamrah, bayan Alhaji Yusuf ya auri mahaifiyata ya ci gaba da kulawa damu tamkar ƴaƴan da ya haifa, ya jamu jikin shi, har muke ji kamar ma bamu rasa mahaifin mu ba, barin ma ni wacce duk abin da zayyi sai ya shawarce ni, hatta abinci ni ke girka mashi, hakan nayiwa mahaifiyar ta daɗi sbd ganin na saki raina daga tunanin rashin mahaifina saboda shaƙuwar da mu kayi. Da farko ban fahimci manufar shi ba yana kirana a duk inda ya ke ina zuwa kamawa office nashi zuwa guest House nashi Ina kai mashi saƙo ko abinci sannan ko yana gida ma haka sai ya kira ni ɗakin shi wai na haɗa mashi tea, ban taɓa zato ko sammanin yana ɗauke da FUSKA BIYU ba kuma har ga Allah kallon uba na ke yi mashi. Wata rana da bazan taɓa manta da ita ba wacce tasa na yi da na sanin haiho ni a duniya, wata safiyar Laraba mahaifiyarta ta sanar damu zata tafi cen Cameroon anyi mata rasuwa cikin dare aka sanar da ita, mu kayi ban kwana ta tafi Alhaji Yusuf ne ya yi mata rakiya zuwa Airport, ba dawo ba sai kusan 10:00pm ya dawo ya kirani a waya a lokacin har na fara bacci, na ɗauka ya ce na same shi a side nashi, na taso na fito duk ƙannena ƙananun sun yi bacci ni kaɗaice ban yi ba, shuru gidan nayi nocking ya bani izinin shigowa na shigo sai dai ganin yanayin shigar shi yasa na juya zan fice ya ce


"Shatu ba damuwa ai ki ƙaraso mana, tea zaki haɗa min"


Jikina ya matukar sanyi babu riga a jikin shi gajeren wondo ne da shi, kai na a ƙasa na wuce inda food flask na ruwan zafi ya ke na soma haɗa mashi, na kammala sannan na kawo mashi, kai na har yanzu still a ƙasa ya ke na miƙa mishi, sai da abin da naji ne yasa na ɗago cikin sauri na kalle shi hannuna ya haɗa da cup ɗin ya rike yana jifata da wani mayen kallon da ya sanya zuciya ta harɓawa, jikina ya soma rawa ganin yanda idanuwan shi ya kanza kala yana fidda numfashi na yi saurin ja da baya ina mai mashi kallon me ka ke nufi ne, ya yi saurin riƙe mun hannu ya dawo dani tare da zaunar dani bakin bed ya yi saurin cewa


"Magana zamu yi, meyasa naga kina jan jiki dani yau Shatu ni ne fah Daddyn ki"


Na sauke numfashi har zuwa wannan lokacin na kasa sakin jiki dashi ina waro idanuwa waje cikin tsoro, ina jin shi yana ƙurɓan tea na shi bayan ya kammala ne ya ajiye tare da riƙe mun hannu yana murza su a hankali jikina ya soma rawa ina tunanin anya Daddyn mu ne ko dai wani ne mai kama dashi, na ɗago kaina sbd na tabbatar da cewa shine ko kuma ba shi ɗin bane

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login