Showing 18001 words to 21000 words out of 74305 words

Chapter 7 - MUJARRABI BOOK ONE BY SAYYADA BARRISTER.txt

18 Jan 2025

4613

sai naga shine yana min wani irin kallo, na yi sauri zan miƙe da niyyar na bar ɗakin ya dawo dani tare da janyo ni jikin shi yana shafa ni tare da sauke numfashi cikin sauri² jikina na rawa na hankaɗe shi na miƙe duk ƙafafuwana sun shanye tafiyar ma neman gagarata take nayi bakin kofa ya yi sauri ya biyo ni, na tsaya tare da juyowa na nuna shi da yatsa na ce


"Daddy kada ka iso in da nake, wlh zan yi maka abin da ba zaka tabaɓa mantawa dashi ba, wlh ka bani mamaki i have never imagine you'll do this to me, har a kullum ina yi maka kallon uba ne wanda ya zai tarbiyyar ta damu ya ɗaura mun a kan hanya madaidaiciya shine ka ke so ka rusamin rayuwata.


Ajiyar zuciya ya sauke ya yi magana a hankali yadda kada wani ma ya jisu, ya ce


"Be wise please Shatu, I'm not your real father, it I'll never be, nothing will ever change from that, I'm only the husband of your mom, don't be confused about our new relationship. It's normally happening in our nowdays so this is nothing.......


Wani ihu na yi da ya sanya shi ya yi baya cikin tashin hankali, yana kallona kamar wata sabuwar shafar aljanu, na nuna shi da yatsa sannan na ce


Ka cuce mahaifiyata, sai Allah ya saka mata sbd cin amanar ta da ka ke yi bata sani ba, tana farin cikin samun ka a matsayin miji, a kullum ƙara alfahari ta ke da kai ashe bata sani ba 2 face gare ka, you showed me your true color and don't ever let her knows, you will regret everything.


Ta sowa ya yi ya iso dab da ni babu kunya babu tsoron Allah ya ce


"Do you mean za ki faɗa mata komai"


Ai ya zama dole tasan wa ta ke aure.


Murmushi ya yi ya ce


"Na sani ba zaki iya ba, kuma in kina ganin za ki iya to bismillah"


Na buɗe ƙofar na fito ina kuka na iso ɗakina cikin tashin hankali, na so a ce wannan abin mafarki ne amma kuma duk inda na waiga ganin a zahiri ne ya faru ina ta juyi har gari ya waye, na tashi da ciwon kai, ban fito ba har yara suka tafi skul ina jin yana tambayar su ina na ke su ka ce dashi ciwon kai na ke yi, sai bayan ya fice daga cikin gidan na samu na fito, haka mu kayi wasan ɓoya na tsawon kwanaki uku, a rana ta huɗe ce ina zaune a palour gidan shuru yara duk suna skul naji sallamar shi, ganin ina zaune a palour yasa ya iso ya zauna kusa dani na yi saurin miƙewa ya dawo dani ta hanyar janjoni ya kwantar bisa kujera ina ta kiciniyar kwace kaina abin ya gagara sbd yadda yake da ƙarfi, ya yi magana


"Shatu bana jin daɗin irin gujemin da ki ke yi kin san yanda na ke son ki kuwa amma ki ke wulakanta ni"


Sabar baƙin ciki da takaici ma kasa magana na yi sau hawaye, jin ya ɗaura hannun shi bisa gashin kaina yana shafa ya sa na ce dashi


Allah ya isa sakanina da kai, ka rusa mana farin cikin gidan mu, sai Allah ya saka mana.


"Uhm Shatu kina bani wahala menene a ciki ina kin ja shekaru baki yi aure ba, kuma a kullum cikin son yi ki ke yi to tunda babu mashinshin ki saki jiki dani zan baki kuɗaɗe daga dubu ɗaya zuwa 100 million, zan miki gatan da ba zaki taɓa da kin sanin aikata hakan ba kuma za kiji daɗin rayuwar.....


Ya Allah ga bawan ka nan yana son cutar da ni da kuma mahaifiyata, Allah ya shiga sakanina dashi, Allah ka maida mashi sharrin sa kan shi.


Cikin ƙarfi na hankaɗe shi na tashi a guje na shige ɗaki na kulle, na fashe da kuka kamar raina zai fita, what anya kuwa Daddy ne wannan, to akan ta zai fara ko kuma daman halin shi ne, tun daga wannan lokacin na tsiri zaman ɗaki har Mommy ta dawo, aranar da ta dawo ta fahimci duk na sauya na rame kuma bana son zama a palour, ta ke tambaya ta ganin tana cikin farin ciki yasa na ki faɗa mata na danne ko ganin idonta zai sauya tunani, amma kuma sai ya nemo wata hanyar da yana bukatar abu sai ya kwalla min ƙira ganin bata san komai ba sai na fito ya ce na dafa mashi abu kaza ko na haɗa mashi tea, amman bana sake mashi, rannan ta fita unguwar ina kwance cikin ɗakina ya shigo tare da sakawa ƙofar key, na miƙe cikin tashin hankali zan sauko daga kan katifata ya yi saurin riƙe ni ya danne ni, tare da rufe min baki ina, na kasa magana ma ballantana na ihu, ya jima yana kallona nima shi nake kallo ina jiran naga ta inda zai fara sai kuma naga kawai kallona ya ke, a hankali ya yi magana


"Shatu ba zan daina bibiyar ki ba har sai kin amince da ƙudirina kuma a nan zamu dinga haɗuwa ba a cen guest House nawa zamu dinga haɗuwa, ina son ki....


Ƙarfi ne ya zo min na hankaɗe shi ya faɗi na tashi zan gudu ya janyo ni na faɗi ƙasa har naji ciwo, ganin na ji ciwo yasa ya buɗe ƙofar a lokacin kuma Mommy ta dawo jin ihu na yasa ta iso ɗakin ganin mu biyu bata ce komai ba sai ma tambayar shi da take akan meyasa meni, cikin kwanciyar hankali ya ce da ita wai faɗuwa nayi ya ji ihu na shiyasa ya iso ƙofata, nan tayi ta masifa ta fice na kalleshi cikin ɓacin rai ya sakar min murmushi ya fice. Tun daga wannan ranar na daina gaidashi na fita harkar shi ko ya kirani bana amsawar, abin ya yiwa mahaifiyar ta ciwo har da marina wai ina raina mata miji ta ya zan je bazan gaida shi ba, ai shima ubane gareni dole na yi mishi biyayya kuma ai da amincewar mu ta aure shi to maisa ni zan fara raina shi, na rasa ta inda zan fara faɗa mata shine na fara gaishe sa, to amma kuma na ƙudirin niyyar faɗa mata komai na shigo ɗakinta na tadda ta zaune ina shigowa ta ce


"Kamar kin san neman ki nake, to menene kuma naga fuskar a dame, wai ma meyake damun ki ne duk kin rame?"


Na sauke numfashi cikin sanyin murya na ce


Mommy magana na ke so muyi akan Daddy.


"To naji kamin ki fara na ki maganar bari na faɗi nawa"


Fito min ta yi da key motar ta ce wai ya bata kyautar ta a ranar hankalina ya matukar tashi kenan babu yadda zan faɗa mata kuma ta amince kawai na ce da ita zan tafi cen Cameroon na zauna, nan ko ta tashi hankali tana ta masifa wai tasani sbd mijinta na ke haka, dan haka bazan je ko ina ba kuma na cire miji na yi aure sannan ya zama dole na girmama shi, kuma na bashi hakuri. Cikin sanyin jiki na dawo ɗakina, kawai na barwa Ubangiji komai na saduda, shikenan mijin mahaifiya ta zai ci galaba a kaina. Bayan ya dawo da daddare ne ta tisani gaba wai na bashi hakuri na bashi. Tun daga wannan lokacin na ɗan sauko ganin kamar ya sauya kwasam ranar Mommy ta ce na ɗau abinci shi na kai mashi guest House nashi zayyi baƙi driver ya kaini, bana son ja in ja da ita na shirya na fito a lokacin kuma babu ita da Rahama sun jera manya manyan kuloli cikin Boot na motar na shiga driver ya kai ni guest House na Alhaji Yusuf mijin mahaifiya ta..........




















Comments and share






*MUJARRABI*




By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA


09021706569


PG 13 & 14




*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*




_________ Muna isowa ya taimaka min muka sauke kulolin abincin, sun kai kala 7 kuma ko wannensu da irin abincin da ya ke ciki duk kuma babu na ƙi, Mommyna gwana ce ta fannin girki, shiyasa Alhaji Yusuf ba ya shakkar gayyatan baƙi cin abinci guest House nashi, ko kala nawa ne Mommy zata girka mashi. Driver ya kalleni ya ce


"Zan iya tafiya ne ko na jiraki?"


A'a ka tsaya mu koma tare....


"Ah har kun iso to sannunku da ƙoƙari"


Banyi mashi magana ba, na juya zan shige motar ya ce


"Shatu taimaka min mu shigar mana"


Ban ƙi ba na taimaka muka shigar sai dai a lokacin da na fito babu driver na dube na ce


Ina driver kuma ya tafi.


"Oh na aike shi ba zai jima ba zai dawo"


Na sauke numfashi na ɗau rogowar kula na shige dashi ciki, sai dai ina ƙoƙarin fitowa kuma na ji ƙofar a kulle, na yi na yi na buɗe abin ya gagara, sai jin takun shi naji na bayana, na juyo ganin babu kaya a jikin shi yasa na ja da baya na haɗe da jikin ƙofar ina waro idanuwa waje, ya matso kusa dani daga shi sai gajeren wondo ya kai hannunsa zai taɓa ni nayi ƙasa tare da matsawa gefe guda na haɗe jikina waje guda ina addu'ar Allah ya kamin ɗauki, daga inda yake tsaye ya kuramin idanuwan shi da suka sauya kala soka koma red da su ya ce


"Ki amince mana ko da na wannan ranar ce, ni kuma zan baki abin da zaki shekaru 10 kina amfanuwa dashi, Shatu ki yarda dani babu wanda zai ji wannan sirrin daga ni sai ke"


Ya matso kusa dani yana lallaɓani akan na amince, rufe idanuna na yi na kwalla ƙara wanda yasa shi yin baya ya kuramin idanuwan shi wanda suka kaɗa su kayi jajir, numfashi na ke sauke shi on on na ce


Alhaji Yusuf, ka buɗe min ƙofa na fice ko kuma dagani har kai duk muyi mutuwar kasko yanzu wlh yanda na ke ji kamar na kashe ka....


Ji na yi ya danƙo ni ya yi min riƙon mutuwa tare da janyo ni ya yi cikin ɗaki dani ya wanke ni da mara, tare da sa hannu zai yage min riga, na samu na ja da baya ina nishi, na ɗauko gwalbar wine da na gani a ajiye na yunƙura zan maƙa mashi ya saurin riƙe hannuna tare da sake jefani kan bed ya danne dukkanin hannayena ya kura min idanuwa yana sauke numfashi, cikin wata iriyar murya ya ce


"Kin aikata babban kuskure wajen ƙirana da Alhaji Yusuf ba Daddy ba, kada kiga ina lallaɓa ki yi tunanin tsoron ki na ke ji, to ki sani ko kusa, kawai ni na fi son muyi alaƙar cikin kwanciyar hankali hakan zai fi faranta min, amma na kula ba zan taɓa samun hakan ba cikin kwanciyar hankali da lallami sai na nuna miƙi karfi na"


Eh na faɗa Alhaji Yusuf, kai da bakin ka ka ce kai ba asalin mahaifina bane kuma ba zaka taɓa zama ba, to gwamma na kira ka da sunan ka....


Shaƙo ni ya yi tare da ɗauke ni da mari ya ce


"Yau sai kinyi da kin sanin zuwanki duniya"


Nan ya soma cire min kayana, na samu na kai mashi cizo, na miƙe tare da ɗaukan kwalbar na makamashi a kai na fice da gudu jiri na ɗibana ta window na samu na fito sbd kulle ƙofar da ya yi, da ƙyar na iya kawo kaina gida ina shiga ciki na tadda Mommy bata nan na tattara duk abin da zan buƙata na ajiye ta dawo da yamma na sanar da ita gobe zan tafi Cameroon nan hankalin ta ya tashi wai sam sai na gaya mata dalilin yin hakan, cewa na yi kawai zan tafi haka muka kwana wai bazan tafi ba, ban samu na tafi a ranan ba sai washegari shine har na shigo na ke sanar da ke. To bayan na tafi da wasu satika ne Mommy ta biyo ni wai Daddy ne ya ce ta je ta taho dani, nan fa na ce ba zan dawo ba, sun yi² na faɗa musu dalili amma naƙi daga ƙarshe dai muka zauna akan a shiga sakanina da mijin mahaifiya ta nan aka ce to na yi harka ta ya yi nashi. To bayan na dawo kuma zaman ya koma babu daɗi yanzu haka Mommy fushi ta ke dani wai bana girmama mijinta har ta kaiga ko gaishe ta na yi bata amsawa abinci ma sai dai ni na girka iya cikina ita ta keyiwa ƙannena, shikuma bai fasa bibiyata ba shine nazo wajenki ki bani shawara na sanar da ita ne ko kuma na yi shiru mu"


Sauke ajiyar zuciya Hamrah ta yi da ƙarfi tare da share hawayen dake bin ƙuncinta, ta matukar kaɗuwa da abin da Shatu ta sanar da ita, what mijin uwa ya ke bibiyar ɗiya, wannan wane irin tashin hankali ne, wane irin zamani aka zo ne, tabbas ƙarshen duniya yazo, a hankali ta ɗago ta kalli Shatu da ta ƙura mata jajayen idanuwan ta, ta ce


Shatu na tausaya miki akan wannan al'amarin tabbas wannan babban tashin hankali amma da yardan Ubangiji komai zai wuce, sanar da mahaifiyar ki kai tsaye zai sake haifar da wani tashin hankalin ne abin da ya dace shine ta ganshi yana yunkurin aikata hakan shine kawai zai sa ta amince sbd na fahimci ta miƙa masa dukkanin yardan ta babu yadda za ayi ta fahimce ki.


"Kina nufin na bari har sai ya yi yunkurin aikata hakan, to ta yaya kenan in kuma ya aikata ba daidai ba fah yazama too late kenan?"


A'a Shatu zamu ɓullo masa ta inda ya ɓullo miki sannan kada ki manta ba ke kaɗai ce yake yiwa hakan ba tayu akwai waɗanda ya yi musu kammin ke, to yanzu abin da na ke so dake shine ki koma gida ki sami Mommyki ki bata hakuri ki ce kin fahimci ke ce da kuskure kuma kin gane dan haka ta yi hakuri shima Daddy ki bashi hakuri a gaban ta ku koma yadda ku ke a cen baya daga wannan lokacin mu kuma zamu fara namu plan ɗin dan ina da tabbacin bazai taɓa ja da baya ba zai sake gwada sa'ar shi, abin godiya ma shine baya haihu dashi ba.


"Zan yi in shaa Allahu sai dai sai na kai zuciya nesa wlh bana son ganin shi kwata kwata"


Ƙawata kada ki damu komai zai wuce, ke dai ki aikata abin da na ce in shaa Allahu, Allah zai bamu mafita.


Hamrah ta yi ta kwantar mata da hankali har aka kira la'asar suka tashi suka shige ciki suka isar tare da cin abinci, Hamrah ta shirya kar fe 5:00pm suka fito, Hamrah ta shige ɗakin Ammie ta tadda zaune ta sake yi mata ya jikin sannan ta fito zuwa wajen aiki. A hankali suke takowa a layin unguwar su suna ci gaba da fira, Shatu ta ce


"Ni kam ƙawata yakama muje shopping gobe tun da kina gida mun jima fa bamu yi siyayya ba"


Uhm gaskiya kam dan nima ina son abun da dama amma kuma ba time haka nake hakura.


"Ai sha'anin aikin ku sai an jure, shiyasa ki ka ga gwamma business da na ke yi bazan iya aikin Hospital ba"


Murmushi Hamrah ta yi ta ce


Ni kuma gaskiya ina sha'awar aikin ko sbd ceton rayukan al'umma, yauwa ban faɗa miki ba kwanakin baya fa na haɗu da Hauwa'u.


"Wacce ce kuma hauwa'u?"


Hauwa'u Jibrin ƴar kyale² wacce muka yi secondary School mana, tana ma tambayar ki.


"Wai ki ce ƴar goal kai naso ganin ta ko ya ta koma"


Aiko tana nan yadda take.


Suna fira har suka iso bakin titi Hamrah ta hau ɗan sahu ta wuce wajen aiki ita kuma ta dawo gida. Akwai shaƙuwa sosai sakanin su tun suna yara haka suke basa rabuwa har suka girma suna tare kuma dukkanninsu ba su yi aure ba.


Hamrah ta iso cikin Hospital ta wuce office na ta kai tsaye office na MD a kulle na Dr Mahmoud ne a buɗe ta shige ciki, a nutse ta fiddo da duk abin da zata buƙata sannan ta kunna system ɗinta ta jima tana aiki a ciki sannan ta rufe tare da lumshe idanuwan ta, sai ta ji babu daɗi da bata sanya Dr ALIYU cikin idanuwan ta ba cikin kwanaki biyun nan sai ta ke jin kamar ba lafiya ba, shigowar shi ko da babu komai tana ƙaruwa da shi kamar yadda yake ƙaruwa da ita sannan akwashi da zolaya. Ta sauke numfashi zata je cen bangaren yaran ko zata samu ta ganshi su yi magana ko ba komai anyi zaman tare. Ta fito ta wuce general ward nan ta ci gaba da duba patients ɗin ta ta jima a ce jin ana kiran sallah magrib ne ya sa ta fito ta dawo office na ta sai bayan ta idar da sallah ishai sannan ta fito ta wuce bangaren yara, bata sha wahala ba ta sami office na shi, cikin sanyin jiki ta turo ƙofar ta shige tare da sallama sai dai kan ta ƙarashe sallamar taga abin da ya firgita ta, wani irin tsawa Dr Aliyu ya daka mata cikin ɓacin rai


"Me ya kawo ki nan, ko nan ɗin ma kin zo ne shima ki rushe min shi kamar yadda ki kayi min a wancan bangaren"


Cike da mamaki ta ke duban shi what, ita yau Dr Aliyu ke dakawa tsawa akan wane dalili kenan sannan kuma meyake nufi da cewa wai ita ta saka aka kora shi daga wancan bangaren, ta danne zuciya tare da cewa


Dr Aliyu, yau ni ka ke wa tsawa sannan ka ke neman ɗauramin laifin da ban aikata ba, ka fi kowa sanin na tsani wannan abu biyun da ka yi min, tsawa da kuma ɗauramin laifin da ban aikata ba ya fi komai ɓata min rai da shiga kunci, sannan ka sani ni ban san abin da ka ke cewa ba dan haka kada ka kuskura ka daura min laifi.


Ta faɗa tana sauke numfashi cikin ɓacin rai.


Ido cikin ido ya ke dubanta cikin ɓacin rai idanuwan shi sun kanza sunyi jajir kamar ya yi marisa ya fito mata a asalin ALIYU HAIDAR zaki, ya ce


"Dr Hamrah kada ki mai dani sakarai nasan abin da na ke yi kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login