Showing 1 words to 3000 words out of 74305 words
*MUJARRABI*
( Age is just a number)
A 2024 novel
By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA
09021706569
The writer of
Wa ya fi so na? ❤️
Ƴar gwoggo
RUƊIN ZUCIYA 💔 2024
And now
*MUJARRABI* (A destiny love story)
_Wannan littafin ƙirƙirarren labari ne, banyisa dan muzantawa kowa ba in dai yazo daidai da labarin rayuwar mutum amin afuwa, nayi shine SBD mu fahimci irin kalubalen da sauran ƴan uwan mu mata wanda suka faɗa a jarrabawa ta jinkirin aure suke fuskanta hakan bayin kansu bane, haka irin tasu MUJARRABIN yake, Allah ya kawo musu abokan zama nagari sannan mu sani wani jinkirin alkhairi ne, na SADAUKAR da dukkanin littafin gare su._
*Godiya da jinjina da kuma ban girma ga shugabar Kungiyar mu ta MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION Nimcy luv much love for you.*
PG 1 & 2
_MAIDUGURI OLD GRA_
________ Katafaren flat House ne mai ɗauke da babban gate baki, Ɗaɗaɗɗen gini ne duk painting jikin gidan ya koɗe, ga dukkan alamu gidane na tsohon ma'aikacin gwamnati wanda yayi ritaya, tsarin gidan na da burgewa musamman yanda jerarrun flower's suke da koren ganye duk da daɗaɗɗu ne, flat ne ɗaya mai ɗauke da ɗakuna masu yawa da babban palour ɗaya mai ɗauke da maroon lader sit wanda ya gama koɗewa da kuma fara yayyagewa, akwai tsoffin standard fridge guda biyu kusa da corido, da kuma babban plasma TV.
Turo ƙofar toilet tayi ta fito cikin nutsuwa ga dukkan alamu watsa ruwa tayi saboda yadda jikinta ke tashi da ƙamshin pawpaw and ALOE vera soap and gel. Ɗaure take da farin towel daga saman ƙirjinta zuwa tsalatsalan cinyoyinta, cikin takun ta kamar mai tausayin shimfiɗaɗɗen blue Black carpet dake ɗakin ta iso gaban mirror mai ɗauke da mayyukan jiki da kuma na gashin kai, da kuma turaruka masu ƙamshin gaske. A hankali ta zauna bisa ɗan madaidaicin standard chair tare da ƙurawa kanta idanu ta cikin mirror na tsawon 5minit sannan ta sauke ajiyar zuciya, tana mai jin tausayin kanta ganin irin kyau da kuma tsura ta masha Allah da Ubangiji ya yi mata amma kuma har tsawon wannan shekarun nata batayi aure ba. Hannu ta saka ta warware tulin gashin kanta wanda ta yi masa naɗin rawanin buzu sbd tsawon sa, in ba hakan ta yi ba zai dinga takura mata, a hankali ta sakesa ya zubo tare da rufe dukkanin bayan ta, ya sauko har kan tudun mazaunanta. Hannu tasa ta buɗe JET oil da kuma man gurguwa sai pink oil ta ɗebo ta haɗa waje ɗaya ta kwaɓa tare da shafe dukkanin gashin kanta sannan ta taje shi ta sake tufke shi da ribon ta ɗaure sannan ta sake naɗe shi, tissue ta ɗauka ta goge hannun ta, sannan ta janyo normal versilene ta shafa a farar skin nata mai sheƙi da laushi, bata shafa man da zai sa ta hasken skin sbd irin skin nan ne da duk wuya duk rintse yana nan yadda yake. Fashe jikinta ta yi da body's spray, sannan ta miƙe ta sanya doguwar riga wacce ta yi daidai da coca cola shape nata ta yane jikin ta da veil na rigar sannan ta ɗau wayar ta tana shirin fitowa, turuss tayi ta tsaya sbd ganin sa da tayi yana tsaye bakin kofan ɗakin ta, ta haɗe fuska.
Murmushi ya sakar mata daman ya zaci hakan daga gare ta, ya sauke ajiyar zuciya a hankali yayi magana ciki silent voice na shi
"HAMRA (Farar mace) yau baki da duty ne a hospital?"
Sauke numfashi ta yi ta ƙaraso kusa dashi, ta ɗago kanta tana kallon sa ba tare da ta sake fuskarta ba, yana da tsawo ya fita sosai kamar shine gaba da ita ta ce
AMMAR ( UMAR) for how long, zan yi ta maimaita maka cewa you have to say salam and get permission before ka shigo min ɗaki, ba ka san yanzu ka girma bane?.
Murmushi ya sake sakar mata sbd a kullum ce masa take yaro, yau kuma ta ce ya girma a hankali ya kwantar da kai ya ce
"Yau ni ki ke cewa na girma lallai a bin da mamaki, ba ki bani amsa ta ba Hospital za ki tafi ne?"
Ta sauke numfashi a hankali ta ce
Yau night duty nake dashi, a bin da yasa na ke cewa kai yaro ne sbd kana kasa dani.
Daidai ta tsayawar sa ya yi ya ce
"I'm sorry, ban jima da shigowa ba, ina shirin tafiya ne and na shigo ne ko kina da sakon da zan karɓo miki, in na tashi dawowa gida anjima"
No, babu but in ma akwai we'll talk through phone.
Ya yi murmushi yana mamakin irin son girma na HAMRA so tari ana cewa ƙanwarsa ce sbd yadda yake da girman jiki da tsawo amma ita har kullum kallon yaro ta ke masa, ba abu mai wuya bane a wajenta ta kira shi ta aike shi, raɓewa tayi ta gefen shi ta fito main palour ba tare da ta sake cewa komai ba. Hayaniyar da taji ne ya tabbatar mata da baƙi cikin gidan ta wuce side na Mommynta, ganin su Ayshe (A'isha) ne ya sa cikin farin ciki ta ce
Shine ba sanarwa kawai sai gaku nan.
Murmushi Ayshe ta yi ta ce
"Ai na san da zaran na ce dake ina hanya za ki ce za ki ɗaura girki shiyasa ma na taho da abinci ba sai kin wahala ba"
Murmushi HAMRA ta yi ta ce
Ayya habibty na gode, but ina yaran nawa ne yau?
"Uhm suna gidan kakarsu wai sai next weekend zasu biyo ni"
"Yaya HAMRA barka da gida?"
Ta maida kallon ta ga Zeenat wacce ke zaune dirsham kan carpet da katon ciki, cikin kulawa ta ce
Alhamdulillah Zeenat, ya karfin jikin?.
"Sai godiya na ƙagu ma na haihu"
Da yardan Ubangiji kamar yau ne ai.
"Hakane"
Cewar Ayshe, HAMRA ta maida kallon ta ga Waleed wanda yake kan bed yana ta dukan bayan mahaifiyar sa a kan ta tashi, ta ce
Wannan sarkin baccin an fara sana'ar kenan, ke Maryama ki tashi, kina jin yaro yana kuka ki tashi ki ba shi abincin shi yasha mana.
Amma ta yi kamar bata jita ba sai da ta maimaita sannan ta tashi ta zauna ta kalli Waleed sannan kuma ta
ɗago ta kalli HAMRA cikin ɓacin rai ta ce
"Wai ke menene haka HAMRA a duk lokacin da kika ga na taho gida ina hutawa sai kin shiga cikin rayuwa ta, nazo gida sbd na samu na huta amma anan ɗin ma baza a barni ba, ina ni na haife shi kuma ni na san zafin haihuwar shi to kinga ai na fiki sanin darajar shi"
Deep kowa ya ɗauke wuta sbd furucin da ta yi. HAMRA ita ce babbar su baki ɗaya amma Maryama ta ke faɗa mata bakaken maganganun da basu dace ba tana ƙanwarta ta huɗu...
Kalaman ta sun yiwa HAMRA zafi amma SBD yadda take da juriya ta ɗauke kai Ayshe ce cikin ɓacin rai ta ce
"Maryama, baki da hankali ne wa Yaya HAMRA ki ke faɗin waɗannan kalaman, to ki sani ko ni ban isa na faɗa mata ba ballantana ke, me kike takama....
Saurin dakatar da ita HAMRA tayi ta ce,
Ayshe ki bar zancen, ina sbd na faɗi gaskiya shiyasa ranta ya ɓaci ba laifin ta bane, ni ne da laifi in dai ni ce ba zan sake yin magana ga mai da ɗanki ba....
Maryama dake baiwa Waleed nono tayi saurin maida martani
"Uhm kada kiyi ai sbd baki san zafin haihuwa ba ne shiyasa, in fisari banza ne kaza tayi mana"
Wannan karon zancen yasaka HAMRA tayi shock dayawa what, abinda wasu suke faɗa mata shine yau ƙanwarta ta huɗu ke faɗa mata, take ranta ya matsanancin ɓaci, ana faɗamata hakan amma bai damun ta sai dai jin hakan daga bakin Maryama ya matukar taɓa ta...
Sauƙar mari suka jiyo tasss, a lokaci guda suka ɗago ganin AMMAR ne ya ɗauke Maryama da mari yasa Ayshe da Zeenat cewa
"Kayi daidai, tun da ta ce ta zaɓi tayi mata rashin kunya"
Duk da Maryama tayi mata rashin kunya amma marin da AMMAR ya yi bata ji daɗin sa ba ta kallesa duk jikin ta ya yi sanyi ta ce
AMMAR, why did you slap her?, because of...
"Yeah, Hamrah I'll do more than that ma in dai ta ci gaba da yi miki rashin kunya"
Sauke numfashi HAMRA tayi ta san hakan ba zayyi musu kyau ba.....
Saukar muryar mahaifiyar su suka ji tana magana daga bakin ƙofar ɗakin,
"Wai meke faruwa ne na ke jin hayaniya tun ɗazu?"
A hankali Hamrah ta ɗago ta kalli mahaifiyar su da su ke kira da AMMIE kuma sai ta lumshe idanuwanta, AMMAR ne ya ce
"AMMIE, Maryama baki ɗaya ta kanza dabi'un ta a ƴan watannin nan, wlh muddin bata daina ba to....
"Stop it AMMAR, you knows nothing and slap her while she's a married woman, kada ka sake"
Cewar AMMIE cikin ɓacin rai, duk jikin HAMRA yayi sanyi a hankali ta miƙe ta fice, ta iso ta zauna ƙarƙashin bishiryar darbejiya dake sakiyar gidan ba tare da ta shimfiɗa komai ba ta kishingiɗe jikin ta tare da zaunawa kan jijiyarta, ta lumshe idanuwanta a hankali take sauke numfashi tana karanta addu'ar innalillahi wa inna ilaihi rajiun.......
"Yaya HAMRA"
Ta buɗe idanuwan ta a hankali ta zuba su ga Ayshe wacce take tsaye hannun ta ɗauke da babban darduma da kuma basket mai ɗauke da food flask babba da karami sai plate da spoun, da kuma goran swan water a hankali ta ajiye basket ɗin ta shimfiɗa dardumar sannan ta zauna tare da sake cewa
"Ki zauna mana kan darduma ai yadda kika zauna jikin bishiyar nan sai jikin ki yayi ciwo"
Sauke numfashi HAMRA tayi tare da sakar mata da murmushin da shi ba na farin ciki ba kuma shi bana baƙin ciki ba, ta sauko ta zauna kusa da ita...
"Yaya HAMRA, kiyi hakuri da abin da Maryama.....
Kada ki damu Ayshe ba komi. Ga dukkan alamu ya nuna akwai abinda ki ke son sanar dani yau, sbd da naga hakan kan fuskar ki.
Cewar HAMRA tana kallon ta, buɗe food flask babban Ayshe tayi ta ɗauko mulmulan semo biyu ta buɗe ta ajiye sa kan plate ɗin sannan ta buɗe ƙaramin food flask ta zuba miyan Agushi wanda yaji manja da kayan haɗi, ta ajiye gaban HAMRA ta ce
"Eh hakane, nazo ne mu tattauna kan matsalata kin san bani da wacce ta wuce ki da ki ke sharemin hawaye na, yanzu dai ki fara cin abinci tukuna"
Hannu HAMRA ta kai cikin basket ɗin ta ɗauko spoun da kuma roban swan water ta buɗe ta ɗauraye sa ta soma cin abinci a hankali yau tun da ta tashi bata sa komai a cikin ta ba, ta ce
Ina jinki Ayshe.
Gyara zama Ayshe ta yi, take ranta ya ɓaci da ta tuno da abin da ke damun ta, ta ce
"Uhm BUKAR ne yake son ƙara aure"
Waye BUKAR?.
HAMRA ta tambaya tana ci gaba da cin abincin ta, numfasawa Ayshe ta yi tasan HAMRA tasan me take nufi amma kuma so take ta gyara sunan ta ce
"Alay BUKAR mijina"
Murmushi sosai Hamra tayi ta ce
Yanzu Ayshe sbd zai ƙara aure shine kike kiransa da sunan sa na yanka, ina soyayyar da kike masa ne, ina har choculety kike kiran sa dashi.
"That was then yaya Hamra, ban taɓa tunanin zai juna min baya ba balle kuma ya munafunce ni, wlh ya matukar bani mamaki, uhmm na miji ba ɗan goyo bane, da yaji kanjin naira sai ya juyawa mace baya"
HAMRA ta kammala cin abincin daman mulmulan kanana ne, ta juyo ta kalli Ayshe wacce ke zubar da hawaye ta ce
Daman ita rayuwa haka ta gada, yau in kaine da farin ciki watarana ba kai bane, ki sani shi na miji ba a iya hana sa aure kuma ba a saka shi, in yayi niyya babu mai hana sa, amma wane hukunci kika ɗauka tsawon kwanakin da yace zayyi auren?.
"Na daina kulasa na fita hanyar sa, shima yana ganin haka ya watsar dani shine nayi tunanin kawai na dawo gida na hakura da zaman auren"
A hankali HAMRA ta ɗaura hannunta kan na Ayshe ta ce
Maimakon ki gyara Ayshe amma kika sake lalata a bin, wannan a bin da kikayi zunubi kike ta ɗebar wa kanki, dan mijin ki zayyi aure bai kamata ki sauke duk wani abin da ya wajaba a kan ki ba koda baya yi ki daure ki sauke naki hakkin.
"Yaya HAMRA abinda ya fi bani haushi fa har yau bai buɗi baki ya faɗamin zai ƙara ba nima a bakin ƙannensa na ke ji, shine kawai na ce zan bar masa gidan"
A'a Ayshe ke ce baki basa wannan damar ba, da kinyi hakuri baki nuna masa kin sani ba ta hanyar ƙaurace masa da zai sanar dake komai. Ba ina goyon bayan sa ba ne kuma bance yayi daidai ba, amma kuma duk inda kika je shi bashi da laifi ke za a ɗaurawa laifi, yanzu yaushe ne ranar bikin?.
"Uhm wai nan da 2weeks"
To shawarar da zan baki shine, kiyi hakuri ki koma ɗakin ki, sannan duk wani ɗawainiyar sa da yake kanki ki sauke kuma kada ki nuna auren ya dame ki. Ki saki ranki kamar yadda ki keyi a cen baya.
Sauke numfashi Ayshe ta yi tana jinjina zancen Hamra anya zata iya jurewa.....
Ayshe, kin haifa masa yara har kusan biyar ina kike ganin zaki tafi kibar su, wa kishiyar ki ko wa dangin sa, dan haka kiyi hakuri, ƴan mata da yawa suna neman irin rayuwar gidan ki basu samu ba, kuma ma yanzu in kika fito sai kizo mu haɗa sawu a gida, ni ba aure ba ke kuma kin yi kin fito.
Jikin Ayshe yayi sanyi da jin kalaman Hamra cikin sanyin murya ta ce
"To ni ba a bin da nayi fa haka nake zaune, jiyama ƙanwarsa harda goranta min wai ban kanza set nawa ba gashi aure ya matso"
Sauke numfashi Hamrah ta yi ta ce,
Wannan ba a bin damuwa bane, ki yiwa Sulaiman furniture magana nawa zaki ƙara masa akan naki set ɗin, duk yadda ku kayi sai ki faɗamin zan turamasa kuɗin.
Rungumar Hamrah ta yi tana godiya tare da share hawayenta a daidai lokacin kuma Zeenat ta fito da ƙyar take iya takowa ta ƙaraso ta zauna tare da cewa
"Wacce wainar ake toyawa ban dani a ciki?
HAMRA ta ce aiko wannan wainar daɗi gare ta kuma babu ta wuce ki.
Nan suka saka dariya. Anan sukai sallah azahar har la'asar, suka soma shirin tafiya, itama HAMRA zata je wajen aiki, suna shirin tashi sai ga Maryama ta fito ɗauke da Waleed ko kulasu batayi ba tayi hanyar waje da alamu mijin ta yazo ɗaukanta, dogon tsoki Zeenat tayi ta ce
"Ni wai me wannan yarinyar take takama da shi ne, sbd ƴan canji da mijinta ya samu shine take wani ji da kai, munanan sai tazo ta neme mu"
Murmushi HAMRA tayi ta ce a'a Zeenat kada ki faɗi hakan ita ɗin ƴar uwar ki ce, kuma ai yarinya ce, da sauran ta...
"Wacece yarinya, Maryama ce yarinya tasan namiji ma shine zaki ce yarinya kawai rashin kunya ce, ni zan sauke mata shi"
Dariya sukai suka wuce ciki, ko wacce ta shirya suka fito suka tafi, HAMRA ta dawo ɗakinta duk a bin da take buƙata ta ɗauka ta shirya ta fito, ɗakin Ammie ta shige ta tadda ta zaune kan dardumar tana azkhar na yammaci ta ce
Ammie zan wuce wajen aiki, sai da safe.
Ta miƙe ta fito dan ta san ba amsa mata za tayi ba, kawai ta sauke hakkin ta ne a matsayin ta na ɗiyar ta. Ta fito kenan alokacin kuma AMMAR ke shirin fita cike da mamaki ta ce
Wait, daman baka fita bane?.
A hankali ya juyo yana kallon ta, ya ce
"Bacci nayi sai yanzu zan fice, aiki zaki wuce ko, to mu fita nima ta hanyar ki zanbi"
Ta sauke numfashi tare suka fito a motar shi suka shiga ya fice daga gidan, kai tsaye ya wuce da ita AL'UMMA SPECIALIST HOSPITAL, ya sauke ta ta shiga shi kuma ya wuce, a nutse ta shigo cikin Hospital ɗin cikin fara'a suke gaisawa da mutan wajen ta wuce office nata, a hankali ta zauna ta buɗe drower ta fito da duk a bin da za tayi amfani dashi ta ajiye shi kan table, sannan ta sanya white coat da kuma white eyes glass nata ta kunna system nata, turo ƙofar Dr Aliyu yayi tare da sallama ta amsa ya karaso ya ce
"Dr HAMRA, akwai patients yau a VIP rooms kuma mutanen MD ne ya ce a basu kulawa a maida hankali gare su abar duk wani patients da ake dubawa daren....
Hannu ta ɗagawa Dr Aliyu alamun ya isa, ta ce
Bazan duba ba, ba haka aiki ya ce ba, sai na duba patients nawa tukuna zan duba nasa.
Sauke numfashi Dr Aliyu ya yi yasan tabbas hakan zai faru HAMRA ba zata taɓa yarda ba, aikin ta cikin gaskiya ta keyi amma ya ce
"Sako ne daga MD kuma kinsa...
Na sani, kada ka damu jeka abin ka.
Ya fice yana mamakin ta, ta kammala duk abinda ta keyi ta wuce general room (ward) da patients ke ciki suna ganin ta, cikin farin ciki suna ɗaga mata hannu sbd tana basu kulawa sosai kuma tana ɓata lokacin ta wajen jin a bin da yake damun su ganin yau ita ke da duty yasa suke murna, bayan sun gaisa sannan ta dawo officer sbd gabatar da sallah magrib a nan ta zauna har ishai sannan ta fito ta ci gaba da duba patients nata a tare da ita a kwai Dr Zalihat, anfi ji da ita ne sbd ta ƙware wajen iya aiki kuma ta dalilin ta suke samun yawan patients sbd ta iya kulawa dasu. HAMRA bata da cusa kai a kan a bin da bai shafe ta ba, iya abin da zata iya ta ke yi kuma bata so taga ana rashin adalci. Sai kusan 11:00pm sannan ta wuce v.i.p rooms tana bi one by one tana duba su sannan ta dawo officer ta ɗan kishingiɗa sbd huta gajiya. A hankali ya turo ƙofar ya shigo babu ko sallama bata buɗe idanuwan ta ba balle kuma ta ɗago amma taji motsin shigowa, ya tura kofar ya rufe ya iso inda ta ke