Showing 24001 words to 27000 words out of 60233 words

Chapter 9 - AUREN FARI Complete by Maman Abdallah.txt

24 Nov 2024

15071

leko shi tayi ta kallo,
Umaimah fa hada yan kwalla ta rasa in da zata sa kanta mamee tayi tambayar duniya amma tayi shiru har ta sa mata ido.
Har an yi sati a haka duk susuce, ya dan fara zama akai akai. Amma ba abinda ke hada shi da ita.
Bayan kwana biyu yana zaune falo shida mamee suna magana, ta koma can gefe ta tsare shi da ido yana cikin magana ya dan waiga ya hangota ta glass. Gaban sa ya fadi ya kalla sosai shi din take kallo.
Tun daga ranar sai ya sa mata ido aikuwa ya gano irin kallon kurullar da ta keyi mishi a boye.
A gajiye ya dawo aiki, tana sama tana mishi gyara, koda taji shigowar sa ta watsar da gyaran ta rugo tare da lafewa in da take boyewa, yana kallon ta don yanzu duk wani maboya nata ya sani, suna ta labari da mamee tana ta lekowa tana kallon sa da taga zai juyo sai ta koma,
Ta koma kenan ya tashi yayi saman tana lekowa zata kalla ......kwatsam taga mutum gabanta......


*godiya ta musamman ga*:-
1. Agamcy
2. Rahama nahaja
3. Maryam Yusuf.


*MAMAN ABDALLAH*


😘😘😘😘😘😘😘😘😘
[1/25, 7:39 PM] ‪+234 813 180 9991‬: 💑 *AUREN FARI* 💑


0⃣1⃣7⃣


....... Ta tsorata matuka, ga wata masifaffiyar kunya data addabeta.
Ya sha mur, wa kike leke?
Ta yi dabur dabur..... Ta dan ja baya, ya bita, ta kara baya ya bita, table ya to kareta ta yi baya zata fadi ya tallobota abinda yake so kenan, ta koma jikin sa da karfi ya mata wani riko,
Wa kike leke ina tambayar ki?
Ta daddage ta cije cikin karfin hali ta motsa jikin ta amma rikon da yayi mata bata iya ko taki daya sai ma ya kara hada ta da kirjin sa sosai, Allah sai kinyi magana zan kyaleki, waye kike leke?
Ta dago kadan amma ta kasa kallon fuskar sa, ta saki harara *yo ni kai nake kallo*?
Na ce kina kallo nane?
Leken me kikeyi?
Malam ni ba leke nake ba zan dauko bokiti ne na taho na ganka gaba na.
Duk nan sama ba bucket sai kin sauka?
Jiya fa da zan fita wacece na hango bayan labule tana kunno kai???...... Kirjin ta ya harba da Sauri na shiga uku, idan ina magana da mamee sai ki koma bayana kina mun kallon kurulla ko shima duk zaki dauko bucket ne?
Cikin ta ya kada, lallai ya gano ni, sai gara in nannade kunyar nan da hauka.
Ta tattakura ta ingijeshi yayi taga taga....
Idan kai baka kalleni ba ta yaya zaka San ina kallon ka?
Allah ya sawake ni banga abin kallo jikin ka ba, wata kila kuma kallon tausayi nake ma babban mutum kamar ka amma kullum ka tsaya *sa'in sa* da diyar cikin ka, ka kasa fita harka ta........ Shut up.
Ya hayayyako mata karya kikeyi wallahi kallo na kikeyi kullum ina lura dake, shekaran jiya da kika fita da gudu kika boye bayan flowers kina lekena zan fita ko shima duk tausayin ne?
Ya fizgo hannuwan ta ya rike gam, idan kina da wani abu a ranki ki fidda *kada ki jefa kanki ga wahala, masifa, da tashin hankali*....... Gaban ta yayi wani mummunan faduwa na shiga uku.
Duk illahirin jijiyoyin jikin ta suka saki.
Ke 'yar abun nan har kin isa kiji tausayi na?
Yanzu dai cika ni!.ta fada a sanyaye.
Ya kalleta sosai shima sai jikin sa yayi sanyi,
Ranta yayi mugun baci gashi yana gani a fuskarta amma ta kasa magana.
....bazan cika ki din ba ki kwaci kanki idan kina da karfi.... Sai kawai tasa mishi kuka.
Ya tsare ta da ido shi kadai yasan azabar da kukan ta ke haddasa mishi.
Ya ci gaba da kallon ta jira kawai yake ta motsa zata gudu ya rungumeta.
Yaga dai bata da halin motsawa ya cire bandir din dubu dari aljihun sa ya birkito tafin hannun ta ya saka *ga cikon kudin ki da albashin ki*
Yana dorawa ya saketa, tayi kasa da gudu, ta fada toilet din falon don ta gyara fuskarta.
Ya bita da kallo, *Wai ita din nan ta iya boye abu a rai* mtseww yayi tsoki.
Zukunne tayi ta dora hannu a ka *na shiga uku ni umaimah* sai kuka.
Sai da tayi mai isarta tukun ta wanke fuskar ta tafito.
Har lokacin yana inda ta barshi, tana fitowa ya gangaro da sauri, ita kuma tana ganin sa tayi ciki da gudu.
*Au na kuma yin laifi?* turkashi sai kawai ya koma sama cikin damuwa.
Mamee na baya, sai kawai tayi kwance bisa gado. *kada ki jefa kanki ga wahala, masifa, da tashin hankali* maganar sa ke dawo mata ta mata amsa kuwwa.
Har yaushe ni umaimah? Ai na gama janyowa kaina duk abinda ka zayyano.
Ta tashi zaune, waya aikeni? Wannan wace irin masifa ce?
Da kwalla sun taho sai ta hadiye. Zuciyarta tayi mata nauyi. Qalu innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Ta daga hannu sama *ya Allah kada ka jarabeni da wannan masifa. Allah ka tausaya mun ba don halina da maraicina ba sai don darajar annabin ka SAW*
Kwalla suka shatato mata. Tayi saurin gogewa ta tafi kewaye tayo alwala kawai sai ta hau kwalliya kada mamee ta gane taci kuka.
*Madaki* kuwa yana hawa sama ya fada wanka shirin kananan kaya yayi .
(Basai na misalta ba kun San dai ruwan designers ne ).
Shiri yakeyi yana Sabbatu. Na gaji da rigimar yarinyar nan *Wallahi so na ta keyi* amma Girman kan ta zai wahalar da zukatan mu. Ko kuwa ni zan ce ina son ta don ta daukeni sakarai?
Ni da zata furta sai in fake ta nan koda tana kawo man raini in ce taimakon ta nayi. Amma ina bada kaina gareta wallahi *sunana sorry*
Yayi guntun tsaki *ina!!! This will never happened*
Yana gama salla ya zo ya zauna yana barazanar karatun jarida.
Biyar da rabi ta wuce ta fito, hannunta cikin hijab ta rungumo kudin da ya bata cikin bakar ledar data saka su. Har lokacin mamee na baya gun yan aiki.
Ya bita da kallo, tana fita ya mike yabi bayanta.
*Ke tsaya*!
Ta yi chak ba tare da ta juyo ba ya sha gabanta.
Meye kike kuminiya dashi cikin hijab?
*ko ya fara mun zargin sata?* ta dago da sauri tare da fiddo kudin ta warware ranta a bace. *kudin da kaban ne* ko kana tunanin ina sata ne?
Ya zaro ido....... Ta daga mishi hannu, billahil azim ban taba daukar abin wani....... Shut up joo... Ke me yasa kin fiye fassara mun magana bai bai? Daga tambaya, ai nasan kudin ne ..... Au kasan ma sune ka biyo neman magana?
Ke malama taimaka miki zanyi in kaiki gida ko kina tunanin duk da wannan kuminiyar da kikeyi dasu cikin jikin ki baza'a gane kudi bane? Kin San hadarin tafiya da su a haka?
Ina abinda ya dameka? Koma menene ni kai sama ba kaiba meye zai dameka?.....
Ya cumumiyo ta dole ya dameni mana saboda......yayi saurin kulle bakin sa.
Taja baya da sauri, kar ka kuskura ka kara taba ni zan..... Me zakiyi ya fizgota. Ka duba ka hango yanda masu tsaronka ke kallan mu.... Ya waiga da sauri tare da sakinta, karki kara zuwa gidan nan ba jaka daga yau.
Ta balls mishi harara wani mugun haushin sa takeji, a da ina da niyyar siyan ta amma wannan dokar taka yasa na fasa. Kawai ta juya ta tafi.
Ya nufi bakar jeep din sa da sauri ya tayar, body guards dinsa na ganin haka suka shiga tasu ya daga masu hannu alamar kar Wanda ya biyo shi.
Ta na ta sauri har an fara Koran sallah yasha gabanta,
Shigo in taimaka miki in ajiyeki gida.
Bana son taimakon ko Kaine ..... Ya fito da sauri ya fizgi hannun ta yayi mota, ta tokare bafa zan shiga motar ka ba malam... Kawai ya sungumeta yayi ciki ya datse sannan ya zagaya.
Kin fiye taurin kan tsiya ya fada tare da zama, an ce za a taimakeki.... Yau naga ikon Allah na ce bana son taimakon ana dole ne?
Kwarai kuwa gashi an miki?
Ya fada tare da kallon ta yana harara.
Ta yi mishi banza.
Tuki yakeyi amma hankalin sa na kanta.
Duk ta hasala tun dazun, ko baya lokacin ma da suke fitinar gadan gadan yanayin fuskarta baya canzawa haka.
Sai wani fushi kikeyi kina turo baki an fada miki gaskiya, bari a kyaleki kiyi *mussai*...... Ya rama fadin kalmar da tayi mishi baya.
Kan ka akeji dai.
Ta fada.
Me kika ce? Ban sani ba ta fada tana murguda baki.
Kilibabba, dadi ya gama wulakanta ki kin shiga *motar madaki* amma saboda feleke har......... Allah ya tsareni ai ni napep ko mashin ya fiye mun sau dubu da wannan motar, ya dauko waya, *hello,..... Yeah fine,.... Okay .... Yeah only 10-15 minutes no only .... Thanks*
Ta tabe baki *yeah* ta kwaikwayeshi ba tare da ya gani ba sannan ta banka mishi harara.
Ya kashe tare da juyowa *ke me kike fada*...Sai naji zafin makara in maimaita...
Ya ci wani uban birki, ta kankame jikin ta tasan *shaka ce* Sai taga ya bude ya fita.
Ya zagayo in da take ya bude, fito mu je....... Ta kwalalo ido *na rantse da Allah kana tabani zan kwarara maka ihu* ko ka kaini gida ko....ya maida kofar ya rufe Sai yayi locking din ta kawai ya wuce, tabi wurin da kallo. Taga an rubuta, *shop rite*
Gidan uwar wa ya kawo ni na bani?
Yana nufin Sai ya karaci gantalin sa zai mayar dani gida?
Wannan salon wulakanci da me yayi kama anya mutumen nan bai gama karto ni ba? Allah ya karto ni gashi abinda yace dani.
Idanun ta suka kawo kwalla *Tawa ta sameni ni umaimah*
Dole in danne zuciyata ko zan mutu....
Duk layin jikunan ba kowa saboda wayar da yayi aka dauko mishi designers kala kala ya ce wacece *latest?*
Haka aka zabo mishi ta *N250k golden brown* ya biya. Sannan yasa aka kawo mishi katon bokitin ice cream ya fito yaron na dauke dasu.
Burun taji ya shigo har ta dan tsorata tayi zumbur,
Ya kalleta *ke ar can matsoraciya*
Ya bude bayan motar aka saka.
Ya dankwashi kanta *ke me yasa baki iya sannu ba?* Ta Dalla mishi harara, wai kai idan hannun ka bai taba jiki na ba baka jin dadi ne?
Kwarai kuwa, kin san ni ko ina yaro bani da abokin fada yanzu da na sameki ne abun ke mun dadi.
Ta yi mishi banza.
Sannun bazata samu bane?
Eh ta fada rai a bace, ko aiken ka nayi?
Ya girgiza kai ko daya.
Nesa da layin gidan su ya ajiyeta ta kalleshi cike da takaici zata yi magana saboda mashin ko napep har bakin kofa,.... Ya ce idan na shiga da motar nan akaga kin fito za a tuhumeki a fara miki surutai ko in karasa?
Ta yi shiru... Tabbas haka ne.
Ta bude kofar taji gam ta yi saurin kallon sa.
Ai ban gama ba ya sa hannu ya janyo jakar, idan kinayi wa Allah karbi jakar nan ba don ni ba *for your safety*
Ta dan harareshi menene safety?
*ki tambayi Samuel*
Kamar bazata karba ba sai kuma ta sa hannuta fizge.
Ya kalleta kawai ya basar don yasan *kyas* zata jefeshi da jakar taki karba.
Sai ka bude mun ko malam?
Ya fita da sauri ya fara fiddo *ice cream* din sannan ya bude mata, ta duro da karfi saura kadan ya kwashe da dariya amma ya kara tamke fuska,
..... Ungo ki kaiwa yan gidan ku tsaraba.....
Ta yi saurin ja da baya... Tabb in ce ina na sameshi?
Ki ce ubangidanki ya ji Kansu ya siyo..... Wai kai idan baka nemi ci mun fuska ba Baka jin dadi?
Kaji Kansu kamar yaya?/na rokeka ne?
Sai kin roka? Ko an fada miki bana sane da ta'asar da kikeyi wa mamee idan an kawo mata? Nasan suma haka suke da shegen kwadayi kamar ki. To bazan karba ba bama bukata, kawai ta juya ya yunkuro zai dankota ta kwasa guje.
A zaure ta boye kudin cikin zani. Sannan ta shiga.
Kamar kullum kowa na tsakar gida ana zazzaune har an fara kiran isha'i. Fitila ta haske ko ina abinka ga karamin gida.... Ko zama batayi ba taga mutum ya fado...
*KE NI ZAKI BARI DA BOKITI A HANNU BAKIN TITI?*
Ta zabura, tare kwalalo idanu...........


*maman Abdallah*


😘😘😘😘😘😘😘😘😘
[1/26, 9:14 AM] ‪+234 813 180 9991‬: 💑 *AUREN FARI* 💑


0⃣1⃣8⃣


*Godiya ta musamman ga Bollywood addict members na gode da addu'o'i da kaunar Ku. Kamar su Rumaisa, sanah, secret writers, Hanan, khadycute da duk wadanda ban ambata ba ina yinku*😘😘


.... Ta zaro ido, yau na gama shiga uku ni umaimah, ya ajiye ice cream din da karfi ya tunkareta tayi baya baya ya hada da bango hannuwansa duka a kafadunta,
Duk illahirin gidan kowa ya mike kamar an tsira mishi allura kusan mutum hudu zuwa shidda suka hada baki..... *Alhaji umar madaki*????
Me yasa kike da taurin kan tsiya, Ke bakya tausayin kanki ko? Tayi shiru tana kyarma.
Ya daki bango *ki kiyaye ni zan wahalar da ke matukar baki sauya hali ba.*
Har ya juya ya dawo da sauri, bakwai idan ta wuce miki da minti daya gobe baki je aiki ba sai na 6atar dake sannan idan kin cika ke din mai taurin kai ce ki ajiye jakar nan kada kiyi amfani da ita, wallahi ko da kuskure baki dauketa ba sai na baki mamaki.
Ya juya ya fice yana huci.
Goggo hansatu ta kai mata wani uban duka *don ubanki bishi ki bashi hakuri kar ki janyo mana masifa matsiyaciya mai halin munafukai* ta ingizata da karfi, ashe bai fita ba zaure ya lafe tana zuwa ya fizgota tare da toshe mata baki yana magana rada rada.
Wannan dogon layin naku zaki bi? Ke me yasa baki da tunani ko kin manta motata nacan farkon layin. Idan kin bini wazai maidoki?
Ohh ni dai na bani. Wannan masifa har ina?
Tayi tayi ya saketa ya kiya, kwallan da take faman hadiyewa suka shatato.
Ya banka mata harara inda kikafi auki kenan ya juyata ta kalli kofar shiga gidan sai kawai ya ingizata *shiga maza* ya fice da sauri.
Tabi bayan shi da kallo, duk yau bai bata haushi ba, amma tana tausayin kanta.
Lokacin da tashiga an kachame rabon ice cream,
Kowa ya bita da harara, goggo jummai ta ce ke kuwa meye hadinki da *madaki*?
Tayi narai narai gidan sa nake aiki, matar data zo kwanaki mahaifiyarsa ce........duk suka zaburo *gidan sa*???
Ta ce eh, yanzu ma ita ce tasa ya rage mun hanya shine....... Shine don ubanki kikayi mishi mugun halin naki ko? Tsinanniya mai mugun hali.
Wallahi goggo ban san bokitin.....ke ar can munafuka ko baki akayi ki kawo mana mugun halinki zai barki ne? Shi mai kudi an fada miki yana da wannan mugun kudurin ai sai talaka irin ki jakka.
To kin daiji sharuddan shi idan kikayi wasa halaka ki zaiyi sakarai kuma wallahi ko cigiya.
Mai bakin jini ke duk inda kika raba sai an tsane ki anji ba a kaunarki. Kai ina ma amfanin yarinya irin ki shegiya, Goggo tayi karaf, ai idan ina fadi bekena ake gani.
Irin su shatu ne munafukai, idan an kirasu cin arziki sai su zake Suna nuna isa kuma ta banza tunda baka dashi.
Luba dake zaune tana ma ice cream cin tuwo da hannu ta ce,
Kun tuna mun wata munafukar yar ajin mu. Usaina 'Yar gidan kansila kawar mabaruka ce tare suke komai, to labuda kuma kawar mabaruka ce ta janyo ta itama taci arziki.
Kawai sai ta fara kiran ta da *mamana* ai kuwa usaina ta ringa jin dadi tana zabga mata abin arziki, shi kenan tana ganin wuri sai ta fara ma labuda bakin ciki tana gaba da ita, idan gaban usaina ce faran faran da sun kebe tayi mata magana sai ta kyaleta, ai kuwa kowa ya karto tsinanniya aka fara bincike sai gashi an gano ba sunan *uwarta usaina* ba makirci ne da kwadayi irin na munafukan mutane.
Kinji ko? Goggo ta fada, muma Allah kadai yasan abinda ake bamu bata kawowa munafuka.
Ice cream din da umaimah bata sha ba kenan ta nufi salloli.
Tana gamawa ta tafi gidan Alhaji yakuba.
Hajiya na ganinta ta ce me akayi miki kamar kinyi kuka?
Ta kakaro murmushi tayi tayi amma ta kasa sai kawai ta fashe da kuka, hankalinta ya tashi kwarai,
Umaimah ya akayi?
Ta dago fuska sharkaf, wallahi na rasa in da zan sa kaina inji sanyi.
Ya akayi?
Kin san nazo na karbi dubu biyar ko? Abinda ya faru....ta fada mata.
To shine yau ya bani da cikon wancen dana wannan watan kin gansu amma INA tsoron kai kudin nan gidan mu sunyi yawa, idan suka saba ina kai kudi da yawa ranar da ban kai ba na shiga uku saboda wani irin birkitatten mutum ne.
Ikon Allah, yaro ba mutum ba sai ya girma, duk abubuwan naku yazo da yarinta umaimah, kuma wallahi kin mun Kyan kai tabbas *da* da mahaifi sai Allah kinyi zurfin tunani da baki fada mata ba, maganar kudin nan ma wallahi naga hankalinki,
Shi kam yayi wauta da yarinta a matsayin sa bai kamata ya biye miki ba, ina shi in ke?
Ta ce *Hmmmm* kawai
Ta fiddo kudin ta mika mata shine na ce bari in zo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login