Showing 48001 words to 51000 words out of 60233 words
Chapter 17 - AUREN FARI Complete by Maman Abdallah.txt
tsalle kin cika su da tsaraba. Allah ya biya.
Amin mamee, ta fada tana mamakin Yanda suke mata godiya kuma fa duk abinnan daga garesu ya fito.
Kaii samun mutane irin su mamee yanzu wallahi sai anyi da gaske, shi madakin duk ya rikice wai saboda tsaraba, shi fa ya biya mana, kaii wadannan mutane hoo.
Uwani na ce zuwa gobe sai ki tafi gida ki kai masu tasu tsarabar kidan kwana biyu sai ki dawo ko kuwa?
Ta fadada fara'ar ta eh wallahi mamee.
Ta kalleta uwani kenan? Duk muzgunawar da ake miki gidan Ku Har yau baki taba gajiya dasu ba baki taba gudun su ba. Kai halinki na da wahalar samu.
Ta danyi dariya kai mamee.
Kusan yanzu idan suna magana kusan amsarta kenan tace *Kai mamee*
Saboda gajiya da wuri ta kwanta shi kuwa har kusan biyu saura yana tare da mamee suna ta tsara yanda za ayi.
Da safe ta shirya wajen karfe goma mamee ta kara mata tsaraba sosai.
Kamar mamee ta sani ta ce kinga uwani ki sadada *Haruna* ya kaiki kawai don madaki na fitowa wallahi baki tafiya yanzu.
Ta mike tana dariya. Har sai da taga sun tafi sannan ta shigo tana tausayin umaimar saboda zata dawo gidan a matsayin *Mata*
Tana shiga yana kokarin saukowa ya kalleta cikin zolaya ina aka fito hajiya mamee?
Ya dora hannu bisa kai *Qalu innalillahi wa'inna ilaihi raji'un* amma mamee kin gama dani yau.
Ya zauna da karfi idanun sa sun kada sunyi jawur, yarinyar tayi sati uku bata nan jiya kiri kiri kika ce na kyaleta ta huta kuma yau tunda safe ki harba ta gida?
Au harbata ma nayi?
Yayi shiru, ya fiddo waya ya kira Haruna, amma yace mishi har ya ajiyeta ya juyo, ya dafe kai, duk sai jikin mamin yayi sanyi kuma don ransa ya baci sosai.
Kai da sati mai zuwa za a maido maka ita a baka har abada?
Ya daiyi shiru,
Yarinyar nan ta tsargu wallahi bana son ta gane nafi son iyayenta su fada mata..... Na sani mamee amma da sai ki tausaya mun ko kirana kiyi muyi bankwana.
Yanzu idan aka sanar da ita ta birkice fa? Ko zan shawo kanta fa sai idan ta zo gidan nan kin sani.
In shaa Allah hakan bazata faru ba ka kwantar da hankalinka.
Ya mike ya fice yana kumbure kumbure.
Abu yazo ga ma'iya ni *Rabi* ta fada tana rike baki.
Umaimah kuwa Sam bata gane gidan su ba, hada *Gate* sai da ta kalla sosai ta runtse ido ta bude tabbas ba gizo idanun ke mata ba,
Murna tsalle, gida ya rikice yan unguwa kafin kace me, sun cika gida ana kallon umaimah.
Ita dai sai dariya takeyi. Abinda yake daure mata kai kowa ya shigo amarya amarya.
Sai da komai ya lafa ta fiddo ma kowa tsaraba sannan aka kukkulla ta makota.
Malam bawa ya shigo yana ta washe baki ya shige dakin sa ya ce a kira mishi umaimar.
Ta dauki ledojin tsarabar sa ta tafi.
Suka gaisa ta dan bashi labari da wasu abubuwan da suka faru na kyautatawar.
Ya ce Alhamdulillah, Ai Alhajin yazo munje har kauye. Tayi murmushi ai haka naji, ta fada mishi yanda akayi lokacin.
Ya danyi dariya ai ya ce yana tsoron kada ki tayar da hankalinki.
Kin tabbatar kina son sa umaimah kada kisa kwadayi da son abin duniya ki dubi maraicin ki da mutuncin ki. Kina son sa?
Ta danyi murmushi.
Ya kara cewa kada kiji kunya ko nauyi idan bai miki ba kiyi magana.
Ta kara murmushi.
Ya fadada fara'ar sa masha Allah.
To abinda nake so da ke don girman Allah ki sanya ma ranki hakuri kada ki tayar da hankalinki, yayi alkawarin zai barki kiyi karatun da kike so...... Gabanta ya fadi . Wai ya akayi ,ne? Ta tambayi zuciyarta.
Kamar ya karanto tambayar sai ya ce, Ya turo iyayen sa, munje kauye an yi magana kinga dai dawainiyar da yake tayi kinga gida kinga dakunan iyayenki jibi nawa, don Allah kada ki bamu kunya.
Ranar sallah za a daura auren ki dashi.......ta dago ido cikin tsoro baba ranar sallah kuma? Sai ta fashe da kuka.
Ya bata fuska to uwaki za a jira? Au na baki hakuri shine zaki tayar da hankalin naki?
Ni dai baba a bari sai nan gaba duka nawa nake....... Yaro ba mutum ba . amma umaimah kin tabbata sakarai.
Yayi kasa da murya ni zaki kunyata ki tona ma asiri saboda ko habaici ya isheni gidan nan ga shi kinzo kuma zaki kara janyo mun wata maganar. Dama suna fadin asiri akayi daman tallar ki muka kai sun manta lokacin da kika sami aikin ma bakin su na ji.
Ta ci gaba da kuka kawai duk hankalinta ya tashi, sallamar hajiya ta jiyo har zata mike ya ce zauna ta shigo nan.
Hakan kuwa akayi suka taru suna kwatanta mata tare da kwantar mata da hankali saboda ita kanta hajiyar madakin yaje har gida ya sameta.
Ta wuni kwance daki tana kuka saboda shi kanshi dakin an gyara masu shi sosai don yasan zata dan zauna na kwana biyu.
Karfe takwas yazo, har ciki ya shigo ta dan tashi zaune kanta kasa, fuskarta tayi jawur tasha kuka har ta bani.
Hankalin sa ya tashi ya karasa kusa da ita ya zauna *Umaimah kuka kikayi haka?* ..... Kamar ya zugata wasu hawayen suka zubo *Sharrrrrrrrr*...............
*Barkan mu da rana*😃
*Maman Al'Amyn, Amynatu da Abdallah*
😘😘😘😘😘😘😘😘
💑 *AUREN FARI* 💑
0⃣3⃣1⃣
*Dedicated to all auren fari fans group* and you *( DIJA)*😘
....Hankalin sa ya tashi , umaimah ba ki son auren nan a fasa?
Ta yi saurin daga kai alamar eh,
Saboda baki sona baki kaunata?, Gabanta ya fadi.
Kinji?
Tayi shiru, ki ban amsa menene dalilin da baki son auren? Ta goge hawayen *Haka nan* A'a baiyiwuwa ai duk mai hankali baya yin abu babu dalili.
Tayi shiru, ya kara kallonta *Baki so na ko?*
Ta girgiza kai Alamar ba haka bane,
To menene for God sake?
Kwalla suka kara zubo mata.
Ya runtse ido, umaimah don Allah ki rufa man asiri kada ki raba man hankali biyu.
Ga pressure family, gata mutanen gari ga ki ke kuma da zan raba in ji sanyi kin fara kuka .
Ki kwantar da hankalin ki wallahi ina sonki yanda baki tunani umaimah kuma bazan taba cin amanar ki ban ko in wulakantaki.
Idan kika ci gaba da nuna damuwar nan zan hakura da auren nan kawai har sai kin shirya, amma ki sani duk halin da na fada kada kiyi kuka da kowa sai kanki kin amince?
Tayi shiru,
Me yasa dazun kuka hada baki da mamee kika taho ban sani ba?
Na lura Sam ke baki wani doki na ko? Inyi ta rawar jiki akanki kina *Wulakanci da rai* .......lokacin ne tayi murmushi.
Kin tuna *Kalmar?*
Ta daga kai.
To bani ma'anar ta please.
Ta kara murmushi tana goge yan guntun hawaye.
Kinji? Kaima kasan ma'anar. Yayi yar dariya Allah ban sani ba.
Tayi yar dariya zan fada ma . yaushe?
Tayi shiru kawai.
Umaimah kina fama da mulki. Wallahi Jan ajin ki ya fara man yawa, kin gama gano cewar Ina matukar kaunar ki shi yasa.
Zuwa na yi in tambayeki dame dame kuke bukata keda kawayen ki?
Hummm, ta ce,
Ai kinji, ke kam ban San lokacin da zaki waye ba, da wata wayayyar ce cewa zatayi , my love ka bamu miliyan daya, ka siyo mana raguna da katon sa sannan ka kawo mana lemuka da ruwa...... Ta kyalkyace da dariya ganin yanda ya dage yana maganar mata.
Shima yayi dariyar burin sa ya cika ya sanyata dariya.
Ta ce haka mata ke magana?
To yaya kukeyi?
Ta sunkuyar da kai saboda yanayin kallon da yayi mata.
Ni ai bani da kawaye....... Gayyar da khausar tayi fa? Ta amshi kati yafi hamsin wurina.
Kawayenta zata gayyata, ke ba naki bane?
Um, ta ce ataikaice.
Ya mika mata ledar ga naki kema ki gayyato.....Allah banda kawaye.
Ya kyalkyace da dariya yauni tawa ta sameni *Card* din ma kunyar su kikeji?
Tayi murmushi ganin ya karto ta. Aiki ya dubeni .
Ki fada man kudin zan Baku ko kuwa list zakiyi abinda kuke so?
Kasan Allah bani son komai. Ko abincin gidan nan da ka kawo ma ina za a kaishi?....yarinyar nan kin fiye gardama. Ya fiddo daurin yan dubu dubu guda uku ya ajiye, sun isa ko a karo?
Ta kalleshi wai kai kudi kaikayi sukeyi maka da baka iya hakuri idan ance ba'aso?
Yanayin yanda tayi maganar yasa shi kyalkyacewa da dariya. Ai ni duk duniya ke kadai nakeyi ma kyauta kice ba ki so.
Ta harareshi ka dauke kudin nan Allah.
Haba umaimah ke in ba ke ba, wace mata ce mijinta zai mata kyauta ta ce ya mayar bata so?
Au na ma zama matar?
Yayi murmushi cewa zakiyi *Thank you my love*...... Ta rafka mishi filo tashi ka tafi na sallameka...... Ya kara yin dariya A'a'a hada *playing love?*
Sai kawai ta mike ganin kunya zata kassarata, ni bari in bar maka da kin......ya tare kofa yanzu ina taba ki zaki birkice mun gashi ke kuma zaki karya doka ta, wallahi idan baki sani ba ki sani yau idan kuma kin sani kin manta zan tuna miki.
A tarayya ta dake abinda ke saurin hasalani ya bata mun rai shine idan muna magana ki nemi guduwa ki barni a wurin.
Jikin ta yayi sanyi ta dawo ta zauna.
Ya zauna kasan kafafunta ta zaro ido nidai tashi ka zauna don Allah.
Yayi murmushi, umaimah kin kara kyau wallahi umaran nan ta karbeki ana gama biki zan daukeki mu gudu ....... Ya zaro ido nan da nan suka ciko da hawaye, ya tashi da sauri ya zauna kusa da ita,
Bari in baki wani labari, lokacin da muke fada kullum na gama matsarki da kin gudu sai inji zuciyata zata fashe don radadi ko kuma naga kin fara kuka, sai inji wani zafi cikin rai.
Sai daga baya na gane ashe duk *So* ne.
Ya mike bari na tafi sha daya hada rabi, ai mamee ta kwafsa mun wallahi. Ta barmun ke can ta assasa sai kin dawo gida gashi ba abinda kikeyi gidan sai kwanciya kina wani kukan maraicin rashin ganina........ Ta kara dankara mishi harara, Allah ya baki hakuri yi zamanki na yafe rakiyar.
Ka ji,?? Ta fada yana shirin fita, ya dawo da sauri ya akayi inyi zamana ko da asubah na tafi....... Ta kara hararar sa, yayi murmushi to menene?
Kudin nan wallahi sunyi yawa ka bamu dubu ashirin sun ishemu.........umaimah, wai baki son kyauta daga hannuna ne ko kuwa ni din ke ba ki so?
Allah ina so, Ta fada kanta kasa tana wasa da yan yatsu, kyautar taka tana wuce misali, gaskiya sunyi yawa,
Yayi shiru yana kallon ta, yarinya karama amma ta saisaita murya tana zaro magana, taci gaba da cewa , shagalin biki kawai ka bamu har dubu dari uku? Yanzu haka a garin nan akwai wadanda suna can sun wuni basuci ba zasu kwana da yunwa, nidai don Allah a kaina ka daina kashe kudi irin haka ko hidimar da kayi gidan nan yayi yawa.
Yayi murmushi, to naji ki dauki dubu ashirin din ki ajiye mun sauran zan karba kinji?
Ta daga kai, ya kara matsowa *What next*?
Tayi murmushi shi kenan,
Ya kura mata ido *Ya sunana?*
Ta kalleshi da sauri, ya daga kai *Yes what's my name?*
Ta danyi dariya.
Allah sai kin fadi sunana yau.
Kaiji ai ina fada kamar wani dana na fari?
Yayi murmushi to ce inji ko kuma wallahi danki na farko in sa mishi umar kuma in hana a boye sunan.
Ta kara yin dariya duk kunya ta baibayeta.
Ke nake jira ko kuma wallahi yau in kwana dakin nan kin San karamin aikina .......... *Madaki* ta fada da sauri
Ya fadada fara'ar sa toooooo kema *Madaki* kike cewa?
Lallai. Ya tallabo fuskar ta ya bata kiss *sweet dream* ya fice da sauri, gudu gudu..... Ta zaro ido *innalillahi*...... Tare da rike kunci.
Bata kara sanya shi ido ba sai dai waya, ta karaci fushin ta har ta fara begen ganin nasa lokacin sauran kwana uku sallah da kuma daurin auren ta.
Gida ya fara cika da baki, dangin su baba da ga kauye da kuma dangin su goggo.
Umaimah da tace bata gayya sai ga kati ya kare kaf!
Gida dankame da mutane ana zaman jiran kawo lefe, umaimah dai ta hada tarkacenta tayi gidan hajiya, khausar tayo mata waya gobe zasu taho da kawaye duka, ita da farida da wasu kawayen faridar ne suka fara yan shirye shirye, ga azumi ga hidimar biki kai Madaki bala'i ne,
Hajiya ta shiga gyara amarya ta dafa mata kaza da auren tantabara sannan ta ringa bata wasu ruwa tana sha, umaimah da ta motsa sai kuka *Gani takeyi ta gama shiga uku*
Mata cike da gida har la'asar amma lefe shiru dole kowa ta koma gidanta don hada buda baki.
Gashin umaimah har bisa baya yake kadan ne bai karasa hawa kugu ba, ba a gamewa saboda kullum cikin kalaba take sai ta nade shi ta boye,
Tana zaune dakin hajiya suna buda ba ki ya kirata yazo gida bata nan, ta mike da sauri ta fito,
Ta dai ga motoci amma bata ganshi ciki ba, tana shiga sukayi kicibis a zaure, taja baya,
Ya kalleta ke ban son yawo ina kika tafi?
Gidan hajiya ai acan zamu kwana saboda gidan ba ki ne, ta jiyo cikin gida an rangada guda, to ki shiga ciki lefen ki ne na kawo.
... Ta kalleshi Kaine ka kawo lefen?
In ba ni ba wazai kawo?
Ta kama tafa hannu na shiga uku nikam kana janyo mun magana, sai kawai ya kasa ce mata komai don bai san lokacin da zai ma umaimah dai dai ba.
Ta juya, ina zaki?
Gidan hajiya ni bani iya shiga gidannan gaskiya.
Ya kyalkyace da dariya mtseww yarinyar nan gaskiya bata waye ba , eh naji ta wuce, ya bita baba ya kirani dazun sun bani makudan kudi na kayan dakin ki wai bazasu taba mika ki salin alin ba tunda na saka komai to inyi amfani da kudin.
Ta ce *Uhumm*
Sun yanka mun sadaki dubu talatin amma na ce zan kara........ Ta juyo da sauri wallahi ka kara zan maido ma. Ai karancin sadakin mace albarkar aurenta, kai *Madaki* kudi na maka kaikayi.
Ya kyalkyace da dariya to anji ustaziya.
Abokaina zasu zo gobe kada ki saki ki fito, dalili?
Ya sha mur na dai fada miki saboda wurin yan mata zasu zo.
Naji ta fada.
Wai ke ba ki Dan kunshin amaren?
Ta kyalkyace da dariya zanyi mana ai kwana zanyi dashi irin na tsofaffi zanyi duka hannu duka kafa.
Ya zaro ido ki rufaman asiri umaimah na tuba.
Me zatayi ba dariya ba. Kai ina ruwanka to.
Ya langabe kai kada ki yi man haka bana son sa.
Ta Dan sha mur kamar gaske, shi zanyi, ko ka manta laifin da kayi man?
Ya hada hannuwa biyu Allah ya baki hakuri na tuba.
Kawai kayi hakuri lallan ma na cen na jika shi.
Jikin sa duk yayi sanyi ya CE shi kenan ai.
Ni zan tafi, okay sai da safe ta wuce ciki.
Yarinyar nan ta gama dani , ya rasa inda zai sa Kansa. Bai taba ganin ta yi kunshi ba, gata da kyan hannu da kafa ga ta fara kullum yana kiyasta ya zata kara kyau idan an mata kunshin zane.?
Mtseww ya buga tsaki ya wuce.
Washe gari tunda asubah mai kunshin ta tazo , kwararriya ce don duk wani mai kudi da ya amsa sunanta burinsa tayi wa yarsa kunshi ga biki.
Ta tsantasara ma umaimah kunshi abin da ka kunshi.
Na kafar dawisu ta zana kan ya fara daga karamin yatsan kafa bazar ta hau kan kafafun har kusan guiywa.Sai kusan azahar aka gama sannan mai kitsonta ta tazo ta yanyara mata kananan kalabarta.
Khausar Tun karfe tara suka zo. Mai kunshin yan mata daban tana ta masu.
*Madaki* yayi wa faty mamza waya don zatayi ma umaimah *Make up* ranar daurin aure saboda a ranar za ayi dinner bayan an kai amarya.
Bikin umaimah ya bada kala ga murnar sallah ga shagalin biki.
Abokan sa har daga kasashen turawa shi kansa hankalin sa ya fara tashi ganin mutanen da ya tara.
Duk hotel hotel dinsa da guest house ya zuba ba ki amma har wasu na hada dakuna mutane hudu biyar.
Malam bawa ya bada mamaki domin yanda Madaki yayi mishi sai yayi amfani da kudin da ya bashi ya kara yayi hidima yaba hajiya su aka yi ma umaimah gara, ya kuma dibi wasu cikin Wanda madakin ya kawo.
Ko mi buhu goma aka kai mishi banda manya manyan bokitan cin cin da dubulan.
Manshanu kuwa daga kauye haka akayi ta lodo wa shi yasa ta sami manshanu fiye da tsammani.
Sannan aka ware mishi dubu dari biyu za a mishi Karin ango.
A kano suke zaune amma samm basubi al'adar su ba yabi yanda sukeyi can kauye.
Hajiya kuwa sai ta sami katon Kofi ta cika da fura ta tsare umaimah tana kuka amma sai ta shanye ta banda abinci.
Umaimah taga da gaske akeyi, ta fara kukan wiwi ana gobe daurin aure.
Tun da ya kirata da rana yaji bai kara samun natsuwa