Showing 18001 words to 21000 words out of 60233 words
Chapter 7 - AUREN FARI Complete by Maman Abdallah.txt
aciki watan in dauka ya gana man wata azabar, kai *madaki ya shiga uku da masifa* INA dalili.
Ledar magungunan mamee din ne da take sha na hawan jini tare da sauran maganin da take shafawa a kafafu.
Mtseww ta buga tsaki, kyaleshi uwani ai zan tafi umara nima tsaraba sai kin ture.
Ta yi yar dariya kwarai kuwa mama.
Wai tana nufin zanyi asara ne? Tabb ya zabura sai wayarsa tayi kara.
*Yeah Ku shigo ina sama* ya kashe
Abokansa ne wadanda ke kula da wasu kamfanonin sa zasuyi meeting.
Ya kira mamee, a kawo mana abincin mutum goma .
Yayi ta zuba ido yaga umaimah amma bata ciki, abinci ma baici ba don takaici, da la'asar ya sauko, tana ta faman gyara wasu duwatsu kaman na sarka,
Ya kura mata ido yana kallo, babu abinda yake kwantar masa da hankali yanzu irin kallon ta,
Ta dago kai kawai taga ita yake kallo ya sakar mata murmushi ta balla mishi harara kawai taci gaba da aikin ta.
Kai ni kike harara?
Yarinyar nan kin rainani ko?
Tayi mishi banza
Kije ki dauko jakar nan ko kuma wannan watan baki da albashi......ta dago zatayi magana yace wallahi zan hanaki kudinki kin San zan iya ko?
Ta mike ta shiga ciki, sallama tayo wa mamee kawai ta fito tayi hanyar waje,
Ya yunkuro ya kamota da karfi *me yasa kin fiye taurin kai?* ta lumshe ido tare da dafe kanta tana magagi kamar me shirin somewa, ya kara matsarta ya daga murya, kina ganin zaki iya ja dani........luuu ta tafi ya tareta a kirjinsa tare da zaro ido *UMAIMAH*...Ya firgice ya rikice ya waiga ya waiga ba kowa, ya sungumeta yayi bisa kujera ya kwantar yayi ciki da gudu ya dauko ruwa..... Ta bude ido a hankali koda taga ya shige sai ta mike tare da kwasawa da gudu.
Ya fito da kofin ruwa a rude.....kawai yaga wayam. Ya kwala kira umaimah...garam yaji anja kofa. Nan da nan ya fahimci me tayi ya yi wurgi da kofin da ruwa ji kakeyi ratsatsatsa..............
*Maman Abdallah*
Good morning to you allππ
[1/25, 8:02 AM] Bahajatu: π *AUREN FARI* π
0β£1β£4β£
*A rubutu na idan kuka ga MZ to ina nufin MOTHER a hausan ce ina cewa MOZA*
*Ba kowa ke da sunan ba sai Babbar masoyiyata SALAMATU DAHIRU wasu na kiranta SALAME DAHIRU kamar yanda kuke son wannan labarin to tabbatas ita ce jagoran siya mun data ba tare da tayi shawara da kowa ba don in muku rubutun AUREN FARI ku nishadantu ku kuma ilimantar. Zata sami addu'a daga gareku? To ina bara domin nima na ce ALLAH YA KARA DAUKAKA SANA'AR TA YA SHIRYA MATA ZURI'A YA RABATA DA IYAYE DA DUNIYA LAFIYA SANNAN YA KARA FAHIMTA ITA DA MAI GIDA AMIN.* KE MI KIKA CE???π
....Yayi tagumi, anya ba nine ke rikita yarinyar nan ba? Ya dunga tariyo yanayin da ta shiga ganin sa a galabaice.
Mtseww, talaka ba abinda bazaiyi ba idan yana son abinka.
Washe gari tana zuwa tabi ta baya, ko mamee bata ga shigowarta ba, taci gaba da aikinta, ya gama zamansa falo har kusan sha daya baiga tazo ba dole ya hakura ya tafi office, umaimah ta gama lakantar gidan duk inda tasan CCTV zata hasko ta sai ta daina zama wurin,
Tana daki zaune ta fiddo mamee kaf tana kara gyarawa mameen ta shigo,
Au kina nan wai?
Ke bakya gajiya da shirya kaya a durowa? Ga gidan kawu can ana cigiyar ki zaki taya su shirye shirye baffa ke birthday jibi.
Ta yi zumbur ashe zamu sha shagali bari in hanzarta ai ina son bazide din nan saboda kek din nan mai yar madara madara.
Mamee ta kwashe da dariya, ai nan kika fi auki in da kwadayi to karki yamutsan kaya wurin sauri.
Koda ta gama tabi ta baya tayi can.
Tana zuwa ta tarar ana ta hura balloons ita ma ta hau yi.
Aunty kune ke hadawa da kanku? Ta tambaya
Wannan karon daine zamu hada saboda a saman benen *madaki* zayayi kin San baffa da iyaye gashi na gaban goshi ne baya laifi. To sanin ka'ida irin ta madaki gara muyi da kanmu kar ayi mishi ba dai dai ba.
Uhumm, kawai ta ce jikin ta yayi sanyi lallai bata ciki.
A kulla wannan a kwance wancen haka sukayi tayi sai shidda ta tafi gida. Ko sallama sai dai ta waya tayi wa mamee.
Tun biyar ya dawo yana falon mamee a zaune ya latsa wannan tasha ya maida wannan, daya ji motsi sai yayi firgigi, wasa wasa har akayi magrib ya kira cikin yan aikin ke ina uwani? Ta kame hannu tana yar kyarma, ta tafi gida.......sai kawai ya mike yayi sama,
Washe gari ma haka tana gaisawa da mamee ta ce ta tafi gidan su kawu aikin birthday. A dawo lafiya kai uwani akwai son shagali ta bita da dariya.
Ya fito yana yan dube dube bai ganta ba, kawai ya nufi dakin mamee tana bi ta baya yana shigowa, ya fara dube dube ta kalleshi me kake nema? Ya kara kallon dakin ba komi ya fice,
Aiki ya rikeshi office shidda ya iso gida yana ta hanzari yana shiga ya tarar mamee da baki a falon sama sama ya gaishesu yayi cikin dakin mamee yana zuwa wayam! Ya fito ya leka kitchen ke ina uwani? Ta tafi........mtseww ya buga tsaki ya juya.
Wai meke tsakanin Alhaji da uwani? Mansura ta bukata, laraba ta ce ya tsaneta ne ita kuma ta nace yarinyar ta fiye shisshigi ke gaki 'yar aiki amma kina acting kamar diyar gida?
Hajiya ce take lalata yarinyar.
Bilkisu ta dago kai amma bata da raini duk tana bamu girma..... Tabb billahil azim ta raina oga bata tsoron sa ko Kadan....duk suka zaro ido bakin ki aka ji kowa ya watse.
Umaimah kuwa tana can ana shagalin toye toye da soye soye abin na matukar bata mamaki birthday kamar shagalin biki?
Kai masu kudi na yarda suke so. Ta zage ta dunga aiki tana kwasar ilimi duk abinda akayi gabanta to ba sai an maimaita ba, kowa yaba mata yakeyi yanda ta nuna rashin son jiki kuma komi akace tayi bata gardama ko bata fuska,
Sai karfe tara tabar gidan aka dibar mata naman kaji, snacks da lemuka ta tafi gida ko mamee tayi tunanin tun marece ta tafi. Wasu na can sashen mamee da saman madaki ana kulla balloons da kayan kwalliya Sam taki zuwa aikin ta manne wurin abinci duk don ta gujewa haduwa dashi.
Hankali madaki ya gama tashi ya sami mamee na lazimi bayan isha'i.
Yarinyar nan bata aikin ta yanda yakamata ko? Kwana biyu bana ganin ta...... To fitina'u kwana biyun nan ma tafi aiki bana son neman rigima, yaushe zaka basu kudin su ne?
Gobe ya fada da Sauri kowa yaje sama da safe ya karbo don zan danyi aiki bazan sauko ba.
Allah ya kaimu, amma kasan gobe ne shagalin baffa nasan kuma ire iren wadannan shiriritun kamar yanda kake fada gidan kake bari tunda wuri gashi a saman zasuyi komai eh zan fita zuwa goma ina nufin suje kafin lokacin.
Oho to na gane,
Ya fito yana cewa ai shegen son kudi gareta gobe na ganta ba shiri.
Zata manta duk wani laifi da akayi mata akan kudi.
Murna tsalle gida ya rikice ana lashe lashe da tande tande.
Goggo hansatu ta lumba wata tsoka ta cika mata baki, to gobe kwana zakiyi kenan saboda shagalin ko?
Ta dago kai da sauri kwana goggo? Eh mana kya taho ba a gama ba?
Tayi murmushin takaici. A a dawo wa gida zanyi komin dare.
Suka ci gaba da ci.
Tunda safe mamee ta tafi Kaduna an aiko ciwon babbar yayar su ya tashi na ciwon sugar. Ta kira umaimah ta shaida mata don haka koda tazo bata iske ta ba,
Kawai sai ta wuce sashen su kawu, babu Wanda yaga zuwanta. Ko wace ta karbo kudin ta amma bai ganta ba, ta karshen na zuwa yace ke ina uwani?
Wallahi ban ganta ba amma bari in nemo ta, ta karba ta fita da hanzari, ya dauki waya, hello mamee ya mai jikin? Da yake a jirgi ta tafi,
Ta ce gata da sauki amma ina tunanin sai na kai gobe gaskiya, asshha zan shigo anjima a gaishe ta. Yarinyar nan taki zuwa ta karbi kudin fa ya kamata ki kirata a waya ko ki turon number ta. Tayi murmushi uwani sarkin hidima kiri kiri taki zama tunda taji za ayi party.
Bari in kirata,
Eh kirata amma still mamee nima turo man number ta please. Ta ce to ta kashe wayar.
Ashe kina nan? Kizo inji Alhaji ki karbi kudin ki..... Na ji. Ta fada a takaice. Zata kara magana wayar umaimar tayi kara,
Hello mama kun isa lafiya ya mai jikin?
Da sauki uwani, kije ki karbo kudin ki zai fita ke kadai yake jira. To mamah ta fada kamar da gaske.
Tana kashewa wayar ta kuma yin kara, ta dauka mamah yanzu fa zanje......... Sai kin gama bata man loka...... Tayi saurin dauke wayar daga kunnen ta, tana ganin number tayi saurin lace wayar sannan ta kashe ta gaba daya.
Kutumeee..... Dai dai shigowar nafisa yallabai gata nan zuwa.
Umaimah ta bata fuska, Wallahi na yafe kudin, ai shi da ganina sai dai wani tsautsayin wallahi.
Ke da wa kike sabbatu? Aunty ta gani gabanta tana dariya.
Ta danyi murmushi kawai.
Uwani tunda mun gama hada jakun kunan da take away kije gida ki shiryo ki dawo da ke da nafisa, mansura da kuma bilkisu ku ba baki abinci da rabon kayan kuma.
Ta ce to, ta tafi amma azuciyarta bata da niyyar dawowa.sai da taje gida tukun ta kunna waya ya kirata yafi sau goma bata daga ba.
Ya sauko a harzuke ya gamu da bilkisu ke ina uwani?
Tana sashen kawu babba bari na kira..... Ban aikeki ba ya wuce fuuu.....
Kamar daga sama Aunty ta Ganshi bai taba shigowa sashen ba ko sau daya, ko haihuwa tayi sai dai akai mishi yaron .
Ina *uwani*? Abinda ya ce kenan da shigar sa.
Yanzu kuwa ta tafi gida..... *what*???? Ya juya kamar mahaukaci, wai laifi nayi sosai ne?
Lallai na gane fushi takeyi yarinyar nan.
Mtsewww yeah I know ban kyauta ba but at least won't she give me a little bit chance? I regret and ready to show my appreciation..... Ohh my God ya dafe kai.
Tana zaune daki tana gyara jakar kayanta wurin karfe biyar mamee tayi kiranta,
Ta dauka tana fargabar ko ya fada mata bata karbi kudin ba.
Hello, mamee ina wuni,
Lafiya lau uwani kada ki manta ki ringa barmun daki a kulle kinga gidan yau Allah kadai yasan wa zasu shigo gashi bani gari.......gabanta ya fadi ta ce toh.
Tana ajiye wayar ta mike na shiga uku, tabar gidan a gaje.
Tana rufo dakin ta fito kenan tayi kucibis da baffa, yawwa uwani ungo muje sama, ya tasa keyar ta.
Kowa gidan yana can an kawata wurin swimming pool ana ta shagali, nan da nan umaimah ta sake aka fara hada hada.
Khausar ta yafito ta da hannu, jeki dauko ledar tissue na can falon mamee.
Ta ce toh, tana dawowa kenan zata wuce shi kuma ya fito bai taba tsammanin ta ba, yaja wani uban birki, kallo daya tayi mishi ta wuce ya ware murya... *umaimah* amma ina sai ma ta ruga.
Ya salam ya fada wai me yarinyar nan ke nufi kawai sai yabi bayanta.
Yayi saurin dawowa da hanzarin ganin me yake shirin yi, yarinyar nan tsab zata yarfa ni gaban mutanen nan babu ruwan ta yaran da ke ganin kima da mutunci na duk ya zube.
Yana nan tsaye ya rasa me zaiyi.
Ita kuwa tunda taga haka sai ta fara bobboyewa tana neman yanda zata sulale tabar gidan.
Haka kuwa tayi sa'a ana shiga sallar magriba ta fito a hanzarce bayan wasu ita ce taji wuf an fizgeta da karfi, zata kwala ihu saboda firgita ya to she mata baki,
Ke wai me kike nufi?
Ta fizge hannunsa daga bakin ta abinda duk kake nufi shi nake nufi.
Na gaji da fitinar ka wallahi wallahi na gama biye maka na gaji da wulakancin ka.......zuwa ki karbi hakkin ki ne wulakanci? Yaya ina ta binki kina neman hasala ni? Na kira wayar ki kinki dagawa nasan ai ban kyauta ba amma bazaki jira in...... Ta kalleshi au kasan baka kyauta ba da gaske?
To kaban hakuri na rantse da Allah idan baka ban hakuri ba yanda dai nayi takima da aman ka na bata lokaci na ceto rayuwaraka amma......amma me?
Ya ingijeta ke awa zan baki hakuri? Ya nuna ta da yatsa ranar duk da kika kara furta wannan kalmar na rantse da Allah sai na barki kwance.
Ta kalleshi shekeke haka kace?
To ga sharadi kada ka kuskura koda wasa ka kara tanka mun. Bani da wata alaka tsakanina dakai na rantse ko kallo baka isheni ba bana kaunar ganinka ma bare magana ko wani abu ya kara hada ni da kai idankuwa ka kuskura........ya shako wuyanta me zakiyi?
Kina da taurin kai ko?
Ta ingijeshi da karfi, *Zan hada ka da mahaifiyar ka* ko baba ai da babanshi.
Ni yau naga bala'i ta hada hannuwanta duka alamar rokon sa, kayi wa Allah da manzon sa da kuma darajar mahaifiyarka kasa kan mara inyi fitsari, hanyar duk da nasan kana wurin zan kiyaye binta bana son ko kallo ya hada ni da kai bare magana ta fatar baki......ta juya abinta .....ya mika hannu zai kamota ta kwasa a guje ..... *Umaimah*...... Amma inaaa tayi wajen get da gudu.....
*Ni din dai ce taku mai son ku mamar Abdallah diya ga Aunty rabi*
ππππππππππ
[1/25, 8:02 AM] Bahajatu: π *AUREN FARI* π
0β£1β£5β£
Ya dunkule hannu ya kai ma wani icce duka. Taurin kan yarinyar nan yayi yawa.
Amma banga laifin ta ba nine na damu da kucaka *let me snub idiot* ya juya ya wuce.
Ka dauki tsanar duniya ka daura mun wannan jaraba har ina? Karar sa zan kai wallahi ya kuma takura mun. Dole in sanar da mamee idan bata dauki mataki ba zan hakura da aikin. Ta je gun hajiya cikin kudin ta takarbo dubu biyar takai ma goggo hansatu ta ce ga albashinta. Ta ware dubu ta bata ta boye dubu biyu, Ta ajiye biyun idan baban nasu yazo ta bashi.
Washe gari ma taki yarda su hadu, shima ya dan share abin na can cinsa a zuciya amma ya daure.
Kausar tunda akayi dan shagalin nan sai jinin ta ya hadu da umaimah taji kaunarta a zuciya gasu kusan sa'anni amma yanda komi ta ce umaimar tayi bata musantawa, ta shigo suka sha fira abin su umaimar ta ce don Allah idan ta sami lokaci tana so ta dan ringa koya mata boko don ta gane baki, tun a lokacin kuwa suka fara.
Sai dare suka dawo tare da mamee, jiyan bai sami zuwa ba sai yau. Tuni umaimah ta dade da tafiya gida.
Madaki sam yaki yarda ya kuma amince da cewar zuciyarsa ta kamu da kaunar umaimah ba tare da ta tsaya shawara da kwalwar sa ba, ya rasa inda zai sa ransa don kuna.
Ya kwanta ruf da ciki, ya runtse ido wallahi *So bai mun adalci ba* in rasa son da zan fada sai na wannan banzar yarinyar?.....kai ba so bane.
To meye? Haka ya dunga kai gauro da mari, kafin kace me ya sami attack na ulcer don zubewa yayi yana firowa sallar asubah.
Hankalin kowa ya tashi gidan masu kuka nayi masu kyarma nayi don bai taba irin haka ba. Akayi sama dashi likitanshi ya fara aune aune, nan da nan ya gano damuwa ce ta yado mishi ulcer. Mamee tayi ta jinjina abun a ranta damuwa? Ko dai don ta kawo mishi yaran nan? Nan da nan hankalin ta ya tashi.
Umaimah tun a gate ta fahimci kowa yayi zugum, saboda kullum kafin ta shigo sukan dan mata 'yar raha.
Ta iske mamee zaune idanu sunyi luhu luhu. Ta isa da gudu har ta kusa faduwa, mamah meya faru ko mai jikin ce?
Ta girgiza kai..... *madaki* ne...... Gabanta yayi wani mugun faduwa . ta zaro ido yayi me?
Baya lafiya.....ta saki ajiyar zuciya har mamin ta kalle ta, kai na firgita mamah , Allah ya raba mu da mugun ji, mugun gani da mugun aike shi kuma Allah ya bashi lafiya......ta mike . Aaammmeeenn uwani.
Ta danyi murmushi rashin lafiyar ne kika sha kuka haka? Ta Dalla mata harara. Ana kakkabe mishi file ne yayi kura ba inda zai tafi sai munga jikalle....... Bata San lokacin data kwashe da dariya ba. Tayi ciki itama tana dariyar ko kefa amma kinyi kicin kicin da rai ni duk kin kadan yan hanji.
Ta bita tana murmushi, barkwancin yarinyar yasa ta shiga ranta fiye da kima.
Abokansa lodi lodi , zandi zandi da ma'aikatan sa haka ake wuni zarya gaisheshi. Ta tabe baki, kodan kudin sa ai mutane sa soshi. Marassa zuciya biye ake....
Kwana biyu kowa ya hau yayi mishi sannu banda umaimah, yaga da gaske mutuwa fa zaiyi kawai ya yanke zuwa ya bata hakuri, a wuce wurin,
Ya sauko daddafe tana ta faman gyarawa