Showing 42001 words to 45000 words out of 60233 words

Chapter 15 - AUREN FARI Complete by Maman Abdallah.txt

24 Nov 2024

15079

son auren kada ya wuce sallar nan idan muna da rabon kaiwa.
Yadan yi shiru, jin malam bawa bai ce komai ba ya ci gaba da cewa,
Wallahi bana son ko tsinke naku na yafe ita kadai nake so ku bani sannan zan dauki duk wata dawainiya ta bangaren ku.
Wannan ita ce alfarmar da nake nema, shawara kuma,
Ina zullumin kada umaimar taki amincewa don yanzu haka na sanya ta karatu tanayi kuma na yi alkawarin wallahi zan barta ta karasa duk inda take son kaiwa a matakin karatu. Shin in sanar da ita ko inyi shiru?
Ya dan yi shiruuuu!!....
Ya langabe baba don Girman Allah ka taimaka man.
Haba yallabai, babu abinda zaka roka in hanaka, matsalar ina da yan uwa kauye zan so na sahawar...... Idan har kana ganin babu damuwa na amince mu je yau ka gabatar dani. Kafin iyayena su koma.
Ya danyi murmushi yallabai hakanan zaka wahalar da kanka in shaa Allah zan je da kaina.
Baba kayi hakuri don Allah ..... To shi kenan bari na shiga na fito kada rana tayi mana hanyar bata da kyau.
To baba maganar umaimah fa in fada mata?
Rabu da ja'ira ni zan mata magana da kaina don kada ta ga laifin ka tunda har kana da tabbacin zata iya birkicewa.... Ya shige gida in ba iyeshe na yaran yanzu ba ita har tana da abinda yafi auren a wannan maraicin nata?
Sai biyu da rabi suka dawo, Madaki na ta murna yanda aka tarbeshi kai wadannan mutane da mutunci suke,
Shima malam bawa yana ta jin dadin yanda madakin ya saki jiki kuma ya girmama yan uwansa ba tare da raini ko nuna kyama ma.
Suna zaune falo ita da mamee ya shigo yayi lilis don gajiya, mamee ta kalleshi yanda ya zauna da kyar,
Wash wallahi na gaji mistake daya nayi da na tuka mota yau.
Ke baki iya cewa sannu da zuwa darling?
Mamee ta harareshi ka dawo zaka sa miyon bakina kafewa ina ka tafi yau wayar ka ma bata samuwa?
Bari mamee wallahi mutanen nan na dade ban ga masu mutuncin su ba, mota ta nacen cike da buhunnan wake da aka bani.
Nan da nan mamee ta dago shi ta kalli umaimah uwani jeki karasa man gyaran durowar kinji....... Kiyi sauri danayi sallah zamuyi zance.
Ta yi ciki tana dariya mamee ta bishi da harara, ina sauraron ka ni ra sa kunya.....
Ya kwashe duk yanda akayi ya fada mata.
To amma kai yanzu ga azumi ya zakayi da wadannan tafiye tafiye ga hada kayan aure, ....ya mike tabbb ni kuwa nasan yanda zanyi mamee ya haye sama
.......


Kuyi hakuri wallahi yau school naje.
Afuwan πŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ˜ƒ


*Maman Abdallah*😘😘😘😘😘😘
[1/27, 7:42 AM] β€ͺ+234 806 091 7227‬: πŸ’‘ *AUREN FARI* πŸ’‘


0⃣2⃣8⃣


........ Daga masallaci ya wuce shi da driver gidan su umaimah, lokacin da suka isa malam bawa ya gama shinfida zaure,
Ya tare shi cikin girmamawa amma Madaki sai sumsumkewa akeyi alamar nauyi da kunya.
Bayan sun zauna malam bawa ya mika mishi hannu alamar su gaisa Madaki ya zukunna har kasa abinda ya kara daure kan sa kenan.
Bayan sun dan zauna jimm, malam bawa ya kalleshi wallahi ranka ya dade tunda naji wayar ka na kasa natsuwa ina ta zullumi da fargabar ko lafiya?
Ya danyi murmushi lafiya qalau baba daman ina son rokon wata alfarma ce kuma da neman shawarar ka.
Alfarma? Wallahi kafi karfin komai a wurina yallabai. A yanda nake jin labarin ka a gari ban taba tabbatar wa ba sai da naga zahiri. Ka cika *Da* na halas! Na ji dadin yanda ka mun duk mai son ka a rayuwa shi ke fada ma gaskiya...... Baba mubar maganar nan ta wuce!
Abinda ya kawo ni ina neman Alfarmar *Auren umaimah*...... Ya dago kai da sauri....... Kada in ce daman furucin ka na farko da gaske kakeyi ko kuwa har yanzu kana da tunanin...... Wallahi baba bani da tunanin komai sai alkhairi.
Ina son umaimah saboda Allah kuma ina son ta zamo *Uwar 'ya'ya na* Alfarmar da na ke ka taimaka man da auren ta karamar sallar nan mai zuwa.
Baba amincewar ka kawai nake bukata wallahi tsinke bana so daga gareku sai ita kadai. Maganar hidima zan dauke muku komai.
Yayi shiruuu...... Kafin yace, Alhamdulillah.
Na ji dadi sosai da wannan albishir domin a gareni albishir ne, gareni baka da matsala, amma ka sani ina da yan uwa a kauye wadanda suma suna da hakki akan yarinyar kuma muma muna da iyaye zan so ka bani lokaci.......
Baba banyi gaggawa ba amma ina rokon ka da idan babu damuwa yau zan kasance tare dakai matukar zaka jagorance ni garesu in gabatar da kaina kafin in aiko da magabatana.
Yayi murmushi wallahi babu wata damuwa sai mu tafi.
Sai maganar shawarar ka, agaskiya ina tsoron fadawa umaimah kada ta birkice mun....... Au daman bata amince maka ba?
.....wallahi tana so na baba, na sanya ta makaranta ne, to bata son katse karatun nata....... Yayi dan murmushi *Au*,
Kuma zan barta ta karasa karartun ta sannan idan ma tana son karawa gaba na amince *Aiki* daine bazan amince ba. Shine na ce in sanar da ita din ko kuwa ana zaku mata bayani?
Malam bawa ya mike tsaye kaima ka zama yaron kenan, kyale ja'ira kada Wanda ya ce mata qala, tunda har kana tunanin zata ki amincewa. Bari na sako babbar riga kada muyi rana yayi ciki.
Goggo hansatu ce ta fara tarar sa malam kai da wa ye haka tunda safe?
Ya fadada murmushin fuskar sa, maneman auran umaimah ne yanzu haka zamuje kauye....... Ta daki kirji *Aure?*
Suna fitowa Abba yazo zai wuce fangan fangan... Malam bawa ya daka mishi tsawa ganin zai ingije bako.
Yayi yar dariya babu damuwa baba.
Kayi hakuri ba natsuwa a hanya yake fada mishi ko waye Abban, ya tausaya masa tare da alkawarin da sun dawo zai daukeshi yakaishi *Rehabilitation*
Yayi mishi bayani sosai ya kuma gamsu yana ta godiya.
Kauye ne mai cunkusassun gidaje,Abinda yaba malam bawa mamaki shine yanda *Madaki* ya saki jiki bai nuna wata kyama ba ko shimfida akayi mishi sai ya yaye ya zauna yanda kowa ya zauna, babu Wanda baiba girma ba. Wannan abu ya wa malam bawa dadi a rai. Hatta kananan yara sai da ya raba musu kudi.
Shi kuma duk gidan da suka je sai an basu ko gero ko wake, haka suka dawo da tumbaye ransa sayau, Yayi yayi malam bawa yabar tumbayen abincin nan amma yakiya.
Hakan ya kara sanyaya zuciyar Madaki kaunar umaimah da tausayin iyayenta ya karu cikin ransa.
Karfe biyu da rabi ya isa gida suna zaune falo mamee taga ana shigowa da yan buhunna , ya shigo mamee ta kalleshi duk ya gaji..... Daga ina haka?
Ya zauna wash!
Sannu da zuwa, umaimah ta ce dashi tana satar kallon mamee.
Yawwa my dear ya gida?
Sannu da gida mamee love.... Kai ban son iyashege kaji ko.
Ya tuntsure da dariya umaimah dai tayi ciki.
Ya bita da kallo *Ke dawo*....... Amma ina ta shige.
Ya kalli mamee yarinyar can dole inyi maganin ta ta raina ni,
Naji, ina ka tafi ko wayar ka ba a samu ka shigo da wasu yan buhunna kamar Wanda yaci kasuwar kauye..... Kin canko dai dai.
Kauye naje mamee.... Kauye?
Wallahi kuwa ya bata labari kaf!
Ta rike baki Allah sarki, wayyo Allah kai masha Allah wadannan mutane sunyi bazata..
Kwarai kuwa.
Gobe zan tafi Abuja zamuyi magana dasu baba Ibrahim muji me zasu ce. Sai in biya Kaduna ...... A a ka bari zan fa da ma su yaya.
Ya dauki waya yawwa kaga missed call dina ko?,......okay ka ganshi? To passport nake so latest jibi don na gama magana da embassy..... Ya kashe.
Me zakayi da passport?
Na umaimah ne umara zaku tafi kuyo mana addu'a kafin ku dawo na gama wasu gyare gyare.
Don Allah? Kai masha Allah.
Amma naso ka bari sai karshe...... Mamee kuyi hakuri bana so kuyi sallah can saboda daurin aure ya mike. A ajiye mun kayana kada a taba mun,
Ka fada mata?
Kiyi shiru sai zaku tafi.... Kai ban son shirme komai ayi shiru komai ayi shiru to sai na fada mata.
Ya haye sama kunfi kusa..
Sallah kawai yayi ya kwanta barci.
A saman yasha ruwa cook din sa ya hada mishi tea da sandwich.
Umaimah taji shiru har ta dawo asham amma bai sauko ba ga mamee zaune tana kunyar ta kirashi sai kawai ta tura mishi text.
*I know for sure that you are my life, Since the time you have left today ,i feel so blue and nothing interests me, i think you have taken a part of me ,And I really can't survive without you ..I love you and I miss you , You should know that I truly do ,Please come down soon!* Ya maida mata amsa *When I say thank you, I mean it from my heart, Dear you helped me achieve so much, You were there from the start, A heartfelt thank you to you, am coming dearest*
Bata karasa karantawa ba ta hango shi yana saukowa, ya sha wanka cikin kana nan kaya *Kai madaki nada kyau* suka hada ido ya sakar mata wani narkakken murmushi ta mayar mishi tare da sunkuyar da kai.
Mamee na lura da ita, sai tayi kamar bata ganshi ba ta mike uwani idan kin gama kallon kya kashe ni kam na gaji...... Mamee barka da shan ruwa ina zuwa kuma?
Au ka sauko? Barkan mu juna, zan dan kwanta ne na gaji.
Yayi murmushi kawai.
Tana wucewa ya ce matso malama ki fassara mun text din ki.
Ta danyi murmushi kawai, ansha ruwa lafiya?
Qalau,
Me kika rage mun?
Kosai.....
Ya kyalkyace da dariya wallahi banci, sai me?
Dan na rogo....
Ya fara dariya.
Ta tashi ta dauko mishi yanballs da samosa, sai dan juice din ta na kwakwa da fresh Ginger, mamee ta ce kafi son mai dan nama nama gashi idan zaka iya ci don kai nayi.
Ki ce Allah!
Allah kuwa,
Ya janyo cooler iyye yarinyar nan fa zatayi *Caring*
Ta ce hmmmm
Ya fara ci yana Santi
Cewa zakiyi nabar banza na tsaya cin sandwich saboda kiwa.
Gaskiya.
Ya dan zaro wani abu gaban aljihun sa kawo hannun ki in baki tukuici.
Ta mika mishi, ya zo zai kama tayi baya dashi da sauri tare da 6ata rai, wallahi kaga abinda na tsana a tare dakai.
Ohh am sorry please. Ya kamata ka fidda wannan muguwa tabi'ar a ranka gaskiya domin wallahi haramun ne,...... I said sorry woo..
Yeah I know but let me tell you, ka fidda fashion a maganar nan ka sanya addini, taba mace baliga haramun ne , me yasa namiji baligi ko baliga idan sukayi alwala akace shafa ko babu sha'awa alwalar ta warware?
Addini fa sauki gareshi wallahi ko musulman mu dake zuwa kasashen turawa suna gaisawa dasu bala'i suke daukar ma Kansu.
Haka ma khausar a school sai da na mata magana ita da kawayen ta kawai kana zaune kato zaizo ya kai hannu ya dafa ka ko ya kai duka wai abobota.
Ya kamata ka daina bana so na fada ma da arziki, na fada ma cikin fushi to yanzu na fada ma a addinance wallahi next bazatayi mana kyau ba.
Wallahi na daina kiyi hakuri ungo zobe ne zan saka miki amma saka da kanki Allah ya bada hakuri ustaziya ta.
Ta yi murmushi.
Shi yasa na ce wa mamee kuje umara tare kiyo mana addu'a kinga sai ki rungumi ka'aba ki Rokan mun Allah ya yaye man wannan hali.......
Umara?
In shaa Allah.
Jirgi zan hau?
Ya kyalkyace da dariya a'a bisa keke zaku tafi.
Itama ta yi dariyar.
Na gode Allah ya kara arziki.
Aminnnnn my love.
Yau fa da wuri zan kwanta bazanyi kwanan zaune ba.
Ya langabe kiyi hakuri mana haba don Allah.
Okay naji sha daya nayi zanje in kwanta.
A a na yarda sha biyu dai.
Zatayi magana ya canza da cewa,
Don Allah kiyi mana dawafi Allah ya tabbatar mana da alkhairin aure na dake, sharrin da ke tare dashi Allah ya karemu kinji.
Banda kai za a tafi?
Gaskiya,
Ta bata fuska, dalili
Akwai abubuwan da zanyi ne kafin ku dawo, yanzu haka ma Gobe Abuja zan tafi.
Kai baka jin azumi?
Ko ina ji ya zanyi mai nema ai baya kwanciya umaimah baki ganin ni maraya ne.
Ta balla mishi harara in kaji maraya raggo.
Ka ma gode ma Allah kai kana da mamee ni kuma fa..... Ke kuma kina da *Madaki*
Hummm
Ko baki sona?
Ni kuwa ke son ka....... Ta yi saurin tsuke baki,
Don Allah karasa tawan.
Hahahhaah kaji abinda kaji.
Kedai bakauya ce wallahi.
Naji wayayye.
Ina so in tambayeki, a tsarin gida wannan ya miki?
Ta kalleshi, ban gane ba.
Ina nufin idan munyi aure zaki zauna anan nida ke muna sama mamee na nan..... Yau na shiga uku ta fada tana tafa hannuwa.
Don Allah ka rufa man asiri ni wace amsa zan baka?
Zai kara magana ta daga mishi hannu nidai canza magana baka da amsar wannan.
Yayi murmushi. To kina iya mun list na abinda kike so batun lefe nake da kamar irin kayan kitchen,....... Ta mike yau firar taka duk kame kame kakeyi sai da safe..... Yayi saurin tarar ta, ya hakuri ki dawo wasa nake.
Ta koma tana hararar sa,
Yayi murmushi, ke yanzu baki iya fada man abinda kike bukata umaimah?
Kinji?
To wai me nake bukata saboda Allah, a hakan ma na gode Allah ya kara arziki.
Ko muyi chatting?
Hummm,
Kinji?
Ohh ni! Ta fada,
Kiyi hakuri mana.
Kaini fa bani bukatar komai.
To takalma fa kina son masu tsini?
Ta mike wallahi kaga tafiya ta yau firar taka tafi karfi na,
Yana tunkurawa tayi ciki da gudu...............


*Ayi hakuri da kadan*πŸ˜ƒπŸ˜ƒπŸ˜ƒπŸ‘†πŸΌ


*Maman Abdallah taku ce*😘😘😘😘
[1/27, 7:43 AM] β€ͺ+234 806 091 7227‬: πŸ’‘ *AUREN FARI* πŸ’‘


0⃣2⃣9⃣


......ya yi murmushi, lallai kina da kawaici da zurfin ciki.
Washe gari ya tafi Abuja.
Yaya kuwa mamee na kiranta tafada mata sai ta hau zage zage wai har yaushe madakin ya sami mata ba a fada mata ba sai da aure yazo?
Bakin ciki da bacin rai ya taso mata, bata taba tunanin zai yi aure haka da wuri ba amma ga mamee ita hakan ma ya jima.
Abinda su yaya keso ko motsi mamee zatayi ta sanar dasu, sannan basa iya tsinana mata komai sai magana da gulma.
Ga hassada, ita hassada mutane basu gane ba, ciwo ce, uwa daya uba daya ana hassada. Kawai sai dai addu'a Allah ya raba mu da kullihin musulmi da ita.
Yana dawowa bayan an sha ruwa ya ce umaimah ta shirya zai kaita gida suyi bankwana .
Jikin ta yayi sanyi.
Suna fita ya kalleta ko dai bakya son zuwa?
Me ka gani?
Duk kin wani darare,
Ta ce hummm,
Kar ki damu kedai kiyo mana addu'a tare da iyayen mu.
Wai kina ma su addu'a ma kuwa?
Tayi yar dariya kwarai kuwa.
Babana fa?
Hada shi.
Ki ce Allah.
Tayi dariya .
Yau ma anan zaka tsaya? , ya gyara parking gaskiya, kinsan manzon Allah SAW ya ce idan alheri ya sameku to ku boyeshi har sai idan ya bayyana.
Ita kadai ta tafi ya zauna yana jiranta a mota,
Sallama tayi duk suka mike ana tsallen zuwan ta, yau ita ce hada dauko kujera wai ta zauna.
Dariya tayi kawai ta raba bakin tabarma. Ta kasa boye mamakin ta. Bayan sun gaisa ta fada ma su abinda ya kawo ta kowa ya fara tsalle ana bata saftu.
Su goggo ta ciki na ciki, amma basu nuna mata ba.
Har zata tafi luba ta ce wai umaimah wanene angon?
Ango? Ta bukata,
Goggo ta dan dungureta ke ban son surutu...... A a goggo kuma fa kuna taso kusan wanene.
Ban gane ba luba.
Jiya wanene yazo wurin baba aka kaishi kauye gaida iyaye?
Gabanta ya fadi, ta tuno dawowar madaki da yan buhunna.
Uhummm kawai ta ce ta tafi.
Tana fita goggo ta ce da luba bita kigano mana ko wanene watakila mai gadin gidan ko direba ne ta samu, don duk yanda akayi jikin gidan shima yake yanda naga malam nata fachaka.
Ta dawo da sauri anya ita kadai take tama shiga gidan Alhaji yakuba.
Duk suka tabe baki.
Sauri sauri ta tarar dashi ya dan kishingida yana jin gwanja.
Ko zama batayi ba ta ce, jiya kauye kuka je?
Duk da yaji faduwar gaba kuma bai san abinda aka fada mata gidan ba sai kawai ya wayance.
Eh, ina ta so in fada miki kinga na manta.
Jiya na je na sami baba akan ina neman izinin fara nemanki da aure ma'ana ( zance ) kamar yanda addini ya tanadar kada suji wai wai a dauka ko na raina su or something like that, shi ne ya ban shawarar in sami lokaci muje kauye na gaida kowa tunda shima yana da na gaba dashi.
A jiyan am free so nayi amfani da daman na ce muje kawai ko nayi laifi?
Tayi murmushi ko daya.
Ya tayar da mota, when last kika je kauye?
Tayi yar dariya gaskiya mun dade.
Shi yasa jiyan akayi ta mamaki wai har kinyi girman da zakiyi aure?
Tayi dariya kawai.
Maimakon gida ya wuce suka siyo ice cream suna tafe suna sha.
Zaki sha ice cream saudiyya mai dadi, ta danyi murmushi kawai.
Me zaki siyo mun tsaraba?
Duk abinda kake so,
A a kawai dai kiyo mun tsaraba da choice naki.
Okay I'll try my best.
Yayi murmushi ya janyo wata leda ungo ga guzurin ki kuyi amfani da dollars sunfi dadin harka.....
A a duk ka hada kabawa mamee idan ina bukata zan karba wurinta.
Ya kalleta da kyau. *Why*?, nake ga hakan zaifi.
To ai itama ga nata nan ya fiddo wata ledar, ta danyi yar dariya yawwa to hade mana wuri daya duk ka bata.......ke ban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login