Showing 51001 words to 54000 words out of 60233 words

Chapter 18 - AUREN FARI Complete by Maman Abdallah.txt

24 Nov 2024

15080

ba sai da yazo da daddare.
Kafarta da safa, hannunta cikin hijab, sama sama ya dan bata baki ya tafi saboda wayoyin da aketa doka mishi.


Mamee kuwa, mutanen ma da bata tunani su ta gani. Gudummuwa kuwa tama rasa in da zata kudi. Saboda wannan shine bikin ta na farko tun haihuwar Madaki bata kara tara taro ba sai yau.
Su yaya kuwa sun ja gefe sunyi zaune banda gulma da hassada babu abinda sukeyi.
Ga hidima sunki shiga ciki, sai dai hakan da sukayi bai rage komai ba sai ma kara ma bikin armashi saboda mutanen arziki ne suka tsaya tare da fidda mamee kunya. Sannan aka sami wasu daga cikin aminnnan suka ringa yada masu magana nan da nan sai duk kunya da rashin gaskiya ya kamasu, ko sisi babu Wanda ya ba mamee cikin su amma kullum suka zo gidan zasu taho da ledoji a jaka su kwashi abinci kala kala, ( kai ya Allah ka raba mu da mutuwar zuciya, da karanta, hassada , jin zafi da bakin ciki ). Amin.
Gidan sai ya fara gagarar su ganin ko sunzo da zuwan nasu da babu duk daya mutanen arziki ke fidda mamee kunyar *AUREN FARI* Na danta kwaya daya tilo.
Karfe goma dai dai aka daura auren *umar madaki da umaimah hamza* a babban masallacin idi.
Yan jaridu, gidajen rediyo da talabijin sai binsa sukeyi amma banda dariya babu abinda yakeyi ya kasa cewa komai.
Umaimah kuwa da ance fito ga yan jarida sai tayi bisa gadon hajiya ta fashe da kuka .
Da kyar suka kwaci kansa shida abokan sa.
Ya kallesu, muje daukar amarya ko?.......
Ka rufar masa ana dariya don ubanka wa zai baka ita yanzu suna tsakiyar shagli?
Ya buga tsaki wallahi sato ta zanyi zaku rufo wata Ku kawo anjima.
Duk suka bushe da dariya ana ci gaba da yi mishi tsiya.
Duk tunanin su wasa yakeyi sai kawai ya bisu da dariya.
Biki yayi biki su umaimah na daki sai kuka akeyi kawaye na waje ana rawar asharalle,
Kokari yakeyi ya zille amma mutane sun hana,
Da kyar ya samu ya kutto.
Nan ma kofar gidan su umaimar yaga mutane da maroka cike, ya tabbatar idan ya fita ya sunan sa sorry, cikin bakar jif dinsa yazo daga shi sai driver yasan ko ya kirata bata dauka ya kira khausar ta fito da sauri.
Ya daka mata tsawa malama shigo mota kada ki hada mun *Go slow* tayi saurin shiga. Jeki lallabo mun umaimah ki kawo mun ita don Allah.
Ta ce toh.
Tayi tsaye gabanta ta rasa wace dabara zata mata, ta zauna kusa da ita,
Kizo inji yaya Madaki.
Ta harareta cikin kuka,
Ina ga fa zuwa yayi ya tambayeki yaushe za a dauki amarya ya ce ya kira wayanki a kashe.
Ki tashi kin san halin shi in har baki je ba tabbas yanzu zasu kawo mota amma idan kika je Kice mishi sai zuwa dare ko kuwa?
Uwar wa kike fada mata? Hajiya ta shigo,
Ta waiga da sauri mama yaya ke kiranta waje,
Au to tashi kije umaimah kinji.
Ta mike suka wuce.
Khausar tayi saurin bude mota ta turata, ita kuma ta shiga daga gaba yaya gata nan.
Ya kalli driver kai muje...................


*Barkan mu da juma'a*


*Maman Al'amyn , Amynatu da Abdallah*😘😘😘😘😘😘
[1/27, 7:43 AM] β€ͺ+234 806 091 7227‬: πŸ’‘ *AUREN FARI* πŸ’‘



0⃣3⃣2⃣
..... Ta firgita ta daka ma drivern tsawa *Wallahi ka tayar da motar nan zan shako ka ta baya muyi hatsari.....* ya rikota ke umaimah...... Ta fizge au an daura auran ma bazaka shafan lafiya ba? Wai meke damunka? Kwallah suka shatato mata.
Gaban khausar ya buga da karfi yaya madaki umaimah ke ma tsawa? *Kut*.......
Umaimah wallahi wallahi idan baka fidda ni motar nan zan bala'in kunya ta ka yau........ Ya bude kofa da sauri *Allah ya baki hakuri*........ Ta fito da gudu tayi cikin gida.
Khausar jikin ta yayi mugun sanyi ta bude mota zata fita ya kirata a hankalii, khausar, da sauri ta ce na'am,
Ki kulan mu da ita please , taci abinci?
Saura kadan tayi dariya ta ce au wai yaya abincin zaka je ka bata yanzu?...... Ya dalla mata wani mugun kallo ke tambayar ki nayi don ubanki.
Tayi sukuy sukuy, eh mama na bata tana ci ko bata so.
Okay jeki kawai.
Ya bita da harara kamar ita ta kashe zomon.
Ta murguda baki kaiji yaya zai huce a akaina. Ta kara jinjinawa. *Kut* lallai umaimah *Tabbb*.... Haka ta ringa yi har ta shiga ciki.
Yana hawa sama abokai suka yo mishi chaaaaa ya sha mur ya wuce dakin sa. Nan ma cike da mutane, ya ingije *Ibrahim bababa* ya kwanta ruf da ciki.
Duk aka kwashe da dariya kuzo *Madaki zai fara kuka*.........nan aka yayyabeshi ana mishi tsiya.
Khausar ta shigo ke umaimah haka kike wahalar da yayan namu? Ina ma laifin....... Khausar fita don Allah ta daga mata hannu.
*Mamza* tayi tayi umaimah ta tsaya ayi mata kwalliya tace bata so a bari sai anjima idan za aje dinner.
Karfe uku aka zo a ka tafi da ita gida anan aka mata fada tun tana kuka ana ji har ya kasance sai dai hawayen kawai ke fita.
Karfe hudu aka dauki amarya, akayi akayi *madaki* yazo su bar gidan ya ce wallahi ba in da zai tafi.
Haka aka kawo umaimah saman cike da abokansa aka wuce da ita daki, sai leken ta akeyi kowa so yakeyi yaga fuskar matar *Madaki*
*Bababa* ya kai mishi duka to don ubanka gata nan mun kawo.
Ya balla mishi harara au bata ce *Bata zuwa ba?* ya maida kansa bisa filo *Duk wayon amarya sai ansha man ta* aka dau ihuuu...... Duk saman benen ya amsa. Hankalin umaimah ya kara tashi ta fashe da kuka,
Da kyar aka lallasheta bayan magariba aka mata kwalliya shima sai da khausar ta kira mamee ta waya ta mata magana.
Takwas dai dai aka fito za aje *Dinner* duk ya rikice kagare yake a fiddo mishi ita. Wani matsiyacin farin boyel ne fari jikin sa kai *Madaki* yayi kyau samira na gefe yake kawai takeyi tana bala'in son *shi* amma inaaa ya mata nisa yau.
Yanda yake ta rawar kafa yasa ta kara saduda.
Yana zaune cikin mota shida Ibrahim sai faman tsoki yakeyi shi kuma banda dariya babu abinda yakeyi mishi.
Ya hango an riko mata riga yan jarida anata binsu da camera ya bude mota.......ya riko hannunsa please *Basar*....... Ya fizge *ubanka ne in basar* kawai ya fice yana zuwa kawai ya dauketa yayi sama da ita......
Yan jarida har gudu sukeyi kofar gidan ya rikice da ihu.
Ya shigar da ita mota sannan ya amshi sauran rigar da suke riko ya sanya ya kalli kowa yana yar dariya *Kowa ya shiga mota*......... *Yallabai yallabai*....kawai ya shiga ya ja kofa yana fadin ban taba ganin banzaye irin yan jarida ba yanzu ne lokacin bayani?
Gabana kake zagin yan jarida madaki?
Ya dafe kai *na tuba* ( mahaifin Ibrahim) tsoron Dan jarida ne.
Ta na ta kame hannu idanun sa ya kai visa kunshi ya zaro ido ya fizgon hannuwan *Wawwww* ...... *kaiiiii*...... Ya daga rigar kadan yaga na kafan ta duma mishi kulli ya fasa kara......kai wallahi ban son iskanci zan fita ka nemo driver.......... *Duka na tayi na rantse da Allah* ya fada yana dariya.
Ya juya yaci gaba da Yuki yana fadin *Tamun dai dai* Kyan ka dukan ai.
Ya kalleta *Wallahi na yi sa'a wurin nan tsantsari*...... Bababa ya tuntsure da dariya.
Ya buga mishi harara Allah ya isa ka kara jin firar mu.......... Ta bika, waya hana ka dauko kurman driver.?
Ya tallabo fuskarta yana murmushi, yau dai a barni in taba inda nake so....... Ta tureshi da karfi zata ja baya ya fizgota *Wasa na keyi jira* sannan ya Dan saketa,yana dariya.
Ka dai firgitataka gani idan........ Allah ba kai zaka maido mu ba don na lura nayi zaben tumin dare don ubanka.
Ya kalleta ki ce mun wani abu mana, Ke ko masifa ce yi mun please.
Dai dai mota ta tsaya, ya buga tsoki ni dama suyi partyn abarmu anan ko umaimah?
Lokacin ne ta harareshi, Yayi Har dariya keni ba harara ba *Say something*
Abokan sukayi wajen motar tare da bude su kowa so yakeyi yaga fuskar umaimah, yayi saurin rungumeta ta soke fuskarta kirjinsa,
Duk suka hayayyako mishi *Wallahi kai mugun dan iska ne madaki*
Kyaleshi ai duk janbakinta zai kare a rigar sa yayi saurin dago fuskar ta hakan kuwa akayi ya tuntsure da dariya ya kalli bababa ka tuna bikin *sadiq* da aka mun barin miya?
Duk suka kwashe da dariya yace Allah ya kawota yau ma don ubanka.......ya juya fuskarta *ita ce* .... Duk suka zaro ido aka dau ihu......
Ya kalleta *yau ma kin bata na AUREN ki*
Ta sunkuyar da kai *ita kawai tasan yanda takeji* ga kukan ma yaki zuwa.
Abokanta suka iso aka fito za a shiga.
Sound ya fara tashi na *Because you love me*
Ya kalli wata ya ce malama je ciki kice a sa mana gwanja........ Rawa zakayi yau ne?
Ya kalli umaimah *To gani dai idan ta amince*
Aka kure sautin best wakar sa *Indosa* aka fara taku hannunsa gam cikin na umaimah.
Gunguni kawai abokan sa keyi bayan sa. *Tsakani da Allah madaki ya dauko mace* tabbb *Ziza*.....:Bashir ya ce *Kai ai wallahi tana da kyau ko hasadun izaa hasada ya ga waccen yarinyar sai ya ce tayi*
Duk aka kyalkyace da dariya.
Yan mata an sha ankon leshi blue da head silver suna ta tattaka rawa, ya dan sunkuyo *ki Dan taka please*...... Ta harareshi dai dai lokacin aka basu flasher....


*Dinner* madaki da umaimah ba a taba irinta ba a kano. Da aka yanka *Cake* ya debo ya bata ta mika hannu aka fara dariya sai zumburo baki takeyi tana fushi ya tabe baki ya sanya mata aka dau *sowa*, wurin bashi nan ma sai da akayi daru ya kawo hannun ya kai bakin sa da kansa, ta wurga mishi harara. Abikan sa sukayi ta kyalkyatar dariya *kai madaki yau na shan harara* shamsu ya fada, bashir ya ce ashe duk kun lura.
Shagali har kusan biyu sannan aka tashi maganar ciye ciye da liki ba sai an fada ba.
Umaimah dai da ance amarya da ango su fito sai tayi tsaye, yayi yayi suyi rawa takiya shi ma sai ya basar.
A gida kuwa , su yaya bayan an tafi party suka hau sama ganin dakuna ana tabe baki,
Ta kalli jamila duk shi yayi komai 'yar kawai aka bashi.
*Hummm* ai ta raina mu kina ganin damu da banza duk daya sai su *maryam hamza* su ne gaba gaba dasu ake komai.
Haka suka yi ta gulma da korafi ko *dinner* sai da kowa ya tafi har an fara suka isa, ko wace ta ledojin ta a jaka na kullar abinda duk aka ci.
A mota suna zaune anata tafiya da mutane, tayi shiruuu kanta sunkuye gani kawai takeyi tamkar a mafarki.Ya mata rada a kunne *Ko sai na siyi bakin za amun magana?*
Kirjinta sai bugawa yakeyi.
Dabara ta fado mishi, ya dan kawar da fuska ina so in fada miki jiya da sai dai kiji mamee a asibiti...... Ta juyo da sauri *Me ya sameta?* ya sha mur hayaniyar mutane ce kawai.
Muryar ta duk tayi sanyi ta canza ta ce *Amma da sauki yanzu ko?*
To ban dai sani ba saboda yau din sau daya ma na ganta...... Ta ce hummm
Ya kusa yin dariya. Me na yi kuma? Ko ban kyauta ba dana fada miki?
Amma da ka kara komawa ka dubota ...... Ya kyalkyace da dariya.
Nan da nan ta gano shi.
Ta yi kasa da kai tana murmushi.
Ya kalleta duk kin rame kin sa ma kanki damuwa zaki zo gidan *Madaki*
Ko kuwa ramar ta an dade ba a kawo ki bane?......... Ya mu ta fi ko?
Bababa ya shigo yana kokarin tayar da mota.
Ya harareshi yi ka sauke mu na gaji da kai *Disturber*.
Suna isa, wani abokin sa ya zo suna magana ta sulale ta gudu.............
Bai kara ganin ta ba sai washe gari da yamma an fiddo ta sashen mamee tana gaisawa da mutane ya hangota lullube, har ya juya zai tafi bashir ya fizgeshi sukayi waje............πŸ˜ƒ


Ba nan na so tsayawa ba na gaji araduπŸ˜ƒ


*Maman Abdallah*😘😘😘😘 juma@ mabruk
πŸ’‘ *AUREN FARI* πŸ’‘


0⃣3⃣3⃣


*NURY*😘😘😘😘 *only u!*


........ Duk ka tsorata 'yar mutane don ubanka.
Ya kyalkyace da dariya, yarinyar can wallahi bazaku gane ba gwala ni takeyi kamar kwallon kafa.
Karya kakeyi kai da kace babu macen da zaka bi, baka ba mace hakuri, baka......Alhaji anji.
Suka kwashe da dariya. *waya fada maka barno gabas take*
Umaimah nata, kuka mamee sai lallashi takeyi, jamila ta turo baki *Yaya dubi mutanen ki*.... Ta tabe baki sa ji dashi kilibabbu.
Kinga sarkar da ta sanya jiya? Murja ta fada tana tabe baki.
Jamila ta ce ki duba wuyanta kiga ta yau tafi ta jiya sau hudu.
Aikin banza waccen figaggar yarinyar cinye su zatayi har babu.
Ai kunji tayi shiru har yau taki cewa da mu komai saboda munafunci da shegen zurfin ciki. Yaya ta fada tana mazurai.
Ku jira Ku gani waccen maryam din data fifita fiye da mu zanci ma uwa munafukan banza..... Yo yaya bakiga kudi ma ita take ba ajiya ba?
( uwa daya uba daya gaskiya basu duba wa mamee ba. Allah ya raba mu da hassada )
Hassada ciwo ce wallahi, uwa daya uba daya akwai ta kawai ta wasu tafi ta wasu fitowa,
Mamee ta ringa raba atamfofi super, da barguna masu kyau na kasashen waje, ga wasu robobi, bokitai, glass cups, kai kaya barkatar, su yaya sai tabe baki sukeyi *Karyar banza*
( wai arziki kamar na madaki a kirashi da karya )
Akayi budar kai, kowa na ba umaimah kudi kamar yanda al'ada ta nuna su yaya na zaune turus!
Bayan an maida umaimah sama suka baje bisa carpet, yaya ce me korafi *Naga ana wucewa da tuwo mu banda mu?*
Hafsat tayi tsagal, tuwo zakuci? Yanzu kuwa, ta lodo masu har sai da yaya ta ce wannan tuwo kamar rugaye?
Ta yi dariya tare da yada masu magana ta ce *wai don kuci Ku dauka kamar kullum* Duk sukayi damama ta wuce bata bi ta kansu ba ta ciko wata yar roba da man shanu ta kawo masu da ruwa da lemu sannan ta rike kugu da yake takadara ce ta ce *Sai me?*
Yaya cikin yake ta ce tuwon ya mana yawa da akwai leda dana dauki biyu saboda dumame....... Jamila ta yi karaf nima zan dauki biyun nan........ Hafsat ta ce baku da matsala yanzu zaku ga tuwo, ta je ta sami ledoji hada Wanda zataci ta lodo masu sannan ta ciko wasu robobi da miya ta ce duk gashi ai tuwo baya hada fada gidan mamee.
Duk abin nan mamee ma bata San wainar da ake toyawa ba. Kawai masu tare fada ne Allah ya kawo mata.
Dama hafsat hake take dasu wurin party ance iyaye su fito kawai su yaya suka kalleta suka ce *Sai kuje iyaye* haka kuwa akayi ta tafi ta dunga rawa daman mamee ta bata himilin kudi ta ringa watsama ango da amarya.
Ganin yanda hafsat keyi duk sai suka tsargu rashin kyautawa ya dan damesu. Suna gama cin tuwon suka sulale ko bankwana.
( kai Allah ya ganar da masu irin wannan hali ).
Karfe tara abokai sukayi sukayi su rakashi ya ce wallahi shi zai kai kansa.
Sai da ya sallami kowa sannan. Suka mishi addu'a sosai saboda sunji dadin bikin sa yanda ba a zato ya bada gidan man shi daya duk Wanda zai tafi yaje yayi full tank.
Banda kayayyaki da ya raba, generator, spare tire , mashin mashin, kai abubuwa barkatai.
Ya shigo karfe goma da kwata, mamee na ciki ita dasu hafsat, ya leka suka gaisa ya fito mamin ta biyoshi, ya zauna falo, mamee na gaji.
Ta yi dariya da gajiya *madaki* sannu da kokari wallahi ka cika *Da* na gode Allah ya shirya maka iyalinka ya baka zuri'a dayyiba.
Ammkinnnn mamee love, ya kukayi da mutanen ki?
Tayi yar dariya kai lafiya qalau, girgiza kai kawai kawai yayi yasan fada mishi ke bata son yi.
Uwani duk ta tayar da hankalin ta. Ta fada tare da langabe kai.,
ya danyi murmushi kawai,
Ta kalleshi don Allah ka dubi maraicin yarinyar nan kaji tsoron Allah. Wallahi rikon maraya yana da matukar muhimmanci ga rayuwar dan Adam. Da mutane zasu gane falala da kuma dunbin rabon da mutum ke samu idan ya kyauta ta wa maraya lallai da wasu sun ringa bi gida gida suna sallamawa duk in da yake su dauko.
Mamee zan kwatanta na sani.
Ta harareshi na san ka da zafin kai madaki uwani yarinya ce kada ka biye mata don Allah.
Kadai ji yan surutan da yan uwana keyi idan ka rike kanka idan kuma ka banzatar wallahi zan dauki mataki....... Zan kiyaye mamee.
Jikin sa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login