Showing 45001 words to 48000 words out of 60233 words
Chapter 16 - AUREN FARI Complete by Maman Abdallah.txt
son rashin wayewa malama.
Ta dan harareshi Kaine ba kauye don Wanda ya waye baya gardama kai kuwa kullum sai anyi musu da kai.
Ya ma rasa me zai ce mata?
Kamar ya janyota ya rungume amma ba hali. Ya dan lumshe ido, Alhamdulillah wani jinkirin alkhairi ne tabbas Allah ya karbi rokona.
Ya dan kalleta,
Umaimah duk umara ko hajjin da zance wallahi addu'ata ya Allah ya bani mace ta gari wacce zata soni ta kauna ceni badon kudi ko kyawuna ba, sannan yasa ta so mahaifiyata kamar yanda nake sonta, ta tausaya mata fiye da yanda nake tausayinta.
Ta danyi murmushi, kaima da wata magana, su iyaye ai na kowa ne, wallahi ko na sona ko baka sona mamee ta dauketa tamkar mahaifiyata, bata kyamace ni ba, bata taba zargina ko guduna da duk wani abu nata ba, ta dauki yardar duniya ta dora mun ta yaya zan taba gudunta ko wani abu ya nemi hadani da ita,?
Wallahi ko a lokacin da bama jituwa idan bala'in yayi bala'i naso guduwa sai in tuna yanda ta amince mun sai na gwammace in hakura da takurawar taka in mata halacci.
Ya runtse ido tare da danna hon....masu gadi suka rugo ya shige da motar,
Na ga irin kulawar da kike bata, naga yanda kuke son junan Ku umaimah wallahi nima na yarda dake 100%, kuma ban taba zargin ki ba.
Ya kashe mota lokacin da kike mun gyaran daki baki ga kudade ba?
Na gani wallahi.
Ya juya ya kalleta sosai, wallahi ko buhun kudi na ajiye aka taba ina ganewa, lokacin da na kunna CCTV ina kallon yanda kike kara gyara man kudin hankalina ya tashi domin Wanda duk kika San ya shiga dakin nan wallahi sai an mun sata, shi yasa na hana kowa.
You are different umaimah, cikin dubu da kyar za a sami goma irinki.
I love you with all my heart, ni kadai nadan yanda nake feeling, ta danyi murmushi ko? Ni ma haka.
Suka fito tare da jerawa, yana fada mata yanda ya kagara ta zama matar shi. Sai dai tayi murmushi ta ce *Uhumm*
Mamee na kishin gide falo suka shigo hannuwan sa da ledijin kudin su, ita kuma da dan kingin ice cream,
Cewa zakuyi kwadayi kuka biya shi yasa naji shiru. Mamee ta fada tana ta kokarin tashi zaune,
Ya dan zauna umaimah kuma ta tafi can kusa da ita, gashi ma na rago miki nayi nayi ya siyo dake yace a a.
Ya zaro ido ke.....
Mamee ta karba tare da hararar sa na sani uwani nasan babu yanda zaki mance dani.
Ta yi mishi gwalo, mamee na satar kallonta.
Ya nunata da yatsa nafiki iyawa yarinya.
Mamee ta ce kwarai kuwa ka fita iya rowa.
Suka yi dariya ita da umaimah ya sha mur ni zaku hade ma kai?
Ta kama kunne sowie wasa ne ko mamee?
Shi yasan hakan ne,
Ya kyalkyace da dariya dole aban hakuri........ Ohhh son girma kamar maruru!!
Me umaimah zatayi ba dariya ba kaii mamee wai maruru.
Ya mika mata ledojin kudin ga guzurunku, kince kowa na ware mishi gata nan taki karba tace sai dai na hade duka na baki idan tana bukata sai ta karba.
Mamee ta kalleta da sauri , dalili,????
Zatayi magana ta sha mur ke bani son iyashege yanda nake fama dake anan ina ciwon baki ki dauki kudi kiyo siyayya haka ma can kike so inyi ta babatu?
Maza karba kada ranki ya baci,
Ta dan langwabe kai, haba mamee ni fa ce uwani, kin manta ni ke rokon kudin tsamiyar biri......... Ungo ta yi mata dakuwa, naira ashirin hamsin din?
Ta turbune fuska tare da mikewa, so kawai kike yayi mana dariya kin gwasaleni ta wuce tana zumburo baki.
Ya kyalkyace da dariya na ganku a rana....
Ta harareshi kai tafi can samna, yanzu kai matsayin ka na miji baka iya dabara da lallashi ta karbi kudin ko?.
Nasan uwani da kawaici wallahi kunya bazata taba barinta ko taga abu ta nuna tana so ba, in kuwa hannunta suke tafi sakewa.
Ya watsa hannuwa kawai kiyi ta zuwa da ita kina nunnuna mata amma kada ki bari ta siyi zinari ko zobe, kuci dadi kusha dadi please.
Sai yan kayan kyale kyale sannan kuyo mun tsaraba don ta dawo mun hannu biyu akwai rigima.
Mamee ta mike kilibabbe sai ka ce tayo ma ba muyo ma tsaraba ba.
Kai Allah yasa maka kunya ni *Rabi'atu* ta wuce ciki.Washe gari karfe sha biyun rana su umaimah aka tantsa kasa mai tsarki a *Madaki airline* an kame first class anata wulakanci da rai, da jirgin zai daga yan cikin ta suka yamutse ta kama mamee gammm tace *Wayyooooooo yan hanjina*
Mamee ta tuno umaimah fa bata taba hawa jirgi ba sai ta hau tofa mata ayatul kursiyu. Ta na warwarewa ta kalli mamee *Kut yau na jiyo kamshin lahira*
Me mamee zatayi ba dariya ba?
Madaki kuwa koda yaga tashin su sai kawai ya koma gida don fara shirye shirye saboda hatta hotel din da zasu sauka madina titi kawai ya raba shi da masallaci daga dakin su idan an kira sallah ma suna ji.
Haka garin makka,
Ko motoci akwai wadanda zasuyi jigila dasu inda duk zasuje.
Cikin kwana uku yasa aka fidda kayan gidan daman yayi order wasu daga *Italy*
Sai da aka fente gidan kaf sannan ya mayar da kayan gaba daya tsarin gidan ya canza. Su kawu keta shige da fice da matayen su tare da sauran yan aiki.
Aka kara ma gidan securities, Ga kayan da yayi order na lefe daga kasashe daban daban nata zuwa.
A saudiyya kuwa, mamee ta zama yar gata, bata taba umara mai dadin wannan ba saboda ko abinci umaimah kamar ta bata a baki. Ga ibada tunda ta gane hanya kullum masallaci karfe ukun dare ta ke tafiya sai asubah sannan mamee ta isketa , haka da suka makka.
Duk abinda mamee ta tambayeta me zata siya sai tace turare, ko a madina katuwar jaka tayo. Musamman da mamee ta fada mata cewar ba za a yi masu awo ba. Ta saki jiki duk abinda takeso ta siya.
Har sai da ta kare tayi mata magana a wani babban shago dake *Shahara mansir* uwani wai duk shagon da muka je sai kin siyi turare? Anan fa duk Inda kikayi siyayya kina karawa gaba zaki ga mafiyin sa ko wanka zaki ringa yi da turarukan nan sun isheki hakanan jakuna biyu? Haba.
Ta kaita wani shago na inner wears sai mameen ta dan fita ta bata wuri tare da ajiye mata makudan kudi nan ne ma ta yi ma kanta siyayya amma duk turarukan nan madaki take kwasar mawa tsaraba.
Domin ta rike da turarukan sa wani ko ta mance sunan tana ganin kwalbar zata tuna.
Yaya tazo daga Kaduna ta tarar da gida yanda ya koma hatta fitulu an canza su. Ta buga ma jamila waya hankali tashe kinga gida?
Wallahi abu sukeyi daga ita sai danta babu shawara don ta daukemu sakarkaru.
Haka sukayi mahada suka bude babin tsinewa mamee suna mata mugun alkaba'ai sannan sukayi alkawarin ko kwandalar su gudummuwa kuma bikin ba wani abinda za ayi dasu zasu zuba mata ido.
Madaki kuwa bai tsaya gidan shi kadai ba hada gidan malam bawa a lokacin ne su goggo suka san wa umaimah zata aura.
Gyara abinda ka gyara yayi masu ko wace ya canza mata kayan daki ga abincin hidima ga kudade azumin nan fa su basa jin sa ko kadan.
Jakunkuna set shidda yayi mata ko wane set guda Biyar ne.
Kamar lesussuka da shaddoji *Marley* ya bada aka dinko mata, atamfofin ne ya bayar *Ghana* shima wata manager sa ke fada mishi.
Bani iya lissafa lefen umaimah kawai a kiyasta ga tunani. ( don kun san wurin akwai wulakanci da rai ).
Ya bugo kati, ya fara rabawa iyaye kuma sunje kai kudi dukkan su suka dawo da son barka.
Abokan sa ko wa yaji burin sa ya san wacece wannan?
Musamman yanda sukaga madakin na rawar kafa kowa sai abin ya daure mishi kai. Tambayar daya ce *Wacece wannan lucky girl?*
Kowa kagare yake yaga umaimah.
Mamee kuwa ba ita kadai ba mutanen da suke hulda dasu a can babu Wanda baya sanya ma umaimah albarka yanda take kula da mamee wata mata har cewa tayi mamin ta bata ita danta ya aura tace ai itama surukarta ce.
Babu Wanda baiyi mamaki ba wurin saboda duk daukar su mahaifiyata ce.
Wannan ya kara sa mamee taji ta kaunaceta fiye da baya.
Waya kuwa a rana suna iya wayar fin dubu ashirin ita da madaki saboda a can akwai tsadar kira kwarai da gaske ko shi ya kirata sai an debi kudin ta haka itama . sunfi yawan waya bayan azahar da kuma la'asar sauran lokutan baya samunta tana masallaci.
Yayi yayi ta tura mishi hotuna takiya, shi kuma yana son amfani dasu ne a bubbugo abubuwa.
A kasansu tayi kawa wata barabiya sunan ta *Fatimah* kullum umaimah na gunta bayan isha'i tana koya mata yanda suke yafa gyalen jallabiya a fuska yayi kyau. Ta koya mata kuwa kala kala.
Ranar da zasu dawo baiyi barci ba.
Da kanshi yaje daukosu airport, jirgin na tsayawa motocin na karawa.
Yana ta dube dube, Bai gane umaimah ba tasha wani katon glass baki da wata matsiyaciyar jallabiya ta yane fuskar ta da gyalen tayi nadin larabawa, ya dan kawar da kai yana kara kallon kofa sai kawai mamee ta fito yaga umaimah ta mika hannu ta rikota ya zaro ido tare da hayewa matattakalar........
.
*Maman Abdallah*
😘😘😘😘😘😘😘
[1/27, 7:43 AM] ‪+234 806 091 7227‬: 💑 *AUREN FARI* 💑
0⃣3⃣0⃣
..... Tana hango shi tayi saurin cire glasses din ta dan ja baya tare da dan bata fuska.
Ya dalla mata harara malama ba taba ki zanyi ba kwantas, ta danyi murmushi ganin har ya karanto abinda take nufi ya ruko mamee tayi saurin janye hannunta ganin yana niyyar dan shafowa.
Ta harareshi *Ni zakayima wayau?*
Zaku fara? .... Zaku fara ko sababbu?
Mamee ta fada
Yarinyar nan mamee muguwar bagidajiya ce wallahi ji yanda ta yankwana ni,
Da ta maka me?
Ya kara hararar ta ba sai ta rugo ta dan rikeni ba ko ba arzikin *Hug*....... Tooo lallai kunnenka na kashi ne, to bazatayi hakan ba.
Ya kyalkyace da dariya wasa nakeyi...... Bakinsa ya rufe ganin yan jaridu kamar an ingizo su.
Ya daga masu hannu da sauri kada su ballo mishi ruwa, *Kada Wanda ya ce wani abu* bani da wannan lokacin suka wuce.
mamee ta fara salati da sallallami. Ganin yanda gida ya koma, suna shiga falo ta yi turus!!, daman bai shigo ba ya dan tsaya waje da wasu baki.
Aka fara shigowa da jakunkunan su ana wucewa dasu daki.
Ya shigo da sauri mamee wai wadannan iyayen jakun kunan na menene kuka kwaso?
Ta nuna umaimah gata nan bacin na mata magana kilan da ta rungumo makka ko madina wannan da kake gani.
Ya tun tsure da dariya abu yazo ga ma iya.
An dawo lafiya?
Darling welcome....... Mamee ta wuce ciki tana kwakwazo, wai duk yaushe aka yi aikin?sati ukun da bama nan?
Umaimah ta dan zauna ya zo gaban ta ya zukunna. Wallahi kin canza kinyi kyau umaimah anya zan zauna da ke Nigeria? Wannan fatar bata nan kasar ce ba..... Ta danyi murmushi , mun sameku lafiya?
Ya mike ya zauna kusa da ita, ke ba lafiya lau ba na galabaita wallahi.
Ta danyi dariya, a hakan?
Ya harareta kawai. Ina tsarabata?
Kai ciwon ciki ..... Ka daiyi hakuri ko ruwa in sha ko?
Ya kyalkyace da dariya ni ne ciwon cikin? Gaskiya je ki kawon tsarabata.
Ta ce hummm,
Kinji?
Wai baka bari na in huta?
Aikin me kikayi?
Wallahi kamar an mun tsinannen duka,
Yayi yar dariya wane hutu gareki yanzu?
Bani da shi? Ta bukata tana murmushi. Ya mike tsaye don idan ya saki bai tashi ba sai yayi halin, nidai jeki dauko mun ina jiranki sama.
Zatayi magana kawai ya wuce yana fadin *Ina jiranki*
Kai *Rigimar duniya* ta fada tare da mikewa tayi ciki.
Ta iske mamee tsaye, itama tayi turus!
Uwani kinga gyara?
Ta washe baki, wallahi mamee gidan nan yayi kyau kamar ba shi ba.
Kin dai gani, ai idan madaki yasa kansa abu baya shawara, kina tunanin idan ina nan zan bari yayi wannan almubazzarancin, shine ya koramu yayi bikin kansa.
Umaimah tayi dariya kuma gyaran ya tsaru,
Ta dan kalleta ya yi kyau ma sosai. Ya na ina?
Gashi can ya hau sama wai lallai in kai mishi tsarabar sa.
Sai ki hanzarta ai, neman rigima ce kawai mamin ta shige toilet.
Jakun kuna 3 ne nashi biyu turaruka daya jallabiyoyi da agoguna.
Ta kirawo sadisu ya taimaka mata da na turarukan ita kuma taja na jallabiyoyin.
Yana zaune falo. Yanzu ya daina bari su hadu bedroom din sa, ya bita da kallo, yana ajiyewa ya juya ta dan karasa dana hannunta gabanshi gasu nan.
Ya kalleta lefe kika hado man?
Ta kyalkyace da dariya a'a ka manta *Aure* ya tashi da sauri ya janyo jakunkuna ya fara budawa.
Yayi shiruuuuu , ya kalleta don Allah zauna umaimah. Sannan ya janyo wacce ta riko ya buda jallabiyoyin ma basu da yawa don basu wuce kwara goma ba agogunan ne suka dauki hankalinsa fiye da turarukan.
Ya durkusa gabanta, umaimah: *This gift you gave me was more than perfect in each and every way. Thank you so much for it. I will always preserve and keep it with me forever.* thank you so much my love.
Kun ya ta baibayeta ni dai tashi don Allah.
Ya akayi kika San duniya nafi kaunar turare da agogo?
Na sani mana, ta fada tana wasa da yatsun hannunta. Umaimah ka kira sunanta duk ya rikice, kina azumi? Gabanta ya fadi *Nashiga uku* ko ya gane banayi?
Me zai hanani azumi? Ta harareshi, yayi murmushi in tambayeki zaki ban amsa?
Um, idan ina da amsar zan baka, ta dan kalleshi kadan duk ya diririce,
Ki taimaka man ki aureni umaimah wallahi bani iya hakurin rashin ki, a duk lokacin da kike kusa dani sai inji ina neman fita hayyacina, ranar da duk na wuni ban ganki ba kuwa zan kasa sarrafa kaina in nemi haukacewa.......
Haba dai, Allah na amince da kai kasan haka kuma,
Ki tausaya man, na miki alkawari wallahi zan barki ki karasa karatun ki believe me,
Shi kenan, ta ce a takaice.
Ya mike zo muje ki gani..... Ya fara zagayawa da ita tsarin duk ya canza banda dakin sa ya kara gyara wani an zuba sabbin kayan daki masu launin *White and pink* ta dan saci kallon sa taga ya zuba mata ido...... Ta dan sunkuyar da kai.
Ko bai miki kyau ba?
Ya yi mana!, suka zagaya ta baya dakuna biyu ne na yara daya komai da ke cikin dakin sky blue and white ne,
Daya kuma komai na dakin dark and light pupple.
Ga dakin yaran mu maza daban....... Ta fice kawai ya biyota kin fito ko bai miki ba a canza tsarin?
Ta kalleshi da kyau *Yau me ke damunka ?*
Kaunar ki, umaimah sonki me Neman zautani .
Ka barni na je na huta na gaji........... Ya langabe kai anya kinyi missing dina umaimah? Tayi murmushi nayi mana........ Maganar mamee yajiyo tana kwala mishi kira itama ta hawk saman.
Ta gansu tsaitsaye, kai kuwa akwai fitinannen yaro bazaka barta ta huta ba?
Zaiyi magana idanunta suka kai ga jakunkunan tsarabar umaimah.Ta rike baki *Au daman duk kai ta jibgowa wadannan turarukan?*
Sai kawai umaimar tayi kasa da gudu.
Ta bita da kallo kya gudu ja'ira. Uwani taki ci taki tsinana ma kanta uwar komai kullum ta fita sai ta dawo da turaruka ko agogo.
Ya yi murmushi miji ake ma tsaraba mamee, ta dalla mishi harara kai dai wallahi baka San annabi ya faku ba.
Ya kyalkyace da dariya, suka fara zagayawa, mamee kamar ta goya shi.
Suka dawo falon sa, naga akwatuna dakina set biyu.
Ya ce au zo muje kiga lefe.
Wancen naki ne...... Nawa ne me? Kana hauka nima lefen zakayi mun? Zata fara fada ya rungumota haba mamee love haka zaki ci bikin ba dinkuna?
Ta harareshi kana dai son kara janyo mun zagi gurin su yaya ko?
Kin San kuwa tazo..... Ya fada mata wulakancin da ta zazzaga. Tayi murmushi kawai ta ce *Uhumm*
Kai Allah ya saka ma da alkhairi *madaki* Allah ya baku zuri'a dayyiba. Wallahi duk abinda kayi ma uwani ta cancanci fiye da haka ta bashi labarin kyautatawar da tayi mata saudiyya tana kara fada mishi kyawawan dabi'un ta.
Addu'a takeyi yana ta faman *Amin mamee*
Ta kalleshi don Allah na sanka da saurin daukar zafi kamar wutar murhu madaki ka sanya ma ranka hakuri ga zaman aurenku.
Har yanzu uwani yarinya ce kada ka biye mata kuyi ta yarinta don Allah ka bada mamaki.
Zanyi mamee trust me.
Kamata yayi tunda saura sati daya gobe ta shirya ta koma gida saboda suma a basu daman shirye shirye kuma can su sanar da ita.
Nidai mamee da kin kyaleta nan sai ana gobe daurin aure?
Ta mike saboda kana mahaukaci ko?
Ya marairaice don Allah kitaimaka man mamee , ta wuce ma tabarshi wurin tana fadin abin naka ya wuce mizani.
Ta iske daki tana da yan gyare gyare , to agogo aikin ne?
Ta danyi dariya kai mamee.
Ta zauna bakin gado.
Na wuto su Mansurah nata