Showing 36001 words to 39000 words out of 60233 words
Chapter 13 - AUREN FARI Complete by Maman Abdallah.txt
zauna cinyar sa da karfi, ke kwantas na fada mata mun jone ya karasa maganar yana murmushi tare da kashe ido daya.
Mun shiga uku ta zabura me ka ce mata?
Ke ban son rashinin wayewa baki lura yanda za... Read more
[1/27, 7:42 AM] +234 806 091 7227: 💑 *AUREN FARI* 💑
0⃣2⃣5⃣
Ya fi mintuna ashirin bai ce qala ba kafin Ya dago kai yana murmushi, ko alokacin jahiliyya ranka shi dade ban taba jin anyi haka ba.
Hasali ma idan son yarinyar kakeyi kaine zaka tarar da iyayenta komin kudin ka komin mulkin ka ba iyayen yarinyar zasu kawo kansu ba kamar yanda mukayi yanzu.
Aure rahama ne yana daya daga cikin dokokin Allah da manzon sa cewar a girmama aure a kuma daratta shi, umaimah marainiya ce ni na saki nono mahaifin ta ya kama.
Wallahi matukar nayi mata haka ba la'antar Allah kadai ba tsinuwar dangi da mutanen gari bazasu taba sanya ni in zauna lafiya ba.
Amma ina mai baka hakuri idan abin da na fada bai ma dai dai ba.
Ya juya Allah shi gafarta malam ga maganata akwai gyara?
Ba liman yayi magana ba *madaki* ne yayi
Hakika babu gyara ga maganar ka baba.
Kuma naji dadin maganganun ka . kafin in sanar da kai dalilina ina son ka amsa mun tambayoyi biyu zuwa uku,
Na farko me yasa kabar gidan ka sakaka babu kula?, ya akayi duk yaranka na makaranta banda umaimah?, sannan minene ka gwammace tabi gidaje aiki akan zaman gida bata aikin komai. Saboda ko kafin umaimah ta fara aiki gidana ta dade da fara bauta gidajen unguwar mu?
Yayi shiruuuu.... Kafin ya nisa, idan ma na boye muku to bazan boyewa mahalicci na ba.
Na farko ina iya kacin bakin kokarina a kan gida matsala daya aka sami da na karo mata ta uku shine cin mutunci ya fara shiga har matan nawa suna zagina ko su sanya 'ya'yansu manya su nemi sa'in sa dani. Sai na yanke shawarar idan na fita kasuwa tun bayan fitowata sallar asubah sai talatainin dare sannan zan dawo.
Umaimah kuwa, gaba daya daukota ma da nayi shi ne ya kara jagula duk wata matsala, ko na fita na barta zata tafi makaranta to bata zuwa, tsinke wannan idan na siyo da sunan ta tabbas ranar na janyo mata masifa da ni kaina shi yasa na tattara na watsar.
Aiki gidaje kuwa shi ne in da tafi ko ina samun natsuwa, zata ci zata sha zasu bata tsumma ta daura. Wannan shine dalilina na barinta tana yi don kada yunwa ta kassarata.
Ya juya gun su liman Malam kunji da kunnen Ku?
Hakika munji yallabai. Suka fada. Ya ce good,
Baba, kayi hakuri amma maganar gaskiya dalilin da yasa na kiraka anan shine da ka kuskura an daura Aure na da umaimah wallahi da sai na sa an daureka don ka tabbata baka San *Hakkin Dan Adam* ba, idan kuma baka amince ba to shi yasa na kira malamai don kamar yanda na ji bayanin ka na tabbatar akwai rashi ko karancin ilimi sai Suyi maka wa'azi.
Ina Neman afuwar ka baba....... Ya sunkuyar da kai haba haba babu komai, babu komai.
Liman yayi gyaran murya, to Alhamdulillah, shi musulunci sauki gareshi kuma Aure kamar yanda ka fada ne babba. Namiji ga gidan sa shi *Linzami* ne, shi yasa Allah SWA ya ce *ARRIJALU QAWWAMUNA ALAN NISA'I....* a wurin Allah wannan ba hujja ba ce, Suka fara mishi wa'azi daki daki hakkin iyali, hukuncin Wanda ya zalunci maraya da sauran wa'azi.
Iyakar kunya malam bawa yaji ta, sannan ya tausaya ma kansa akan saken da yayi.
Ya sallami su liman sanna ya ce wadannan kudin baba ka dauki dauri biyu ka ba aminin ka daya, Ku kara jari. Zamu je da kai can gida kaga inda umaimar take domin hankalin ka ya kwanta....... Babu damuwa.
Malam nasidi ya ce nikam zan koma rumfa mun baro yaro marar wayau.
Mansurah ta dunga tuntsurar dariyar keta,
Wai ke ya akayi ne? Sai da tayi mai isarta sannan ta fada masu.
Bilki ta zaro ido anya kina cikin hankalin ki kuwa? Kin manta duka gidan ko ina akwai kamara da yallabai ke ganin komai?
Kina tunanin zaiyi shiru bazai bincika ba?..... Bata rufe baki ba mansura ta baza da gudu tana zuwa ta tarar da kawar khausar ita kadai, daman ta wuto su a kitchen. Ta ce kije inji khausar tana fita tayi saurin bude jakar ta mayar da kayan dai dai lokacin da dayar ta fito toilet.
Tayi waje da Sauri, ta bita da kallo cikin tsarguwa.
Suka fara mata dariyar har taji babu dadi, ke kin fiye sauri irin gidan nan an fada miki haka kawai zaka bigi gaba kayi tuggu? Ko kuwa duk wannan feleken da daukakar da uwani ta samu an fada miki haka kawai ta shigo zikau bata shirya ba? Bilky cikin dariya ta ce, ai idan baki fitar da ita ba ke kya fita saurin me kikeyi?
Suna gama cin abincin suka tafi.
Ita kuma ta kabbara sallah, raka'ar karshe mamee ta fara kwala mata kira, tana karasawa ko addu'a batayi ba ta ruga sanye da hijab din mamin domin ita da gyale tazo,
Gani mamah, Aunty murja ta kalleta Tun daga sama har kasa *Ina kika sami gadararriyar yar aiki?* Aunty jamila ta yamutsa fuska, yaya mai mutane.... Saboda samun wuri yar aikin ce da hijab dinki?
Ashe jita jitan da mukeji da gaske ne tabdi.
Lallai zamu kowa Aunty yaya da bayani....... Au har kunji labarin uwanin?
Kwarai kuwa ance ta raina kowa ke da madaki ma tsoron ta kukeyi to........ What? Aunty jamila kuna hauka ne?...... Mamee ta daga mishi hannu. Sam bata yarda ya raina mata yan uwa ko Kadan.
Babu Wanda yaga shigowar sa. Sukayi sukutiii don tsoron sa sukeyi kamar me.
Baba bisimillah ya daga murya. Umaimah ta zaro ido baba ta tareshi tana yar dariya.
Mamee ta kalleshi alamar tambaya *Baban ta ne* ya fada tare da zama bisa kujera.
Mamee ta washe baki kai maraba maraba. Ya nuna mishi kujera ya dago suka hada ido da aunty murja, kawai ta mike ita ma jamilar tabi bayanta.
Munafukan banza ya fada cikin rai.
Bayan gaisuwa da mutunta juna. Mamee ta kalli sadauki wallahi kayi kokari kayi Kyan kai. Wanin uwani bai taba zuwa gidan nan ba. Ta mike tsaye sannu baba.
Mamee zama zakiyi na sameshi ne akan umaimah ta zauna anan zuwa bayan sallah kada zaryar tayi mata yawa ga azumi.
Mamee ta fadada fara'ar to ya amince da hakan? Umaimah dake kusa dashi ta taunkulo cinyar sa tare da girgiza mishi kai wai yace A'a . sai ya kwashe da dariya ya kai mata duka aka, kaniyar ki da mintsili na....... Mintsili????? Me zasuyi ba dariya ba. Wallahi mintsili na tayi wai in ce A'a. Mamee ta kasa magana don dariya, madaki ya kalleta *Yanzu baban kike mintsili?* ta zumburo baki ta noke kai,
Uwani hoo, mamee ta fada
Ba zaki zauna ba kenan?
Baba ya amince kyaleta mamee ita tana tausayin kanta ne?
Ta bishi da harara,
Inji waye uwani zaki zauna ko kuwa...... Haba hajiya shawara za ayi da ita? Ya mike tayi zamanta can din me takeyi daman ai barci ne kawai ke maida ta.
*Madaki* ya buga kafa *Good papa* mamee ta baka mishi harara. Malam bawa dai kansa kasa yana ta murmushi.
Su Aunty murja na labe, anya wurin can babu alamar tambaya?
Hmmm ai muna ganin ikon Allah ni jamila.
Ya mike zan tafi Allah ya kara arziki. Ta mike ai nima lokacin tafiya ta yayi gobe na dawo da kayana duka,
Madaki zaiyi magana mamee ta daga mishi hannu dole yanaji yana gani tabi baban ta.
Suna zuwa suka tarar da himilin kayan abinci buhu buhu da jarkunan mai banda kayan shayi ba abinda babu.
Matan suka tare shi, suna mishi bayani. Ya ce eh na san dasu daga gidan aikin umaimah ne suka bamu zakka...... Ya wuce ciki.
Umaimar ce ta tsaya yi musu bayanin gidan zatayi azumi. Luba kuwa ta dunga kuka saboda dan kurmusun da sukeyi cikin dare.
A gidan Alhaji yakuba tayi sallar magriba. Ba karamin dadi taji ba amma har yau kunya ta hana umaimah fada mata cewar madaki na son ta.
Tana gidan ya kirata a waya yana jiranta a mota. Bata yarda hajiyar ta ga wayar ba tana soke cikin zane, lokacin da ya kira kuma ta dan fita, ta ce zata koma gida ta shirya kaya. Ta fiddo mata sunkunan ta ta ce ungo tafi da su.
Yana hangota ya fito tare da bude mata kofar mota, *Barka da isowa ranki shi dade* ta dan bata fuska *Ya kake*? Yayi murmushi ya rufe yana shiga ya ce lafiya garas tunda gani gabanki.
Ta ce *Good*....... Malama wai lafiya kike wani basarwa ko nayi wani laifin ne?
Ta girgiza kai ko daya naga dai *Kaima haka kake wulakanci da rai* idan ana baka girma.....
Dariya yakeyi har yana kwanciya, *Kai umaimah ke karshe ce* watan wulakanci nake da rai.
Tayi murmushi eh mana suyi ta kyarma suna tsoron ka....... Ya kara yin dariya ai ke bakya tsoro na ko?
Tayi yar dariya Allah ina tsoron ka..... Ko maganar ka naji sai gabana ya fadi.
Ki ce Allah!
Allah kuwa,
Tabb wallahi nima haka,
Ta kalleshi da sauri yayi murmushi, da gaske nake wallahi dana tunkaro gida sai gabana yayi ta faduwa. More especially idan fararen kaya ne jikina, a office wani lokacin har zabura nakeyi ina firgita idan na tuno masifar ki.
Ba wani nan, kullum kai ne ke tokala ta,
Ai matsalar da na ganki sai inji kawai mu kafsa, saboda ko gardama ba'a taba yi dani ba ko bakiga yanda nake *wulakanci da rai ba*?
Tayi yar dariya na gani kuwa.
Ya kai mata duka,...... Da an canza ma suna yau. Ai nasan hannunka sai ya taba ni.
Ya tuntsire da dariya kin San kuwa dana fara son ki burina kawai mu hadu kina bala'i ni kuma ina rungumrki......laaaaaa ta ce tana hararar sa.
Meye kika kawo mun a leda?
Ba komai dun kuna ne...... Allah? Cewa zakiyi gayu zan sha, ta dan harareshi *Wai ma*...... Wayar sa ta fara ringing ya duba kamar ba zai dauka ba ta tsareshi da ido, yana dagawa ya saisaita murya kamar bashi ne ne raha yanzu ba.
Hellooo..... Lafiya, zan kiraki zuwa anjima ya kashe wayar.... Umaimah ta bude marfin mota yayi saurin fizgota ke ina zuwa?
Ta murtuke fuska zan baka wuri ne don ka sami halin kiran nata ba ma sai anjima ba.......ya kyalkyace da dariya yanzu dai rufo kofar kafin sauro ya halakamu. *kut*.....kishi umaimah ki ce na shiga uku. Tayi kicin kicin ita dole fushi takeyi ya kwanto jikin ta ya janyo kofar tare da locking kawai ya baje bisa kafafunta....... Malam daga ni banda kwari kada ka karya ni.
Ya mata banza ya latso lambar da aka kirashi, yasa hands free, hello sir,
Yawwa ina jinki menene?
Dama jirgin nan ne da zai sauka lagos da kaya yazo, na port Harcourt kuma munyi waya in the next two hours zai iso.
Okay yayi kyau sai ki kira *BASHIR* Suyi magana da Agents.
Okay sir, ya kashe yana kallon umaimah, *What next?*
Ta danyi murmushi yo wani abu na ce?
Sai kince wani abu? Gashi zaki gudu kuma wai ni duk ina kokarin baki full time bana son wani issue ya shiga lokacin ki.
Wasa fa nake... Ya tallabo fuskarta karya kikeyi wallahi kishi ne.
Ta runtse ido *Wayyo Allah* ya tashi da sauri lafiya?
Kafafu na sukayi *Yami*
Ya kyalkyace da dariya wallahi baki kyautawa yami kamar wani kwanannen abinci?
Ya bata labarin yanda sukayi da Babanta, ta ce, Ohh Allah sarki. Ashe Allah yamun *Alam nasharaha* ta banka mishi harara ai wallahi da kauye zan gudu.
Ina zullumin gobe wallahi saboda zama kusa da mamee takurani yakeyi banga dalilin da zaisa ka assasa sai na dawo gidan da kwana ba.
*Baza ki gane bane yarinya*
Gobe zan aiko a daukeki da safen saboda kayanki....... Bana so. Ya yi murmushi to kawo wannan nayi miki gaba dasu.
Hmmm kawai ta ce,
Sai sha daya saura suka rabu.
Karfe tara ta fito gida amma anan waje ta tarar da drivern shi. Babu yanda ta iya dole ta shiga, su lubabatu na ta mamaki. Malam bawa kuma yaki cema kowa komai.
Isarta bata tarar dasu Aunty jamila ba madaki ya masu korar kare jiya bayan ya koma ya tarar sun tsare namee suna mata tambayoyi da maganganu akan umaimah.
Karfe goma ya sauko zai tafi office mamee ina uwani?
Ta na ciki tana shiri,
Shiri?
Eh zan aiketa cikin gari ne.
Okay to tayi sauri na ajiyeta daga nan mu biya office kawai ta dawo miki da sakon,
Kwarai kuwa kaga har na manta da munyi maganar.
Ta fito cikin atamfa dinkin doguwar riga yasha stones, ta yafo dan gyale batayi tunanin yana falon ba ta fito da gyalen a hannu tana gyara dauri.
Mamee ta washe fuska, fara'ar ta ta karu, Uwani ashe kin dinka atamfar nan?
Nima kuwa yau tawa zan saka kai amma naji dadi. Ta danyi yar dariya, waya miki dinkin nan?
Hajiya ce ta bada mun......au haba?
Ya kasa motsi kamar ya rukota yakeji kalacin da bai karasa ba kenan ya ce muje kawai,
Ta kalleshi tana harara....... Mamee fada mata kada ta batan lokaci ya fara duba agogo.
Zai ajiyeki ne amma zaki karbo mun sako wurin sa.
Ta ce toh, suka fita,
Yana rufe kofa ya janyo ta *Wai ke yaushe zaki waye?* Me nayi?
Ba ko gaisuwa? To sakeni dai ka kalli gabanka, bai saketa ya dan waiga masu gadi ne da jama'an gida suka taho gaisuwa.
Ya kara riketa ya sha mur,
Haka ya gaisa da kowa duk wanda ya gaidashi sai ya ce *Ranki shi dade barka da safiya* mutum biyu ta amsawa, kunya ta dunga tsunkulin sa ta baya yayi mata banza.
Suna shiga mota ya shako wuyanta ke wai *Yar fari ce?* ........ *kuma auta* ta fada.
Kina mintsili na gaban mutane.
Allah cizonka zanyi.
Ya kyalkyace da dariya.
Yanzu ni zan gaisheki ko kuwa kece?
Wanda duk ka zaba .
Yayi murmushi ina kwana,
An tashi lafiya?
Ya kara yin dariya naga kin fara *Wulakanci da rai* ta yi murmushi *Wai ma*
Ya na zuwa office ya tarar da dandazon yan jaridu, yaki fita mota ya ce maza ace su tafi sai karfe biyu su dawo baida appointment da kowa yanzu.
Sai da ya tabbatar sun watse sannan suka fito shida umaimah taki jerawa dashi daya Dan waigo sai ta nemi kwasawa da gudu ta rike riga,
Ya sha mur meye kikeyi haka?
Eh anji wuce dai muje zan bika abaya.
Murmushi kawai yayi ya wuce body guards sun baibayeshi sunata mazurai.
Dai dai an bude mishi kofa wata matashiyar mata ta iso..... *Yaro matashi*.......ya waigo da sauri yana murmushi tana zuwa ta fada jikinsa sukayi *Hugging* umaimah ta ja baya da sauri tare da fiddo ido kirjinta ya buga da karfi.
Tare suka fara shiga office din , umaimah na ganin haka ta yi baya tabar wurin da gudu.
Tana fita harabar office din ta tari mashin tare da fadin *TAL'UDU*................
*Good morning all*
*Maman Abdallah*😘😘😘
https://chat.whatsapp.com/8RrbAeADj5FLV7LZ24rBDH
💑 *AUREN FARI* 💑
0⃣2⃣6⃣
........... Ya waiga bai ga umaimah ba , ya fito da sauri ko tsayawa tayi , babu ita... Ya kira security din sa da suka zo tare yana tambayar sa yayi damama ya fara dube dube ya daka mishi tsawa *Are you mad*???
....... Hankalin kowa ya dawo wurin duk aka mimmike tsaye, billahil azim idan baka nemo mun ita ba a bakin aikin ka ya yi hanyar waje duk aka rufa mishi baya.
Ina yarinyar nan ta tafi?
Ya kwadawa securities din bakin gate kira suka kwaso a guje yarinya ta fita yanzu?...…. Eh yallabai ta hau mashin....... *What????* Kuna hauka ne *Don ubanku*
Ya dauko waya yayi kiran duniya taki dagawa.
Ya kira mamee kamar yayi hauka,
Mamee yarinyar nan ta dawo gida?
Lafiya, Menene?
Ta dawo?
A'a me ya.... Kit ya kashe
To wai ubanwa yasa kuka bari ta fita.... Ya zaro ido ohh my God *Anya ba ganin samira yasa ta gudu ba?*
Kaiii kishi umaimah ke gareta sosai??
Tawa ta sameni ya kara kiran nameee...
Ta ce ka ganta? Tana daga wayar.
Ina ne kika aiketa?
Gidan hajiya bara'atu tal'udu.....kit, ya kashe.
Ya kalli driver *Maza dauko mota*.....
Kadan kadan yayi tsoki, rigimar yarinyar nan tayi yawa.
Daga nesa ya hangota hannuwanta rike da manya manyan ledoji suna rinjayar ta, tana shirin hawan adai daita, ya daka mishi tsawa *Kada ka bari ta shiga*
Kawai taga mota gaban ta, tayi saurin fadawa adaidaita ya sauko da sauri... *ke kina hauka ne?* mai adaidaita ya zaro ido ganin *Umar madaki*
Ta kalleshi a wulakance daga turu na fito malam muje..... Wallahi ka tayar da mashin din nan zakayi asarar ta.
Yasa hannu zai fizgota ta ingijeshi na rantse da Allah ka taba ni zan tara ma jama'a, ta daka wa mai adaidaitan tsawa *Malam na ce muje ko?*
Sai kawai ya fado ciki muje malam..... Ta yi saurin fita ta dayar kofar ta barshi ciki kafin ya fito ta haye dan mashin......
Ransa yayi mugun baci, suka bi bayanta. Hon sukeyi amma ta ce wa mai mashin din