Showing 12001 words to 15000 words out of 60233 words

Chapter 5 - AUREN FARI Complete by Maman Abdallah.txt

24 Nov 2024

15064

*What?* ya zaro ido yana kallon wayar. Ya kara kira zata fara ringing kenan yaga *number busy*
Ransa yayi mugun baci ya kara kira a hasale *the mtn number you are trying to call is currently.......* yayi wurgi da tasa wayar..............


*maman Abdallah*


😘😘😘😘😘😘😘😘
[1/25, 8:02 AM] Bahajatu: 💑 *AUREN FARI* 💑



0⃣1⃣0⃣


*INA JIN SAKON NIN KU MASOYANA INA GODIYA SOSAI ALLAH YA YABAR SO DA YARDA LOVE YOU WITH ALL MY HEART*😘😘😘


.....iPhone X ta tarwatse tayi rugu rugu amma ko ajikin sa, me yarinyar nan ke nufi lallai bazan dauki salon wulakncin ta ba.
Ya mike ya fara sintiri a daki.
Umaimah ta hade rai tana maganar zuci, yau ni naga jaraba, shin mutumin nan bazai kyale ni haka ba. Ina amfanin abinda baya taba wucewa duniya ya dameni ya addabeni bana son hada shi da mahaifiyar shi amma tabbas ya ci gaba da takura man zan fada mata. Haba! Saboda bala'i har ya samo nomba na? Abin nan duk ya isheni kawai ina dagewa ina rama abinda yakeyi ne amma har cikin zuciyana ina jin babu dadi abu yaki ci yaki cinyewa. Mtseww ta doka tsaki....kowa ya kalleta.
Nan da nan ta hankara tayi murmushi kawai tana Sosa kunne.
Tun karfe bakwai ya sauko ya zauna falon mamee ya kunna computer kana latse latsen bogi yama rasa me zai latsa, kadan kadan ya duba agogo, da ya ji motsi kuma yayi saurin daga kai. Mafi yawan yan aikin gidan anan suke kwana da sun fito suka ganshi zaune duk wacce ta wuce bata kara dawowa.
Ya buga tsaki, me ya tsayar da ita ne yau har takwas ta kusa? Ya fada yana kallon agogon hannunsa.
Ya runtse ido wai me yasa na damu da tunanin yarinyar nan? Tun jiya na kasa sukuni. Ya kara buga tsaki kai wallahi bata isa inyi tunanin ta ba, kawai ina tsoron takai karana ga namee.....lafiya kake faman doka tsaki *madaki?* me kakeyi kasa da sassafe haka.
Ba komi mamee kawai ina wani aikine. Antashi lafiya?
Lafiya lau yaushe ne tafiyar ka Germany?
Ya kalli a gogo *yeah am preparing for it*
Ya bata fuska, ta kawar da kai da alama yau miskilancin yakeji ta fada a zuci.
Ina maganar mu karshen wata yayi. Kar ki damu mamee ina kai 'I'll let......burum aka turo kofa maganar tashi ta tsaya chak! ya bita da kallo......
Ta wangale baki kamar kullum tayo kan mameee tana yar dariya, itama tuni hankalinta ya koma kanta tunda ta shigo.
Ta zukunna gabanta tare da dafa cinyoyin ta, ina kwana?
Lafiya lau uwani yau ma kasan kika taho duk da ansha kudi jiya?
Ta kyalkyace da dariya tabb yau hayar dan adaidaita nayi ni kadai na wataya. Ta bude jaka ga salalar ki na siyo miki lalle da tsamiyar biri mutuniyar ki. Mameee ta kyalkyace da dariya sosai *Uwani tawa*
Lalle dai kika siyo mun tsamiyar biri ai daman kece kike shanye mun ita.
Allah yasaka da alkhairi uwani na gode na gode, ta kalleta tana yar dariya tare da mikewa tsaye lallen ake ma godiya?
Yayi sakakaka.... Yana wani irin mamaki wannan wace irin mayaudariyar yarinya ce, duk waftar da nayi ma kudin shine hada siyo wa mamee tsaraba?
Ko kallon shi batayi ba tayi ciki abinta, tana zuwa bakin kofa ya daka mata tsawa ke!!
Tayi ciki sarai tana jinsa.
Ya mike....kutumee... Kai madaki ina zaka?
Mamee yarinyar nan tafi karfin ta gaisheni?
Zauna ya hakuri in don uwani kilan ma bata ankara dakai bai. Ta daga baki *Uwani*....
Na'am ta fito da sauri.
Ki gayar da *Madaki*......ta barshi bana so, ya fada a hasale
Ina kwana, ta ce tare da juyawa
Ya kara kulewa mamee baki son gaskiya bazan dauki raini bafa,
Ka faya daukar komi da zafi na rasa wannan fitina *madaki* ina CE ta gayar da kai ko?
Amma kina ganin na kirata tana jina tayi ciki ko?
Kayi hakuri zan mata fada.
Umaimah na jinsu ta tabe baki *sunana ke* da zan amsa. Ai bazai kyaleni ba ko? To wallahi sai dai ya hanani albashi amma da ya mun zan mishi.
Aka hada kalaci kamar kullum mamee tayi tayi umaimah ta fito suyi kamar yanda sukeyi idan yayi tafiya ta ce ta koshi.
Ya kara kulewa kawai ya tashi fuuuu yayi sama.
Ta bishi da kallo tun yana karami yake da wannan muguwar zuciyar har yau.
Saman ma ya kasa zama, menene dalilin yarinyar nan nakin daukar wayata jiya?
Zaune take tana guyiguyar kashi gaban mamee cikin kalacin da suka rage suna labari mamee nata dariya, ya sauko cikin kananan kaya tana ganin saukowar sa tunda tayi kasa da kai bata dago ba kada ma yace ko ta harareshi.
Saukowa yakeyi idonsa na kanta tana ta cin namanta,
Mamee zan fita office.
Adawo lafiya. Ta ce dashi har lokacin bata gama yar dariya ba.
Muje in baka sako. Sukayi daki, umaimah na gamawa tayi baya, ko da ya fito bai ganta ba yabi wurin da harara ya wuce.
Sama sama yakeyin aikin duk motsin da zaiyi sai yaganshi kwance bisa umaimah. Ya mike tsaye shi kadai a office.
Umaimah kuwa tana can ita da mamee suna ta labarin su na nishadi a bedroom babu ko hijabi kanta daga zani sai wata yar shamudaddar riga mai kama jiki.
Ke bari in shiga kewaye kinji kada kisa inkai ga na saki fitsari.
Sauri kawai yakeyi baya son ya tarar har ta tafi gida, ya shigo ransa ya baci ganin ba kowa falo ya wuce dakin mamee ita kuma mamee na shiga ta mike ta shawo ruwa.
Tana bude kofa shima ya kawo da sauri suka afka ma juna tayi taga taga zata fadi ya tallabo kugunta ta dawo jikinsa ta daki kirjin sa sai kawai ya maida hannuwansa bayanta tare da runtse ido...... Ta ingijeshi ya kalleta ido jawur, ke me yasa baki da natsuwa idan kina tafiya?
Maimakon ta bashi amsa kamar yanda yayi tunani sai kawai ta raba shi zata wuce, ya finciko ta magana nakeyi miki.
Ta kalleshi sake ni. Bazan saki ba jiya na kira kin katse mun waya ke ga marar kunya ko?.........Uwani. Mamee ta kwala mata kira,
Yayi saurin sakinta dayaji motsin bude kofa, ta kallesu a tuhume, yaushe ka shigo?
Yanzu,
Gani mamah, ina kika je?
Ruwa zan shawo shine........ Yunwa nakeji mamee aban abinci.
Ya datse mata maganar.
Uwani dauko Qur'an din nan ki kara maimata mun. Ta wuce ya bi bayanta tare da juyowa ya na hararar umaimah itama ta rama ta wuce.
Yana gama cin abincin ya hau sama, ita kuma tana gama biya wa mamee sauri sauri tabar gidan.
Ya sauko da sauri please mamee sa agyaran bedroom please yanata waige waige. Ta tafi gida kuwa uwani .
Ko a sa mansura?
A'a , ya ce a takaice
Ya tashi kawai.
Abin mamaki yau umaimah tare da lubabatu sukaci tuwo kwano daya. Gidan an rage tsangwamar ta.
Gidan Alhaji yakuba tayi fira yau sai goma ta wuce ma ta shiga gida.
Karfe takwas ta isa yau, a bakin gate take jin mamee ta fita zuwa asibiti. Daman duk sati takanje ziyarar marassa lafiya. Haka shima madaki. Nan ta fahimci farkon haduwar su dubiyar ce yaje.
Ta shiga gidan tana dan tsalle irin na yara murna fal acikinta madaki baya nan.
A kitchen ta tarar da mansura .
Suka gaisa ta ce da ita, hajiya ta ce a fada miki ta tafi asibiti ki gyara mata kayanta kuma ki hau sama ki gyara ma 'Yallabai.
Ta ce juya toh bari in gyaro saman kafin su dawo nan duk mai sauki ne.....
Ta bita da kallo kamar ta ce mata bai sauko ba sai kuma ta kyaleta.
Ta dauko mukulli inda mamin ke ajiyewa tayi saman da sauri tana bambami ai bazan kara yarda mu hadu ba har ya haye man in kasa hakuri,
Ko ina karara kamar kana cikin fridge ta tabe baki shi kam sanyin nan bai masa lahani ta murguda baki tijararre, ta bude kofar ta afka abinta, duk ya zubdo kaya cikin wodrop din sa ta isa tana linkewa tana kara shirya masa..... Taji burumm an bude kofa a tsorace ta duba.
Daga shi sai towel gabanta yayi mummunan faduwa idan ta ce ta fito rikota zaiyi a hakan, tunda tayi mishi kallo daya tayi cikin wodrop din da fuskarta , tana jin takun sa bayanta jikinta ya dauki rawa,
A gidan Ku ba 'a koya miki tarbiyya ba? Ina kika sami mukulli kika shigo man daki?
Um..um.. Wallahi nayi tunanin tare kuka tafi ta fada kamar zatayi kuka ,
Ya juyo ta karfi ta fuskance shi jikinsa sharkaf da ruwa.
Ta kalleshi cike da takaici ta mayar da kai kasa idanun ta sun kawo ruwa, ke baki da biyayya ko kin raina ni baki ganin kimata da mutunci na, ya daka mata tsawa ta zabura tayi baya ya bita jiya dama cike nake dake ina ke har kin isa 'yar abun nan dake zaki kashe man waya? Yanzu kuma kin dauko key kin shigo man daki ........ A hasale ta dago, in ba cin hajiya ta bar sallahun inzo in gyara ma daki me zai hawo dani sama an fada ma ina sha'awar nan bangaren ne? Ya dan ja da baya ganin fuskar su dab da juna, ka fiye neman rigima da rashin son a zauna lafiya, ka kwashe mun albashi na kyaleka me zaka ce dani da ka kira waya? Ina ruwan ka dani da zaka kirani a waya ko kai nake ma aiki?
Ka fito na maka rantsuwa akan bansan kana nan ba amma baka yarda ba tsoron ka nake ji da zan ma karya? Ka isheni da masifa da bala'i ka haifeni ne?
Ta buga tsaki ta raba shi zata wuce wuf...ya chafko hannunta tare da murdota ta dawo da karfi bisa kirjinsa, ya hada da hannuwan nata ya matseta a kirji.
Wa kikeyi ma tsoki? Ya matseta kwalla suka shararo mata ta fara shasshhekar kuka.....tambayar ki nake ya sha mur.
Ka..ka..ka..kyaleni in yafi ta fada cikin kuka muryar ta a sarke ya tsareta da ido yaki sakin ta.
Komi ya gani? Sai ya ingijeta tayi baya dai dai lokacin mamee ta turo kofa. ..........


*Maman Abdallah*


😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘


💑 *AUREN FARI* 💑


0⃣1⃣1⃣


.....wallahi nasan za ayi haka duk laifin na mansura ne. Umar baka da hakuri ko kadan...... Ta shigo tana bambami,
Naji jiya kana son a gyara ma daki shine nabar sallahu amma bazata kara hawowa saman ba daman ni ke tilasta mata muje uwani....
Mamee yarinyar nan fa rashin kunya takeyi mani ina fada tana fada dubi jikina kawai ina fitowa naganta ciki ba halin in tambayeta?
Na fada mishi kece kika turo ni har rantsuwa nayi mishi amma bai yarda ba....anki a yarda din.
Mamee ta banka mishi harara, umaimah tayi gaba abinta, ai bazata kuma zuwa ba sai kayi hakuri da gyaran su mansuran ganin kana yabawa da natan ne yasa nake tilasta mata.....
Au ni yanzu laifi na kika gani?
Don me zanga laifin ka tunda kai ta tarar?... Mamee....ta nuna shi da yatsa rai a 6ace tunda ka nuna ban isa da kai ba kaje madaki abinda duk ka iya kayi. Yarinya marainiya ba uwa ba uwa, inda take bataji dadi ba nan din ma ka takura ta ka hana yar mutane shan ruwa? Kai haka akayi maka!
To wallahi kaji tsoron Allah na fada maka.....ta fice jikin sa yayi mugun sanyi
Tabbas yau yarinyar nan batayi niyyar biye mishi ba kureta yayi. To ai kuma ni shirun nata ke ban iya jurewa. A gurguje ya shirya ya sauko sai mazurai yakeyi ta inda zai ganta,
Simi simi ta fito tana goge kwalla fuskarta duk tayi ja.
Kawai sai yaji wani iri alamar rashin yin daidai.
Ta saci kallonsa kawai ta gittashi ya bita da kallo....
Yasan ko yabi ta wurin mamee shareshi zatayi sai kawai ya fice.....
Duk tayi sukuku ranar har yanzu gabanta bai daina faduwa ba. Ita bata taba ganin babban mutum ba kaya ba sai yau.
*madaki nada kyau amma ba shi da kirki* matarsa ta gama shiga uku ta fada a fili. Mansura ta sameta ta bata hakuri ta ce ba komi.
Tunda na gama mamah zan tafi gida.
Ta kalleta a nutse zo nan uwani ta kamo hannunta tare da zaunar da ita bisa kujera kusa da ita.
Kinyi sukuku idan kika biyewa madaki ko ruwa bazaki sha ba, haka yake kwanaki da ya taso wata mai aikina dole ta hakura da aikin wai kazama ce,
Ke kuwa yayi ya gama muna nan tare in shaa Allah aure ka rabamu,
Tayi murmushi kawai.
Duka fa yanzu karfe biyu ki yi zamanki kinji?
Zatayi magana ta ce af! Ke dauko mana tsamiyar birin nan mu birirriketa sai ta kwashe da dariya. Shi kenan ta wasanshe
Suna sha suna raha kamar kullum, ya shigo rike da jakar *system* din sa.
Tana ganin sa jikin ta yayi sanyi.
Aaaaaaa mamee kurmusun me akeyi? Ya fada idonsa na kan umaimah yana kallon yanayin yanda take tsotsar abin a bakin ta.
Murmushi mamee tayi kurmusun tsamiyar biri,
A bani in shaa... Ta dubeshi da sauri ganin ya miko hannu, ta ce uwani mika mishi ta fada tana yar dariya.
Af kinga ina zuwa inji mamee ta mike ta shiga ciki da hanzari alamar wani abu ta tuna.
Ta dauko ledar ta ajiye mishi kasan kafafun sa ta barshi da hannu sake,
A hannu zaki ban.
Ta dauko ta mika mishi, tare da mikewa zata bar wurin yayi saurin riko hannun ta,
Wai kai idan ba ka taba jikina ba baka jin dadi?
Ya yi sauri ya saketa to ki koma ki zauna sannan kidaina gigin matsawa ko ki tashi daga inda kike matukar ina miki magana..... Yanzu magana kake mun? Ka ce in baka na baka sai me?
Ya sha mur sai ki zauna ki ringa barewa kina miko mun yanda kikeyi wa mamee.... Bazan ba ko kai mamee ne?.....ya fincikota ta fada jikin sa.
Ke bakinki bai mutuwa ko? Ya matseta.... Sakarni malam ko gantsara maka cizo......mansura ta fito uwani kizo inji...... Maganar ta tsaya ganin madaki, ta yunkura ya kara riketa, jeki ce tana zuwa, tayi baya da sauri,
Kwalla suka shatato mata, ya bisu da kallo duk tsiwarta bata da wuyar kuka, ya hade hannayenta dauko kiban sannan ki tafi.
Taga ba sarki sai Allah ta dauko ga hannuwansa duka rike da ita, sai ya bude baki, ta balla mishi harara sannan ta watsa mishi.
Ya saketa barkanki yarinya da....... Tuni ta shige ciki da gudu yabi bayanta da kallo.
Gani mamah,
Zo nan ki tayani gyaran sarka,
Ya tashi yayi sama cikin nishadi yana tsotsa.
Cewa nayi a kira mun ke kada ya miki wata muguntar. Ai cikin satin nan dai zai tafi Germany ki huta.
Murmushi kawai umaimah tayi.
Mamee bazata bar yarinyar nan ta zo ba kona kira.
Ya dauki waya hello mamee don girman Allah kibar yarinyar nan tazo ta gyara man daki wallahi kinji nayi rantsuwa bazan kuma sata kuka ba. Na daina biye mata please.
Ka tabbatar? Wallahi eh kinji nayi rantsuwa.
Shi kenan ta ajiye, Uwani jeki gyara mishi dakin ki sauko.
Bata San lokacin da ta ce innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ba. Ta kalleta zuwa saman keda wannan salatin? To bazaki ba wallahi ina dalili. Kyaleshi ai shi ya jiyo.
Ta langwabar da kai don Allah mamah tunda na gama in tafi?
Tausayinta ya kamata yanzu har tafi sha'awar tafiya gida da zama da ita saboda masifar madaki.
Tashi ki tafi kinji.
Zumbur ta mike tana murna ta bita da kallo.
Shiru shiru sai kawai ya sauko, baisan ko wacece ba zata wuce ya ce ke ina yariyar mamee?
Yanzu kuwa ta tafi gida..... *what* ? Da daka tsawa har ta dan firgita. Yayi ciki mamee! mamee!! Ya na bude kofa ya fara masifa,
Kinga abinda na ke fada miki ko? Yarinyar nan fa gida ta tafi.....eh ina sane da hakan. Yayi turus!
Ka firgita 'yar mutane kwata kwata yanzu bata sha'awar zama gidan nan duk ta tsorata ka hanata sakewa wannan masifar taka ta yi yawa.
Shine kika bata dama ta tafi? Fine! Kawai ya juya yayi sama.
Gashi ya rarratsa wayar da yake da numberta don bai wani tsaya saving ba, mtsewww yaja dogon tsaki sai kawai ya fara hada jakunkuna.
Umaimah kuwa tana fita gidan ta mance komai cikin sa'a tana zuwa ta tarar an maido wuta ta kwashi kayanta ta nufi gidan Alhaji yakuba guga.
Karfe shida na safe tana lazimi ya shigo, mamee zan tafi Germany sai Allah ya mana dawowa.
Yau ne? Ina ce sai jibi,
Eh akwai shirye shiryen da zanyi ne. Ya mike. Tabishi da kallo a dawo lafiya.....
Ya wuce yana fushi, tunanin umaimah zai zautashi mamee kuma na babbakewa gara yayi nisa da gidan wata kila zai mance dasu din.
Abinda madaki bai sani ba zaman sa gidan a haka ne saukin sa, domin da ya tafi sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login