Showing 9001 words to 12000 words out of 60233 words

Chapter 4 - AUREN FARI Complete by Maman Abdallah.txt

24 Nov 2024

15067

ta ya daka mata tsawa, *Are you mad*? ke baki iya sallama ba kuma bazakiyi knocking ba a baki izini zaki fado man daki haka gatsal idan kika tarar dani cikin wani hali fa?
Wane hali bayan wannan dana sanka dashi na masifa? Daga bude kofa ka hayayyako mani da bala'i kamar ka haifeni....... *are you serious?* ya fada tare da dirkowa . koma kiyi sallama. Ta rike kugu bazan koma ba yau dai kam sai kuma a tari wani jikon ya tunkaro ta a hasale ta fara kwana, suka fara zagayen dakin yana son tsafko ta taki tsayawa, kaban kudina in fita ni yau naga jaraba kai kullum kamar kana jirana?
Jiranki nake don ubanki ya yunkoro zai kamata ta haye gado tayi tsaye. Ni kike takawa gado? Ya zaro ido naje na taka kaban hakki na mana in tafi ko zan tsaya ne ka gana man azaba? Yayi tsalle ya haye gadon ta dirko kasa hannunta ya kado wata robar mai da bai rufe dai dai ba a dressing mirror ya fara zuba.
Rezar da ke hannunta ta yanketa Sam ta manta da ta dauko reza tayi saurin wurgi da ita jini ya fara zuba ya zaro ido muguwaaaa yau ma zuwa kikayi ki yanka ni?
Ta balla mishi harara hannunta dafe, haka nan zaka kirani inzo ne ta kai duba ga hannun ta, Rannan ma mamata kayi..... Ya mameta ya dirko gabanta tare da damko ta amma sai sulbin mai ya kwasheshi dashi din da itan suka fadi rikichaaaaa tayi baya ya haye ruwan cikin ta.
Na shiga uku ta fada da karfi. Jikinsa ya wani bada tsammmm... Tunda yake a rayuwarsa bai taba rike hannun mace ba, ko gaisawa ba yayi dasu a duk inda suka hadu kuma ko wace kasa yaje, kallabin ta ya cire an mata sabuwar kalaba kana duk ta rufe mata fuska, ya kura mata ido *Me yasa yarinyar nan bata tsoro na ne?*
Tayi kichin kichin malam dalla daga ni kada ka karya ni.
Ko motsi baiyi ba ya kura mata ido ta samu da kyar ta zaro hannun da ta danne. Tayi tayi ta tureshi ta kasa,
Kai dai mugu ne wallahi ta fada da kyar, da azaba ta isheta sai ta wawuro kuncinsa da karfi ta cije, ya wuntsila a wahale yana fadin kai kai kai ni kika ciza?
Ta dauki kallabinta zata kwasa a guje ya riko hannunta da karfi, ta fado bisa shi sai kawai ta rushe da kuka. Ya kura mata ido kawai yana kallon ta.
Kuka takeyi tsakanin ta da Allah, sai ya saki hannun a hankali ya tashi itama ta mike, ya kalleta zan baki kudin ki ne karki gudu ya fada a hankali kawai ya rasa menene yasa jikinsa yin sanyi.
Yana juyawa ta kwasa da gudu zata bar dakin ya bita ya riko, ke me yasa kike da kafiya? Ya daka mata tsawa tare da sanya ma dakin key, ya saketa ya juya ina zakije hannunki da ciwo haka ko baki ga yanda kika bata man jiki da daki da jini ba?
Hello gaya nan ya kulle daki zai dakeni......... Ya waigo da sauri yaganta tsaye tana waya, sai kawai ya juya yaci gaba da abinda yakeyi, first aid box ya dauko...... Zo in miki dressing.
Bana so,
Yayi mata wani kallo cike da takaici don zan taimaka miki?
Bana so da in baka hannun nan ka taimakeni na gwammace in tsaya haka jinin ya tsiyaye. Zai yi magana yaji bugun kofa *madaki* bude kada ranka ya baci........ Ya kalleta rai a bace kawai ya wuce. Da sauri ta shigo me ta maka zaka dake ta?
Karya takeyi gashi nan yankewa tayi zan taimaka mata take man rashin kunya zata fita na rufe kofar shine fa naji tana kiranki a waya,
Ya akayi ta yanke daga karbar kudi? Ta daga mishi tsawa, zaiyi magana kana hauka ne?
Menene ke damunka wai?
Ganin ranta yayi mugun baci yasa yayi shiru kawai ta ci gaba da fada sosai ya kura ma umaimah ido ko zatayi bayani amma tayi shiru,
Mamee tambayar ta ina ta sami reza wallahi da abinta ta tazo, na rantse da Allah babu ruwana. Ya daga hannuwa sama yanda yara keyi.
Uwani ina kika sami reza ya akayi kuma kika yanke?
Gabanta ya fadi. Anya zata fada wa mamee wurin guje guje ne? To me yasa su hakan rashin sallamar da tayi kuma ta bishi da rashin kunya....... Wallahi babu ruwana ai kinji tayi shiru, kai wannan wauta taki uwani Allah ya rabaki da ita. Ka hanzarta daure mata hannun na baro baki ciki.
Ta juya har ta kai bakin kofa ta tsaya ganin ta biyota, ta ruko kunnenta ina zaki bini haka je ya daure miki hannun ki sauko ina jiranki zaki raka ni unguwa. Taja kofar.
Ta isa gun dan akwatin ta fiddo bandeji ya rike mata hannu. Sakarni zan yi da kaina. Ya kura mata ido wallahi mamaki take bashi ba za a saki ba ya damke hannun tayi tayi ta kasa kwacewa, ya da dauko auduga da spirit ya goge jinin da hannu daya hannu daya rike da ita,
Mtseww na tsani shisshigi wallahi, na ce bani so bani so kamar dole, ya kalleta har zaiyi magana sai kawai ta bashi dariya . yayi Dan murmushi kadan yaci gaba, ya daure wurin.
To ka sakeni tunda ka kare malam........idan kika kara magana zan dauko rezar can da kika yar in farfade hannun kin San kuwa zan iya...... Kut ta hadiye wani miyau a tsorace. Ya kusa sakin dariya ga tsinannen tsoro ga jan fada ya fada a zuci.
Yasa hannun aljihu ya dauko daurin kudi na dari biyar biyar ya wurga mata a jiki sannan ya saki hannun *kilgi dubu talatin kudin aikin ki*
Ta yi saurin kallon sa
Koni yaron ki ne da zan kilga in baki?.
Ta kalli kudin ai duk kwara biyu dubu daya kenan kada ya fahimci bata iya lissafi ba ya kara rainata sai kawai ta kwance, ya kura mata ido ta daddage tsakanin ta da Allah tana hada biyu biyu tana cewa *daya, biyu, uku, hudu....* ke yi a zuci kin cika mun kunne.
Ta balla mishi harara Da Allah ni ka rudani. Ta kara lalowa sai kawai ya bushe da dariya. Ta kara hararar sa taci gaba sai da ta kai sha takwas ya ce malama kina batan lokaci kilga kamar kina lissafin gero...... Innalillahi ta rafka salati ta watsa mishi kudin ungo kilga tunda bazaka iya yin shiru in kilga ba.
Ya daure fuska ya watsa mata kudin itama wallahi sai kin kilgi kudin ki yau ko ki rasa. Mtsew ta buga tsaki.
Mamee ta gaji da jira ta kirata a waya ya fige wayar yasa hands free uwani ko in tafi?
Tafi mamee ta na gyaran daki ne. Zatayi magana ya to she mata baki,
Saboda rashin imani zaka sanya ta aiki ga yankewa, ya kalli umaimar ita ce ta ce zatayi..... Sai ka biye mata...... Hello hello mamee ba 'aji ya latse wayar.
Yaudaraaaaa to wallahi sai na fada mata karya....... Ya buge bakin idan kika zageni sai kin wahala kilgi kudin ki kiban wuri.
Ta zumburo baki mugu. Ta fada ciki ciki,
Me kika ce?
Ban sani ba ta fada tare da fara kilga .
Kallonta yakeyi tsakani da Allah.
Tana da kyau yarinya ce karama. Ya danyi jimm may be tayi 14-15. She's preety and crazy. Yarinya karama amma ta raina shi. Wai me yasa bata tsorona?
Kawai sai yaji yana son Sanin amsar dalilin da yasa ba ta tsoron sa...........
Qala kus kaci kanka ta tofa mishi miyau. Yayi firgigi ke kina hauka ne?
Ni ce kai, tun dazun ina cewa na gama ka kuran ido. Ta watsa mishi ragowar dubu ashirin dinsa, ga ragowarka ta damtse nata zata mike. Ya janyo ta ina zaki?
Zaki fidda mun dubu goma wacce zaki ringa biyana kayana da kika 6ata a baya ko zan dauki asara ne sabbin shaddoji na ko wane kin wulakantar?
Zaki fidda dubu uku kudin mai na dana kaiki gida ranar da kikayi dare, zaki fidda dubu biyar Wanda shima zan ringa cirewa yankan da kikayi mun nayi asarar jini na, sai dubu biyu kudin energy na dana yi waste yau kika sanya ni gudu a dakin nan. Sannan Zan fidda dubu biyar bisa ga alfarmar baki San dokar ba daga yau zata fara, duk rashin kunya da maganganun da zakiyi man nan gaba zan fitar da kudin su sai ki ware dubu biyar kiban sauran...................


*Maman Abdallah*


😘😘😘😘😘😘😘😘
[1/25, 8:02 AM] Bahajatu: 💑 *AUREN FARI* 💑


0⃣0⃣9⃣


*KO KUN SAN INA DA WATA BOYAYYAR MASOYIYA A SOKOTO? DON ALLAH KU SA MATA ALBARKA SUNAN TA BILKISU ABDULLAHI GADA INA MATUKAR GODIYA BILKY WALLAHI TA NA GYARA AURE SOSAI.*


*AI KUN SAN ME NAKE NUFI TUNDA NA AMBACI SOKOTO DA GYARA KUMA*😉


Jikin ta yayi mugun sanyi, zuciyarta ta ringa tukuki, a yanda taji tarihin biyan ma'aikatan gidan a dubu talatin ita ce mai karamin albashi ma kamar yanda tafi kowa karancin aiki, dalilin biyan ma'aikata albashi mai tsoka shine don a fidda musu kwadayin sata a gidan, yana daya daga cikin gargadin da akeyi ma duk wata mai aiki banda sata. Amma ga mamakin umaimah sai dai taji labari ita kam ba a mata ba, wannan wane irin rashin tausayi ne?
Ko yaya Abba ya ce ta ware mishi dubu cikin albashinta. Ta runtse ido *Ya Allah duk sharrin da ke cikin wadannan kudin ka fidda mun shi, ka kuma kareni da duk wata fitina*
Ya kura mata ido jikin sa yayi mugun sanyi wani tausayi ya diri zuciyar sa bai daya,
Ya kalleta *sharri?* wane sharri kuddin ke dasu?
Yanayin muryar da yakeyi ma mamee idan yayi laifi ya bada hakuri yayi mata. Ta kara tsanar sa a zuciya ko kallon sa bata kaunar yi.
Ta mike tsaye ya daga hannu zai kara fizgota ta fincike ta watsa mishi dubu ashirin da da biyar jikin sa.
Wannan kudin tattare suke da sharri don ba da zuciya daya kaban ba yau ka tabbatar mun da kai din mugu ne baka kuma da tausayi.....ya yunkura zai kamota tayi baya, ka lissafa ka ajiye magana yanzu na fara, kasan dukiyar taka bata gama isar ka ba ka kawo ma'aikatan da suka fi karfin ka? Can kudi, can kudi can kudi duk basu isheka ba sai ka ci hakkina?
To kayi a banza wallahi dukiyar ka bata dada ni da kasa ba aiki ne ba kai nakewa ba wallahi kasan wacce ta kawo ni to darajar ta ko naira daya ka bani zan karba haka kuma zan iya mata aikin kyauta amma wallahi kai ko zaka biyani miliyan dari inshigo gidan nan kawai in fita kasan kayi kadan......wuf ya chafko ta..shut up!!!!!!! Ya daka mata tsawa.
Ko gezau batayi ba, ji hargagi to cinyeni damisa ka tsaya ga yar cikinka kana wannan kurarin duk bai isheka ba aikin da nake kuma su ka sanya wa ido.......waje ya bankada ta ya janyo kofa ya rufe,
Ya dafe kansa hannuwa biyu biyu ya runtse ido *Why why why????* kalmar da yake maimaitawa kenan.
Ya kife bisa gado look at maganganun da yarinyar nan ke fada man me ta dauke ni wai?
Ya runtse ido why all this rainin?
Tafe takeyi tana rokon Allah ya kubutar da ita daga sharrin mutanen gidan amma abin mamaki gidan ba kowa yara duk sun tafi islamiya, goggo jummai kuma taje suna, goggo hansatu ce kadai zaune a tabarma tana jin redio, tayi sallama ta shigo, ko da ta dago taga umaimah sai ta kawar, ko ajikinta domin ta saba da hakan da kuma rashin bata abinci a gidan tun da ta fara aiki kullum ta dawo bata da kwano.
Ta zukunna can karshen tabarma goggo barka da yammaci.
Ta dalla mata harara an dawo?
Eh, gashi anbiyani yau ta mika mata dubu biyar jikin ta na rawa, tana ganin kudi ta wangale baki, haba?
Nawa suka Baki? Tayi shiru don ta gani da kanta sai kawai taga ta mike tsaye ta makure jikin ta taji ta inda dukan zai fara, sai kawai taga goggo na tikar rawa.
Ta zaro ido ta bude baki.
Wane gidan arziki ne kike aiki haka?
Umaimah tayi shiruuu au kai gidan fa ba'asan ina aiki gidan *Umar madaki* ba fa kawai sun tsaya a ina aiki gidan matar tazo 'yar uwar hajiya basu san wacece ba.
Da na kawo dubu talatin din nan goggo yau sai ta goya ni. Mugu ya mun bakin ciki....... Ta dafa ta sauraranni ungo dubu boye taki ce, idan kowa ya dawo kice dubu biyu ne albashin ki gata na ware har babanku kice haka ake biyan ki idan za a raba kuma damu ciki idan sun dawo.
Duk wata zan ringa baki dubu ina daukar dubu biyu ina Sana'a kinga nice matsayin uwarki idan kin tashi aure 'yan siyayyar uwa ni zanyi.
To goggo umaimah ta fada tana washe baki da ajiyar zuciya. Bari in shiga wurin hajiya in dawo....jeki maza adawo lafiya.
Ohhh ji goggo anga abin duniya, ta tabe baki ta fice zuciyarta fes!
Ta biya shago ta siyo jikkar klin babba ta dari uku ta kaima hajiyar. Ta ce kisa albarka an bani albashi ko kewaye kya wanke.
Ta dunga sa mata albarka, akwai kudin ki fa wurina. Hajiya kiyi amfani dasu. A a wallahi ai na rantse bazan taba ba. Tayi murmushi ajiye mun tsaron lalura, kayan ma na dauki atamfa daya sauran da zaran naji zakuyi wani abu zan dunka miki ince ni na miki ko kuma can gidan *madakin* na sansu da shagali.
Tayi godiya ta tafi ta siyo lalle na dari biyu. Ta fito kenan ta hadu da yaya Abba. Ta kwala mishi kira ta mika mishi dari biyar ba zato ya buga tsalle don yanzu ya gama maular hamsin. Ta ce albashi na dubu biyu ne nawa aka raba aka bani na baka kasan bazaka sami dubu.....ke share na gode ya watsa da gudu. Ta bishi da kallo wani abin sai aikin shaye shaye,
Kai kace gidan biki ake ko suna tun a kofar gida take jiyo hayaniya na rabon kudi. Ina ma yaban kudina chif, yau da nasha dadi gidan nan ta buga tsaki mugu kawai,
Dari biyu ta samu cikin kasafin da akayi tana karba ta yi daki ta kwaso tulin wankinta ta hau yi.
*Madaki* kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye abubuwan da suka faru yau ke dawo mishi daya bayan daya, ko abinci ya kasa ci da ya zauna ko ya kwanta sai ya tuno gashi nan bisa umaimah ya haye ta da suka fadi,
Ya fada kewaye ya sakar ma kansa shower amma da ya runtse ido hakan yake gani. Da ya bude sai maganganunta su dunga tariyo mishi.
Ya dunkule hannu ya hada kanshi da bango ya fasa kara *wai tunanin na uban meye*
Ya ga wannan bata fissheshi ya fito ya koma falon mamee amma bata dawo ba, ya dauki waya
Mamee wai kina ina?
Gani a hanya lafiya?
Ni kadai ne fa a gida......ina tafe ai nace kayi aure kakiya da kana da matarka yanzu wane kewa?
Ya tsinke wayar kawai ya runtse ido *she won't understand*
Yan aiki keta kara kaina ya kalli wannan ya kalli waccen Sam ita bata wannan safa da marwan aikin ta tafiyin na zaune ko tsaye bata yawan motsa jikin ta .......ya buga tsaki kuma fa da yarinyar nan ce da yanzu mun gwabza fada, to wai meke sanya mu fadan? duk sai suka bashi haushi ya daka musu tsawa *kar wacce ta kuma fitowa idan ta shiga wacce ta fita kuma karta dawo*
Zuwa yayi falon don ya sarara da tunanin umaimah amma suna Neman rikita shi.
Me yasa na hanata kudin ta duka?
Ranta fa ya sosu, da alama bakinta yaso furta wani abu na lura da hakan, gobe me zata fadawa mamee? Nasan tabbas sai ta tambayeta.
Ba karamin 6aci ranta zaiyi ba kuma yarinyar nan tunda ta kirani da mugu babu dalilin da zaisa ta 6oye mata shaida zatayi man.
Ya danna abin kiran yan aiki, agurguje suka karaso don basuji dawowar mamee ba .
Waye ke da number uwani? Duk suka ce babu.
Ya ce su tafi.
Mamee na shigowa ya karbi wayarta, ya kuwa yi sa'a uwanin tayi saving da no.
Ya na dauka yayi sama da sauri. Ta bishi da kallo. Ta girgiza kai agogo sarkin aiki wani abun ya tuna baiyi ba tayi ciki.
Gidan yau gaba daya cikin nishadi ake. Umaimah tsumu tsumu ana fira da ita hada su dariya. Abin kara armashi kowa ya karbi number ta sun sa mata nasu.
Mamaki kawai takeyi gidan ya zame mata sabo.
Wayarta tayi kara har sau biyu taga number kawai ba sunan. Mamee kadai ke kiranta tayi tunanin ita ce, duk akayi tsit, hankalin kowa ya dawo kanta, tana dauka ta ce mamah biki kikaje halan naji shiru shiru.......
Ke natsu magana zanyi dake ya daka mata tsawa, tayi jimm
Gabanta ya fadi . Kowa ita yake kallo
Gobe idan kinzo.....eh mama..To sannu da zuwa ba komi goben da wuri zanzo.... Ke saurareni madaki....ta latse wayar.
Ya hasala

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login