Showing 21001 words to 24000 words out of 60233 words

Chapter 8 - AUREN FARI Complete by Maman Abdallah.txt

24 Nov 2024

15070

mamee akaifa, basu ji saukowar sa ba, har sai da yazo daf dasu yace mamee....... Da dagowar kanta da faduwar gabanta duk suka wanzu lokaci guda. Idanun sa an kanta, suka hada ido tayi saurin maida kai kasa, *kai wallahi ya rame da yawa*
......bazakayi waya akawo ma abinda kake bukata ba ka sauko?
Idanun sa har lokacin na kan umaimah ya ce *Abinda nake bukata bai dauko ta waya mamee*..... Me?
Yayi firgigi to ina son dan mike kafa ta ne na gaji da kwanciya kamar ruwa ya karasa maganar yana dan murmushi yana duban mamin...... Umaimah ta mike zata bar wurin, ya ce, kowa ya je ya mun sannu yarinyar ki ta kasa zuwa saboda girman kai..... Ya salam, mutumin nan sai fita harka ta kuwa?
Subhanallah uwani, Saboda me? Zo nan amma baki kyauta ba..... Ta dan zukunna naje sau biyu yana barci.....karya kikeyi......kai jira, tsaya na ce. Koma dai menene ki gausheshi yanzu ina ji shi kenan ko?
Ta dan kaikaita *Allah ya kara lafiya* kawai tabar falon tayi ciki. Ya bita da wani kallo...... Sai kawai ya maida bayansa ya kwantar tare da rufe ido.
Ya rasa ya zaiyi duk ta inda ya bullo sai umaimah ta zulle, kwatsam bayan kwana biyu mamee taje asibiti ya rutsa ta a daki, ta ganshi sarai sai ta basar,
*Ina son magana dake* kawai ya juya. Tabi bayan shi da harara *Ai sai ganina kam* taci gaba da aikinta.
Kusan mintuna biyar ya kara shigowa, *Da ke nake fa* ta dai yi shiru. Ya nufo ta a hasale, ta makure jikin gado sai kawai tasa mishi kuka.
Duk illahirin tsikar jikin sa ta tashi yaji wani *yarrr* ga wata kasala. Yafi mintuna uku yana tsaye yana kallon ta.
Ta dan sassauta kukan abinka dama da *sharbe*
Ya rasa ta in da zai fara. Motsa baki kawai yakeyi ya rasa me zai ce mata?
Ya dan kwantar da murya, banyi tunanin abin zai miki zafi haka ba, har ga Allah bana yi da mummunan manufa ba......ya danyi shiru.
Sautin kukanta ya tsaya chak!
Na rasa ta inda zan bullo miki ki fahimceni kin fiye taurin kai, na mini tsaraba kanki ki karba, albashin ki ma kin yafe, na kira waya kinyi rejecting. *You wrongly and negatively understood me* yanda duk kika daukeni ba haka nake ba.
Yayi shiru!!!!....... Ko zata ce wani abu amma motse taki motsawa,
Duk jikinta ya dauki wani sauti,ya zukunna gabanta *Umaimah*..... Saura kadan ta saki fitsari tsikar jikinta ta yi *yarrr* gabanta yayi wani irin faduwa da bata ta ba irin sa ba ta kara makurewa tana kyarma. Wani irin abu takeji da bata ta ba jinsa ba...... Ya ruko hannunta zo muje sama inyi magana dake a nutse bana son mamee tazo ta tarar dani nan ke kuma kina kuka......ta kankame jikinta, ya kura mata ido cikin tashin hankali kada fa yarinyar nan bacin kiyayyar da takeyi mun hada tsoro na ta fara.....? Tabbas yarinya ce karama kamar yanda mamee ke fadi, to wai nima wane rashin hankali ya shigeni na biyewa mitsitsiyar yarinya kamar wannan muna *Scandal*?
Ya kara sassauta murya yanzu ya kike so ayi?
.......ka tafi kaban wuri,
Ta fada tana shassheka,
Taurin kanki keja muna fitina, yaya ina lallashin ki kina dada rikicewa?
Ikon Allah ta ce a zuci,
To bazan tafi ba idan kin ga na tashi anan to kin biyoni zuwa sama.
Bata kara magana ba yayi yayi amma tayi shiru,
Ina son ki fada man abinda duk bakya so daga gareni na miki alkwarin zan daina kuma zan baki hakuri.....lokacin ta dago ido, fuskar duk tayi ja abinka ga farar mace,
Ina so ka fita hanya ta ka kyaleni bana son ........ Ke kina hauka ne? Ya daka mata tsawa sai kawai ta kara fashewa da kuka.
*Yau na shiga uku* bai San lokacin da yace haka ba.
Ya matsa hannuwanta murya kasa kasa *Umaimah ki dubi girman Allah kizo muje sama kada mamee ta shigo, kin San Allah yau sai mun gama maganar nan koda kuwa zaki kwana gidan nan...... Na gama magana dakai na hakura kayi wa Allah ka kyaleni haka.
Kamar zaiyi kuka kinfi so kullum muna fitina kamar kaji bakya so mu daidaita?
Tayi shiruuu!!!.... Idan ke abin baya damunki ni yana damuna ina so kiban lokaci muyi maganar nan.......mamee oyoyo yara suka fara ihu daga haraba. Ya zaro ido kawai sai ya mike ya sureta kamar jaririya yayi sama a guje......
Zatayi ihu ya hada fuskarta ta kirjinsa ya toshe da kyar take numfashi.
Ya dire ta a tsakar dakinsa ya maida kofa ya rufe da key, kana hauka ne zaka kasheni?
Da'allah yi mana shiru fanko, Ashe baki da nauyi kamar na dauko karmami ke 'Har abun nan kike ja da *madaki*.
Ke nake sauraro ki fada man abinda kike so da Wanda bakya so ko ma daidaita mu daina fada.......ina son yanzu ka bude in fita, sannan bana son ka kara Shiga sabga ta.
Dalili?
Ban sani ba...
Ki fada man dalili ni kuma daga yau zan kyaleki zan kuma baki hakuri,
Saboda na tsani inganka kusa dani. Ta fada a hasale,
Maganar ta daki zuciyar sa ya matso daf da ita , tayi saurin ja da baya yaci gaba da binta har ta kai ma bango, ta runtse ido tana jiran ya shako ta Lamar kullum ya sunkuyo daf da fuskar ta ...... *Am very sorry* kiyi hakuri. Jikin ta yayi tsammm!!!!!
Ya ja baya a hankali ya nuna mata kofa da hannu.........


*MAMAN ABDALLAH*


💑 *AUREN FARI* 💑


0⃣1⃣6⃣
*KINA RAINA MARYAM ALIYU YAR ADUWA. M. ALI* 😘


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/8RrbAeADj5FLV7LZ24rBDH


....Ta kalleshi sosai, ya nutsar da nashi idon cikin nata yana aika mata sakonni, tayi saurin kawar dasu ta wuce kamar wacce kwai ya fashewa.
Ya bita da kallo kamar ya kamo ta amma ya daure ya barta ta tafi, dole in danyi baya baya da yarinyar nan in dan fita harkarta kadan kuma na daina damunta da hayagaga matukar ina son shawo kanta mu daina fada, in ba haka ba zan rikita ta in gigitata ina ji ina gani ta tsorace ni ta kuma kini, kiyayya mai tsanani.
Ya zauna gefen gado, amma me yasa na damu da yarinyar nan haka?, saboda me bana hakurin rashin ganin ta ko yaya ne duk da kullum haduwar tamu bata arziki ba ce? A duk lokacin da na ganta kusa dani ko nesa dani burina kawai najita bisa jikina, shin me yasa hakan?
Komin yanda na hasala da ita tana fara kwalla zuciyata zata karaya *Why?*
Mtsewww ya ja guntun tsaki,
Nasan dalili, duk duniya babu wanda ko wacce ta taba yi mun abinda yarinyar nan tayi mun ba, ban taba ganin Wanda baya tsoro na ko shakka ta ba irin ta.
To wai saboda me? Me yasa bata tsoro na?
A baya babu abinda ya tsana irin zama falon mamee saboda hayaniyar yan aikin ta, amma yanzu duk fadin gidan nan kawai yake sha'awar zama.
Kullum burin sa ya tokali umaimah suyi sa'in sa ko da kuwa zuciyar sa zata yi kuna, *to me yasa?*
Umaimah kuwa har sai da mamee ta kare ta tambayeta ko bata lafiya?
Lafiya ta lau mamah ta fada tana dan murmushi,
Ta kai hannu a wuyanta don ta tabbatar sannan ta ce, duk kinyi sukuku kamar wacce tayi karya lafiya dai ko?
Ohh mamah, lafiya lau fa.
Ta dungureta ganin har ta kosa da maganar, karya kikeyi da abinda ke damunki ko kun kara fada da *madaki*? Sunan sa kawai da taji sai da ga banta ya buga, ta ce *ni ina ma ya ganni?*
Ina so in baki labari mamah, tayi saurin janza maganar, jiya khausar aikin da ta bani duk na cinye sa,
Au haba? ,
Uwani Allah ne yasa bazakiyi ilimi mai tsawo ba amma maganar kokari kina dashi sosai.
Tayi murmushi.
Ko karatun nan fa ji nisan da kikayi wa kowa gidan nan.
Da zamuyi sirri da ke da na nemi alfarmar ki,
Alfarma? Ta bukata,
Eh,
Ta me?,
Kija bakin ki kiyi shiru amma,
Mamah wa zan fada mawa?
Tayi murmushi, nasan baki da surutu kam,
Zan lallaba *madaki* ya sanya ki makaranta........ Wani tsalle ta buga tare da fadawa jikinta ta kankameta tana ihu.
Ke karki karya ni don kaniyar ki.
Amma ina tumurmuzarta takeyi tana tsalle dai dai shi kuma yana saukowa daga sama, yayi turus yana kallon su.
Ta dago fuskarta zaki dagan kafafu ko sai kin sha kulli?
Ta yi saurin tashi ta juya mata bayan *dunkule hannu ki tuma min* duk suka kyalkyace da dariya ta kara kankameta.
Ya lumshe ido yana wani irin nishadi, fuskarsa kunshe da murmushi, yarinyar nan ta maida mun uwa kamar ta ta ko? Shin ko dai shagwababbiya ce?
Amma ita da take marainiyaniya wa zata yi ma shagwaba?
Ya daure fuska tamau ya sauko *ke* daga mun uwa ko sai kin karya kafafun da nake faman *treating?*
Zumbur ta mike ta zauna nan da nan annurin fuskarta ya 6ace,
Ya kalli mamee *murnar me ta keyi ne?*.....ina ruwan ka sirri ne ko uwani?
Ta dubeta tana murmushi.
Sirri? Har akwai sirrin da zakiyi da wannan yarinyar da ba zan ji ba?
Ta daure fuska kadan gashi ma kaga zahiri.
Ya kalli umaimah *ke fada mun tsallen me kikeyi?*
Sai kawai ta yunkura zata tashi....ya fizgota da karfi ta fada jikin sa ya harde kafafun sa ta baya ya kange ta, ta zaro ido wata kunya ta dirar mata tsikar jikin ta tabada *yarrr* ... a gaban mamee?
.....mameen kuwa tsawa ta daka mishi tana cewa wallahi ka daketa sai ranka ya baci sakar ta.
Yarinyar nan fa ta gama yi mun shiga hanci da kudundune mamee nema takeyi ta kwacen fada wajen ki......bazaka saketa ba? Ta daka mushi tsawa.
Ya warware kafafun sa ta yunkura sai ya kara tabiyota yanda ta fada mishin sai da fuskar su ta hadu.
Ta mike da sauri shi kuma ya dafe hanci kai kai kai ni kika bige? Ya yunkuro zai chafko ta mamee ta janyeta da karfi ta boyeta bayanta.
Wai kai wane irin maketacin yaro ne *madaki?* ta fada a hassale,
Haba mamee baki ga ketar da ta yi mun ba?
Kana ganin don iyayenka banga lokacin da ka tabiyeta da kafa ba? Allah ya kara, alhakinta ne.
Umaimah dai tayi sukutiii...kamar ta bude kasa ta shige, yau kawai ta tsinci kanta da wannan kunya, ko don bani da hijabi? Amma sau nawa muna hakan babu hijab kuma banji komai ba, kawai don a gaban mamah ne,
Ya bita da wani mugun kallo amma ta sigar harara ta kara soke kai bayan mamee.
Tashi ki dauko hijabi ki tafi gida shidda ta kusa, ki dauki sauran naman ki tafi dashi tunda baki ci ba....
Ya mike nima fita zanyi.... Zauna! Ta nuna shi da yatsa.
Allah mamee....wallahi ba in da zaka je har sai ta tafi, muguntar ka ke ban sani ba?
Wallahi babu abinda zan mata mamee....... Allah bazaka fita ba na ma rantse. Ya zauna rai a bace,
Ta fito simi simi ta wuce ya bita da kallo idon mamee na kansa. Ta buga tsoki, Allah ya raba ka da wannan mugun hali. Ka fitina wa yarinya saboda shegen son zuciya kai da abun duniya bai taba wucewa wurin ka....
Mameee... Kawai ta mike tayi ciki tana fadin halinka ne ban sani ba ko kuwa mugun rikon ka ke ban sani ba?
Ya tabe baki yana 'yar dariya mamee masu 'ya duk ta hakikance. Bayan isha'i ne mameen ke fada mishi dalilin murnar umaimah, wani dadi ya ziyarce shi ya ce *anzo gurin* sannan yayi murmushi lallai tana son karatu amma *Mr samuel* ya fara mata *lesson* kona wata biyu ne tukun tunda kin ce tana da ganewa. Baki mamee ta bude tana kallon sa bata taba tunanin abin zai zo da sauki haka ba, ta shirya taro mishi ta inda duk ya bullo.
Ya zungurota mamee.....yana murmushi.
Ta kara kallon shi, tsakanin ka da Allah har azuciyarka haka maganar nan taka take ba wasa?
Yau na bani wai daukar me kikeyi man ne don Allah? Kina tunanin duk abinda kike so zan kishi ne mamee?
Yau kuma? Ta bukata tana ci gaba da kallon sa.
Ya dafa kafadarta mamee *I mean it please* bacin amincewa ma hada shawara na bayar.
Ta fara shi mishi albarka yayi sokoko yana kallon ta yanda ta dage tana nuna tsantsar farin ciki. A zuciyar sa kuwa kagare yake gobe ta yi yaga kalar murnar da umaima zata yi idan taji ya amince. Don wacce ta yi marar dalili ce yayi murmushi. *Gobe zata yi mai dalilin kam* daga ni sai ita bata taba mun dariya ba ko ta mugunta kuwa, sai dai na gani a sace ita da mamee shima tana ganina zata gintse... Yaja guntun tsoki.
Su goggo nata shagalin nama umaimah na daki ta makure, ohh ni umaimah na shiga uku da wannan mutume.
Tsikar jikinta ta kara tashi *yarrrrrrrr* tana hasko ta bisa jikin sa kwance, ta kudundune kai a cinya lokacin da amon muryarsa yazo mata, *am very sorry kiyi hakuri* yau ni madaki ke ba hakuri. Ya ce yana so mu daina fada gashi a gaban mamee ya mun abinda bai taba ba, ko ya daina jin tsoron ta?
Jikinta ya kara sanyi ta tuno sungumar da yayi mata ya kaita sama, *ohh ni ina na kai kaina ni marainiyar Allah*
Ta dago kai, nima ina so mu daina fada, idan ba masifa yakeyi ba muryar sa na da dadin sauraro, yana da masifar kyau gashi dan gayu, da yawa ina son kallon sa amma ina tsoro.
Jijiyoyinta suka kara tsinkewa da ta tuno shi zukunne gabanta yana magana a tausashe. *ohh ni umaimah* mai kudi kamar *madaki* ta ce *Hmmmm*
Haka ta susuce ta kwana tunanin sa. Ta kagara gari ya waye, daren yayi mata tsawo juyi kawai takeyi.
Karfe uku yau ta yi wanke wanke da duk abinda ta saba, lokacin da aka kira sallah tana shafa mai har tayi wanka,
Ta yi tagumi gaban jakar kayanta, wane zan saka?
Ta fiddo wannan ta mayar, sai da ta kare kaf, ta yi tsoki tafi mintuna ashirin da a haka, da kyar ta amince da wata atamfa roba wacce ta siyo dari tara lokacin bikin *Asma'u* dinkin riga da skirt ba kwalliya amma kayan na mata kyau. Ta rangada kwalliya saboda gwana ce sosai karambanin ta yasa ta iya kwalliya sosai da daurin kallabi, idan ana sabga ita ke wa mutane da dama. Abinda ke hanata yi karancin kayan shafan.
Ba ta hauka tayi ba, bayan ta gyara gira yar hoda kawai ta shafa da dan Jan baki sai kuwa kwalli data zizara, abinka da ba sabanba umaimah ta yi wani fayau.
Shidda da rabi tabar gidan, bakwai da kwata ta isa.
A gurguje ta gama aikin ta baro mamee ciki ta dawo falo. Kadan kadan ta kalli sama shiru bai sauko ba, tayi zugumm!!!! Haka kawai yau ganin sa take son yi.
Mamee ta fito uwani shirya mana break yunwa ta gargado ni, ta tashi da hanzari, tanayi tana waige amma shiru bai sauko ba,
Mamee na zama ta dauko flask kenan zata zuba ruwan zafi ya fito *a slow motion* ta rinka ganin takun sa, sanye yake cikin wani farin boyel mai zanen kwallo kwallo ya kashe hula har goshi kansa sunkuye yana faman daura agogo duk falon ya dauka da kamshin turaren sa.
Kirjin ta ya shiga harbawa ta fara yar kyarma ta sunkuyar da kai tana zuba ruwan zafin,
Idanun sa yakai kanta har ya iso bai daina kallonta ba ita kuma taki dagowa,
*Morning mamee! Ina sauri zanje office for an urgent meeting*
A aika mun da break by 11:30am.
Ta dago da sauri har ya kusa kai kofa. Wani abu ya tuko mata,
*Allah ya bada sa'a* inji mamee
Daga can waje ya ce amin ya kara gaba.
Na shiga uku wai me ke damuna?
Ke lafiya?
Ta yi firgigi,
Menene? Ta kara Bukata,
Ta danyi *pretending* cikina ya dan katsa, ta sa hannuwa a cikin.
Yunwa ce maza hada kalaci, ta tsareta. Haka nan take cusawa amma Sam ko dandano bata ji. Ta fada mata zata fara *lesson ** daga litinin din nan. Ta danyi murna mamin bata damuba tunanin ta ko cikin ne ya dameta.
Shiru shiru har Biyar da rabi bai dawo ba, hankalin umaimah ya tashi *kadai fa son madaki nake na shiga uku?*
Ta dauko kayanta ta yi sallama, tana Jan kofa yana budewa yayi Saurin rabewa jikin bango ya bata wuri alamar ta wuce fuskar sa ba yabo ba fallasa. Ta dan kalleshi kadan ta wuce,
Ta na bada baya, ya bita da kallo kamar ya janyo ta amma ya sha alwashin daga mata kafa har sai zuciyarta ta dan saki dashi sannan yana gudun kada ya takura mata ta botsare ta ce karatun ma bata so. Wannan shine rashin sani....
Ta dan waigo har ya turo kofa.
Na shiga uku ya fita harka ta?
Ta juya sukuku.
Abu kamar wasa ya ma rage zama gidan, kullum sai ya ce a bishi da kalaci, abin ya dameshi amma ya daure, musamman da yaji ta fara lesson. Ga umaimah kuwa ta gama rikicewa, yanzu labewa ta keyi tana kallon sa ba tare da ya sani ba, wani karin takaici da ya hau sama ya ganta tana gyara sai ya koma falon mamee. Haka zata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login