Showing 51001 words to 52988 words out of 52988 words

Chapter 18 - HAYAR MACE! BOOK COMPLETE BY OUM HAIRAN.txt

“Kikace me Sakina akan wannan karuwar kilakin yarinyar?" Nan Sakina ta karkace ta rin?a karanto ?arya da gaskiya tana zayyanawa Safiyyah da Dr Salima da Hisham sukayi mutuwar tsaye lkcn Kumbo bata parlourn Saida Sakina ta gama tsaf sannan Safiyyah ta rushe da kuka tace “Eh naji ni karuwa ce yar Kawali dama ba abin mamaki bane don nazama a haka amma abin mamaki ne ?ar sarauta da suke ta?amar asali da nasaba ta zama karuwa taxi no garage kowanne ?an iska ya shigeta ya ficeta sannan Ni na godewa Allah daya kasance wannan da kike haukan akansa shine ya fara sanina kuma dashi muka lalace sannan shine uban shegen da kike magana akansa, Sakina banason nayi Miki tareran banka?a amma tunda kin za?a muyi" nan ta fara zubo zantuka tana nuna Sakina ga uwarta ga yayarta a gurin tana cewa ko ?arya nayi Miki ko kuma kin manta ranar da kaza da kaza ta faru ko kin manta lokacin da na rakaki asibiti aka cire Miki cikin wata biyar saboda kince bana mijinki bane duka kin manta Sakina da har zaki fa?i aibina ko an gayanki zanji kunyar Hisham yasan wani abu game danine wlh banaji domin duk abinda na zama shine farko kuma in duniya zata?i yarda dani nasan shi zai ?aunaceni kodon ha??i so gani gaki ga Hisham yau ranar ?ar tin?e sai ya yanke hukunci idan ya za?eki Banida asara don dama ke kike haukan sonsa Ni bansoshi ba bansan dai ko nan gaba ba......."








Hayaniya ce ta ishi Kumbo dake sallar walaha ta mi?e ta nufo parlourn saboda jiyo gunjin kukan ?ar tata da takeyi yana ta?a zuciyarta daidai lokacin da Mom ta cakumi wuyan Hisham tace “na rantse da Allah indai Ni Zainabu buzuwar agadas kasha nonona ka girma saika saki wannan yarinyar.......
Caraf idanunta suka fa?a na Kumbo dukkansu sukayi turus Mom na sakin wuyan Hisham ta nuna Kumbo da hannunta tace “Hajara meye ha?inki da wannan gidan?" Itama da mamaki tace “Zainabu dama rai kanga rai...." Rugawa sukayi suka rungume juna Mom tace “Shekarun baya Mal yake cemin anganki bayan ?atan da kikayi harma kin sake aure kina Abuja har lambar ki na kar?a saidai duk sanda zan kira sai naji a kashe, Hajara meye ha?inki da gidannan?" Murmushi Kumbo tayi tace “Safiyyah ?ata ce ta cikina...." Zaro ido tayi tace “?arki?" Jinjina mata kai tayi tace “Hakane ke fah?" Sunkuyar dakai tayi cikin tsananin kunya tace “Yanzu Safiyyah yarki ce?"
[8/24, 10:30 PM] Am Oum Hairan: _*HAYAR MACE LAST PAGE*_








Jinjina kai tayi Hisham ya cije le?e cikin matsanancin farin ciki yana jiran yaji amsar da hajiyansa zata bayar sai yaga ta zauna da?ar tace “Na shiga uku Ni Zainabu Allah ya rufamin asiri kunyarki ka?an naji yanzu da nayi wani abu da yafi wannan da ina zan tsoma raina Safiyyah ?armu ce ashe Hajara Hisham ?anki Safiyyah ?ata ya akayi hakan ta faru meyesa ?addarar ha?uwarmu da aurensu yazo a haka?" Tana maganar tana cacumo Safiyyah da taketa kuka tanajan zuciya tace “Duk abinda ka za?a Hisham wlh wata kusan tafi wata Safiyyah ?ar uwarka ce da Mal kakanku daya haifeni da kakan Safiyyah daya haifi uwarta uwa ?aya uba ?aya kaga kuwa duk kusan gona batakai ?aki ba kuma hannunka bai ru?ewa ka yanke ka jefar saidai a cire makashi dole Nikam na kar?i wannan ?addarar Hajara ga jikanmu nan tsakaninmu sai muyi masa gata"








Hawayen farin ciki Kumbo ta share tace “Haka Allah yake ikonsa ina gdy ga Allah daya ?addara kece kika haifi Hisham duk da Nima a farko kamar yanda bakiji zaki kar?i Safiyyah ba haka banji zan kar?i Hisham ba saidai yanzu komai ya goge saiga yaran.....
Da sauri Safiyyah tace “Ni ban kar?e shi ba...." Ba Hisham ba hatta Mom Saida ta kalleta yayi saurin zubewa yace “kiyiwa Allah karki gujeni" Hajiya Mariya ce tace “Kai jinan karku mayar damu sakarkaru ku bawa ?ata mafita don bazan iya wannan barba?ar ba" murmushi Hisham yayi yace “Sakamakon inada ?an shege ita kuma Sakina bata cancanci ri?on ?an shege ba kawai taje na datse igiyar aure na mara amfani da taketa dakonta taje in tasamu wani mai rabon ya ?auka Nikam na jefar....."










Wani ihu Sakina ta saki tace “Ni kasaka Hisham ka sakeni fah kace?" Bai bata amsa ba yaja hannun Amjad suka fice a gidan.
Da?yar Hajiya Mariya taja Saknah suka fice a gidan tana gunjin kuka tana cewa “wlh Safiyyah taci amanarta dama ta shigo rayuwarta ne don ta rabata da mijinta" to itama Safiyyah bataji da?in hukuncin daya yanke ba taso ace ya h?r a rufawa juna asiri tunda dai dukkansu sun riga sun samu tasgaro amma ta fahimci yau manyan miskilan ne a kusa, daganan fah sabuwar duniya ta bu?e tafiya Abuja harda Mom wani farin ciki sukeji kawayen kuruciya an ha?u Mom cewa tayi sai Safiyyah ta shirya taje taga inda uwarta take haka suka dunguma har Hisham shikam ya lura gwanar tasa ta kasa sanin Annabi ya faku har yanzu huhhura hanci takeyi ita a dole anyi mata laifi bayan kansu sukayiwa laifin ita ya lura ma lalurarsa har yanzu bata fara damunta ba.








Koda suka sauka a Abuja Safiyyah ta raina kanta ganin daular da Kumbo ke ciki tabbas Allah ba abin wasa ba nan akaci akasha ?a?an Alh Hamza sai jan Safiyyah sukeyi aunty sama aunty ?asa itama ta rikesu kanne anan suka shashance har sati guda Mom anan ta barta Kumbo tace tanaso ta ?an gyara mata jiki aikan tasha gyara na sati Uku shidai Hisham gajiya yayi yazo ya ?auki matarsa saboda ya samu wani me magani ya bashi magunguna sannan ya tabbatar masa aljanar da akayi masa asirin bin mata da ita itace ta mutu kafin ta mutu kuma tayi ?o?arin ta kashe masa mazakuta Allah baiyi nufi ba wannan ne yasa gabansa ya daina aiki.
Aikan daga amfani da maganin yaji wasu kuzarai na saukar masa ?arfi kamar na ingarman doki a ranar yaji shifa da matarsa yakeson kwana, koda suka taho bai nuna mata yaji sau?i ba dake ta ?an ware dashi tanajan gyemunsa tana cewa “talasurun mijina yau inason kayimin ?o?ari gsky Kumbo ta tsumani sosai har wani ?iga nakeyi"






Murmushi kawai yayi mata suna zuwa gida kuwa ya cafeta yayi sama da ita gidan ma ba wancan bane sabo ne, bazar da ita yayi a gado ya kulle ?ofar ya fara cire kayansa bata wani dauka gaske ba Saida taga ya zare boxes dinsa ta diro a gadon da gudu ganin yanda penis ?insa ke Nishi tace “Wayyoh Hisham da wasa nake maka Allah....." Ha?e bakinsu yayi yana aika mata da wani masifaffen kiss me kashe lakar jiki.
Ta rintse idanunta tanajin yanda yake yawo da harshensa da hannunsa a jikinta har kawo lkcn daya cire mata rigarta ta shammaceshi ta ?wace tayi bayi da gudu yayi saurin binta yana cewa “plea... Please Fiyyah Don Allah karkimin haka wlh ina cikin matsanancin yanayi...."
Danno ?ofar tayi bugun duniya yayi ta?i bu?ewa yayi magiyar har ya gaji ?arshe sai ha?ura yayi itakuwa tana ciki da gayya tayi masa haka kalmarsa ce ta janyo da yake iya fa?a mata wai ba da?in gindinta ne yasa yakeson zama da ita ba har yana cewa shi ?yankyaminta ma yakeji wannan kalmomi sun ta?ata kuma ko zata yafe kowanne zata garashi da wannan.








Ranar duk yanda Hisham yaso hutawa ta hanashi haka ya h?r suka kwana ya kwalowa jin da?i ta goce masa har kuwa wata ?ar rama yayi, haka sukaci gaba da wannan mugun zama duk da?in da sukeyi idan ta lura yanason saku?arta saita narke shikuma ya kasa yi mata dole ana haka labarin jinyar Baffi ya samesu an kawoshi asibitin Shika na nan Zariya yana jinya tare sukaje da Safwan handsome guy yaro Hutu ya zauna masa kamar ba shine me tallar pure water a danjar kwanar magi da U.D.B road ba bangaren ?an ?anjamau aka kaisu daga shiga hankalinsu ya tashi karshe bangaren wadanda suke halin rai ko mutuwa aka kaisu halin da suka ishe Baffi ba mai kyau bane duk dakiyar zuciya irinta soja Saida Hisham ya zubarwa da Baffi hawaye ya ?an?ame Safiyyah yace “My pleasure ina ?ara godewa Allah da baisa zamuyi irin wannan ?arshen ba....."








Basu zataba sukaji Muryar Baffi a karkatse yana cewa “Tabbas rahama na bibiyarku yayana banta?a nadamar rayuwa ba Saida na tsinci kaina a wannan halin ashe da gaske ne da Hajara take cemin naji tsoron mummunan ?arshe ashe shine yake bibiyata wayyoh kaico Safiyyah na cutar daku nayi watsi da ha??o?inku ?arshe na watsaku duniya a nufina na kuma ku gur?ace duk da ke abin ya nasheki amma ?arshe sharrin ya dawo kaina mugun tanadina ya kife dani nasan ma na riga na lalace ban tsinanawa rayuwata da taku komai ba sai asara kaico Safiyyah musamman ke ki yafemin don Allah kuma kuce da Hajara itama ta yafemin inna mutu ko sunana banaso kusa a zuri'arku tunda Hausawa sunce suna linzamin meshi......"








Jiki a mace suka koma gida tundaga wannan rana Safwan ke jinyar mahaifinsu badon ransa naso ba sai don tursasawar mijin mahaifiyarsu da yace suyi kokarin sauke hakkinsa kar suyi faduwar ba?ar tasa suma, haka sukayita hidima dashi har zuwa ranar da ajali ya sauka ranar Laraba da asuba ya cika a asibitin anan akayi masa sutura suka daukeshi aka kaisa gidan Safiyyah akayi masa jana'iza kamar yanda addinin musulunci ya tanada sannan aka kaisa makwancinsa.
Bayan shudewar komai Safiyyah ta saduda ta rungumi mijinta sukaci gaba da gudanar da soyayya kamar ba itace a farko aka ha?ata da rainon jariran karnuka ba ashe tafiya na tafiya ubangidan karnuka zata raina idan suka zauna suna tuno rayuwar baya sai suyita dariya wani lokaci suyita tubarwa Allah.
Yanzu damuwar Hisham ?aya haihuwa babu ?asar da bai fitar da Safiyyah ba an juya mahaifar amma ciki ya?i samuwa shekaru sai tafiya sukeyi kusan shekaru goma sha biyar har shekarun girma sun fara hawanshi ana haka bayan sunje umara sun dawo Safiyyah ta fara zazza?i me zafi da farko ma ta ?auka kawai gajiya ce Saida abu ya ta'azzara aka kaita asibiti suna gwadawa sukace ciki ne da ita, wayyoh murna gurin Alh Hisham da duk wani masoyinsa post a duniya kam ta shashi matar shugaban sojojin ruwa na ?asa ta samu shigar ciki bayan shekara goma sha bakwai ana nema gashi Amjad har ya zama saurayi shekaru ashirin kacokan Alh Hamza ya daukeshi ya tura shi jami'ar Tumbouctor dake Mali yana karantar bangaren addinin musulunci saboda a cewar Alh Hamza nutso cikin sanin ubangiji shine zai hanashi ya?i da iyayensa ya ?auki sanadinsa ?addararsa.






Lokacin haihuwa yayi Safiyyah ta haifo yarinyarta mace ranar suna taci suna Zainab abin mamaki shekara bata zagayo ba ta haifo yan biyu mace da namiji Hamza da Hajara tundaganan haihuwar ta tattara ta tafi suma ganin sun samu basu wani damu ba sai kuma hankali ya koma kan yara.
Ina labarin Hajiya Iyani ne ita ce mace ta farko data fara yima Amjad gorin da Saida yaron ya kwanta jinya dake Amjad ya taso da jin isa da izza irinta ubansa gashi kakanninsa sai tatashi sukeyi musamman Mai martaba da Allah ya jarabceshi da wani masifar son yaron kamar bashida wasu jikoki bayan shi.
Wannan yaja tsanarsa ga Hajiya Iyani aikuwa ranar da ta fa?awa Amjad waye shi itama bata kwana a gidan sarautar ba saki uku Mai Martaba yayi mata an ta?a zuciyarsa Amjad na warkewa Mai Martaba ya ha?a auransa da yar ?anwar babansa Yusrah akasha biki na bam mamaki Yusrah ta amarce da angonta ya dauketa sukabar ?asar ma gaba?aya.............










Tammat bih hamdullah






Bayan gwagwarmaya da tsilla tsillah yau dai Allah ya nufemu da kammala wannan labari me cike da darrusa da ba kowa ke iya gane su ba.
Ina godiya gareku masoya ha?i?a kun nunawa OUM HAIRAN ?auna ta hanyar siyan littafin hayar mace Allah ya ?ara muku nauyin aljihu???






Masu jiran complete kuma gashinan ya zama ready sai ku biya ku samu naku akan 500 cmplt document
Acct details 0255526235: Fauziyya Tasiu gtbank ko 3184512451 first bank ko katin waya MTN.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login