Showing 45001 words to 48000 words out of 52988 words

Chapter 16 - HAYAR MACE! BOOK COMPLETE BY OUM HAIRAN.txt

matsalata na kasa samu sai Shonikan shi ka?ai ne yasan wani abu cikin damuwata"
Tureshi tayi tace “Wlh indai bazaka rabu da wannan yarinyar ba to babuni babu kai har abada....." Da gudu Safiyyah ta fice a ?akin tana haki tabbas yau tana ganin masifa ashe haka iyaye sukeji idan suka samu labarin ?a?ansu sun lalace? To ita meye yasa nata iyayen basajin haka akanta anya kuwa haihuwar ta sukayi?"
Ji tayi an ri?ota ta baya ta zube a gurin ta rushe da kuka tace “Nayi maka haka ne don nasan bazaka iya yiwa kanka ba Hisham kai ?an gatane meye yasa ka gur?ata kanka da datti me naso kaico da banzo a irin gatanka ba da banzama kangararriya irinka ba Hisham ka barni na tafi don Allah kada kasa na zama silar yankewar farin cikin mahaifiyarka wlh gata takeyi maka da takeson rabaka dani banida wani amfani garek...."








?agota yayi idanunsa na tsiyayar da hawaye ya ha?ata da jikinsa muryarsa a tausashe yace “ko ?aya banji haushinki ba hasali ma sonki na ?ara Safiyyah Mom ta fusata amma nasan zata sauko karki yanke hukuncin rabuwa dani a daidai wannan lokacin mu tsaya mu jajirce mu gina rayuwar Amjad karya taso dajin mun lalata masa nasaba kuma munyi watsi da rayuwarsa na rantse duk abinda kikeso zanyi Miki muje gida karki ?ara fitowa kinji"
Gaba?aya sanyinsa na yau tausayi ya bata matu?a sai ta kasa yi masa musu ya ?auki Amjad yana ri?e da hannunta har suka shiga mota shine yakejan motar yanayi yana satar kallon Safiyyah da har yanzu take sharar hawaye suna zuwa gidan ya bu?e mata ta fito shima ya fito ri?e da hannun Amjad suka shiga ciki ta zauna a kujera ta kuma fashewa da kuka tace “kowa iyayensa na ba?in ciki idan ya lalace Ni nawa uban shine ya siyamin lasisin karuwanci Kumbo batayi ba?in ciki irin wanda Mom tayi ba lkcn da taji labarin gur?acewar ?anta meye yasa?"
Share mata hawayen yayi yana girgiza kai yace “Ita Kumbo tun farko anfi ?arfinta akanki itako Mom itace ke zartar da komai akanmu Ni ka?ai ne Zakka da Mai Martaba ya ?auki so da kulawa ya ?oramin ya kasance Mom batada ikon yanke hukunci akaina komai nawa Mai Martaba wannan yajamin tsana a ?angarori biyu na gidannan bangaren dangin mahaifina da ?angaren kishiyar mahaifiyata Hajiya Iyani.








Safiyyah Hajiya Iyani bata ta?a sona ba tunda aka aurota har kawo yanzu da take da shekara ashirin da biyar a gidannan, batada ?a a gidanmu amma tanada yara uku a garin su Bauchi mata biyu namiji ?aya, Fiyyah labarin da tsayi ki nutsu na warware Miki waye ni"
Gyara zamanta tayi ya kwantar da kanta a jikinsa yace “Tunda Hajiya Iyani tazo gidanmu taga irin ?aunar da mai martaba yake nunamin sai tasa ba?in ciki a ranta ta rin?a kusheni gurinsa ke har sharrin sata tasha rataya min Allah yana fitar dani akwai wata rana da bana mantawa na dawo daga school sai Mom ta bani sako tace na kaiwa Hajiya Iyani na nufi part ?in ta da sauri na harda guduna na shiga har parlourn ina zuwa naji itan da wata yar uwarta suna tattaunawa akan Mom Iyani tana tambayar ?ar uwar tata “Samirah kin tabbata in Zainab tasha wannan ruman ?in labarinta zai shu?e sai buzunta?" Jinjina kai Samira tayi tace “?warai kuwa dashi na kashe ?an mijina ai shima wannan yaron Hisham bayan an gama da uwarsa zamubi takansa don na fahimci cikin ?a?an gidannan duka babu me fadarsa kuma kinsan idan aka sake yakai labari akwai matsala don zai take kowa ne a gidannan kuma duk zaku zama a ?ar?ashin ikonsa...."








Motsin da naji yasani saurin nufar ?ofa na fice na samu guri na ?uya a wajen parlourn suka gama binne binnensu duk akan idanuna Saida suka koma ciki sannan na samu na sulale na nufi part ?inmu nida Sa'ad raina a jagule hankalina a tashe nasani Allah ya ?orawa Mom son ruman indai taga wannan ruman ?in bazata?i ci ba.
Dabara ce ta ba?omin na tashi na nufi part ?in Mai Martaba a lkcn ma bai zama sarki ba yana matsayin General ?insa dake tsohon soja ne yana ganina yace “Magaji waye ya ta?aka ne naga kamar an ta?a zuciyar maza?" Matsawa nayi nace “Allah ya taimake ka ruman naje Mom ta bani ta hanani" murmushi Mai Martaba yayi yace “Kacika rashin uzuri ungo je ka siyo babu ruman a gidannan ya ?are in ka tashi ka raba ka bawa kowacce nata ka kawomin nawa kaima ka ?ebi wanda zai isheka"








Murna ta cikani na kar?i ku?in na fita nasa driver ya ?aukeni ya kaini inda ake siyar da irin wadannan kayan na siyo da yawa na dawo gida ban kaiwa kowa ba na sashi a store Saida lkcn dinner yayi Hajiya Iyani itake da girki ta shirya komi a dinning ta koma ciki ina ganin ta koma na fito na isa kwandon data zuba fruit ?in na tsince duk ruman ?in dake ciki na zuba wasu na fice daga dinning area ?in da sauri na.
Lkcn dinner yayi kowa ya hallara duk da kasancewar Ni ba ma'abocin zuwa dinner bane ranar na samu shau?in zuwa, kamar yanda na tsammata kuwa Mom na zama idanunta yakai kan ruman ?in nan tayi ajiyar zuciya tare da cewa “wow mai favorite nayi missing naka two days general yaki siya mana"
Tana maganar tana luntsumashi a baki Hajiya Iyani tayi wani murmushi tace “Aifa gashinan sai kiyita sha" Mai Martaba ne yace “Dazu na bawa Hisham ku?i ya siyo ai bai kawo muku ba?" Da sauri nace “Na manta da nakai store ban fito dashi ba bari nazo na rabawa kowa ya ?auki nasa"








Gani nayi ta kafeni da Idanu nayi mata murmushi tare da mi?ewa nabar gurin don dama ba abincin ne damuwata ba, kwana ?aya biyu har uku Mom bata mutu ba tun wannan lokacin Iyani ta ?ulla min babu abinda zanyi inyi daidai a wajenta a haka muka ?ebi shekaru zuwa sanda General ya samamin aikin sojan Ruwa dake da karatu kuma da hanya sannan da ku?i na fito a babban matsayi to a sannan ne kuma gaba?aya tuggu da makircin Iyani yabar kan kowa ya kuma dawowa kaina saboda ku?in da taga ina fantamawa dasu gashi General ya sakarmin ragamar dukiyarsa musamman wacce take tsakanin Lagos Port-Harcourt da Ogun.
Duk yanda nakai da takatsantsan Saida matar nan ta rin?a shiga tsakanina da Mai Martaba itakam Mom gaba?aya tayi mana farra?u ko ganina Mom tayi tashi take daga inda take da wannan ta shigo da maganar aurena da ?iyarta Samha tare mukayi master's programs da ita a Uganda duk da ba ?angare ?aya mukayi karatu ba amma halinta babu wanda bansani ba cikakkiyar ?ar lesbian ce sannan yar shaye? da wannan nace a'a banaso da aka matsa na fa?i gskyr abinda na sani game da ita to lkcn shi Mai Martaba ya fahimceni aikuwa yace a'a to ayi fatan Allah ya ha?a kowa da rabonsa.
Kawai tana tashi a gurin sai cewa tayi Samha tanason Hisham saboda ba Janan bace ka?i tsaya mata to ka rubuta ka aje kafin Hisham yayi aure saiyayi abinda yafi na Samha zama abin kunya a duniya wanda kai kanka saika tsaneshi.......
[8/21, 8:17 PM] Am Oum Hairan: Wannan magana bata damu kowa ba kuma babu wanda ya wani dauketa da muhimmanci kowa ya ?auka kawai irin furucin nan ne da dayawan mutane sukeyinsa idan sun kasa cimma nasarar wani shiri nasu, haka rayuwa taci gaba da tafiya kwana kamar yini har muka cinye watanni lokacin ne kuma wasu al'amura suka rin?a ba?untata a baya inada burin idan na girma nayi aure na hayayyafa Nima amma lkc guda batare da wani dalili da zan iya ?orarwa ba kawai na tsinci kaina da tsanar duk wata hira data shafi aure.
Sai shai?an ya samu dama ganin ku?i ya fara zauna min ya rin?a yimin hu?ubar to meye ma zai dameni da wani batun aure tunda ga mata nan kala? tunda na fara rayuwar barrack suke kawomin caffa bana kulawa kuma inada ya?inin komai zan samu a jikinsu, da wannan hu?ubar ta shaidan ?udrat ta fara yin nasara a kaina, wata bazawara ce ?anwar matar ogana a gurin aiki watarana mun fito da Oga zamuje unguwa yace yayi mantuwa zai biya gida.








Muka isa gidansa ya barni a mota ya shiga ciki shiru kusan 20 minutes bai fito ba nikuma na gundura da zaman mota don haka na fito na tsaya jikin motar ina danna wayata.
Sallama naji anyimin na ?ago bakina yana amsa sallamar tayimin murmushi tace “handsome guy Oga yace ka shigo ciki" raina ya ?aci da wannan rainin hankali na Oga bayan mintinan daya bata mana har wani lkcn shiga ciki ne damu? Banda mafita bayan bin bayanta tana tafe tana karka?a mazaune tana wani kwarkwasa tun ban gane dani take ba harna fahimta amma sai na share.
Mun shiga ta saukeni a wani madaidaicin parlour ta kawo min tarkacen lemuka da abinci da farko banyi niyyar cin abincin ba ganin amala ce da miyyar ganye yaja raayina na ware ciki na fara cin abincin lokaci zuwa lokaci ina kallon TV data keta aiki ?udrat dake zaune tana ?aremin kallo tace “Da alama kanajin da?in abincin nan fah Oga" sai yanzu na dubeta gajeriya fara zubin yarabawan gaske naja fasali nace “na gde" da haka naci gaba da latsa wayana can Ukashat yaron Oga yazo yace na fito.








Dama na ?agara da kallon da wannan mata kemin don haka na mike na fice muka fita da Oga Allah ?aya daga wannan rana na manta da babin ?udrat ashe ita ina ranta bansan ta ina tabi ta samu number ta ba saiga sa?wannin tayin kai sun fara fa?owa wayata bana kulawa kuma banabi takai kai har takai ?udrat ta fara takowa tana zuwa gidana da zummar wai tazo gaisheni mukan gaisa nayi mata shiru shima don ina ganin mutumcin matar Oga banson taji na wula?anta ?anwarta.
Ana haka nayi wata rashin lafiya da bansan ya akayi ba nidai cikin dare na farka naganni a ?akina a kwance na yun?ura na mi?e kunne na na jiyomin alamun ?arar ruwa a cikin bayi, duk da kasancewata me zuciyar mazan fama Saida na ?an razana na mi?e tsaye jiri na ?ibana naji anyi saurin ri?eni Muryar ?udrat tace.
“Aiyah sannu Oga jiki babu ?arfi" zaunar dani tayi na zubanta Idanu da tsananin mamaki nace “me kikeyi a gidana baki tafi gida ba har yanzu 1:35am?" Sunkuyar da kanta tayi tace “ka samu rashin lafiya ne sosai da kake bu?atar kulawa so bazan iya tafiya na Barka ba Oga inason ka samu sau?i sosai" naji da?in yanda ta nuna kulawarta gareni na mi?e batare da nace mata komai ba na nufi bathroom ban jima ba na fito na bu?e wardrobe na ?auki abinda nasan zan bu?ata na nufi hanyar fita tace “Oga ina zaka?" A kasalce nace mata “ki kwanta a nan zan kwana a ?aya ?akin" ina fa?in haka na fice ta ciji yatsa tare da buga ?afa Nikam sallolin da ake bina nayi sannan na kwanta.








Daga lkcn nan ?udrat ta fara fitomin da asalin abinda takeso sani ina dojewa nidai bansan ya akayi ba wataranar asabar ina gida ban fita ba da yamma naji ana knowking na bada izinin shigowa ta bu?e ta shigo taci kwalliya tayi kyau cikin ?ananan kaya, tunda ta shigo tayi masifar ?aukar hankalina fiye da kullum tana yau?inta ta iso gareni ban ankara ba sai jinta nayi a cinyata ta sa?alo wuyana da hannunta tare da ?ora lips ?inta a nawa.
Daga wannan bazan ?ara iya cewa ga abinda ya faru ba sai bayan tsayin lkc na dawo nutsuwata wai naganni tu?e nida ?udrat kwance gado ?aya, aikuwa na shiga damuwa na lkc har na kasa jurewa nake Bama wani abokina Shazan inajin kinsanshi shine yake nunamin to meye ma zan damu kawai na saki jiki muyi rayuwa.








Daga wannan lokaci ?udrat tasha wahala kafin ta samo kaina mukaci gaba da rayuwa da iya ita mun ?auki lokaci aka daukeni daga garin su aka kaini Port-Harcourt acan ne fah komai ya canza na zama cikakken mazinaci takai ma bana iya ?oyeta sai a iya iyayena kawai,
Amma kuma fah lamarin aure da zancen sa duk sai suka janye bana ?aunar ayimin maganar aure yanzu zamu ?ata da mutum duk kusanci haka naci gaba da gudanar da rayuwata likkafar arzikina sai bun?asa takeyi ina rayuwa ta hutawa holewa da fantamawa.
Ja'afar aboki nane kuma ?an uwana ne da Mai Martaba ya sama mana aiki lkc ?aya shine kawai yake yimin nasiha da nunamin wannan rayuwa dana za?a ba daidai bace, to shima ba barinsa nakeyi ba nakan cinye mutuncinsa tsaf na ?ara masa da warning akan ya daina shiga rayuwata, so shine ya fara kaiwa Mom tsegumim halin da nake ciki ita kuma Mom irin mutanen nan ne da basa yarda da laifin nasu take tace masa zata bincika.








Ta kirani tana bugun cikina na zille mata da haka ta barni har nayi nisan da nayi a wannan duniya, wata har?allar kasuwanci ce ta shigar dani Kano tun a Lagos wani abokina ya bani number Zubair kawali yace idan naje ina bu?atar me ?auke kewa na nemeshi, shigar dare nayi na sauka a wani Hotel nan tarauni har na kwanta naji bazan iya rayuwa babu mace ba wannan tasa na nemi numbersa na kirashi bugu ?aya ya ?aga muka gaisa na sanar dashi abinda nake bu?ata yacemin to bari ya dubamin ya gani.
Cikin abinda bai wucce awa ?aya ba saiya kirani yake cemin ansamu wata zazzafa amma fah ta yanka ku?i da yawa don Abuja ma zata hucce ya dakatar da ita, banja ba nace suzo suka iso na fito tundaga kallon yarinyar naji bata kwanta min ba, yace “Ranka ya da?e wannan sunanta Basrah ita alhazzan birni ke yayi yanzu duk irin salon da kakeso zatayi maka gatanan ku daidaita"
Jan hannunsa nayi muka ke?e na dubeshi nace “batayimin ba ba test ?ina bace a nemo wata" da mamaki yace “duk ha?uwar nan Alh Ni kaina da bankai ba na ha?iyi yawu?" Zubansa Idanu nayi nan ya fito da babbar wayarsa ya shigarmin ?angaren hotuna ya bani ina dubawa ina dubawa har nazo kan hotonki nan naci birki na zubanki Idanu ina Miki kallon ?urullah da sha'awa, Zubair yace “Oga an samu ne?" Nuna masa hoton nayi ya kar?a ya duba ya ?ago ya dubeni yace “Wannan ?wailar?" Numfashi na sauke nace “tayimin" shiru yayi can yace.








“Bazan ?oye maka ba wannan tsatso na ce ?ata ce ta cikina Safiyyah kenan so gsky bata wannan harkar amma idan kana so zan iya farauto maka ita domin Ni indai da ku?i komai me sau?i ne"
Zubansa Idanu nayi ina mamakin kalamansa amma kwadaituwa ta gareki bai bani damar yin wani furuci ba sai tambayarsa da nayi kamar nawa?" Babu kunya yacemin idan iya dare daya ne zan bashi dubu ?ari biyu da hamsin idan satine kaza idan watane kaza idan kuma hayarki zan ?auka na shekara kamar biyu ko uku to zan bashi million shida amma na fara saka masa hu?u gobe da safe idan na koma gidana sai na zo na daukeki saboda bayason atafi dake inda zakibada matsala, har ya ?aramin da cewa ke?in ce bakida rabo yabawa wani bayamale hayarki kika?i yarda yanzu inna bashi ku?in zai turawa wancan kudinsa ne sai yasan yanda zai yi ya bani ke"
Da wannan na tura masa four Millons ?in na koma ciki ya ?auki tsumman daya kawomin suka tafi, da safe kuwa saiga kiransa yabani address da komai na biyo hanya Inayin parking ya fito dake ya jefaki a motar, tashin farko kallon fuskar mahaifiyarki data biyo bayanku tana kuka shine ya kashemin gwiwa har naji a raina anya kuwa ke?in ba ?ar tsintuwa bace ko kuma ?ar wannan baiwar Allah da take kuka shi kam inajin kamar babu ala?a.






Daga wannan lokaci muka fara rayuwa dake har kawo lkcn da komai ya gudana nasani na aikata babban kuskure da ?addara ta hukunta mutuwarki ta dalilin haihuwar Amjad amma sai Allah ya musanya ta zamana sa?anin hakan.
Yanzu abu ?aya zuwa biyu shine matsalata a rayuwa furucin Mom da Mai Martaba da kuma lalurata da nakasa samo bakin zaren warwareta.
Na da?e ina tunanin wannan wacce irin rayuwa ce wanne irin ubane da ya za?i yan canjikan da bazasu gama masa rayuwa ba akan sauke hakkin da ubangiji ya ?ora masa? Safiyyah tun kawoki gidana ba kiyayya bace tasa na kar?eki a rayuwata bana zama da abinda banaso saidai abu ?aya daya nemi gagarata koda yake shima ba gagarata yayi ba barinsa nayi, Safiyyah nasani kinyi bakin ?o?arin ki wajen ganin kin kare kanki kuma kinyi try saidai fa?owarki komata ya gaza tsallakar dake tabbas kinyi ?o?ari a matsayin da kika taso na tasgaron tarbiyya.
Da wannan nakeso ki bani dama muyi rayuwa mai tsafta Ni dake matsayin ma'aurata ba ma?arnata ba Safiyyah kinji tsoro da nace Miki ina cikin halin lalura sama da shekara biyu? To ki tambayeni meye matsalata mana".....
?agowa tayi da Idanunta ta suka rine sukayi ja ta janye hannuta daga ri?on da yayi mata takai hannu kwarmin idanunsa cike da kasala tace..........






_In kunjini shiru ku ?ara yimin uzuri akan wanda kukemin wlh da?i baisa na?i muku typing saboda nafiku son naga na sauke ha??inku yanda ya kamata._
_lfy sosai wlh yau ne d la'asar na ?an ji ?wari har na ?arasa muku wannan Page ?in._


_Littafi na na ku?ine sis kiyiwa Allah karki karanta in baki biya ba, 300 PC 700 view acct details 3184512451 first bank or 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank._
_Ko kati MTN ta WhatsApp number na 09013718241_
_?an Niger zaku tura kati Airtel na 500f ta waccan number dake sama_
[8/23, 6:53 PM] Am Oum Hairan: *_HM 57-58_*






Me kake tunani da rayuwarka game da Hajiya Iyani?" Baison sanyawa zuciyarsa zargi hakan yasashi mi?ewa yace “Babbar matsalata a yanzu ita ce lalurar dake damuna shekara biyu bana a matsayin namiji bazan iya biya wa kowacce irin mace bu?ata ba Safiyyah wannan itane damuwar dake gabana ba waccan ba"
Zuba masa idanu tayi tare da ha?iye wani abu da taji ya tsirga zuciyarta ta mi?e tace “to meye zai dameka da son saika biyawa mace bu?ata bayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login