Showing 18001 words to 21000 words out of 47397 words

Chapter 7 - MEENALYN DADDY Complete Book By Fadila Sani Bakori.txt

06 Jan 2025

2929

ba,dan Allah ka barni in cika alk'awarin da na d'aukar mata".
"Kwantar da hankalinka Sani,babu wanda zai ma Amina auran dole".Cewar Sarki.Alhaji kallan sarki yayi ya ce"Alk'awarin da na d'aukarma Abdurrahman fa?,Sannan Amina bawai Abdurrahman bane bata so kuwa ma baso take ba".
Shiru sarki yayi sannan ya ce"Duk da haka alhaji baza ai ma Amina auran dole ba".
alhaji da ran shi sosai ya b'ace ganin yadda Sani ya fito k'iri-k'iri ya nuna baya son d'an'juma,hakan yasa alhaji cikin tsantsar b'acin rai irin Wanda daddyn meenal bai tab'a gani ba ya ce"Sani tashi ka tattara kaida iyalinka kubar garin nan yanzu-yanzun nan!".
Daddyn meenal ganin yadda ran mahaifinshi ya b'ace sai kuma hankalinshi ya tashi ,kallan maihaifinsa yayi ya ce"Alhaji dan Allah kayi hak'uri".Alhaji cikin d'aga murya ya ce"Sani ka d'auki iyalanka nace ku koma Kaduna ka cikama 'yarka alk'awarin da kai mata ".
Daddyn Meenal cikin sanyi ya ce"Alhaji kai fa?".Bazan tafi da kai ba,gobe Sule yazo ya d'aukeni ".
Daddyn meenal shiru yayi,k'arshe ya gama zamanshi ya tashi ya tafi cikin sanyin jiki".






Alhaji Abba ko da ya fita rasa inda zaiyi ya yi , dan baisan gidan da su meenal sukeba.Tunanin number da meenal ta kirashi ta fad'omai,hakan yasa ya ciro wayar shi ya Kira number d'an'juma.
D'an'juma ko dama yayi serving number daddyn meenal,hakan yasa daddyn Meenal nakiranshi ya gane mai Kiran ya d'aga yana mai yin sallama.
Alhaji Abba amsawa yayi sannan ya ce"Meenal ce ta kirani da number nan,dan Allah ko tana kusa"."A'a bata kusa, ina Funtua ne ,sai dai in nadawo".Cewar d'an'juma"
Shiru alhaji Abba yayi sannan ya ce"Ina son inje wajan su ne,babu yadda za ai?".D'an'juma cikin girmamawa kamar daddyn meenal na kusa da shi ya ce"Kana ina ne sai in turo yaro ya tafi da kai?"."Ina k'ofar gidan sarki"."Tom bari in turo yaro sai ya k'arasa da kai gidan".
D'an'juma na fad'in haka ya kashe wayar ya kira yaran shi sule mai tsaran shagon shi ".






Daddyn Meenal na jikin motar shi tsaye cikin damuwa sosai,sai ga Sule da d'an'juma ya turo.Sule gaida daddyn meenal yayi sannan yayi mai bayanin shine Wanda d'an'juma ya turo yaraka shi gidan su.
Alhaji Abba motar shi ya bud'ema sule ya shiga suka tafi.








B'angaran Meenal ko tana zaune tana shafa mai ,Sule ya shiga gidan .Bayan ya gaida su ne ya ce"Daddyn Meenal ya ce su Meenal su fito su tafi" .
Meenal cikin jin dad'i ta ce"Wayyyo sweet daddy ya iso".Mommyn meenal kallan Meenal ta yi ta ce"Jiki gani meenal".Aiko meenal da sauri ta zira doguwar rigarta ta yafa ma yafinta ta fita da murnarta"






Meenal da gudu ta fad'akan jikin daddynta tana cewa"Oyoyoyo sweet daddy naji dad'in zuwanka Wallahi dama duk atakure nake".
Alhaji Abba bai tankama Meenal ba dan cikin damuwa yake sai dai kanta da yashafa ya ce"Kira mommynki mu tafi".Meenal jin amsar da daddynta ya bata yasa ta d'ago tana kallan shi ta ce"Sweet daddy naganka so silent".Murnushi alhaji Abba ya kuma yi ya ce"Kira mommynki mu tafi yamma tayi".








Meenal kallan daddynta tayi ta juya ta tafi, tana mamakin yadda taga daddyn nata.Meenal na zuwa ta ce"Mommy ki tashi tafiya zamuyi ".Hajiya mariya da babu abinda za tai jakar ta ta d'auka ta rataya ta kalli Mahaifiyar d'an'juma da itama ita take kallo ta ce"Tom Auntyna zamu tafi sai watarana in mun dawo ko kuma ku in kunzo".
Meenal kallan Mommynta ta yi ta ce"Mommy har kina fatar ki k'arazuwa kyauyan nan,tom sai dai kinzo amma ni kam bani ba"."Suma basa gyayyatarki".Cewar mommyn meenal.
Mahaifiyar d'an'juma dai murmushi ta yi ta ce"Tom hajiya Allah ya k'addara saduwar mu".








Mommyn Meenal tun yadda ta hangi daddyn meenal atsaye yayi shiru ta san da akwai matsala.Mommyn meenal cikin fad'ad'a fara'arta ta k'arasa wajan daddyn Meenal ta ce"Barka da zuwa daddyn meenal".Alhaji Abba cikin kasa danne yadda yakeji ya ce cikin sanyi"Yauwa mommyn meenal,na sameku lafiya?". Daddyn meenal ya fad'i maganar yana mai bud'e musu motar su shiga.
Bayan sun shiga ne daddyn meenal har yaja k'ofar ya tafi ,hajiya Mariya ta kallai ta ce"Daddyn Meenal alhaji fa?".
Shiru daddyn meenal ya yi.
Hajiya Mariya kallan Alhaji Abba ta yi da kyau ,tabbas dagani mai gidannata yanada damuwa,hajiya mariya cikin sanyi ta ce
"Daddyn Meenal alhaji fa ?"."Wai ba zai tafi damuba ".
Hajiya mariya cikin mamaki ta ce
"Daddyn meenal lafiya,ko munyi mai laifi ne?".Shiru alhaji Abba yayi dan bai san mai zai ce ma hajiya Mariya ba.






Haka su Alhaji Abba sukaci gaba da tafiya shiru kakeji,dan Meenal ma tayi ma daddynta magana ,ganin daddyn nata kamar yana cikin damuwa yasa Meenal ma taja bakinta tayi shiru.
Daddyn meenal basu suka shiga gida ba sai k'arfe tara na dare(9:00PM).Suna shiga Meenal ta baje afalo.Alhaj Abba ko ciki ya shiga yayi alwallah ya tada salloli biyu da aka biyosu, magriba da isha'i.
B'angaran hajiya Mariya ma haka,itama ciki ta shiga ta gabatar da sallolinta,tana idarwa ta shiga kitchen tayi musu jolop d'in taliya.Hajiya Mariya da ta fito kwance ta iske Meenal kan caution tana bacci .Hajiya Mariya bubbugata ta farayi da k'arfi tana cewa"Meenal bacci kika fara bacin kinsan biki sallah ba,babu irin tashin da hajiya mariya ba taima Meenal ba amma tak'i tashi dole ta k'aleta.Bedrom d'in daddyn Meenal hajiya Mariya ta nufa kwance ta iske shi kanshi asama daga gani dai yayi nisa sosai a tunani,hajiya Mariya zama tayi gefan kadon ,sannan cikin alamun damuwa ta ce
"Daddyn Meenal dan allah mai ke damunka,tun da kaje d'akko mu na lura kanada damuwa amma kayi shiru,ita fa damuwa idan mutum ya furtata yana samun sauk'i daga yadda yakeji".
Daddyn Meenal tashi yayi ya zauna yana kallan mommyn meenal,ya ce"Wa ye Abdurrahman a kyauyan da ku kaje?".Hakanan hajiya Mariya sai taji gabanta ya fad'i batare da tayi tunanin komai ba,ta ce"D'an'juma kenan,jikan sarki,gaskiya yaron nada hankali sosai da natsuwa".Hajiya Mariya ta idasa maganar tana kallan daddyn Meenal.
Numfasawa alhaji Abba yayi ya ce"Yaron ya nuna yana son Meenal ne?"
Gaban Mommyn meenal fad'uwa yayi jin abinda daddyn meenal ya ce,kallan shi ta yi ta ce"Eh tom,gaskiya ni banga wata alama ba,amma Meenal yau kwana biyu kenan ta shigo tana kuka wai yaron da kake magana ya ce yana sonta,dan ta dad'e tana kuka,nan ma dai mahaifiyar yaron ita taita lalla shinta".Shiru mommyn meenal tayi sannan ta ce
"Wani abu ya faru daddyn meenal?"
.Alhaji Abba shiru yayi kamar ba zai ce komai ba sannan ya ce
"Jiya alhaji ya kirani akan inzo yau ,tom shine bacin naje yake sanar dani wai yayima yaron alk'awarin auran Meenal".Alhaji Abba ya idasa maganar cikin damuwa sosai.
Hajiya Mariya ko ai rud'ewa tayi ta ce"Daddyn Meenal alhaji ya bada auran meenal kace fa?,A kyauyan nan ya bada auran nata?".Kai daddyn meenal ya jinjina ya ce
"Haka alhaji ya ce min,da nanuna banyadda ba shine ya nuna min b'acin ranshi sosai,har ya nuna bazai biyomu ba ,tom Wallahi tunda alhaji ya furta maganar nan narasa natsuwata,nama rasa yadda zan b'ulloma al'amarin".
Wai Allah,hankalin hajiya Mariya ai sosai ya tashi,dan yafi na alhaji Abba tashi ma.
Cikin Sanyi hajiya Mariya ta ce
"Kabari zamuyi maganar da alhaji nasan insha Allah zai fahimceni"Tom Allah yasa".Cewar alhaji Abba".






"Tom ka tashi muje kaci abinci".Alhaji Abba da ya d'anji sauki daga yadda yakeji tashi yayi yabi hajiya Mariya .Kwance ya iske meenal tana bacci,zuwa yayi dan ya tadata taci abinci tak'i tashi ,dama yasan haka dan Meenal akwai wuyar tashi idan tayi bacci.Alhaji Abba bayan ya gama cin taliyar ziboma meenal yayi a plate ,da kyar ya samu ta tashi,ka d'an taci ta tafi zata kwanta hajiya Mariya ta kalla mata harara ta ce
"Sallah fa?".Meenal turo baki tayi ta ce
"Ai tunda kikaga banyi ba sai ki rubu dani ko ,kinsan bayi zanyi ba".Meenal na fad'in haka ta d'agama daddynta hannu ta ce"Sweet daddy good night"."Good night too meenalyn daddy ".






B'angaran alhaji ko bayan daddyn meenal ya tafi sarki hannu alhaji ya kamo ya ce
"Alhaji mubi komai ahankali dan Allah,idan Allah yasa Amina rabon Abdurrahman ce tom babu abinda zaihana ya aureta inda wani bai auran matar wani".Hakane malam Haruna,nima bawai zantsauwala abin bane,dama ina tuna alk'awarin da naima yaron nan ne,sannan kai abinda baka fahimta ba Sani baya son Amina tai aure yafi son yayita ganinta agabanshi.Wallahi malam Haruna idan ba wani ikon Allah ba Sani bazai bar Amina tai aure ba,inda itama bason auran take ba,ita kuma 'uwar ba isa tayi ba,lokacin da ita kuma zataso auran in ba sa'aba babu samarin kuma".Cewar Alhaji .
Shiru sarki yayi,dan shi harga Allah cikin zuciyar shi bama son d'an'juma da yarinyar yake ba.








B'angaran d'an'juma ko bai San da tafiyar su Meenal ba.Dan koda yaje gidan bai gansuba kasa tambayar mahaifiyar shi yayi bakamar yadda yaga tana ta d'aure mai fuska ba ,hakan yasa ya koma gidan Sarki,nanma ba damar tambaya yanajin kunyar kakan meenal hakan yasa yaja bakin shi yayi shiru.
D'an'juma da daddare yana kwance ad'akin shi kan shi sama yana ta tunanin sahibar shi Meenal, ahaka bacci ya kwasheshi.
Washe gari d'anj'uma yaje kaima tsofaffin abin Kari ya iske alhaji wato kakan Meenal ya zagaya bayi,d'an'juma cikin jin dad'in rashin ganin alhaji ya kalli sarki ya ce
"Sarki ina bak'in mu ne?".Aiko kamar d'an'juma ya tunama sarki ya ce
"Yauwa Abdurrahman dan Allah abinda nake so da mai kasamu alhaji kace mai kajanye maganar son yarinyar nan da kace,saboda kaga yanzu haka alhaji ya d'au fushi da mahaifin yarinyar nan ,dan Allah Abdurrahman ka naimi mata akyauyan nan kayi auranka".
Shiru d'an'juma yayi sannan ya ce"Sarki kamar yadda na fad'ama ban tab'a jin ina sha'awar inyi aure ba Wallahi sai akan yarinyar nan,sannan ni kaina nayi yak'i da zuciyata ganin na cire sonta araina tun kafin kaikankama in furtama amma abin yak'i yuwuwa,dan Allah Sarki katayni addu'a kawai".
"Abdurahman ka kwantar da hankalinka insha Allah zaka auri Amina kamar yadda nace maka da farko,kai dai kawai abinda nake so da kai kayi addu'a".Cewar alhaji da shigowar shi kenan d'akin ya riski maganar.
D'an'juma cikin jin sanyi ya ce"Nagode sosai da karramawarka gareni alhaji"."Babu komai Abdurrahman ".Cewar alhaji .






Sarki dai bai ce komai ba.Bayan sungama shan tea d'in da d'an'juma ya kawomusu babu dad'ewa ishuhu yazo d'aukar alhaji.Sosai sarki yaji babu dad'i .Haka dai su kai sallama alhaji ya tafi"






Da yamma daddyn meenal ya je gaida mahaifin shi yayi mai sannu da zuwa,amma haka daddyn meenal ya gama zaman shi alhaji bai tankamai ba,k'arshe ya gaji ya tashi ya tafi,haka yaje gida duk ba dad'i.








BAYAN SATI D'AYA:Haka kullum daddyn meenal idan yaje gaida mahaifin shi sai dai ya gama zaman shi ya tashi amma ko gaisuwar shi baya amsawa.Dan yau da yajema Alhaji kallan daddyn meenal yayi ya ce
" Sani nikam daga yau na yafema wannan gaisuwar da kake zuwa yimin,daga yau ba sai kazo ba kayi zamanka a inda kake nagode".
Daddyn meenal kallan mahaifinshi yayi zaiyi magana ,alhaji ya d'aga mai hannu ya ce
"Sani dan Allah bana son doguwar magana sai anjima".








Alhaji Abba tashi ya yi ya tafi .Yana zuwa yayi part d'in shi yana mai dafe kan shi.Hajiya Mariya ganin yadda Alhaji Abba ya shigo ne yasa tabi shi da sauri,sai dai yadda ta ganshi rik'e dakaine yasa ta rud'e ta ce
"Daddyn Meenal lafiya?".Alhaji Abba ba magana ,k'arshema kawai sai ya fashe da kuka".Hajiya Mariya cikin tashin hankali ta fita ta kira Meenal.Meenal da ita kanta yanzu kusan cikin damuwa take ganin yadda take ganin daddynta dan ya daina fira da ita sosai,magana ma yabar yin mai tsawo.Meenal cikin kuka take girgiza daddynta tana cewa"Daddy Lafiya wayasa kuka daddy,dan Allah kayi shiru".Daddyn meenal ko rik'o hannun Meenal yayi ya ce
"Meenal gara in mutu da inga wannan rana,Meenaln daddy zuciyata bazata iya zurewa ba in ganki cikin damuwa,bazan iya jurewa ba Gara Allah ya d'auki rayuwata zaifi min dad'...."."Haba daddyn Meenal akan abin nan ne har zaka rik'a kirarin mutuwa?".
Meenal ko fad'awa tayi kan daddynta tana cewa
"Wayyo daddyna bazaka futu kabarni ba,dan Allah kar ka mutu daddy,Mommy dan Allah kice ma daddy karya mutu"."Tom ki yi shiru ga docter nan na Kira zai zo yanzu ya duba shi".






Su mommyn Meenal sunanan zaune sun tasa daddy Meenal da ke ta faman juye-juye saboda yadda kanshi ke mai .
Su hajiya Mariya na nan zaune abokin alhaji Abba ya shigo,yana zuwa ya yima alhaji Abba aune-aunan da yakamata yayi mai,ya kalli hajiya Mariya ya ce
"Hajiya gaskiya jinin Alhaji Abba ya hau,amma babu damuwa da akwai magani da zan kawo mai yanzu,kuma gaskiya ayi k'ok'arin ganin yabar shiga damuwa,Dan shi yayi sanadin halinda yakeciki yanzu haka".








Hajiya Mariya dai godiya taimai.Shi kuma fita yayi samoma alhaji Abba magungunan da suka kamata.
Hajiya Mariya ko kama hannun Meenal da keta kuka tayi suka koma Falo suka zauna.Hajiya Mariya kallan Meenal tayi ta ce
"Meenal daddynki na cikin wata damuwa wadda ita ce tayi sanadiyar da jininshi ya hau.Alhaji yau kusan kwana goma kenan baya amsa gaisuwar daddynki Meenal,k'arshema yau yace mai baya son ya k'ara zuwa inda yake,Wanda inada tabbacin shine yayi sanadiyar da jinin daddynki ya hau.Meenal daddynki na sonki da yawa baya son kwatakwata yaganki cikin damuwa ko matsala,duk wannan yana daga cikin abinda yasa jinin shi ya hawa".
Shiru mommyn meenal tayi tana kallan Meenal kamar mai nazartarta,sannan taci gaba da cewa
"Meenal ko kinsan babu abinda ke saurin kisa kamar irin damuwar da daddynki yake ciki yanzu?,ina tsoran karmu rasa shi ,ya zamu idan ya mut...".








Kukan da Meenal ta fasa ne yasa mommyn meenal yin shiru.Hajiya Mariya ganin yadda meenal ta rud'e jin daddynta zai mutu,rungume Meenal tayi tana lallashinta ta ce"Ki yi shiru,insha Allah daddynki zai samu sauk'i,amma sauk'in nada gareki ne Meenal,duk da nima ban amince ba amma sai naga da murasa daddynki gara inyi hak'uri..".








Meenal katse momynta tayi da cewa
"Mommy ki min bayani mekesa sweet daddy adamuwa?".
Hajiya Mariya kallan Meenal tayi yadda duk ta rud'e ta k'osa taji aninda zatace.Hajiya Mariya ta ce"Meenal alhaji ne wai dole sai kinyi aure ,tom kinsan daddynki nason abinda kikeso,shine yak'i yadda dan yasan baki son aure,tom shine alhaji yake fushi dashi,tom kinsan hukuncin Wanda iyayanshi ke fushi da shi, idan ya mutu wuta zashi,shi yasa daddynki duk ya tada hankalin shi har jininshi ya hau,kuma kinajin likita yace ayi k'ok'ari abarbari yana shiga damuwa.Meenal dan Allah kije ki samu daddynki kice mai kin yadda zaki auri wanda alhaji ke so dan hankalinshi ya kwanta".






Meenal da gudu tana mai k'ara tsananta kukanta ta ruga bedroom d'in daddynta,tana zuwa ta fara buga daddynta tana janye mai hannun shi dake rik'e da kanshi, ta ce
"Daddy ka tashi karka mutu na yadda alhaji yayi min auran ..............✍️








Meenalyn daddy group, Comment d'inku yayi k'aranci.Amma......🀐🀐🀐🀐🀐🀐🀐.








πŸ“š MEENALYN DADDY πŸ“š
πŸ””πŸ“š
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONπŸ“š*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.WπŸ“šπŸ–ŒοΈ*


Na
Fadila Sani Bakori.








Page 19 & 20.






Meenal da gudu tana mai k'ara tsananta kukanta ta ruga bedroom d'in daddynta ,tana zuwa ta fara bubbuga daddynta tana janye mai hannu shi dake rik'e da kanshi ta ce,"Daddy dan Allah katashi karka mutu ,na yadda alhaji ya yi min auran..."Meenal ta idasa maganar tana kuka.
Daddyn meenal jin abinda Meenal ta ce,lallab'awa yayi ya tashi yana kamo hannun Meenal d'in yana bubbuga baayanta,alamun lallashi tayi shiru daga kukan da take,sannan cikin dauriya dan sosai kanshi kemai ciwo,ya ce,"Yi shiru Meenalyna,ya isa haka kibar kukan".Meenal cikin kuka ta ce,"Tom daddy dan Allah karka mutu,Allah inka mutu nima mutuwa zanyi".




Alhaji Abba lallan shi meenal yayi ya ce,"Ki yi shiru tom ai bazan mutu ba sai kwanana sun k'are".
Hajiya Mariya da shigowarta kenan,zuwa tayi ta janye meenal ta ce,"Meenalyn daddy mai nake gani haka,tom ai sai kik'aramai wani ciwan".Meenal jin haka da sauri ta goge hawayanta,tana cewa"Sweet daddy sannu".Alhaji Abba kai ya jinjina ma Meenal ,dan bayason magana,kanshi saramai yake sosai.








Hajiya Mariya lallab'a Meenal ta yi ta janyeta suka fita,dan alhaji Abba ya samu ko zaiyi bacci,dan doctor ya had'a mai da maganin bacci.






Allah yasa suna fita ko bacci ya d'auke alhaji Abba.
Hajiya Mariya shiryawa tayi ta ta tafi gidan kakan Meenal.
Bayan hajiya Mariya sun gaisa da alhaji ne ta ce"Alhaji tun safe da daddyn meenal yazo gaidaka da kyar ya koma gida yanzu haka bashi da lafiya,likita yazo ya duba shi yace jinin shi ne ya hau,alhaji dan Allah ka yi hak'uri ki rik'a amsa gaisuwar daddyn meenal,Wallahi cikin damuwa yake sosai,shine ma abinda yayi sanadin ciwan shi".Shiru alhaji yayi,sannan zuwa can ya ce,"Mariya nazaci ba Sani ba na isa da abinda Sani ya haifa,ashe bahaka bane,ni Sani zai kunyata saboda karya b'ata ma 'yar shi rai,a abinda Nina san alheri ne da Amina,soboda Wallahi yadda kuka lallata Amina ba kowana yaro zai iya zama da ita ba,amma Yaran nan ina tabbacin zaiyi hak'uri da duk shurman Amina,amma Sani agaban kakan yaran nan ya nuna shi ba zaiba wannan yaran Amina ba, harda wata k'aryar banza da wofi,wai yayi ma Amina alk'awarin ba zai mata auran dole ba".Shiru alhaji yayi kamar mai tunani sannan ya ci gaba da cewa,"Wallahi Mariya indai ni ban isa da Sani ba,tom banga amfanin gaiduwar da yakemin ba,shi yasa nace bana so,sannan shi yaron fa ba a kyauyan zai ajeta ba,shi kan shi kuna gani ba'anan yake har kokinshi ba.Mariya matuk'ar Sani ba zai aminta da maganata ba ke kanki ina dab da daina amsa gaisuwarki "Hajiya Mariya numfasawa ta yi ta ce,"Alhaji yanzu haka nazo nai in sanar da kai Meenal ta amince da auran".Hajiya Mariya ta fad'i maganar kamar zatasa kuka,dan tabbas tafi daddyn Meenal tsanar auran nan dan dai bata da yadda za tai ne ,sannan bata san daddyn meenal ya sab'a da Mahaifinsa.
Alhaji jin abinda mommyn meenal ta ce wani k'ayataccan murmushi yayi ya ce,"Nagode Mariya da wannan kunyar da kika fitar dani,duk hankalina ya tashi ina tunanin yadda zanyi da alk'awarin da na d'aukar ma yaran nan,nagode yadda kika fiddani kunyar nan kema Allah ya fidda ke kunyar duniya da lahira"Mommyn meenal cikin sanyi ta ce,"Ameen alhaji"Yanzu kije gida ,anjima zansa Issuhu ya kawoni inga jikin nashi,gobe kuma insha Allah zani garin su yaran nan in mai albishir shima".Hajiya Mariya dai jikinta duk a mace yake ,haka ta tashi tayi ma alhaji Sallama ta tafi".








Alhaji ko kamar yadda yace issu na zuwa yasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login