Showing 6001 words to 9000 words out of 47397 words

Chapter 3 - MEENALYN DADDY Complete Book By Fadila Sani Bakori.txt

06 Jan 2025

2922

tabar sa Meenal aiki suka dawo kamar yadda suke da Meenal da daddynta,suka dawo kamar da.
Yau ta kama Weekend Alhaji Abba zaune suke shida iyalinshi suna fira Kira ya shigo wayar shi,Alhaji Abba shiru yayi yana sauraran Kiran da aka ce mahaifin shi na mai,cikin fargamar zarkin Kiran nashi da ya yi ya ce"Okey,gani nan zuwa yanzu".
Dama Alhaji Abba da shirinsa na fita,hakan yasa ya tashi ya nufi gidan Mahaifinsa da baida nisa da gidan shi.






Alhaji Abba zaune gaban Mahaifin shi,bayan sun gaisa ne,Alhaji Abba ya kalli Mahaifin shi ya ce"Alhaji gani".Shiru Alhaji yayi,wato kakan Meenal,sannan ya ce" Sani akan maganar da mukayi da kaine,yau kwana goma sha hud'u kenan"Numfasawa dattijon yayi sannan yaci gaba da cewa"Nagaji da zuwa nai man auran Meenal da akeyi wajena,nayi maka magana akan Yaron gidan Alhaji Musa,amma shiru Sani ba kaimin maganar ba har yau ,tom yau ya sake dawomin ".Alhaji wato kakan Meenal ya idasa maganar cikin damuwa.
Numfasawa Alhaji Abba yayi,sannaya ce"Alhaji yaron ne ban yadda da tarbiyar shi ba shi yasa kajini shiru ".
Alhaji kallan Alhaji Abba yayi kawai ya girgiza kai sannan ya ce"Sani fad'amin kai ne baka son aurar da Amina koko Aminar ce bata son yin auran inji,ina fa sane, rashin kula masu nai man auranta da bakayi ne yasa aka fara zuwa wajena naiman auran Amina".Alhaji Abba shiru yayi dan bai son abinda zai ce ba,shiko kakan Meenal jin haka sai cewa yayi,"Sani yau zan fad'a maka abinda baka sani ba,kuma itama Amina ina tunanin kai tayi gado inma ciwone ko kuma ra'ayi,wato Sani sai da nasa akai ta maka addu'a ana baka kana sha sannan nasamu hankalinka ya juyo akan maganar aure,sanin kankane abokanka babu Wanda baiyi aure ba sannan kayi,nasha surutun muta ne akanka,tom kadubafa kai namiji ne akaimaka shurutu ina ga Amina Amina fa mace, Allah ya yi Amina da farinjini amma kai da ita kunk'i,tom koma dai menene insha Allah abinda nayi maka shi zan mata,dan haka ka shirya kai da iyalanka zuwa gobe zamu je Katsina wajan Malam Abdullahi Wanda mukai karatu tare shine dama alokacin ya yi ta tofamaka addu'a aruwa ina kawoma kana nasha tom amma kai alokacin faka fashinci komai ba,kuma cikin yaddar Ubangiji Allah yasa hankalinka ya dawo akan maganar auran,tom inajin itama Amina hakan za ai mata tun wuri,kuma mu tafi gaba d'aya tare mu gaida shi zaiji dad'i kaga nima nayi tsohon zuminci,dan rabona da shi tun lokacin naje mai da albishir d'in auranka,Sai kuma gobe insha Allah zamu tafi dan haka ka tashi kaje kasanar da su"
Alhaji Abba da gaba d'aya zifa yakeyi kota ina dan shi kanshi bai shirya zuwa Katsina ba yanzu,hakan saya cikin sanyi da naiman alfarma ya ce"Alhaji Katsina fa yanzu bata shiguwa,dan Allah idan ma hakane tom ka bada sak'omana akai mai,sannan inada meeting gobe,dan Allah Alhaji kabar magan...".Hannu Alhaji ya d'agama Alhaji Abba ya ce"Wallahi koda na samu Wanda yasan gidan Malam Abdullahi tom bazan ai ka mai ba,ai da kunya shekaru kusan talatin ace in akamai da sak'o,ko bama haka ba zuwa da kai yafi sak'o.Sannan Katsina da kake maganar babu lafiya yanzu ,ai ba cikin Katsina bane kyauyan Katsina ne,dan in ba yanzu ba garin ko network basu da shi"






Alhaji Abba cikin damuwa ya ce "Alhaji ai kyauyukan ne abun gudu,saboda anan ake ta'addancin ai,alhaji dan Allah ka yi hak'uri da tafiyar nan sai n...""Sani babu abinda zai hana tafiyar nan gobe insha Allah,tashi ka tafi".Alhaji Abba da yarasa abin cewa tashi yayi ya yi ma Mahaifinna shi sallama ya tafi"






Koda Alhaji Abba ya koma gida ,Allah yasa bai iske kowa afalo ba hakan yasa yayi part d'in shi,yana shiga ya Kira hajiya Mariya awaya yace tasamai part d'in shi"






Hajiya Mariya bayan ta zauna ne ta kalli Alhaji Abba ganin yayi shiru da'ido kawai yake binta ta ce"Daddyn Meenal lafiya kuwa?"
Numfasawa Alhaji Abba yayi ya ce"Mommyn Meenal Wallahi abinne yasha min kai ban san yadda zanyi da Meenal ba ta yadda da wannan tafiyar.Alhaji wai dole sai munje Katsina gobe kuma harda Meenal,kuma kyauye ".Shiru hajiya Mariya tayi sannan ta ce"Lafiya meza ayi a Katsinar?"."Wai Meenal za'aima addu'a kinsan tsofaffin nan da k'irk'irar abu,idan ba hakaba yarinya lafiyarta lau babu abinda ke damunta amma wai sai anyi tattaki anyo mata addu'a sai kace mai wata lallurar" Ita kanta hajiya Mariya shiru tayi dan ta jinjina tafiyar ,dan Meenal takan fad'i da bakinta haushin d'an kyauyan mutum takeji shi yasa tama gode da basu da 'yan'uwa akyauye.Hajiya Mariya kallan Alhaji Abba tayi da yayi tagwumi sai kace wadda aka aikoma da wani bala'in ta ce"Tom Daddyn Meenal ni kaina abin nama rasa abinda zance dan Wallahi bansan wayan da za'ai ma Meenal ba ta yadda aje kyauye da ita,dan har fariya take basu da "Yan'uwa akyauye,duk da tace koda suna dasu Wallahi bazataje ba,kuma bazatayi zuminci da suba,ba adad'e ba ina nan ina kallan wani film da arewa tasa ,ashe itama tana kallo tashi tayi ta kashe tibin ,wai da me zan k'aru zan zauna intasa tibi gaba ina kallan abin ta kaici.Gaskiya ganinake in dai dole sai antafi da ita, tom karka fad'amata inda za'a ,dan indai ta sani bazata ba"
Shiru Alhaji Abba yayi na d'an wani lokaci sannan ya ce"Kina nufin inyi ma Meenal k'arya?".Ikon Allah sai kace Uwarka.
Alhaji Abba yacigaba da cewa"Bazai yuwuba in b'oyemata gara in fad'amata gaskiya in samu in lallasheta,yanzu ki sameta ki fara mata maganar tafiyar kiji me zatacemiki,amma karfa ki mata maganar dalilin tafiyar"Dariya hajiya Mariya tayi ta ce"Nida nasan halin 'yan kayana akan me zan fad'amata,so kake in ruguza tafiyar kenan".hajiya Mariya na fad'in haka ta tashi ta ce"Bari inje inyima ta maganar tun yanzu"








Meenal kwance kan caution tana game awayarta,hajiya Mariya tazo ta sameta.Hajiya Mariya kallanta tayi ta ce"Sarkin buga game,daddynki ya ce ki tashi ki shirya gobe zamu Katsina"Meenal aje wayar tayi tana kallan Mommynta ta ce"Mommy katsina kuma ,wannan wata irin tafiya ce babu shiri,kuma daddy yana da dangine a Katsina?".Hajiya Mariya zama tayi ta ce"A'a abokin Alhaji ne zamu mu gaid..."Hajiya Mariya mata gama maganarta ba Meenal ta amshe maganar da cewa"Mommy nikam gasjiya bazani ba,sai kun dawo,haka kawai Katsinar da bazaman lafiya ake ba".Hajiya Mariya rufe bakin Meenal tayi ta ce"Kul!Karki k'ara cewa bazaki ba,wannan tafiyar dolece ,dan haka karma in k'arajin maganar bazaki ba.Maganar Katsina kuma ba lafiya ai ba cikin gari zamu ba,kyauyan Katsina zamu".Meenal tashi tayi ta zauna tana ajewayarta ta ce"Mommy dan Allah inma daddy ne ya aikoki ki cemai bazani ba,kema dai kinsan bazanje ba,ni me zai wani kai ni kyauye,koma lafiya bare kuma kyauyan Katsina,gaskiya mommy bazani ba"Meenal na kaiwa haka ta tashi ta nufi part d'in daddynta tana turo baki,tana zuwa ko sallama babu ta ce"Daddy kaji kuma abinda Mommy ta k'ara tsiro da shi kyauyan Katsina zamu tafi gobe wai?"Daddyn Meenal hannun Meenal ya kamo ya ce"Zokiji Meenalyn daddy,ba Mommynki bace ta ce nina ce"Meenal kamar za tai kuka ta ce"Amma dai daddy ai kaima kasan ni bazanje ba,kuma wai akanmema sai dani dole za'a?"."Haba Meenalyn daddy tunda nina ce dan Allah ki shiya mu tafi,idan mun'isa da wuri tom ba zamu kwana ba,muna zuwa zamu dawo"Meenal juya baya tayi tana turo baki,babu dai alamar ta amince.Alhaji Abba ko cigaba yayi da lallashin Meenal daga k'arshe yayi mata alk'awarin daga sun dawo zai kaita Mina wajan yarinyar k'anwar Hajiya Mariya da Allah ya had'a jinin Meenal da ita.Meenal jin haka yasa ta amince da sharad'in bazasu kwana ba.
Dole alhaji Abba ya bitada "Eh".Saboda ta yadda amma ya san dole sai sun kwana bazai yuwuba suje su dawo ranar kodan tsoran hanya".




Alhaji Abba sosai yaji dad'in amincewar Meenal,dan bai tab'a tunanin zata amince ba.






Da daddare Alhaji Abba na kallo Meenal kuma na chart da yarinyar k'anwar mamarta ta Mina wato Hafsat tana sanar da ita tafiyar da zasuyi gobe.Hafsat jin Meenal zata kyauye yasa taita mata dariya daga k'arshe ta ce"Kar dai kije wani d'an kyauyan ya mak'alemiki ,kuma wallahi bashi zamuyi"bak'in cikin maganar yasa Meenal ta aje wayar batare da ta rufe ko datarta ba.Alhaji Abba da hajiya Mariya da hankakinsu ya koma kan kallo sai ji sukai Meenal ta d'ad'e da kuka.Alhaji Abba da Hajiya Mariya kusan atare suka iso wajan Meenal ,bakamar alhaji Abba ba ,cikin damuwa ya ke cewa"Meenalyn daddy lafiya,yi shiru ki fad'amin karkanki yayi ciwo?".
Meenal cikin kuka ta ce"Ba Hafsat bace wai kar in samomusu d'an kyauye" .Alhaji Abba lallashin Meenal ya fara yana cewa"Kiyi shiru dan Allah karma kanki yayi ciwo akan shirman maganar nan"Haka alhaji Abba ya dage sai lallashi yake dakyar ya samu Meenal tayi shiru.






Washe gari da wuri suka gama shirinsu suka kama hanyar gidan Alhaji,Meenal dai yau bata magana da kowa,dan daddynta ma ganin Meenal kad'an take jira tasa mai kuka yasa shima yaja bakin shi yayi shiru.Koda suka je gidan Alhaji,wato kakan Meenal sun samu ya shirya su yakejira.
Hajiya Mariya da alhaji Abba haka suka gaisa da kakan meenal cikin girmama,inda Meenal ko kallan shi tak'iyi.
Alhaji kallan Meenal yayi ya ce"Amina har yanzu kinanan da halinki na miskilanci ko?".Meenal turo baki tayi ta ce"Karabu dani dan bagaidaka zanyi ba,kawani jawoma mutane zuwa kyauye muna zamanzamanmu lafiya"."Uwaki nace kice bazakiba mana dan'ubanki tafiyar duk danwa za'ayita badan keb....".Daddyn Meenal jin Mahaifinshi zai janyomai rigimar meenal yayi saurin katse shi da cewa"Alhaji rabu da Meenal kazo mutafi kar lokaci ya k'ure"
Alhaji Abba shiga yayi inda Meenal da Mommynta suka zauna a baya.Alhaji Abba yaja motar suka tafi..................✍️










Shere & Comment please🙏🏻






📚 MEENALYN DADDY📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌️*




Na
Fadila Sani Bakori.






Page 7&8.






Kasan cewar tsakanin Kaduna da funtua tafiyar two hours ce,hakan yasa cikin lokaci suka iso funtua,suna shiga funtua Alhaji Abba ya kalli mahaifinshi wato alhaji ya ce"Alhaji kace kyauyan Funtua ne,tom gamu cikin Funtua ta ina zamubi?"Alhaji shiru yayi sannan ya ce " Ikon Allah shekaru aruru kaga hanyar ta b'acemin sai dai muyi tambaya asamu ahanya,ka fita kasamu wani ka tambaye shi layin kad'anya"
Daddyn Meenal fita yayi daga cikin motar ya tambayi wasu nan dake zaune bakin titi.Nan fa suka nuna mai hanya suka ce kafin kakai d'andume anan zaka dauke hanyar ,sai karik'ayi kana tambaya"Godiya daddyn meenal yayi ya koma cikin motar,sai da ya koma baya sosai sannan yabi kwatancan da sukai mai.Alhaji Abba yana tafiya yana tambaya ahaka har suka kama hanyar kyauyan layin kad'anya.Nanfa suna tafiya mota na sama tana k'asa kasan cewar hanya babu kyau,ahaka suka shiga cikin garin layin kad'anya ,suna shiga daddyn Meenal ya kalli Mahaifinsa ya ce"Alhaji gamu a cikin garin,zaka'iya gane gidan?"."Ina Sani bazan ganeba,amma ka sauka katambayi gidan Malam Haruna mai allo".Daddyn meenal fita yayi ya tambayi wasu matasa da ke zaune.Aiko yana tambaya suka bashi amsa da basu San shi ba, juyawa daddyn meenal yayi ya koma cikin motar,gaba suka k'ara nan ma dai amsar iri d'aya basusan gidan ba,ak'alla sun tambayi mutane da dama amma amsar kenan basu san gidan ba.Alhaji Abba kallan Mahaifin shi yayi ya ce"Alhaji ko dai kamanta sunan shine,kaga kowa muka tambaya sai suce basu San shiba,in da ko sunan shi kenan inma ya mutune zasu ce ya rasu,shi yasa nace ko dai ka manta sunan ne?"." Mudai matsa gaba,amma taya zan manta sunan Haruna ,haka ake mai lak'abi da mai allo,mu matsa gaba mu tambaya".Daddyn Meenal shiga yayi suka matsa ,wani d'an dattijo suka gani suka tsaya ,Alhaji da kan shi ya bud'e ya fita,bayan Alhaji ya mik'amai hannu sun gaisane ya ce"Malam dan Allah gidan malam Haruna mai allo nake tambaya?".Shiru tsohonnan yayi yana tunanin inama yasan sunan nan,can bayan dogon nazarin da yayi ya ce"Wayyo haba nifa nasan nasan sunan nan da dad'ewa,amma sai na shafa'a,ai malam idan ka fad'i sunan sai ka b'ata sai dai irin mu da muka kwana biyu,amma kafi shekara talatin rabanka da kyauyan nan?".
Meenal da ke jin su daga cikin mota tsaki tayi ta ce"Kaji daddy wallahi d'an kyauyan mutum nada wuyar sha'ani,daga tambaya ya dage sai zuba ma tutane surutu yake idan yasani ba sai ya fad'amana ba muwuce idanma bai sani ba ne shima musani amma ya wani turke shi da fira".Daddyn meenal murnushi yayi ya komo hannun Meenal ya ce"Meenalyn daddy kenan ai yanzu zai fad'imai mu tafi".
Daga can kuma,shohon nan ya ce"Ai malam Haruna mai allo yanzu ai shine sarkin nomar garin nan,tun da aka bashi sarkin noma sunan shi ya b'ata da Haruna mai allo ya koma Sarki,yanzu ai indai ba Sarki kace ba mutane da dama bazasu gane ba,dan ko mu da muka kwana biyu wani ya manta sunan .kaga wata kuka can ko?,tom daga nan duk yaran da ka samu kace mai gidan sarki za'akaika".




Godiya sosai alhaji yayi mai ya ciro canjin ajjihun shi ya bashi,sannan ya koma motar suka tafi.






Suna zuwa dai_dai kukar suka tambayi matasan gun gidan Sarki daga nan aka nuna musu gidan suka k'arasa.Yaran da ya nuna musu gidan ne ya shiga yayi musu sallama da Sarki .
Sarki fitowa yayi yana musu sannu da zuwa, ya yi musu iso izuwa "yar ma dai_dai ciyar fadar shi.Bayan sun gaisane,Alhaji ya kalli Sarki ya ce"Malam Haruna bakaganeni ba ko?"."Wallahi Alhaji kabani sani?".Dariya kakan Meenal yayi ya ce"Tom Malam Haruna Abdullahi ne na Kaduna".Ai Sarki naji hanka ya zabura yazo ya rik'e kakan Meenal ya ce"Malam Abdullahi kaine ,Masha Allah barka da zuwa ,sannu_sannun ku"
Nanfa akafara sabuwar gaisuwa.Bayan an k'ara gaggaisawa ne ,Sarki ya ce"Gaskiya naji dad'in zumincin nan,dama bakamantani ba Malan Abdullahi ,kaddai kacemin wannan Sani ne ?"."Aiko shine banmantakaba duk da kai kamanta ni"."Wallahi banmanta da kaiba lokacin da kazomin da maganar auran sani tom nima alokacin na samu Sarkin noma na kyauyan nan har dama k'ananun kyauyukan da ke kusa damu,tom ince yau zanzo ince gobe da haka da haka dai na shafa'a,gashi kasan bantab'a zuwa ba bazan gane kwatancan da kaban ba,gashi lokacin ba lokacin waya ba kamar yanzu".Nan dai fira ta b'arke tsakanin su.Sarki wayar shi ya ciro ya mik'ama Alhaji wayar ya ce" Lalibomin number D'an juma ya kawo muku abin sanyi sana'ar shi kenan".
Dariya kakan Meenal yayi ya ce"Yo idon namu ai duk d'ayane nima baganin nake ba sosai".Kakan meenal mik'ama Alhaji Abba yayi wayar ya ce"Lalibomai number".Amsa alhaji Abba ya yi ya ce"Me ye sunan?"."D'an juma zaka gani".Cewar sarki"






Aiko Alhaji Abba na dubawa ya ga number,Kira d'aya d'an juma ya d'aga,yana d'agawa ,alhaji Abba ya mik'ama sarki wayar ya ce"Gashi an d'aga".






Sarki amsa yayi ya ce"Assalamu aikum,d'an juma kananan ne koko ka shiga Funtuar ne?".Banji mai akace ba sai ji nayi ya ce"Tom dan Allah ka aikoshi yanzu ya kawo nayi bak'ine".yana kaiwa haka ya kashe wayar yana cewa"Dama nayi tunani bayanan, ka ganshi nan kullum yana Funtua kome yake zuwa Funtua yi kullum oho mai".Murmushi kakan meenal yayi ya ce"Wai ina Yahaya ne?"."Malam ,da yake haka yake kiran shi,ya ce"Ai yaran nan da na kira d'an wajan shi ne,kasan shima Allah bai bashi haihu da wuri ba,sai da yayi wani auran ma,tom shine kad'ai yaron shi Namiji,sauran duk mata ne,nima dai shikenan jikan namiji".Sunanan suna hira wani matashin yaro ya shigo ya kawo musu laimummuka,bayan yaron ya aje zai fita ne, kakan Meenal ya ce" Shine d'an juman "."A'a shine dai Yaron da d'an juma yake barma tsaran shagon shi".Yaron zai tafi ne sarki ya kirashi ya ce"Isihu maza kaje wajan Maryama kace nace nayi bak'i daga Kaduna ai musu girki".








Sarki mik'amusu ledar da yaron ya kawo yayi ya ce"Malam Abdullahi ga laimu fa kusha dan Allah kafin ai muku girki,babu dai sanyi kasan Nepar tamu sai ahankali,dan ma d'an juma da daddare yana tada inji dan kayan suyi sanyi".Alhai mik'ama Mommyn Meenal yayi ya ce"Mariya kusha ko".Mommyn Meenal bud'ewa tayi taba kowa,sannan ta mik'ama Meenal da ke can gefe rakub'e tace Meenalyn daddy zoki amsa".Meenal cikin ya tsune fuska ta ce"Bazan shaba mommy".Sarki da sai yanzu ya lura da Meenal ,kallan Alhaji yayi ya ce"Ko ba afad'i ba nasan itace tawajan Sani,dan ga kama nan, a Kadunar take aure?".Alhaji wato kaka Meenal kai ya jinjina ya ce"Kaganta nan ko saurayi bata da shi bata da ranar aure ga mahaifinta nan ya d'aure mata gindi".Sarki kai ya jinjina ya ce"Wallahi Malam Abdullahi abinda ke damuna kenan ga d'an juma nan shima zaune babu ranar auran dan ko a wajan ku sai an mai surutu".
Sarki maida hankalin shi yayi ga Meenal yana al'ajabi dan shi gani yake ko abirni sai amma wannan surutun rashin aure,suko anan ai ba'ama magana.
Sarki kallan Meenal yayi ya ce"Zoki sha kinji irin nakune na binni".Alhai wato kakan Meenal kallan sarki yayi ya ce"karka biyema wannan miskilar banzar ,rabu da ita karta sha d'in kanta tayimawa".Kakan Meenal tashi yayi ya ce"Malam Haruna zamuyi sallah ga la'asarnan ana kira bamuyi azahar ba"."Tom bari in kira d'an juma ya turomin yaron da ya turo d'azu ya kawo lemu,sai ya rakasu can suyi sallar suhuta,mu kuma sai muyi zaman mu nan".




Sarki number d'an juma yasa aka k'ara kiramai ,ya ce ya turomai da isihu ya raka bak'in da yayi gidan su".
Aiko suna gama wayar ba dad'ewa yaron ya iso.Sarki sashi yayi ya ce" Karaka su gidan su d'an juma shashin Maryama"






Meenal dai na zunb'ure_zunb'ure ta tashi,sukabi bayan yaron.suna tafiya Mommyn Meenal na ma meenal na siha,tana cewa"Meenalyn daddy dan Allah kisaki ranki insha Allah gobe zamu bargarin nan,kinsan mutanan kyauye da tsegumu,karmu tafi anayi dake,dan Allah kiyi hak'uri karkiyi abinda zaki jawoma kanki magana".
Meenal dai bata tankama Mommynta ba,ahaka suka isa gidan.
Babban gidane Wanda akekira gidan gandu,dan gidan cike yake da yara da manya.Su meenal na shiga kallo ya dawo kan su ,nan fa mutane suka rik'a mamakin daga ina suke.wata daga cikin matan gidan ta ce"Bukuga shashin Maryama sukai ba,kunsan d'an juma ne zai kawo su".
Mommyn Meenal dai haka suka ri'kabin shashi_shashi suna tafiya,dan wadda aka Kira da Maryama wato surikar sarki ita ce Uwar gida agidan,hakan yasa sashinta ne acan k'arshe.Hajiya Mariya koda taga shashin da yaron ya shiga dasu sosai taji dad'i dan ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login