Showing 12001 words to 15000 words out of 47397 words

Chapter 5 - MEENALYN DADDY Complete Book By Fadila Sani Bakori.txt

06 Jan 2025

2923

.Meenal na zuwa taja ta tsaya kusa da mashin d'in.D'an juma ta gefan ido ya k'ara satar kallan Meenal d'in dan ya lura bata San kallo shi kuma baya son raini hakan yasa ya kalleta asace.
D'an juma ya hau mashin d'in ,yaji bata hauba taja ta tsaya,cikin ko in kula dan shima miskilin ne ya ce"Ki hau muje ".Meenal sai da ta kallai jin yadda yayi mata magana,agadarance,ita dariyama yaso ya bata ,azuciyarta ta ce"Dan kyauye ko da me zai gadara har da zai min magana ahaka,ta ce koda yake ance d'an kyauyan mutum akwai iyayi" .








Meenal zata iya rantsewa bata tab'a hawa mashin ba,inda ita dai duk inda zata daddynta ke kaita amota ko a motar Mommynta.Meenal rasa yadda zata hau mashin d'in tayi sannan ta dafa d'an juma tana mai jan tsaki ta hau.
Kasan cewar hanyar bawani kyau gareta ba,hakan yasa Meenal kejin kamar zata fad'i.Wani rami suka fad'a Meenal ta rungumo bayan d'an juma cikin gigita tana mai cewa"Da Allah malam kayi ahankali karka kadani ".D'an juma sai da yaja burki ,ya tsaya ,sakkowa yayi daga kan mashin d'in ya ce" Sau biyu kenan kina min tsaki kar ki yi na uku". Meenal da ke cikin haushi ,gashi ya k'ara mata wani haushin maganar shi ,cikin b'acin rai ta ce"Idan na k'ara mai zaka iyayi!?".Ki k'ara kiga abinda zan iyayi".Meenal da takaici da haushi suka cikata wai ita d'an kyauyan nan yake cema haka.Cikin d'aga murya Meenal ta ce"An maka tsakin,an kuma an maka tsakin me zakayi!".D'an juma d'aga mashin d'in yayi Meenal ta tafi zata fad'i.k'ara ta saki na rik'o d'an juma cikin tsoran fad'uwar da zatai, ta kwanta kan bayan shi tana rik'e shi katakam tana zaro ido irin na mutum in yaji tsoro sosai.D'an juma abin dariya ya bashi yadda ta furgita,kuma dama shi ba kadata zai ba,hasalima abinda taimai duka baiji haushi ba,kawai dai dan ya samu hanyar da zasuyi magana ne ko mara dad'i ce yasa ya biye mata.D'an juma rik'e mashin d'in yayi da k'arfi dan yadda ta rik'e shi din yasa ya kusa sakin mashin d'in ta fad'i.
Meenal jin ta zauna bata fad'iba ,ajiyar zuciya ta sauke.Ran meenal sosai ya b'ace ga bak'inci ya isheta ga yunwa ta isheta ka wai sai ta fashe da kuka.
Sosai abin yaba d'an juma mamaki,yadda take kuka sosai,ci gaba da tafiya yayi bai tsayaba inda sun kusa gidan.Dai-dai k'ofar gidan D'an juma ya tsaya ,yana kallanta alamun ta sauka.Meenal sakko wa ta yi tana mai ci gaba da kukanta.D'an juma rashin sanin abinda zai ce mata yasa suka shiga gidan haka tana kukan,dan bai san me zai ce mata ba,duk da sai yaji zuciyarci cikin k'uncin kukan da takeyi.Ahaka Meenal da d'an juma suka shiga gidan.
Sarki da alhaji da mamaki suke kallan Meenal ganin yadda take kuka.Sarki cikin damuwa ya kalli d'an juma ya ce" Abdurrahma,da yake so dadama yafi Kiran shi da sunan shi,ya ce"Abdurrahman lafiya ,me akai mata?".D'an juma kallan Sarki yayi ya ce"Nima bansani ba,muna tafiya naji tana kuka".Sarki hannun Meenal ya kamo yana cewa"Yi hak'uri Amina me akai miki yi shiru dan Allah kar kanki yayi ciwo".Babu maganar da sarki baima Meenal ba amma ko d'ago kai ta kalle shi tak'i.Alhaji ne da abin ya fara ba haushi ya ce"Amina wai bazaki fad'i abinda akai miki bane zakibzo ki tasamu kina mana kuka?".Alhaji ma wato kaka Meenal babu irin maganar da baima Meenal ba ,amma tak'i sauraran shi,ganin haka yasa ya ce"Malam Haruna rabu da ja'idar yarinyar nan da iyayanta suka sangartata d'akko mata addu'ar tasha taba mutane waje".Sarki d'akko addu'ar da yayi ma Meenal yayi ya bata ya ce"Gashi ko kisha da bisimillah".Meenal bata d'agoba daga kukan da take bare kuma sarki yasa ran zata kula shi.Alhaji wato kakan Meenal sosai ran shi ya b'ace hakan yasa ya kalli D'an juma ya ce"Abdurrahaman idan mu tarainamu tana ganin bama iya mata dan Allah in dai bata shaba ka d'ura mata shi nina saka ja'idar yarinya mara kunya".Alhaji na fad'in haka ya kamo hannun sarki ya ce" Dan Allah mu fita in barjin kukan ja'idar yarinyar nan" .Sarki bin shi yayi aka bar Meenal da D'an juma.
D'an juma ruwan addu'ar ya d'auka ya matsa kusa da Meenal ya ce"Ba'ama tsofaffi gaddana ,amsa ki sha".Meenal amsa tayi babu zato babu tsammani d'an juma sai dai yaji ta watsa mai ruwan addu'ar a fuska,dai_dai nan Alhaji da Sarki suka dawo d'akin.Aiko Alhaji wato kakan Meenal hannu yasa ya yarfama Meenal mari zai k'ara na biyu Sarki ya rik'e hannun shi da sauri,yana cewa"Haba Alhaji me yasa zaka mareta ai abin dama sai da lallab'awa ,idan bazata shaba shikenan sai arabu da ita".Alhaji cikin jin haushi ya ce"Wallahi Malam Haruna Amina bazata bar garin nan ba sai ta sha maganin nan adadin yadda ya kamata,idan kuma ba hakaba sai dai mu shekara anan".Alhaji wayar shi ya ciro ya mik'ama d'an juma ya ce"Lalibomin numbar Ubanta in sanar da shi............โœ๏ธ










Meenalyn daddy group Comment d'in ku yayi k'aranci .




idan kin karanta ki daure ki Comment sister.






Share & Comment please๐Ÿ™๐Ÿป.






๐Ÿ“š MEENALYN DADDY ๐Ÿ“š


๐Ÿ””๐Ÿ“š
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*โšœ๏ธยฉJ.A.W๐Ÿ“š๐Ÿ–Œ๏ธ*




Na


Fadila Sani Bakori.






Page 11 & 12










Sarki kallan d'an juma yayi ya c"Abdurraman jeka mai data gida,inda bazata gane ba".






D'an juma fita yayi yana mai jin duk ba dad'i abinda Alhaji yayi ma Meenal,ko ba komai ita d'in bak'uwar su ce.
Meenal ko na fita hanya ta mik'e taci gaba da tafiya tana kuka babu ruwanta da kowa,dan tunda take ba'atab'a b'ata mata rai irin na yau ba.Hanyar da tabi ko kwatakwata ba hanyar komawa inda tafito bace,hasalima hanyar fita cikin garin tabi"






D'an juma da sauri ya bita yana mai cewa" Hanyar da kikabi ba hanyar komawa gida ba ce,kizo ki hau mashin d'in in mai da ki".
Meenal babu alamunma taji abinda d'an juma yace tafiyarta taci gaba dayi babu alamun zata tsaya.D'an juma ma binta yarika yi ya nama mai cewa"Dan Allah kizo in kaiki da akwai inda zani".
Meenal still tafi yarta taci gaba dayi tana mai goge hawayan da ke zubar mata,dan acewarta Alhaji ya tozartata,ga Meenal ba dai iya fushi ba.
D'an juma ganin babu alamun zata tsaya hakan yasa sha gabanta.Meenal cikin masifa dan gwanace a iya fad'a ta ce"Ni ba sa'arka ba ce Malam da zaka taremin gaba ina tafiya,dole ne sai na bika?,Koko dole ne sai na koma gidanku,nace bazani ba ,shin ana dole ne!!?".Meenal ta idasa maganar cikin tsantsar masifa har tana Kumfar baki.
D'an juma cikin kwanciyar hankali ya ce"A'a ba dole bane,amma kuma ni dole ne in cika umarnin sarki".Meenal mamaki,Al'ajabi suka cikata wai ita d'an kyauyan nan kema magana haka,ko da yake babu komai alhaji yaja mata,in bahakaba inama zai ganta bare har yasamu damar fad'a mata magana.
Meenal goge hawayanta ta yi ta ce"D'an asabe ka ke ko d'an me ye,dan Allah jani ka kaini".Murmushi d'an juma yayi yana girgiza kai ya ce" Bazan jaki ba,da k'afarki zaki hau mu tafi".
Meenal ja tai ta tsaya batare da tak'ara tanka ma d'an juma ba.D'an juma kuma ganin haka zuwa yayi ya d'akko mashin d'in shi ya matso da shi kusa da ita ya ce"Beauty dan Allah hau muje mana".Sunan da d'an juma ya ga ya cancanci da Meenal kenan acewar shi,dan ita kyakkyawa ce ya ce".
Meenal kuma jin sunan da d'an juma ya kirata yasa ta kallai batace komai ba ta hau mashin d'in tana mai k'ara goge hawayanta."






Suna gaf da shiga Gida,Meenal taga mai nono da fura,gashi dama yunwa takeji,hakan yasa ta ce"Tsaya" . D'an juma tsayawa yayi yana mai sauraran abinda zata ce,sai ji yayi ta ce"Me nono".Mai nono da saurinta ta k'arasa,Meenal sai da tagama kallanta sama da k'asa wai ko zataga inda take da alamun k'azanta.D'an juma jin shiru yasa ya waiga yana kallan Meenal jin ta tsaida mai nono batace komai ba,ya ce"Kina so ne".
Meeenal banza tayi da shi ta ce"Me nono ki ban ta yadda zan iya shanyewa".Me nonon kallan Meenal tayi ta ce"Tom aini bansan cikinka ba,na nawa dai zan baka".
Meenal tsaki tayi ta ce"Ban ta d'ari biyu"."Tom za'adama maka ne koko abaka kadama"."Bani in dama".cewar Meenal.




Me nonon zubama Meenal tayi aleda ta bata.Meenal ko bata fito da kud'i ba hakan yasa ta ce"Ki biyo bayana ki amshi kud'in".da me nono da d'an juma mamaki ne ya kama su, taya zata iya bin mashin ita dake ak'asa.






D'an juma ciro kud'in yayi ya bata,yaja mashin d'in shi ya tafi,yana mai cewa"Na ranta miki idan mukaje sai ki ban kud'ina".Meenal banza tayi da shi bata tanka mai ba.D'an juma ko sai da ya kai Meenal har cikin d'akin Mahaifiyar shi sannan ya juya zai tafi.Meenal ta ce"Dakata!".
D'an juma tsayawa yayi,inda Mommyn Meenal da Mahaifiyar d'an juma suka tsaya suna sauraran ikon Allah.
Meenal kallan Mahaifiyar d'an juma ta yi ta ce"Ki ja mai kunne ya fita daga har kata saboda ni ba sa'ar sa'insar shi ba ce,idan kuma ba haka ba...." .Tsawar da Mommyn Meenal ce tayi ma Meenal yasa tayi shiru,hajiya Mariya cikin b'acin rai ta ce"Meenal sa'anki ne,koko ita d'in sa'arki ce da kike kawo mata k'ara haka?".
Meenal turo baki tayo.Mahaifiyar d'an juma kuma ta ce" Yi hak'uri kinji Amina,kuma zan ja mai kunne ba zai k'ara ba kinji" .
Abin mamaki kawai sai meenal ta fashe da kuka kamar wadda aka buga tana nuna ma Mommynta fuskarta ta ce" Kalli fa kigani yadda Alhaji ya maran saboda shi,du ba fa ku gani" .Meenal ta fad'i maganar tana k'ara fashewa da kuka" .Daga d'an juma har Mahaifiyar shi da mamaki suke kallanta.
Mahaifiyar d'an juma ce taita lallan shi Meenal tana bata hak'uri ahaka dai aka samu tayi shiru.Mommyn Meenal kuma ta kaici yasa bata tanka ba"




Mahaifiyar d'an juma furar hannun Meenal ta amsa ta damamata.
D'an juma kuma bayan ya fitane ya ba yaro peak milk ta ruwa ya ce a kaima Maman shi ace tadama furar da ita. Mahaifiyar d'an juma bayan ta gama dama furar ne ta kaima Meenal tare da bata hak'uri.Meenal ko kasan cewar yunwa takeji yasa bata wani tsaya sanabeba ta d'aga furarta ta shanye tass.Tana gama shan furar takwanta takama bacci.






B'angaran d'an juma ko yauma kamar kullum yana zaune acikin saif plaza dake garin funtua.D'an juma kallan Kamal yayi ya ce" Kamal kana yawan fad'amin wata magana,da sai yau nake son insan gaskiyarta,ka ce duk yarinyar da nace ina so da wuya tak'ini,shin a cikin kyauyan mu kake nufi koko har acikin gari,ma'ana cikin birni?".Murmushi Kamal yayi ya ce"Abdurrahaman a ko ina nake nufi ba wai a kyauyanku kad'ai nake nufi ba".Shiru d'an juma yayi ya ce"Kana ganin yarinyar da ta fito cikin garin kaduna tayi karatu agarin kaduna,ta tashi cikin gata ,Kamal dan Allah karka yau dareni kana ganin yarinyar nan ko zata iya soni?".
Murmushi Kamal yayi ya kamo hannun d'an juma,dan ya kula abokin nashi ya rufta da yawa ya ce"Abdurrahman,koda cikin garin Abuja ta tashi,tayi karatu acan ,sai dai son zuciya da girman kai irin na mata amma tsab zata soka".
Shiru d'an juma yayi sannan zuwa can ya ce"Kamal kallo d'aya nayi mata ,yadda naji akanta na tabbatar shi akekira so,tabbas yadda naji da kuma yadda nakeji yanzu tambari ne na soyayya,dan Allah ka ce inyi hak'uri Wallahi tafi k'arfina".
Shiru Kamal yayi ,na d'an wani lokaci sannan ya ce"Wacece ita Abdurrahman?"."Nima kaina bansan wacece ita ba,na gansu ne da Sarki,bisaga'alama dai kakanta abokin sarki ne"."Kai tom ai in hakane Abdurrahman kanada dahir,nasan sarki na sonka da yawa zai iya maka k'ok'ari ganin ka sameta".Cewar Kamal"






Shiru d'an juma yayi,sai kuma ya ce,"Ga sunanta mai dad'i ,Amina suna kiranta da Meenal,tana da fad'a da masifa,amma kasan me Kamal?".Kamal kai ya girgiza.D'an juma kuma ya ce"Tsiwarta kyau take mata,ta kasa b'acemin a ido lokacin da takemin fad'a zan kadata"
Kamal kai ya girgiza,dan yaga abin banawasa ba ne ,k'arshema sai cewa yayi"Amma idan haka ne Abdurrahman yana da kyau ka samu soyayyarta kafin ta tafi".Kai d'an juma ya girgiza ya ce"Kamal bazata soni b ,kawai dai nina san tamin shigar sauri,tabbas na kamu da sonta lokaci guda,kuma so mai wahalar fita".






Kamal da sosai ya gaskata maganar d'an juma dan ko dan yanayin yadda yake magana kamar wani maraya yasan tabbas so yayi mai shigar sauri.Kamal kallan d'an juma yayi ya ce"Kuna magana da ita ne?".Kai d'an juma ya girgiya ya ce magana da ita bazata yuwuba,yarinyar miskilar gaske ce,kuma kamar tana da jida kai bisa ga alamunta".
"Tom duk da haka dai ni shawarar da zan baka ,karik'a musu alheri ita da 'yan'uwanta kafin su tafi,sannan bahaushe yace da rashin tayi akan bar arha,lokuta da dama muna ma mututa ne kallan halinda ba d'abiyar su bace sai ka zauna dasu zaka San haka,dan haka ina mai baka shawara ka gwada sa'arka k'ila kadace" .
D'an juma kallan Kamal yayi ya ce"Kana ganin zan iya da cewa?"."Sosai ma kuwa".Cewar Kamal.Ranar dai haka d'an juma ya wuni yana mai jin wata irin fargaba akanta,dan ko ajikin shi bayajin za ta so shi ,hasalima zuciyar shi gargad'in shi take karya sake ya furta kalmar so ga Meenal.Wata zuciyar kuma ta ce "Koma biki gargad'an ba nima bazan iya furtawa".
Haka dai d'an juma ya yi ta sak'arshi yana warware abin shi,kamar yadda ya saba tafiya gida gaf magriba yauma haka ya tafi,sai da ya biya ya sai mata fura,inda yaga d'azu ta siya ,sannan ya hau mashin d'in shi ya tafi".




WAYE D'AN JUMA?:
Mahaifin d'an juma mahaifiyar d'an juma ce uwar gidan shi,sai dai Allah yasa bata samu haihuwa da wuri ba,hakan yasa Sarki wato kakan d'an juma kasan cewar yana son ganin jikan shi yasa Mahaifin d'an juma k'ara aure,inda Mahaifin d'an juma ya k'ara auran badan yana soba,sai dai bayan auran su da Lami da wata goma ta haifi d'iya mace wato Rabi suna ce mata Yaya Rabi.Lami wato kishiyar Mahaifiyar d'an juma sai da ta haifi mata uku babu namiji aciki,hakan yasa Sarki yasa Mahaifin d'an juma k'ara aure ko za ahaifar musu Namiji.Cikin ikon Allah Maryama wato Mahaifiyar d'an juma da amaryar da Mahaifin d'an juma ya aura kusan atare su kai laulayin ciki,dan sati d'aya ne tsakanin su a haihuwa,inda ranar wata juma mahaifiyar d'an juma ta haifi d'a namiji,amaryar su kuma ta haifi mace.lokacin mahaifin d'an juma na da Yara biyar duk mata,hakan yasa Sarki da Mahaifin d'an juma suka rasa inda zasu sa Maryama wato Mahaifiyar d'an juma,tsabar murnar haihuwar Namiji da akai musu.Ranar sunan d'an juma yaci sunan Abdurrahman.Tom kunsan mutanan kyauye da rad'ama mutum sunan ranar da aka haife shi,dalilin ranar juma'a aka haifi d'an juma shine fa suka b'atar da da sunan shi suka rik'a Kiran shi da d'an juma.
Tun ranar sunan d'an juma aka fara cin karo da ban-banci,dan ko sarki ya kashe kud'in da bai tab'a kashe rabin su ba sauran jikokin da aka haifar mai .Haka Sarki da Mahaifin d'an juma suka d'auki son duniya suka d'orama d'an juma.D'an juma na yaro sosai akazo layin kad'anya akai gina musu primary School,tun ana ginin makarantar d'an juma ya kwallafa rai dan gani yake wani abunne,hakan yasa ana gama ginin Sarki da kan shi ya d'auki d'an juma ya kai shi.Allah kuma yasa d'an juma nada k'okari ,ahaka dai ya kammala aji shida,kasan cewar babu secondary agarin hakan yasa Sarki ya samar mai gurbin karatu a d'an dume dan babu nisa sosai tsakanin su,ahaka-ahaka dai d'an juma ya kammala secondary d'in shi,daga nan ne fa Sarki yace ba zai shigema kafuran nan da yawa ba dan haka ya isa hakanan karatun,dole d'an juma ya hak'ura badan yaso ba.Tom daga nan fa sai kuma ya fara zaman gida babu sana'a,gashi shi saboda Makaranta da yayi bai iya aikin gona ba.Sosai rashin sana'ar d'an juma ta fara damun Maryama,ana hakane Allah yayi ma Mahaifinta rasuwa,tom da aka rabamusu gado ne Maryama ta ba d'an juma ya bud'e provision, kusan babu abinda bai sai dawa .A funtua yake zuwa Sarin kaya,hakan yasa ya fara abokai,ahaka-ahaka dai suka saba da ogan nashi,ahankali-ahankali ya fara jawoshi jikin shi yana tsare mai kayan shi,shi kuma d'an juma shima can sai yayi yaro shima yana bashi tsaron nashi,tom inda d'an juna ke tsarewa plaza ce babba ba laifi.Abinda yasa yake b'oyema sarki gani yake kamar zai hana shi,shi yasa sarki bai San abinda d'an juma ke zuwa funtua yi ba kullum.
Layin kad'an ya Yaro d'an shekara goma sha bakwai,Shatakwa,ashirin suke aure, hakan yasa d'an juma ma tun yana matakin secondary suke bashi aure amma yak'i,atakaice dai har izuwa girman shi na cikakkan namiji .Wanna yasa akema d'an juma surutu sosai,dan wasu cewama suke k'ila aljana ce ta aurai.Shiko d'an juma tunda ya taso Allah yasa baida ra'ayin irin auran garin su,macan yarinya shima angon yaro.
Tunda d'an juma ya fara mallakar hankalin shi yafi buk'atar budurwa wadda tasan abinda takeyi ba kwaila ba irin na garin su.Wannan kenan"






D'an juma haka ya hawo mashin d'in shi ya dawo gida .
Meenal ko tun da ta farka daga bacin da tayi take neman wayar da zata Kira Daddaynta ta kai k'arar alhaji wato kakanta ,akan maganar shan addu'ar da ya ce sai ta sha, idan bata sha ba baza ta tafi ba.Wayar mommyonta ko tun jiya da tayi wurgi da ita ta d'auke, wayar mahaifiyar d'an juma kuma babu caji,hakan yasa ta rasa wayar da zatai kiran.
Meenal sosai take jinta atakure zaman kyauyan,dan ko abinci rana da Mahaifiyar d'an juma ta kawo musu k'in ci tayi.
Meenal kallan Mommynta ta yi, ta ce"Yanzu mommy da ban gama Exams ba haka mutunin nan zauzo nan kawai ya kama zaunar da muta ne,Allah ni dai kije ki mai magana,idan ba haka ba zaki nai man kirasa,dan ni daga gobe bazan k'ara kwana kyauyan nan ba,tun da nazo wayana baya aiki,inda ni M.T.N garan ,dan Alllahi nidai ki san yadda zaki Mommy Allah duka mutanan garin haushin su nakeji".Meenal dai har ta gama maganarta Mommynta bata tankamata ba,hakan yasa tayi shiru.
Meenal har dare tak'i cin komai kuma dama da daddaran tuwan gari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login