Showing 42001 words to 45000 words out of 47397 words
Chapter 15 - MEENALYN DADDY Complete Book By Fadila Sani Bakori.txt
Mommy ba ce ke had'a babyn nan da wannan!" Daddyn Meenal da bai fahimci abin da Meenal ke nufi ba d'aurewa ya yi ya ce"Mariya ba fa na son haka! Sanin kanki ne yarinyar nan bata gama warwarewa ba,dan haka kar ki naimi abin da zai b'ata mata rai bana so!"Mommyn Meenal kallan Daddyn Meenal ta yi da mamaki ta ce"To,Daddyn Meenal za'a canza ma tuwo suna ne? Wai wannan babyn nace tana kama da Abdurrahaman shine fa take kuka"To inda ta ce bata so ba shikenan ba,kuma ni banga ta inda yarinyar nan take kama da yaran nan ba"Yana gama fad'in haka ya juya wajan Meenal ya ce"Meenalyna ki rabu da mommyn ki ni banga ta inda kyakkyawar babyn ki ke kama da yaran nan ba"Meenal murmushi ta yi tana goge hawayanta.Daddyn Meenal ganin Meenal na son babyn zama ya yi ya ce"To nima a ban babyn in gani?"Mommyn Meenal mik'a mai babyn ta yi.Shi kuma kallan ta ya ke yana murmushi wai yarinyar Meena d'in shi ce a hannun shi ikon Allah.Daddyn Meenal kallan Meenal ya yi ya ce"Meenalyna wana suna ki ke so asama babyn ? In mata hud'uba?"Meenal cikin murmushi tana rufe ido alamun wai kunya ta ce"Daddy, Fatima"
Mommyn Meenal katse su ta yi da cewa"Daddyn Meenal gaskiya kar ka biye ma Meenal, a bari a fara tambayar Abdurrahaman aji ta bakin shi tukun"Meenal fara bubbuga k'afarta ta yi tana kuka tana cewa"Daddy ba zata tab'a daina had'a babyn nan da shi ba!"Daddyn Meenal cikin tsantsar b'acin rai ya ce"Mommyn Meenal wannan Karan duk abin da kike nema zaki sa mai,ki bar had'a babyn nan da yaran nan na fad'i miki idan dai ta nuna bata so, ba shikenan ba" Mommyn Meenal dai bata tanka ba har ya gama b'ab'atun shi ya fita.Bayan Daddyn Meenal ya fita ne Mommyn Meenal ma ta d'auki wayar ta ta fita ta kira D'anjuma,kira d'aya ko ya d'aga, bayan sun gaisa ne Mommyn Meenal ta ce"Abdurrahaman Meenal ta haihu yau d'in nan ta haifi 'ya mace"D'anjuma cikin danne farincikin shi ya ce"Masha Allah,Allah ya rayata mommy,ya ita maijegon fa?"Alhamdullah ,ita ma tana nan cikin k'oshin lafiya" To,Mommy insha Allah zuwa gobe ina nan shigowa"To,Allah ya kawo ka lafiya "
Meenal ko Mommyn ta na fita taje tana kallan babyn inda Mommyn ta ta kwantar da ita ,tana a haka ne Mommyn ta shigo da tea a hanun ta ta mik'ama Meenal d'in .Bayan Meenal ta gama shan tea d'in ne Mommyn ta nuna mata yadda zata shayar da babyn.Meenal amsar yarinyar ta yi ta shayar da ita.Mommyn Meenal kallan Meenal ta yi ta ce"Meenal gobe Abdurrahaman zai zo ganin 'yarsa "Meenal turo baki ta yi sannan ta ce"Mommy baki ji abin da Daddy ya ce ba?"Ban ji ba dan k'aniyar ki !"Mommyn Meenal na fad'in haka ta fita ta bar Meenal nan tana turo baki ita kad'ai.
Ko da dare ya yi Meenal tare da mommyn ta suka kwana.Yarinyar ko mai hak'uri daga ta farka aka bata nono shikenan, Meenal zata mik'a ma mommyn ta ita kuma ta juya ta kwanta ta ci gaba da barcin ta.
B'angaran D'anjuma ko da daddare bayan ya je wajan mahaifiyar shi ne ya sanar da ita haihuwar Meenal.Sosai ta yi mamaki dan bata san da cikin ba,ta ce"To Allah ya raya ,ranar suna ai sai k'anwar ka ta bika taga 'yar ta su"D'anjuma sama-sama su kai fira da mahaifiyar shi ya yi mata sallama ya tafi,tare da sanar da ita zuwa Kaduna da zai yi gobe.Fatan alkairi ta yi mai,amma ta yi alk'awarin ba zata k'ara sa baki akan ya yi aure ba ta barshi ya yi yadda ya ga dama.
Washegari D'anjuma da wuri ya shirya ya nufi Kaduna. Misalin k'arfe goma na safe ya isa.(10:00AM) Lokacin Mommyn Meenal na shirya baby ta gama mata wanka kenan wayar D'anjuma ta shigo wayar ta.Bayan ta d'aga sun gaisa ne ya sanar da ita yana k'ofar gida."Ka shigo ciki mana Abdurrahaman"
Mommyn Meenal sosai taji dad'in zuwan D'anjuma da wuri,dan har ya gama abin da ya ke Daddyn Meenal ba zai dawo ba.Mommyn Meenal kallan Meenal ta yi ta ce"Meenal ki je falo ga Abdurrahaman nan zai shigo yanzu"Meenal baki ta turo kamar zatai kuka ta ce"Mommy to ni mai zan mai?"Meenal na yi tunanin idan kika haihu zaki rik'a ganin mutuncina kina girmama maganata ,ashe tunanina ba haka yake ba,Meenal baki son Yarinyar nan da ke hanun ki ta rik'a biyayya da maganar ki nan gaba ko? Shikenan kar ki je"Meenal jikinta sanyi ya yi jin abin da Mommyn ta ta ce,dan tabbas ba zata so watarana ba ta yi ma Fatimar ta magana ta k'i ji ba,hakan yasa ba dan ta so ba ta sab'a yarinyar tana turo baki ta fit..........
Afuwa ,insha Allah daga yau za ku rik'a jina kullum .
Fadila Sani Bakori ce
📚 MEENALYN DADDY📚
Page 41
D'anjuma na zau ne ,Meenal ta yi sallama ciki-ciki ta shigo falon.D'anjuma tashi ya yi ya tari Meenal kafin ta zauna ya amshi babyn hannunta,sannan ya zau na,kallan Meenal ya yi ya ce"Barka da fitowa gimbiya ya kike? Ya kuma k'arfin jikin ki? Ya babyn mu?"Meenal ciki-ciki tana yatsine fuska ta amsa ma D'anjuma da "Alhamdulillah" Ma sha Allah" D'anjuma ya dad'e ya na kallan babyn sannan ya ce"An mata hud'uba ne?"Meenal kamar ba zata amsa ba ,sannan zuwa can ta ce"Uhm"Wana suna aka sa mata?"Fatima"Ma sha Allah,Allah ya raya Fatima ya sa ta biyo halin mai sunan ,Nana Fad'imatu, ada kafin in haihu na so yarinyata ta fari in sa mata sunan mahaifiyata ,to, amma babu damuw in da kin riga kin mata hud'uba da Fatima ,Allah ya kai mu nan gaba"Uhm"Meenal ta ce tana tashi ta ce"bani babyn zan shiga ciki"D'anjuma ko kallan Meenal bai yi ba ya ce" Zaki iya shiga, idan na gama ganin babyna sai in ba mommy ita"Meenal so take ta tafi kuma ta kasa tafiya ta bar babyn, haka nan ba dan tana zargin zai ma babyn wani abu ba tana jin ba ta iya tafiya ta bar ta,hakan ya sa ta koma ta zau na"Shiru-shiru babu Wanda ya yi magana,sai zuwa can D'anjuma ya ce"Amina ki koma d'akin ki mana ko dan babyn nan a yi suna acan" "Meenal wani kallo taima D'anjuma,sannan ta ce"Idan ma kana sa ran watarana zan koma gidanka to tun wuri ka bari,dan ba zan k'ara zama gidan ka ba har abada,bani babyna zan shiga ciki"D'anjuma tashi ya yi daga zau nan da ya ke ya ce"Zaki dauwama da aure kanki kenan dan Wallahi ba zan sakeki ba"Ba damuwa ai akwai kotu ko? Idan aka makaka kotu ai dole ka sakan!" Wani k'ayataccan murmushi D'anjuma ya yi ya ce"Amina kenan,Wallahi ko kotun bangon duniya zaki kai ni bazan sakeki ba,wannan alk'awari na yi ma kai na,yarinya kuma daga kin gama shayar da ita zan amshi a bata"D'anjuma na kaiwa haka ya aje babyn kan caution ya juya ya tafi.Sai da ya je waje sannan ya kira Mommyn Meenal a waya ya sanar da ita ya tafi.Mommyn Meenal cikin sanyi ta ce"Haba,Abdurrahaman ko ruwa fa baka sha ba,ina kitchen ina k'ok'arin samar ma abin da zaka ci"Babu damuwa Mommy ina sauri ne"Shiru Mommyn Meenal ta yi ,sannan taimai fatan sauka lafiya ta kashe wayar.
Meenal da kuka ta shiga bedroom d'in mommyn ta,tana zuwa ta d'auki wayarta za tai kira Mommyn Meenal ta rik'e wayar ta ce"Ya a kai ne?, Wani abun Abdurrahaman d'in ya yi miki?"Dan gara ta kashe wutar tun kafin ta kira Daddyn ta.Meenal goge hawayanta ta yi ta ce"Mommy na gaji da zama da auran nan a kai na ,in da dai Alhaji ya rasu shi da ya had'a abun nan to ina so cikin satin nan Daddy ya sa shi ya sakan!"Shiru Mommyn Meenal ta yi sannan ta zau na kusa da Meenal d'in ,ta ce"Meenal ki yi hak'uri ko dan babyn nan ki koma d'akin ki,ki rik'e 'yar ki da hannun ki, idan ba haka ba ina ji miki tsoran nan gaba ya ce zai am shi 'yar shi"Hmmm,Mommy kenan,ai ko yanzu ma ya yi min kurarin shi na banza wai daga an gama shayar da ita zai amshe ta to Wallahi bari Daddy ya dawo"Mommyn Meenal dai ba ta ce komai ba,jan bakinta ta yi tai shiru.
Da yamma bayan Daddyn Meenal ya dawo suna zau ne ya Meenal ta kallai ta ce"Daddy ,dan Allah ka sa wannan ya sakan bana son shi Daddy,kuma wai har da wani cewa zai amshi babyn nan "Daddyn Meenal da kula ya kalli Meenal ya ce"Ki kwantar da hankalinki ,kamar ma ki ta da hankali ,bai isa ba ya amshi 'yar nan,maganar saki kuma ki bari sai kin yi arba'in dan naga yaran nada kafiya sai an danganta abin da kotu"
Ana saura kwana uku suna Daddyn Meenal ya sa mu Mommyn Meenal bedroom d'in ta ,ya ce"Mommyn Meenal karfa ki ce zaki tara min mutane da sunan taron suna,ba na buk'ata" To,in sha Allah"Abin da mommyn Meenal ko bata sani ba Meenal ce ta rok'i Daddyn ta haka.
A na gobe suna D'anjuma ya je Kaduna,bai sanar da Mommyn Meenal zuwan ba, sai da ya isa sannan ya kira ta awaya yana k'ofar gida."To,Abdurrahaman ka shigo ciki"Mommyn Meenal, Meenal ta kallah ta ce"Meenal Abdurrahaman ne ya zo,dan Allah ki je ku gaisa nasan dai wani abun ne ke tafe da shi"Mommy ki je kawai Allah ni bana son ko ganin shi"Mommyn Meenal b'ata rai ta yi ta ce"Meenal babu yadda za ai in saki abu ki yi cikin dad'in rai ko?" Meenal tana turo baki ta tashi zata fita,Mommyn Meenal hannun Meenal d'in ta kamo ta ce"Ki d'auki babyn mana ki kai mai ita ya ganta"Meenal d'aukar babyn ta yi ta fita tana mai tunanin maganar da zata fad'ama D'anjuma ko zai yi zuciya ya saketa.
Meenal ko sallama ba ta yi ba ta shiga falon,tana zuwa ta ce"Ina ji ? Sauri na ke"D'anjuma shiru ya yi sannan ya ce" Bani Fatimar in ganta"Barci ta ke"Ba ni ita haka ai ba tashinta zan yi ba"Baka ita ne ban yi miyya ba,naga kana nuna kamar kana da iko da ita ne,to ina so ka cire cewa wai kai ne mahaifinta dan Wallahi ba zan tab'a bari ta kira ka da Baba ba,garama ka cireta a ranka kamanta kana da wata dangantaka da ita"D'anjuma kud'in aljihun shi ya ciro ya ba Meenal ya ce"Gashi ki ba Mommy zan sanar da ita ko kud'in me ye,Fatima kuma da kike magana ni yanzu bani da lokacin wannan maganar har sai ranar da na zo amsar 'yata "D'anjuma na fad'in haka ya aje ma Meenal kud'in ya juya ya tafi ya bar Meenal nan tsaye.
Bayan D'anjuma ya tafi ne ya kira Mommyn Meenal ya sanar da ita ga kud'i nan dubu saba'in a siyi ragon suna da su ba yawa .
Ranar suna haka aka yi suna babu taron mutane,dan Daddyn Meenal ko in ce Meenal ta hana.
B'angaran D'anjuma ko zuk'ema mahaifiyar shi ya yi da maganar zuwa sunan da ta ce k'annan sa za su yi.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya har Meenal ta yi arba'in.Ranar da Meenal ta cika kwana sittin da haihuwa,Daddyn ta na zau ne ta zo ta sa mai ta ce"Daddy dama a kan maganar da ka ce in bari sai na yi arba'in ne "Shiru Daddyn Meenal ya yi sannan ya ce"To,bari in Kira shi a waya yanzu"Daddyn Meenal wayar shi ya ciro ya kira D'anjuma,yana d'agawa sama-sama suka gaisa,sannan Daddyn Meenal ya ce" Ka zo zuwa gobe ina son ganinka" Yana fad'in haka ya kashe wayar.Meenal kallan Daddyn ta ta yi ta ce,"Daddy dama da ce mai ka yi gobe ya zo da takardar saki"Murmushi Daddyn Meenal ya yi ya ce"Meenal yaron na da taurin kai gara in mai haka"
Washegari D'anjuma da wuri ya isa Kaduna.Kasan cewar ta kama weekend ne Daddyn Meenal na gida,suna zau ne a falon dukkan su kiran D'anjuma ya shigo wayar Daddyn Meenal,D'anjuma sanar da shi ya yi yana k'ofar gida."Ka shigo ciki"Cewar Daddyn Meenal.Mommyn Meenal da bata san abin da ake ba saidai ganin D'anjuma ta yi ya shigo.......
Fadila Sani Bakori ce.
📚 MEENALYN DADDY📚
Page 42
D'anjuma cikin natsuwar shi ya shiga ya zau na,bayan ya zau na ne ya gaida Mommyn Meenal, da Daddyn ta cikin girmamawa.Mommyn Meenal ,Meenal ta zungura da k'afa alamun ta gaida D'anjuma,amma Meenal sai ta share tak'i gaida shi.Daddyn Meenal ko jin falon ya yi shiru,ya ce"Abdurrahaman,dama na kiraka ne akan Meenal,in da ta nuna ba zata koma gidanka ba,to ka yi hak'uri ka saketa"Daddyn Meenal na gama fad'in haka ya mik'ama D'ajuma takardar da biro.
D'anjuma shiru ya yi kamar ba zai yi magana ba,sai zuwa can ya ce"Daddy ka yi hak'uri abin da na fad'ima shi zan k'ara sanar da kai ina son Amina ba zan iya rabuwa da ita ba"Daddyn Meenal cikin b'acin rai ya ce"K'aryarka,Wallahi dole ka rabu da ita ,idan ka k'i rabuta mata cikin lallami zaka rubuta mata inda baka shirya ba.
D'anjuma dai kan shi a k'asa bai tanka ba.Daddyn Meenal ganin babu alamar ma zai tanka ya ce"Tashi ka bar min falona zamu had'u a kotu da kai cikin satin nan"D'anjuma tashi ya yi batare da ya tankaba ya fita daga falon.
Mommyn Meenal ma batare da ta kanka ba itama ta tashi ta bar Meenal da Daddyn ta,dan sosai ta ji zafin abin da Daddyn Meenal ya yi ma D'anjuma.
Meenal ko bayan Mommyn ta ta tashi kallan Daddynta ta yi ta ce"Daddy ni kam ina tsoran aje kotun yak'i sakina"Meenalyna kenan,ai bai isa ba,dolan shi ya sakeki,bari in Kira Barrister Hassana in sanar da ita abin da ke faruwa"Daddyn Meenal Barrister Hassana ya kira ,bayan su gaisa ne yasanar da ita maganar sakin Meenal da ya ke so mijinta ya yi shi kuma yana da taurin kai sosai.Barrister Hassana sanar da Daddyn Meenal ta yi ya zo court d'in su sai su yi maganar.
B'angaran Mommyn Meenal ko bayan ta je falon ta ,wayarta ta d'auka ta kira D'anjuma,bayan sun k'ara gaisawa ne ta ce"Abdurrahaman,ka yi hak'uri da abin da Meenal su ke maka ita da Mahaifinta,hak'ika ina son auran ka da Meenal dan na san kai ka d'ai zaka iya hak'uri da Meenal,to amma ita da mahaifinta ko kuma ince mahaifinta ya biye mata sunk'i,Abdurrahaman inda abin ya zo da haka bana son abin ya kai ku ga kotu, ka yi hak'uri ka saketa"Mommy ki yi hak'uri amma ba zan iya sakin Amina ba kamar yadda kika ji na ce,amma idan har ke ma kina buk'atar in saki Amina har ranki,to zan yi hak'uri zan yi abin da ki ke so"Numfasawa Mommyn Meenal ta yi, sannan ta ce"Abdurrahaman,har'abada bana fatan abin da zai sa ka saki Meenal,dama ina ganin ko danni ne,amma inda haka ne ko kotun suka kai ka ka bari ni kuma zan had'aka da Yayana shi ma Louya ne,na san zai tsaya maka"Godiya sosai D'anjuma ya yi ma Mommyn Meenal ya kashe wayar shi.
Daddyn Meenal zau ne agaban Alk'ali ya yankar ma D'anjuma sammaci tare da jagorancin Barrister Hassana.Daddyn Meenal ko gida bai koma ba bayan fitowar shi daga kotun,waya ya yi ma driver Alhaji inda ya san Funtua sosai kuma har gidan D'anjuma ya sani,takardar sammacin ya bashi tare da number D'anjuman.
Haka driver Alhaji ya kama hanyar Funtua,sai gaf magariba ya shiga garin Funtua.Ya na shiga ya Kira wayar D'anjuma,yana d'agawa ya sanar da shi Mahaifin Meenal ne ya aiko shi daga Kaduna.Kasan cewar har kofar gidan D'anjuma ya sani ,hakan ya sa ba tare da shan wahala ba ya isa har k'ofar gidan.Yana isa lokacin D'anjuma na Masallaci ya na sallah,hakan ya sa sai da ya foto sannan ya bi Kiran da a kai mai.Yana kira ko ya sanar da shi yana k'ofar gidan shi.D'anjuma zuwa ya yi ya samu bak'on.Bayan sun gaisa ne ya mik'amai takardar sammacin da aka aiko shi da ita.
D'anjuma amsa ya yi ,shi kuma ya juya ya kama hanyar komawa Kaduna.D'anjuma da mamaki ya amshi takardar sammacin,bayan ya shiga gida ne ya kira Mommyn Meenal ya sanar da ita abin da ke faruwa,shiru Mommyn Meenal ta yi sannan ta ce"Karka damu Abdurrahaman,na yi ma Yayana magana,na sanar da shi abin da ke faruwa,zuwa gobe ka yi k'ok'ari ka shigo da wuri,sannan dan Allah Abdurrahaman karka sanar da Iyayanka abin da ke faruwa"In sha Allah,na gode Mommy"
Washegari D'anjuma da wuri ya shiga garin Kaduna,kasan cewar Mommyn Meenal ta ba D'anjuma address d'in gidan Yayanta,hakan ya sa direct can ya yi.D'anjuma zau ne a falon Alhaji Usman,Wanda ya ke wa, ga Mommyn Meenal,uban su d'aya.
D'anjuma na nan zau ne a falon Alhaji Usman ya shigo,da kula ya kalli D'anjuma ya ce"Yi hak'uri ka zo ina da bak'i"Cikin garmama D'anjuma ya gaida Alhaji Usaman,bayan sun gaisa ne Alhaji Usman ya kalli D'anjuma ya ce"Ina takarfar sammacin?"D'anjuma mik'amai takardar ya yi.Bayan ya duba takardar ne ya kalli D'anjuma ya ce"Abdurrahaman kar ka ji komai in sha Allah babu mai rabaka da matarka,dan haka zuwa gobe zaka iya tafiyar ka ba sai ka je kotun ba,lauyan da aka d'aukar maka shi zai je"D'anjuma cikin jin dad'i ya yi ma Alhaji Usman godiya sosai,ya ce"Ai dare bai yi ba in haka ne ma yau zan tafi"Babu yadda Alhaji Usman bai yi da D'anjuma ba akan ya kwana amma ya k'i.
Bayan tafiyar D'anjuma ne Alhaji Usman ya kira Mommyn Meenal a waya,bayan sun gaisa ne ya ce"Yanzu muka rabu da yaron ya zo,har ma mun gama magana ya tafi"Mommyn Meenal ,shiru ta yi,sannan ta ce"To,Baban Baby,sai yanzu na yi wani tunani,idan Daddyn Meenal yaganka a kotu a matsayin lauyan Abdurrahaman zai yi tunanin da had'in bakina,ni kuma bana son ya yi tunanin da sa hannuna"Murmushi Alhaji Usman ya yi,ya ce"Mommyn Meenal kenan,ai dama ba ni zani ba da akwai wani friend d'ina da kwanaki irin haka ta faru da shi ni na tsaya mai,to nima yanzu shi zai tsaya a maganar "Gofiya sosai Mommyn Meenal ta yi ma Yayanta ,sanan su kai sallama.
Washegari,Daddyn Meenal da luayan shi k'arfe tara a Court d'in ta yi musu.Daddyn Meenal da lauyan shi da kuma lauyan D'anjuma zau ne a gaban alk'ali.Ba