Showing 27001 words to 30000 words out of 47397 words
Chapter 10 - MEENALYN DADDY Complete Book By Fadila Sani Bakori.txt
kamar yadda suka tsayar,yau ne kuma sarki yayima alhaji maganar suna nan zuwa,sosai alhaji yayi mamakin jin zasuzo amma sai bai ce komai ba yayi musu fatan zuwa lafiya .Alhaji daddyn meenal ya Kira awaya ce yasa mommyn meenal tayi girki da yawa masu auran Amina ne zasu zo.Daddyn meenal to ya ce sanan ya Kira hajiya mariya awaya ya sanar da ita.
Sarki su uku sukazo shida k'annan mahaifin d'anjuma.Alhajima kafin su iso ya kira aminin mahaifin meenal ,wato alhaji Kabiru dama alhaji ya sanar da shi maganar auran meenal.Bak'i ko tun kafin su iso alhaji yasa aka kawo musu abincin da akai musu .
Bayan sun gamacin abincin ne an gaggaisa Sarki ya ce tom dama dai akan maganar bikin nan ne naga lokaci ya k'arato nace bari inzo muyi magana,Abdurrahman ya gama kammala kayan lefe,gidama ya kama haya acikin Funtua kamar yadda yayi alk'awari kafin Allah yasa yayi nasa,tom amma dai dalilin zuwana shine tom kasan mu mutanan kyauye da al'adu kala-kala,wato yau kwana bakwai kenan da Abdurrahman yake sanar dani wai mahaifiyarshi tace bata yadda ya aje Amina Funtua ba sai yayi kamar yadda akeyi,wato mu acan yaro ko da ya gina gida tom ba zai aje matar can ba sai ya fara ajeta gidan iyayanshi sannan koda zai ajeta gidan shi,tom shine kar kukaga abu ba yadda mu kaiba da yake ni namamanta da wannan al'adar tamu shine nazo in sanar da ku,Amina zata fara zama agidan su Abdurrahman koda na sati biyu ne dole abisa al'adar wajanmu kafin ta tare gidanta da mijinta."
Murmushi alhaji yayi yace mata kenan masu rik'o da al'ada,ai inda wannan ne bakomai ,ni Wallahi al'adar sai ta burgenima ankoyama yaro abinda bai iyaba ai,kuma yaro ya saba da surikanshi sosai,gaskiya hakan yayi kuma babu komai,ai ni da kasanar da ni aida bakazo ba,yanzu dan wannan maganarce kawai ka kwaso jiki kazo?."
Dariya sarki yayi yace wallahi Abdurrahman ne ya matsamin wai sai dai inzo in sanar da kai."Abdurrahman kenan ya kwantar da hankalinshi babu komai zai auri Amina insha Allah,wannan ai ba komai bane,ni hakanma yayimin dai-dai ta saba da surikannata da sauran mutane ai kafin su tashi."Cewar alhaji.
Sarki sosai yaji dad'in hakan,godiya sosai yayima alhaji ya ce "Alhaji mungode da wannan k'yauna da kake nunamana,kuma insha Allah nayi maka alk'awari kamar yadda kayima Abdurrahman hallacin wannan auran baka duba matsayishi ba,tom insha Allah shi kuma zai saka maka na rik'e Amina tsakani da Allah."
Alhaji ma sosai yaji dad'in furucin sarki,ya ce "Nagode da wannan albishir d'in,yanzu idan kun koma ana gobe d'aurin aure ko jibi dan Allah ku sanar da Abdurrahman ina son ganin shi kafin bikin."
Haka Sarki suka koma gida,duk da alhaji yayi-yayi su kwana sunk'i.
Yau saura kwana bakwai d'aurin auran d'anjuma da meenal, yau ne kuma alhaji yayi Kiran hajiya Mariya da alhaji Abba.
Alhaji Abba kuwa zuwa yanzu ba k'aramin rama yayi ba,dan har meenal takan tasashi da tambaya tana cewa daddy yanzu kabar fira dani, kabar yawan magana,kabar yawan dariya.Alhaji Abba sai dai yayima meenal dariya yace aikine sukai mai yawa,meenal tun tana tanbayar mahaifinnata har ta bar tan bayarshi tayi shiru,idan kuma ta tambayi mommynta sai ta ce mata meenal duk halinda kikaga daddynki ciki akanki ne,ni dai abinda nikeso da ke duk radda mahaifinki ya naimi kemai wani abu tom komai wahalarshi ki mai meenal,dan mahaifinki bak'aramin so yake miki ba,baki da hanyar da zaki sakamai sai ta hanyar bin umar nin shi,da kuma aminta akan duk abinda kikaga shima ya aminta dashi meenal."
Meenal ko sai dai tayi murmushi ta ce "Mommy kenan,nima ina son sweet daddy kamar yadda yake sona."
Da daddare kamar yadda alhaji ya kira iyayan meenal haka suka shirya sukaje.Bayan sun gaisa ne,Alhaji ya kalli mahaifin meenal ya ce " Sani yau dai saura kwana bakwai d'aurin auran Amina, dama wata shawara ce na kawo nace mai zai hana aje Funtua asaima Amina kayan d'aki acan an huta wahalar d'aukarsu akai su can,amma ku ya kuka gani?"
Daddyn meenal kasa cewa komai yayi sai mahaifiyar meenal ce ta ce "Eh alhaji shawarar tayi,yanzu tom ya za ai?".
Alhaji murmushi yayi ya ce "Tom auran Amina dai inda nina k'ullashi tom ni zanma Amina kayan d'aki,dan haka gobe zanyi magana da Abdurrahman d'in inda shi yasan mutane sosai a Funtua ina ganin basai munjeba sai yayi mana hanyar inda zamu saya sai in baku kud'in ku tura musu ,ala bashi sai su jeramata kayanta.Sai dai wani hanzari ba gudu ba,kasan 'yan kyauye da al'adu kala-kala,tom wai su a al'adarsu sai amarya ta zauna gidan iyayan yaro na satittika koda zata zauna gidanta,tom ni hakan ma sai yayimin dad'i ta saba da su kafin,wai sai Amina ta fara zama gidan su Abdurrahman kafin ta zauna gidansu."
Daddyn meenal dai ya rasa bakin magana sai zufa kawai da yake aikin gogewa ta tsantsar tashin hankakin da ya k'ara shiga,ita kanta hajiya Mariya hankakinta ya tashi da jin wai Meenal zata zauna gidan su d'anjuma kafin su tare anasu gidan.
Hajiya Mariya cikin sanyi ta ce "Alhaji bank'i tatakaba,amma wallahi gara cikin rufin asiri meenal ta zauna gidanta in sansamu ne ita kad'ai, amma Allah meenal bazata zauna gidansu d'anjuma ba,idan kuma anyi mata ta k'arfin tsiya ta zauna tom abubuwanda da zataima masu gidan wallahi kai kanka ina tunanin sai kayi da kasanin had'a auran baki d'aya,amma idan gidanta ne komai zai dai-daita ahankali kuma kaga duk abinda zatai basujiba basu gani ba,kasan dai surutu irin na mutanan kankara,kuma idan can Funtua ne inda tana gani ba kyauye bane zatafi hak'uri."
Shiru Sarki yayi ya d'auki dogon lokaci yana tunanin maganar ,sannan ya ce "Aiko maganarki Mariya hakane,indai hakane tom tafiya gobe ta kamani dole inje in naimi alfarma awajan iyayan Abdurrahman."
Alhaji har ya gama maganarshi daddyn meenal bai tankaba,sai dai hajiya Mariya ke magana.Daga k'arshe su ka tashi suka tafi.Alhaji Abba har suka isa gida bai iya cewa komai ba,hajiya Mariya ma jan bakinta tayi ta yi shiru.
Washe gari kamar yadda Alhaji yace da wuri yayi shirinsa Isuhu ya jashi suka nufi garinsu d'anjuma.
Sarki da fara'arshi ya tari alhaji.Bayan an gaggaisa ne alhaji ya ce "Sarki wanna tafiyar ta mahaifan Abdurrahman ce,idan sansamune ina son magana da mahaifiyar Abdurrahman d'in".
Sarki wayar shi ya lalibo yaba isuhu ya kiramai d'anjuma,bayan d'anjuma ya d'aga ne sarki ya ce "Abdurrahman kaje gida yanzu nan ka kiramin mahaifiyarka."
D'anjuma ko dama yana nan bai riga ya shiga Funtua ba,dama kuma yana k'ofar gidan nasu,shiga yayi ya sanar da mahaifiyarshi kiran sarki.
Alhaji da sarki na nan zaune suna hirarsu d'anjuma suka shigo shida mahaifiyarshi,d'anjuma bayan sun gaisa da alhaji fita yayi.
Alhaiji ko bayan sun gaisa da mahaifiyar d'anjuma ne ya ce "Tom wannan tafiyar dai baki d'ayanta taku ce,nazo naiman alfarma ne,kinsan yaranmu na birni sai suyita abubuwan da su aganinsu wayewa ne ,wanda anan ko abin magana ne babba ,nasan dai kin zauna da yar gidan taki kinga yadda take,shine nake naiman alfarma kinsan yaran yanzu sai addu'a dan Allah abar d'anjuma ya yi zaman shi da matar shi a Funtua gudun abin magana ,kin san dai halin 'yar gidan taki."Mahaifiyar d'anjuma da bazata iya musama alhaji ba,cikin sakin fuska ta ce "Haba alhaji indan wannan ne ai da bakazo ba,shikenan babu komai wallahi,tayi zamanta d'akinta."
Alhaji sosai yaji dad'in yadda mahaifiyar d'anjuma ta nuna mai bakomai ,godiya yayi mata sosai,sannan tayi musu sallama ta tafi.
Bayan mahaifiyar d'anjuma ta tafine,alhaji ya kalli sarki ya ce "tom zamu tafi amma ana jibi biki zamu aiko asiyi kayan d'aki anan Funtua kaga shikenan anhuta wahalar d'akko su daga can."Eh kuma hakan yayi ."Cewar Sarki.
Nan dai su alhaji suka k'ara tattaunawa game da bikin,sannan sarki yayima alhaji sallama suka kama hanyar Kaduna suka tafi."
Haka kwana kai sukaci gaba da tafiya inda yake dai-dai da yau saura kwana uku d'aurin auran d'anjuma da meenal,Wanda har yau meenal batasan da maganar bikin ba,alhaji tun safe ya aiko da yana son ganin hajiya mariya,haka hajiya mariya ta shirya ta nufi gidan alhaji.Bayan sun gaisane,alhaji ya kalli hajiya mariya ya ce "Mariya na kirakine cikin 'yan'uwanki gobe zaki tura guda biyu Funtua su saima Amina kayan d'aki ala bashi sai su shirya komai,koya kiga gani?".
Hajiya Mariya cikin sanyi ta ce "Eh alhaji hakan yayi Allah ya kaimu goban."
"Ameen Mariya,Allah yayi miki albarka".
Hajiya Mariya da ameen ta amsa ta yima alhaji sallama ta tafi gida,tana zuwa ta kira yayarta da k'anwarta ta sanar da su maganar zuwa Funtua gobe.
Washe gari da wuri 'yan'uwan hajiya Mariya sukayi sammakon tafiya Funtua,inda alhaji ya d'auki kud'i masu yawa ya basu yace duk abinda ya dace su siya su jera mata,ya had'asu da numbar d'anjuma.
Hajiya Jamila yayar hajiya Mariya suna isa Funtua,inda ake saida furnitures suka nema,nan fa suka saima meenal kujesu masu kyau sosai,suka biya kud'in sannan sukaje b'angaran kayan d'aki nan ma dai haka suka sai duk wani abu da ake amfani da shi na kayan aiki,sannan sukaje b'angaran labulaye da zanin kado da katifa suka siya.Suna gama siyayyar suka Kira d'anjuma awaya,dama ya San da zuwan su shida abokinshi suka zo da mota tar d'aukar kayan,nan cikin k'ank'anin lokaci aka sa kayan cikin mota,cikin mutunci d'anjuma suka gaisa da iyayan meenal,sannan d'anjuma ya samar musu adaidaita suka hau suka nufi gidan da za akai meenal.
Hajiya Jamila kallan k'anwarta tayi ta ce "Aisha gaskiya na yaba da yaran nan da zai auri meenal,ni wallahi jin ancemin d'an kyauye ne nazaci d'an kyauyan ne na gaske,yanzu wannan idan ba anfad'amaba wa zai kallai ya ce d'an kyauye ne,gaskiya da yarinyar nan zatayi hak'uri da ta amshi auran nan hannu biyu yaron nan baida wani aibu wallahi dan meenal ma sai dai ta nuna mai haske,amma Allah yama fita kyau".
Aisha dai hmmm ta ce,ta ce "Aunty Jamlila nifa idan meenal ta nuna bazata zauna ba tom Allah laifin iyayanta ne,kina ganifa kamar tsoranta sukeji b'oyemata auran akeyi fa,har yanzu fa batasan da maganar auran ba,yo wani abunma da takeyi ai ni gani nake suke sata,inba daurema k'arya gindi ba,kina ganin wai ko taro ba za ai ba wai karta sani,nikam na zuba ido inga yadda abin zai kaya."
Dariya Jamila tayi ta ce "Ke dai bari Aisha tunda nake ban tab'a ganin tab'ara irin ta yarinyar nan ba,garama Allah da kakan yayi mata haka dan inajin inda ba hakaba da baza tai auran ba,dan gani tak'e tafi k'arfin kowa,kuma fa in ba hasken fatar ba ba wani kyau gareta ba,yarinya kamar wata sanda."Isowarsu gidan yasa sukayi shiru.
Gidane d'an ma dai-daici na zaman mutum d'aya , ciki da falo sai kitchen da toilet.
D'anjuma abokanshi uku ya Kira suka jajjera kujerun su kuma suka jera kayan kitchen d'in,su nayi Aisha na dariya tana cewa "Aunty Jamila niko zanso inzo inga yadda zaman meenal zai kaya acikin gidan nan,anya ko kina ganin zaman nan zaiyuwu?."Jamila dai itama dariyar tayi ta ce "Tom Aisha wannan abin sai dai kazuba ido kayi kallo ,amma abin kam sai dai shiru,amma wallahi gidan baida wata makusa sai dai su yaranmu na yanzu suna duba inda suka tasone ,bakamar kuma meenal ba maiji da isa da k'asaita."
Haka dai suka gama shirya kayan, sukace zasu tafi, d'anjuma babu yadda baiyi dasu su kwana ba amma sukak'i,da yake isuhu da alhaji yasa ya kawosu yana nan hakan yasa suka kama hanyar kaduna gab da magriba.
Su hajiya Jamila ba su suka isa Kaduna ba sai tara da rabi na dare(9:30PM).Suna isa sukaci abinci suka wanta kasan cewar sungaji.
Washe gari bayan sun gama karyawa ne,Hajiya Jamila yayar hajiya Mariya kallan hajiya Mariya tayi ta ce "Mariya banga meenal tana shirin komai ba na biki,kardai kicemin har yanzu kuna b'oye mata buku sanar da ita ba?"
Ajiyar zuciya Mommyn meenal ta sauke ta ce "Tom mahaifinta ya hana afad'amata ,tom nima da da farko dai na goyi bayan hakan,amma zuwa yanzy kam ya kamata ace ansanar da ita,amma yak'i ." "Aiko ya zama dole asanar da ita yau d'in nan,taya jibi za'a d'aurama yarinya aure ace har yau bata sani ba,ko dan d'an k'unshi da kitso ai ansanar da ita,koko haka za a d'auketa akaita gidan mijin babu kitso babu k'unshi?".
Shiru mommyn Meenal tayi sannan ta ce "Tom Aunty Jamila ko zaki sanar da ita ki bari sai kinsata tayi kitson da k'unshi sannan,dan wallahi meenal indai ta san da maganar auran nan tom bazata yadda tayi k'unshi da kitson ba."
Tsaki Jamila ta yi ta ce "Wallahi Mariya kunji haushi tarbiyar da ku kai ma meenal,gashi nan tsoranta kukeji baku isa da ita ba,har fargabar ku b'ata mata kukeyi,kiramin meenal d'in."
Hajiya Mariya Kiran meenal tayi awaya,tasanar da ita tazo falo yanzu ta sameta.
Meenal da ke zaune tana game awayarta tashi tayi taje.
Tana zuwa Jamila da yake babu wasa ta ce "Ungo taki".tayi mata da k'uwa,ta ce "Dan uwarki kinsan mun kwana anan shine bazakizo ki gaidamu ba ko?".
Meenal sosa kai tafara ta ce "Mommy Allah na manta anan kuka kwana,ina kwanan ku."lafiya klau,maza kije ki tsafe kanki kizo".
Meenal kallan Jamila tayi ta ce "Mommy aini kaina atsafe yake."Yauwa tom ina kikeyin kitso,kije aimiki kitso da k'unshi mai kyau mai tsada ni zan biya kud'in gobe zaki rakani Kano."
Meenal wani tsallan dad'i tayi ta ce"Wayyo mommy wannan surprise haka,aikam yanzu ma kuwa".Meenal dama tayi wankanta hakan yasa ciki ta shiga ta d'akko mayafinta.
Hajiya Jamila dubu goma taba meenal tace gashi nan ayi mai kyau,amma karki kitson attachment idan kuma ba hakaba kinsan halina".Meenal baki ta turo ta ce "Mommy indai hakane na fasayin kitson,banfa da wani gashi taya kitson zaiyi kyau ,nikam nafasa zan tafi da kaina haka inda hakane."
Jamila da yake duk yaran dangi tsoranta sukeji hakan yasa kallan meenal kawai tayi ta yi shiru ta yafa mayafinta ta tafi kitson.Meenal na fita alhaji ya kira wayar hajiya Mariya,bayan sun gaisane ya ce"Mariya yau d'in nan ba sai gobe ina son kusanar da Amina jibi za'a d'aura mata aure,idan kuma kunk'i kunajin tsoranta tom ni zanzo da kaina in sanar da ita...........✍️
📚 MEENALYN DADDY 📚
📚 MEENALYN DADDY📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*⚜️©J.A.W📚🖌️*
Na
Fadila Sani Bakori.
Page 27 & 28
Meenal na fita alhaji ya Kira wayar hajiya Mariya ,bayan sun gaisane ya ce "Mariya yau d'innan ba sai gobe ba inason kusanar da Amina jibi za'a d'aura mata aure ,idan kuma baku fad'a mataba kunajin tsoranta tom ni zan zo da kaina in sanar da ita."
Hajiya Mariya numfasawa tayi sannan ta ce "Alhaji yanzu muma mukagama maganar sanar da Meenal,tom munyi shawarar turata k'unshin da kitso ne kafin musanar da ita ,saboda indai ta san da maganar bazatai kitson ba,daga ta dawo zamu sanar da ita"
Alhaji kashe wayar yayi .
Meenal ko ba ita da dawo ba sai gaf magriba,tana da wowa taita b'oye kitson kanta batason hajiya Jamila ta gani dan kitson k'ari tayi (attachment) Bayan meenal ta ci abincine tayi sallah ta kalli mommynta ta ce "Mommy daddy fa?."Bai shigoba"
Meenal wayarta ta ciro ta kira daddynta awaya Kira d'aya ko ya d'aga ,meenal cikin shagwab'arta ta ce "Sweet daddy banganka ba fa tun safe?"Alhaji Abba cikin lallashi ya fara magana kamar haka "Meenalyn daddy ki yi hak'uri kinji tafiya ce takamani zuwa Abuja ko mommynki ma ban fad'amawa ba"Meenal kamar zatai kuka ta ce "Daddy gashi gobe zamu Kano da mommy Jamila"Alhaji Abba da yasan babu wata maganar zuwa Kano k'ila dai amma ta wata dubararne ya ce "Babu damuwa meenalyna ki yi tafiyarki idan nazo sai inzo kano d'in kiganni ai haka yayi miki ko?"
Meenal cikin jin dad'i ta ce "Tom sai ka dawo"Tana fad'in haka ta kashe wayarta.
Hajiya Mariya ko sosai ta yi mamakin tafiyar daddyn meenal baisanar da ita ba,amma da ta tuna gobe zai dawo sai ta share.
Bayan hajiya Mariya da 'yan'uwanta sun gama duk abinda zasuyi misalin k'arfe tara suka Kira meenal falon,hajiya Jamila ce ta kalli meenal ta fara magana kamar haka "Meenal nasan kinsan kwanakin baya da ya wuce daddynki ya sanar dake maganar samiki rana ko?" Meenal kai ta d'agama hajiya Jamila.Hajiya Jamila kuma taci gaba da cewa " Tom kamar yadda ya sanar da ke anfasa awancan lokacin ya fad'amiki hakane dan baya son ganinki cikin damuwa amma ahak'ik'anin gaskiya magana na nan yanzu haka jibi juma'a idan Allah ya kaimu za'a d'aura auranki ina fatan zakiyima mahaifinki biyayya ki amshi auranki batare da tada hankalinki ba ,dan kinsan ba zai zab'a miki abinda yasan zai cutar da ke ba."
Meenal cikin kuka ta ce "Mommy Jamila Wallahi bana sonshi,ni na yadda daddy ya auramin koma waye amma banda d'an kyauye dan Allah ."
Hajiya Jamila da yake bawasa zarema meenal ido tayi ta ce "Ke banason shashanci kina son ki maida mahaifinki k'aramin mutum ne bayan anriga angama magana yanzu kuma sai ya koma yace anfasa ,tom kinsan dai halina wallahi ban iya lallashi ba yanzu sai in miki dukan da zaki kai kanki kafin jibi dan haka tun kafin kowama yaji ki shiga hankalinki ."
Sosai Meenal kejin tsoran hajiya Jamila hakan yasa ta tashi ta ruga da gudu ta shiga d'akinta tana mai ci gaba da kukanta,waya ta d'akko ta kira number daddynta ya fi ak'irga amma bata shiga ya kashe wayar ,dole ta hak'ura taci gaba da kukanta kafin daddynta yazo afasa acewarta ,haka dai bacci b'arawo ya saceta.
Bayan meenal ta shiga d'aki ne hajiya Jamila ta kalli mommyn meenal ta ce "Mariya wallahi karki nunama meenal wasa amaganar auran nan duk abinda zatace kice mata tayi hak'uri tayi biyayya ga Mahaifinta,idan taga babu goyan bata ta ko'ina zata hak'ura ta zauna"Hajiya Mariya dai saboda bata son yi ma yayarta gaddama shiru tayi,amma ita tasan meenal kome za'ai mata bazata tab'a hak'uri ta zauna ba dan tasanta da kafiya sosai.
Haka dai suka k'araci tattaunawarsu game da bikin kafin suka kwanta"
Washe gari daga mommyn meenal har 'yan'uwanta babu wanda yabi takan meenal haka sukaci gaba da harkokinsu Aisha ce k'anwar Mommyn meenal ta kalli hajiya Jamila ta ce "Aunty Jamila kinga fa har k'arfe sha biyu har yanzu meenal