Showing 36001 words to 39000 words out of 47397 words

Chapter 13 - MEENALYN DADDY Complete Book By Fadila Sani Bakori.txt

06 Jan 2025

2936

nan ni na yadda ki yanke min duk hukuncin da ya yi miki indai zaki bar kukan kar kanki ya yi ciwo"Ina wayata?"D'anjuma sanin ko ya ba Meenal wayan Daddynta zata kira ta tona mai asiri yasa ya k'i bata wayar ya ce"Amina idan na baki wayar me za ki da ita? Idan wani abun kike buk'ata ki fad'amin zan kawo miki yanzu?"Meenal cikin goge hawayanta ta kuma tsantsar tsanar D'anjuman da take ji ta ce"Wallahi Allah sai ka yi da kasanin abin da kaimin! waya kuma kaje ka rik'e ,bazan d'an gidan talakawa wanda bai gaji arzik'i ba,indai ka cika kai D'an halak ne ka sakan yanzun nan!"D'anjuma murmushi ya yi mai ciwo dan Meenal ta kaishi bango.Jajayan idonshi ya d'ago yana kallan ta ya ce"Amina tabbas ni d'an halak ne,saki kuma da kike magana ba wai sai na sake ki bane ya tabbata ni d'an halak ne,abin da zan yi in nuna ni d'an halak ne shine duk da kika kasance ke d'in ba mai tarbiya bace in daure in zauna da ke d'an in nuna ma Alhaji ni d'an halak ne kar in watsa mai k'asa a ido,amma bacin haka ke baki da abin da ni zan so ki har in nace miki, saboda ko ta ina baki da tarbiyar !Sai yanzu nake danasanin bijere ma shawarar iyayena da nayi na auranki ,sakarya kawai shashasha!"Meenal cikin tsiwa irin ta cikakkun marasa kunya ta ce"Ashe kaima baka da tarbiyar inda har b'akar matar nan mai kama da kai ta hanaka aurena amm...."Maganar Meenal mak'alema ta yi saboda dukan da D'anjuma ya kai mata ko ta ina.Meenal tun tana zagin D'anjuma har ta fara bashi hak'uri da taji wayi.D'anjuma ko saida ya yi ma Meenal dukan da ko magana ta gagareta sannan ya rabu da ita,ya zuk'unna kusa da ita yana kallanta ya ce"Saboda ki tabbatarmin baki da kunya shine zaki kalli cikin idona ki kira mahaifiyata da sunan banza ko?"Meenal da gaba d'aya take tsoran D'anjuma ya kamata kaita ta girgiza mai.D'anjuma kuma cikin fushi ya kuma cewa"Saki kuma ba zan sake ki ba! duk inda zaki ki je!Amma fa ba wai dan ina sonki ba,kawai dan in baki abin da kika rasa agidanku ne wato tarbiya,sai na koya miki yadda ake magana da manya sakarya kawai shashasha!".
D'anjuma nagama fad'in haka ya juya ya fita ranshi b'ace .
Meenal ko da jikinta ko ina ke rawa dan sosai ta bugu.Tana ganin D'anjuma ya fita ta tashi ta lallab'a ta sa ma yafinta ta fita gidan da sauri tana fita ko taci karo da mai Napep ta tare ta hau.






Meenal na sauka kud'in da ke hannunta taba mai Napep d'in.Haka ta fara takawa kad'an-kad'an ta shiga gidansu ,lokacin Daddynta da Mommynta na breakfast.Dukkansu da sauri duka d'ago jin kukan Meenal da sasafe haka.............










📚 MEENALYN DADDY 📚








Page 36






Meenal na sauka kud'in da ke hannun ta taba mai Napep d'in.Haka ta fara takawa kad'an-kad'an ta shiga gidansu,lokacin Daddyn Meenal da mommynta na breakfast dukkan su da sauri suka d'ago jin kukan Meenal da sassafe haka.
Meenal ko na had'a ido da daddynta ta kuma sakin baki ta fashe da kuka iya k'arfinta.Daddyn Meenal har yana tuntub'e wajan saurin ta shi ya yo wajan Meenal inda ta durk'ushe tana kuka.Daddyn Meenal rungumo Meenal ya yi cikin tashin hankali yana cewa"Meenyna lafiya kike kuka haka?Wani abun ya yi miki ko?"Meenal dai ba baki kukan ta kawai take.Daddyn Meenal d'ago muskar Meenal ya yi maganar da zai yi tsayawa tayi sakamakon taban marukan da ya gani fuskar Meenal,cikin gigita ya ke cewa"Meenalyna yarannan ne ya mare ki haka?"Meenal cikin kuka ta ce"Daddy fyad'e ya yi min amma haka bai mai ba ya kamani ya yi ta duka yana zagina ,kai kan kama sai da ya zageka ya zagi mommy ma ,kuma ya ce banga komai ba sai ya koyamin hankali ya yi min tarbiya wai baka ban tarbiya ba!"Meenal ta fad'i maganar tana kuma rushewa da kuka.
Abin mamaki Daddyn Meenal ma kukan yasa yana cewa cikin kuka"Mommyn Meenal zo kika dukan da yarannan ya yi ma Meenal ,yanzu duk abin da ya yi mata bai isheshi ba sai ya had'a mata da duka?"Mommyn Meenal ta sowa tayi ta zo inda Meenal d'in take.Sosai itama taji zafin dukan da D'anjuma ya yi ma Meenal d'in,amma kuma tasa Meenal k'ure shi zata yi .






Daddyn Meenal kama Meenal ya yi ya shigar da ita bedroom d'in shi ya kwantar da ita ,sannan ya d'auki key d'in motar shi zai fita.
Mommyn Meenal da sauri ta kamo hannun Daddyn Meenal ta ce"Daddyn Meenal ina kuma zaka?"Mommyn Meenal Wallahi duk wanda ya tsayama yaran nan yau sai ya raina kanshi,dubi dukan da ya yi ma yarinyar nan?,Meenal nawa take da har zai Mata irin dukan nan haka? Idan ya kashe ta fa! to Wallahi ba zan yadda ba !".Mommyn Meenal cikin damuwa ta yi saurin kamo hannun Daddyn Meenal ta ce"Haba Daddyn Meenal yanzu wana mataki zaka d'auka akanshi ? Ni Wallahi nafi tunanin Meenal k'ureshi tayi ,kai kanka kasan Meenal bata da kuny..."Marin da Daddyn Meenal ya yi ma Mommyn Meenal ne yasa tayi shiru tana kallan shi da mamaki,shi ko sa kanshi ya yi ya fita yana huci.






Direct Station Daddyn Meenal ya wuce yana zuwa ya Kai report akan dukan da D'anjuma ya yi ma Meenal.Take aka had'ashi da 'yan sanda biyu suka nufi gidan .








D'anjuma ko b'acin rai ya sa ya manta ya fita bai rufe get d'in gidan ba.Ko da ya dawo baiga Meenal ba baiyi mamaki ba yasan haka zata faru,tea d'in da ya amso ma Meenal da Indomie ya zauna yana cin Indomie yana cikin cine Daddyn Meenal ya shigo shi da 'yan sandan ,yana zuwa ya nuna musu D'anjuma.Take d'aya daga cikin 'yan sandan ya d'aga hannu ya wanka ma D'anjuma Mari.Daddyn Meenal ko cewa ya yi"Ku tafi da d'an iska can har sai na neme ku!"
'Yan sandan tasa D'anjuma su kai suka tafi da shi.
Sosai 'yan sandan suka bigi D'anjuma daga k'arshe kamar yadda Daddyn Meenal ya sa su suka ce ya basu takardar Meenal.D'anjuma da sosai ya bugu hannun 'yan sandan kai ya d'aga yana kallan 'yan sandan ya ce"Ko kashe ni za kuyi ba zan sake ta ba!"Haka suka ci gaba da bugun D'anjuma.Amma abin da yake maimaita musu ke nan, Ba zai iya sakin ta ba.






Can ko Daddyn Meenal na komawa gida ya kalli Mommyn Meenal ya ce"Mariya Wallahi indai naji Maganar yaran nan na hannun 'yan sanda wajan Alhaji to nasan a wajan ki yaji kuma Wallahi ran ki zai b'ace sosai!"Mommyn Meenal kallan Daddyn Meenal ta yi ta ce"Daddyn Meenal dan Allah kar ka ja mana abin magana dan Allah kasa asaki d'an mutane"Daddyn Meenal ko sauraran Mommyn Meenal bai yi ba ya yi shigewarshi ciki inda Meenal ta ke.
Zaune ya isketa tayi wanka ta shirya tana cin jollop d'in taliya.Daddyn Meenal zama ya yi kusa da Meenal ya ce"Meenalyna ya jikin naki? Ko Asibiti zamu a duba ki?"Meenal kai ta girgizama Daddyn ta ta ce kamar za tai kuka"Dadda ni so nake kasa shi ya sakan dan Allah"Kan Meenal Daddyn Meenal ya sha ya ce"Ki kwantar da hankalinki Meenalyna kin gama zama da d'an iskan yaran nan,yanzu haka yana hannun 'yan sanda kuma nasasu su amsar min takardar ki"Meenal cikin jin dad'i ta rungume Daddyn ta tana cewe"Allah ya bar min kai Daddy bacin kai da ya kasheni"








Yau kwanan D'anjuma uku kenan hannu 'yan sanda kuma ba yadda basu yi ba,amma yak'i sakin Meenal.






Mommyn Meenal zaune suke ita da Daddyn Meenal da Meenal a Falon suna breakfast,Mommyn Meenal kallan Daddyn Meenal ta yi ta ce"Daddyn Meenal wai ya maganar Abdurrahaman ne? Ko har yanzu yana hannun 'Yan sandan ne?"Ai yaran nan yana da taurin kai to mu zuba ni da shi,anyi-anyi yak'i sakin Meenal"Mommyn Meenal ran ta a b'ace ta fara magana kamar haka"Daddyn Meenal gaskiya kasa a saki yaran nan haka nan kar ya kuma kwana wajan nan,haba dan Allah ka san fa halin Meenal ,ina da tabbacin k'ure shi ta yi har ya bugeta haka"Mariya ba zan sa a saki yaran nan ba har sai ya ban takardar Meenal"Mommym Meenal tashi ta yi ta ce"To Wallahi ka tabbatar da yau ni kuma zan kira Alhaji in sanar da shi halin da ake ciki "Mommyn Meenal na gama fad'in haka ta yi hanyar bedroom d'in ta.








Daddyn Meenal na shiga ya yi wuf ya amshe wayar hannun mommyn Meenal ya ce"Me ki ke Shirin ai katawa haka?"Alhaji zan kira ,kuma baka son in kira shi to ka kira kasa a saki Abdurrahama"Daddyn Meenal cikin b'acin rai ya ce"Wai Mommyn Meenal me kike fad'i ne haka? Ko so kike ki ce min kinfi son yaran nan ne akan Meenal?"Ni dai na fad'ima Wallahi idan har baka kira yanzu aka saki yaran nan ba to babu abin da zai hanani fad'ima Alhaji abin da ke faruwa" Daddyn Meenal wayar shi ya ciro ya kira 'yan sandan ya sanar da su a saki D'anjuma.








D'anjuma ko ana sakin shi kud'in da ke hannun shi ya yi amfani dasu ya yi kud'in motar Funtua.Yana isa da zazzab'i sosai ya k'arasa gidan shi,yana zuwa ya kira wani abokin shi ya duba shi ya bashi magani.




Washegari D'anjuma ya tashi jikinshi da k'arfi ba laifi,saidai kallo d'aya za kai mai ka hangi ramar da ya yi yana shiryawa ya nufi layin kad'anya.Mahaifiyar D'anjuma da mamaki ta ke kallan D'anjuma ta ce"Lafiya naga ka rame?Kuma jiya k'annan ka sun je suka ce gidan a rufe lafiya?"D'anjuma kai ya sosa ya ce"Eh na kaita gidan abokina ne lokacin,rama kuma na d'an yi zazzab'i ne"Allah ya kyauta"Mahaifiyar D'anjuma ta ce.






Bayan wata d'aya. Haka Meenal taci gaba da rayuwar ta a gidansu hankalin ta kwance.B'angaran D'anjuma ma hakane rayuwarshi ya ke hankalin shi kwance ya cire damuwar Meenal a ran shi.
B'angaran Alhaji ko Mommyn Meenal da kanta ta samai ta sanar da shi fad'an da Meenal su kai da D'anjuma amma ta b'oye mai kai D'anjuma hanun 'yan sanda da Daddyn Meenal ya yi.Daga k'arshe ta k'ara da cewa"Alhaji abin da nake so da kai dan Allah karka kuma shiga maganar Meenal da D'anjuma ni kaina na cire hannuna , ai dai dole nan gaba su su gaji da zaman su samai kuma shi ya sanar da su ba zai tab'a sakinta ba,dan haka ka zuba musu ido dan Alllah"Alhaji cikin gamsuwa ya ce"Insha Allah Mariya ba zan kuma sa hannun a al'amarin Amina da Sani ba.....








Fadila Sani Bakori ce










📚 MEENALYN DADDY 📚








Page 37








"Insha Allah Mariya ba zan kuma sa hannuna a al'amarin Amina da Sani ba"Sosai Hajiya Mariya taji dad'in abin da Alhaji ya ce.Godiya ta yi mai ta tafi gida.Bayan Mommyn Meenal ta koma gida ne ta Kira D'anjuna a waya dan tun da abin ya faru har yanzu ba suyi waya ba kunyar Kiran D'anjuma take.D'anjuma na bakin kasuwancin shi Kiran Mommyn Meenal ya shigo wayar shi,D'anjuma cikin na tsuwa ya d'aga wayar yana gaida Mommyn Meenal cikin girmamawa,Mommyn Meenal cikin jin kunya ta ce"Abdurrahaman kunyar abin da Daddyn Meenal ya yi maka yasa na kasa kiran ka dan Allah ka yi hak'uri ka zo ka samu Alhaji ka yi mai magana idan yasa baki Meenal dolanta ta koma d'akin ta"D'anjuma cikin na tsuwa ya ce"Mommy na bar Amina har sai lokacin da ta yi ra'ayin zama gidana da kanta sannan dan samun kwanciyar hankali"Sosai hakan ya yi ma Mommyn Meenal dad'i dan dama tana son hakan su zuba musu ido suka yadda abin zai kaya nan gana.Haka mommyn Meenal suka gama gaisawa sosai da D'anjuma sannan ta yi mai sallama ta kashe wayar ta.






B'angaran Alhaji yau ya tashi ba ya jin dad'in jikinshi ya tashi da niyyar zazzaga ko zai ji dad'i jikin nashi ya yanke ciki ya yi muguwar fad'uwa.Isuhu da ke kula da Alhaji da sauri ya k'arasa wajan Alhaji.Sosai hankalin shi ya tashi jin Alhaji ba ya motsi.Daddyn Meenal ya kira a waya ya sanar da shi.Daddyn Meenal da sauri ya bar abin da yake ya k'arasa gidan.Saidai ganin jikin Alhaji d'aukar shi ya yi ya yi Asibiti da shi.Suna zuwa ko aka fara bashi taimako kasancewar Asibitin Daddyn Meenal ne.Saidai sakamakon fad'uwar da Alhaji ya yi da k'arfi ya sa ya samu karaya a cinyarshi.Hakan yasa a kai musu transfer zusa Asibtin Shika dake Zaria.
Daddyn Meenal sai bayan sun isa Shiga ne ya samu damar sanar da Mommyn Meenal abin da ke faruwa.
Mommyn Meenal bacin sun gama waya kallan Meenal ta yi ta ce"Kin ji Daddyn ki na Shika shi da Alhaji ba lafiya ki tashi muje mu duba shi.Meenal kallan Momnynta ta yi ta ce"Mommy Allah bana iya zuwa bansan meke damuna ba bana jin dad'in jikina kwata-kwata kusan sati d'aya ke nan.Mommyn Meenal kallan Meenal d'in ta yi ta ce"Sannu ki sha magani,ko kuma ki shirya mu biya Asubitin Daddyn ki a duba ki"A'a Mommy bafa wani sosai bane kawai dai ina jin kasala ne da rashin k'arfin jiki."To Allah ya baki lafiya inda ba zaki Asibiti ba a duba ki".
Mommyn Meenal shiryawa ta yi ta nufi Asibitin Shiga,kasan cesar ba wani nisa ba ne sosai tsakanin su yasa cikin lokaci ta isa.Daddyn Meenal sosai ya yi mamaki ganin ba a zo da Meenal ba,kallan Mommyn Meenal ya yi ya ce"Meenalyn Daddy fa ya akai bata zo ba?"Wai bata da lafiya kuma na ce ta zo a dubata tak'i"Daddyn Meenal waya ya ciro ya kira Meenal .Tana d'agawa ya ce"Meenalyna baki da lafiya kuma kink'i zuwa a duba ki me ya sa?"Meenal da tana nan inda Mommyn ta ta barta cikin kasalallar muryar ta ta ce"Daddy na ji sauk'i fa?"To Allah ya k'ara lafiya,amma fa ki sha ko paracetamol ne"To Daddy insha Allah"Sannan ya kashe wayar.
Mommyn Meenal kuma tafiya tayi dan kar tai dare.








Meenal ko haka mommynta ta dawo ta sameta inda ta barta kwance.Mommyn Meenal na zuwa Meenal ta kalle ta ta ce"Mommy yunwa nake ji ki kawo min abinci"Mommyn Meenal kallan Meenal ta yi ta ce"Meenal wai meke damun ki kwana biyu ne? Yanzu ko sallah ma ba zaki tashi kiyi ba?"Meenal kamar za tai kuka ta ce"Mommy ki kawo min abinci sannan yunwa nake ji"Hajiya Mariya kitchen ta shiga ta ziboma Meenal Jollop d'in cous-cous da tayi.Meenal loma d'aya tayi ta fara kakarin amai, da kudu ta ruga toilet,sai da ta amaye duk abin da ke cikin ta.
Mommyn Meenal toilet d'in ta shiga tana k'are ma Meenal d'in kallo,sai yanzu ta lura da hasken da Meenal d'in ta yi .Mommyn Meenal murmushi ne ya kub'uce mata ta ce"Alhamdullah Allah na gode maka"Meenal kallan Mommyn ta ta yi ganin tana murmushi ta turo baki ta ce"Mommy murmushi kike dan ban da lafiya ko?"Mommyn Meenal rungume Meenal d'in ta yi ta ce"Taya zan ji dad'i gudan jinina bata da lafiya wani abun can na tuna nayi murmushi"






Tun daga ranar Meenal bata kuma yin amamai ba sai in taci cous-cous ,amma fa har yanzu rashin k'arfin jikin nan na nan,dan har abinci wani lotun a kwance ta ke cinsa.
Meenal kallan mommyn ta ta yi dake ta shirin zuwa Asibiti duba Alhaji dan yanzu abin sai a hankali dan kusan Alhaji bai san waye akan shi ba.Meenal kallan Mommynta ta yi ta ce"Mommy nima zan daure inje in duba jikin Alhajin daga nan nima inje a dubani ,Wallahi mommy bikiji yadda nake jiba yanzu "Mommyn Meenal gabaan ta fad'uwa ya yi jin abin da Meenal d'in ta ce dan bata son Meenal da Daddyn ta su san da cikin jikin Meenal d'in yanzu .Mommyn Meenal kallan Meenal ta yi ta ce"Meenalyna kinga dai ke ba ma'abociyar shan magani bace,Asibitin ko kin je ce miki zasu yi shawara ke damun ki ,ai tun ranar da ki kai aman nan na fahimci shawara ce,dan haka zan samo miki maganin gargajiya ki sha"To amma duk da haka muje in duba Alhaji"Shiru Mommyn Meenal ta yi sannan ta ce"Amma fa kar ki ce ma Daddyn ki baki da lafiya dan inhar kika ce mai haka to kinsan magunguna zaisa a baki "Meenal da ba son magani take ba ta ce"Bazan sanar da shi ba ai".








Haka Meenal ta shirya suka je suka duba Alhaji,saidai jikin nashi Masha Allah ba kamar yadda suka ji a waya ba,inda har ya bud'e ido ya kallesu magana ce dai ya kasa musu saidai hannu ya d'aga musu.










Haka rayuwa taci gaba da tafiya Daddyn Meenal gaba d'aya ya bar zaman gida ya koma na Asibiti saboda jinyar Alhaji,jiki sai ya yi kamar yaji sauk'i sai kuma ya k'ara rikecewa.






Yau watan su Alhaji d'aya ke nan a Asibiti.
B'angaran Meenal ko ta fara jin sauk'in yadda ta ke jin jikin ta.Mommyn Meenal tana kitchen tana musu girki dan yanzu Meenal a kwai saurin jin yunwa.Meenal shiga ta yi ta kamo hannun Mommyn ta ta ce"Mommy ni fa ina son inje Asibiti a duba ni "Mommyn Meenal cikin fad'uwar gaba ta ce"Haba Meenalyna me kuma zaki a Asibiti ?Bayan kinji sauk'i!"Meenal cikin damuwa ba wai dan tana zargin tana da ciki ba ta ce"Mommy 3 Months fa kenan banga period d'ina ba"Shiru Mommyn Meenal ta yi ta ce"Ki kwantar da hankalin ki Meenal har Daddyn ki ya dawo ya duba ki da kan shi"Meenal kallan Mommyn ta ta yi cikin damuwa ta ce"Mommy Daddy yau she zai dawo Alhaji har yanzu ba lafiya , zan je Asibitin Daddy yanzu a duba ni"To shikenan Meenal in da kin matsa sai kin dawo"Meenal har ta tafi Mommyn Meenal ta yi saurin kiranta ta ce"Meenal amma dan Allah karki kira Daddyn ki ki sanar da shi baki da lafiya,kinga dai yana d'ora al'amuran ki akan shi dan Allah Meenal kar abun ya yi mai yawa ga ciwan Alhaji"To Mommy ba zan fad'a mai ba na tafi.......








Fadila Sani Bakori ce.








📚 MEENALYN DADDY📚








Page 38








Meenl na tafiya Hajiya Mariya ta d'akko wayar ta ta kira ma'aikaciyar asibitin su Daddyn Meenal.Bayan sun gaisa ne ta ce"Sister Hafsat nasan kinsan labarin auran Meenal wajan Daddyn ta,to kisan mutuniyar taki yadda take,yanzu haka ciki ga reta to ina tsoran ta sani, Wallahi tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login