Showing 30001 words to 33000 words out of 47397 words
Chapter 11 - MEENALYN DADDY Complete Book By Fadila Sani Bakori.txt
bata fito ba ta naimi abin kari (breakfast) ko in dubata dan Allah?"Jamila tsaki tayi dan bata son naci ta ce "Aisha bikijiba akace maganin biri karan maguzawa tom meenal indai muna son tayi biyayya da zab'inmu tom dole sai mun rintse ido mun nuna mata k'arfin ikonmu akanta,mun nuna bamu damu da wata shirman damuwarta ba,ana barin yaro ya tab'a wuta bawai dan ba'a sanshi ba ne ,a'a sai dan gaba ya kiyaye ".
Dole Aisha taja bakinta tayi shiru amma tana lure da mommyn meenal duk ta shiga damuwa ta rashin fifowar meenal d'in.
Mommyn meenal jin daddyn meenal shiru waya ta d'auka ta kirashi amma wayar shi kashe tana aje wayar tana tunanin lafiya saiga kira da bak'uwar number tana d'auka ta ji muryar daddyn meenal .Hajiya Mariya cikin sanyi ta ce "Daddyn meenal lafiya inata Kiran numberka bata shiga?"Daddyn meenal cikin kwantar da hankali ya ce " Mommyn meenal ki yi hak'uri aikine yayimin yawa,naso na dowa yau amma sai gobe zanyi sammakon dawowa aiki yayimin yaw..."Mommyn meenal cikin katse daddyn meenal ta ce "Daddyn meenal gobane fa d'aurin auran meenal,kuma kace sai gobe zaka dawo?"Tom mommyn meenal nima naso ace yau na dawo kodan meenal amma abin bai yuwu ba,gobe insha Allah zanyi sammako."Tom shikenan Allah ya kaimu goban".Tana fad'in haka ta kashe wayar ,mommyn meenal yayarta ta kallah ta ce " Aunty Jamila kinga daddyn meenl ya tsira tafiyar nan ne saboda gudun rigimar meenal ne fa, dama tunda nakira wayarshi najita akashe nayi zargin haka"Hajiya Jamila cikin kwantar ma mommyn meenal da hankali ta ce "Ai garama da yatafin kinga munyi taranmu hankali kwance, inda indai daddyn meenal nanan meenal sai tafi yima mutane iskanci,kuma ni dama nagayyaci 'yan'uwanmu dan yanzu haka 'yan Kano na hanya,inko yana nan ba bari zai ba inda kince yace bai son agayyaci kowa kinga yanzu sai muyi taran mu cikin kwanciyar hankali"
B'angaran meenal ko tana can kwance sai aikin kuka take bunubuni ta Kira wayar daddynta amma kashe ,tanan kwance ga yunwa ga damuwar rashin samun daddynta awaya ga kuma babbar damuwar da takeciki ta auran da za ai mata.Tananan kwance Aisha k'anwar Mommyn meenal ta lallab'a ta shigo,kusa da meenal ta zauna tana mai k'are mata kallo sannan ta ce "Meenal ki tashi ga abin breakfast na kawomiki,sanan shi kukan nan da kike babufa maganin da zaimiki,ni indai zakiji maganata kiyi hak'uri Meenal ki ma mahaifinki biyayya kina ganin shima bason auran nan naki yake ba,amma ya yi hak'uri ya yi biyayya ga mahaifinshi tom kema ki yi biyayya ga mahaifinki mana "Meenal dai bata saurari Aisha ba haka taci gaba da kukanta Aisha kuma ta tashi ta fita.
Meenal ganin yunwa zata ka sheta tashi tayi ta d'auki abincin taci kad'an.
Zuwa dare 'yan'uwan Hajiya Mariya suka iso inda akazo harda Hafsat yarinyar hajiya Jamila wadda suke sa'a da meenal.Tana zuwa d'akin meenal ta shiga ,kwance ta isketa idon nan yayi jajir alamun tasha kuka tagaji,Hafsat cikin sanyi ta dafa meenal dan taji komai game da rashin son auran da meenal batayi,ta ce "Meenal wai meye haka sai kace akanki aka fara aure ,tun jiyafa mommy tace min kike kukan nan."
Meenal tashi tayi tana kallan Hafsat ta ce "Hafsat kinsan wa daddy zai auramin kuwa?, d'an kyauye fa Hafsat!"Hafsat da mamaki ta kalli meenal ta ce wai dan Allah da gaske ki ke d'an kyauye daddy zai aura miki?"Kai meenal ta d'agama Hafsat .Hafsat kuma tacigaba da cewa "Amma shine mommy ta ke cewa in lallasheki ai ko wallahi bazan goyi bayan ki auri d'an kyauye b....."Ubanki nace Hafsat ubanki dama kinzo ne ki zigata ?".Hafsat cikin turo baki tace "Mommy Allah ni bansan d'an kyauye zaku aurama sister ba,gaskiya mommy ba ai mata adalcib..."Marinda hajiya Jamila taima Hafsat ne yasa tayi shiru,sannan ta nuna meenal da hannu ta ce "Ke kuma sakarya idanma kin d'auki zugarta ke ki ka sani dan babu abinda zai hana auran nan sai wani ikon Allah!"Meenal kuma fashewa da kuka tayi hajiya Jamila kuma juyawa tayi tayi tafiyarta.
Bayan Hafsat taje ta lek'a ta tabbatar da mahaifiyarta ta tafine ta dawo inda meenal take ta ce "Meenal share hawayanki kibar asararsu akan wani banza can,kiyi hak'uri kamar yadda suka nuna sai anyi anyi d'in akaiki da kanshi zai gaji ya sakeki,wulak'anci yau da ban nagobe da ban,da kanshi sai fahimci ke ba tsararshi bace ya baki ta kaddarki,yanzu abinda nakeso dake kiyi hak'uri kada kanki yayi ciwo dan Allah, nikaina wallahi ban goyi bayan ad'aukeki aba d'an kyauye ba."Haka dai Hafsat taita zuga meenal da nuna mata irin abubuwan da zata rik'amai nacin mutunci wanda abinma kwatakwata ba zaiyi k'arko ba.
B'angaran daddyn meenal ko waya yakira alhaji yasanar dashi sai gobe zayi sammakon zuwa kafin d'aurin auran .
Washe gari haka gidan su Meenal ya cika da mutane dan hajiya Jamila da kanta ta shiga mak'otan gidansu Meenal ta sanar da d'aurin auran meenal d'in yau.Aiko haka gidan yacika da mutane,inda mutane da dama sun k'osa suga waye angon.
B'angaran meenal ko hayaniyar mutane da takeji wai anzo bikinta hakan sosai ya kuma d'agamata hankali lokaci guda zazzab'i mai zafin gaske ya rufeta.
Rana bata k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya.'Yan'uwan d'anjuma gaba d'aya sun hallara da 'yan'uwan meenal .Ababbban masallacin kawo wato shak Zafar,inda har yanzu babu daddyn meenal balabarinshi .Babban abokin daddyn meenal shi ya bada auran meenal ga k'anin mahaifin d'anjuma.
Bayan an d'aura auran ne da d'an jimawa Alhaji wato kakan meenal ya naimi d'anjuma dan yanason keb'ewa da shi.
D'anjuma zaune afalon alhaji,alhaji ya kalli d'anjuma dakanshi ke ak'asa ya ce "Abdurrahman naso ace tun jiya kazo dan maganganun da nakeso da kai suna da yawa,inda kaga yau ba lokaci inda yanzu zaku juya da amarya,wato d'anjuma da farko dai kafin in fad'i abinda nakeson fad'a maka ina naiman alfarma awajanka?"D'anjuma kanshi k'asa ya ce "Alhaji babu abinda zaka naima awajena banma shi ba,dan bacin kai nasan da bazan samu meenal ba dan haka karkaji komai kome kakeso awajena ni kuma zan maka shi insha Allah ."
Alhaji cikin jin dad'in bayanin d'anjuma ya fara magana kamar haka"Abdurrahman Amina dai ta zauna agidanku nasan ka fahimsu wasu halayyarta ko kad'anne duk da ba zama mai tsawo ta yi ba,Abdurrahman nasan zakasha wuyar Amina sosai kafin kagane kanta ,abinda nakeso da kai dan Allah kayi hak'uri aduk yadda kasamu Amina watarana sai labari kuma mahak'urci mawadaci watarana zaka girbi ribar hak'urin insha Allah, sannan Amina bata san lallashi ba sai ammata jan ido take abu.Babu lokaci katashi kuje Allah yayi muku albarka Allah ya baka hak'urin zama da Amina."Insha Allah alhaji zanyi hak'urin zama da Amina kodan halaccinka agareni,nagode sosai"
D'anjuma na kaiwa haka ya tashi ya tafi dan abokanshi dama sai kiranshi suke awaya suna k'ofar gidansu meenal suna jiran abasu amarya su wuce.
Acan gidansu Meenal ko da kyar Hafsat ta lallab'a meenal tayi wanka tasa gayan da mahaifiyarta ta d'inka mata dan su basuga lefeba.Hafsat na shirya meenal tana cewa "Meenal bana son kina nuna musu wani abu aranki ki saki ranki akaiki d'in ,adai zaman aure bai yuwuwa saida soyayya ko ,da akwai wata shawara ma da zan kuma baki amma kinga yanzu ba lokaci ki bari sai munje can sai muyi magana"
Ita dai meenal cigaba da kukanta tayi ,Hafsat nacikin shiryata ne hajiya Jamila tazo takamo hanunta tace "Muje wajan mommynki kuyi sallama.
Meenal na kuka akakaita gaban mommynta,Allah sarki mommyn meenal d'inma kasa cema meenal komai tayi saboda kuka da yaci k'arfinta,da kyar dai ta iya cewa "Meenal kiji tsoran Allah kiyi biyayya ga mijinji shine abinda zakiyi ki samu ceto ranar gobe k'iyama"Meenal da kuka yaci k'arfinta cikin kuka ta ce "Mommy daddy dan Allah ina son ganin daddyna "Mahaifiyar meenal gogema meenal hawayanta tayi ta ce "Meenal ki yi tak'uri ki tashi ki tafi mutane najira daddynki zaizo har d'akinki ya ganki"
Haka aka tafi da meenal tana kuka tana ciccijewa akasata amota aka tafi da ita .Hafsat ko babu yadda batayiba dan taraka Meenal amma hajiya Jamila lurada Hafsat kamar tana zuga meenal yasa tahana tafiyar da ita.
Mutum biyu suka raka meenal d'akinta daga hajiya Jamila yayar mommyn meenal sai Aisha autarsu Mommyn meenal.Sai gaf magriba suka shiga garin Funtua inda aka kai amarya d'akin mijinta acikin unguwar wanzamai .Meenal haka ta kwana kuka babu yadda su hajiya Jamila basuyi da itaba amma tak'iyin shiru.
Washe gari da wuri abokan d'anjuma suka kawomusu tea da bread suka karya,suna gama karyawa sukayi wanka suka kuma yima meenal fad'a sosai sannan mota tazo ta d'aukesu,aifa da zasu tafi meenal rik'esu tayi tana kuka sosai dan har hajiya Jamila sai da ta tausayama meenal halin da tashiga ,haka dai suka janye suka tafi suka barta suna mai tausayamata dan yadda take nuna k'iyayyar d'anjuma abin yayi yawa.
D'anjuma ko da su hajiya Jamila zasu tafi sai da suka k'ara ankarar da shi akan hak'uri komai mai wucewa ne.Motarsu zata tafi hajiya Jamila takalli d'anjuma ta ce "Abdurrahman kashiga gida kayi lallashi dan mun baro ta tana kuka kuma bataci komai ba".
Bayan motarsu hajiya Jamila ta tashine d'anjuma ja yayi ya tsaya ya kasa shiga gidan yana mai fargabar yadda Amaryar tashi zata karb'ai,dan tunda aka tsaida auranshi da ita magana bata kuma shiga tsakaninsu ba,hasalima shi tunda tabar garinsu bai kuma ganinta ba.D'anjuma cikin shahada da fargaba ya yi Sallama ya shiga gidan jin shiru ya k'arasa cikin d'akin ,can ya hango meenal bakin kadon sai kuka take iya k'arfinta ,d'anjuma ta kawa yayi ya isa inda take ,cikin sanyin ya kalli meenal ya ce.............✍️
📚 Meenalyn daddy 📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*⚜️©J.A.W📚🖌️*
Na
Fadila Sani Bakori
Page 29& 30.
D'anjuma cikin shahada da fargaba ya yi sallama ya shiga gidan,jin shiru ya k'arasa cikin d'akin, can ya hango Meenal bakin gadon sai kuka ta ke iya k'arfinta .D'anjuma takawa ya yi ya isa inda Meenal take,cikin sanyi ya kalli Meenal ya ce" Meenal ki yi shiru dan Allah ki fad'amin damuwarki, kukan ki yana shiga cancikin tsakiyar zuciyata yana min ciwo,sai inga kamar nagazane ina gabanki ace ban magance miki abin da ki ke ma kuka ba,dan Allah ki fad'amin damuwarki kin ji Meenalyn daddy?"Meenal da jajayan idonta ta d'ago tana ma D'anjuma wani irin kallo na raini da tsana,sannan ta tashi daga zaunan da take tana kallan D'anjuma ta ce "Ka ta shi akaina malam zaka wani tsaya kana tanbayata damuwata! Gazawa kuma da kake magana kana tunanin kanada abin da zaka burgenine?Bacin na tsaneka na tsani duk wani abu da ya danganceka ka tashi agabana malam!"Meenal ta fad'i magana cikin tsantsar d'aga murya.
D'anjuma ko shiru ya yi bai matsa ba kamar yadda ta umarceshi , zuciyarshi namishi zafin maganar ta tsaneshi da tayi.D'anjuma da kyar ya iya bud'e baki ya ce "Meenal na sanni mai laifine agareki saboda nayi miki k'utsu cikin rayuwarki sai dai inason kisan komai yana faruwane abisa ga abin da Allah ya k'addara, hakan ya farune saboda k'addarar had'uwar aure tsakanina da ke da Allah ya k' ....."
Wata tsawa Meenal ta bugama D'anjuma ta ce"Ka fita nace bana son ganinka gabana ,bana son jin muryarka!, bana son jin komai da ya shafeka ka fita na ce!"Meenal ta fad'i maganar da k'arfin tsiya Wanda yake nuna ranta amatuk'ar b'ace yake.
D'anjuna ko cikin danne zafin maganganun Meenal ya ce "Naji zan fita amma ki fad'amin me zakici in kawomiki dan ance min bikici komai ba?"
Meenal cikin sanyi kamar za tai kuka ta ce "Bazan iyacin duk wani abu da yafito daga hannunka ba , kai ba wai hannunka kad'ai ba ba zanci duk abin da yafito daga garin nan ba,saboda na tsaneka! Natsani komai dake garin nan saboda kai" D'anjuma cikin damuwa ya ce "Nasan baki sona Meenal amma dan Allah karki hora kanki da yunwa ki yi hak'uri ki fad'amin kome kike so ni kuma nayi miki alk'awarin zan kawo miki shi?"
Meenal tsaki tayi ta taja bakinta tayi shiru dan ta gaji da magana acewarta.D'anjuma kuma ganin tayi shiru fita yayi yaje wajan mai tea da bread d'in kusa da su ya sa aka soya mata indomie da kwai , ya koma gidan tare da addu'ar Allah yasa ta yadda taci.
Meenal ko na ganin D'anjuma ya fita ta tashi tafara naiman wayarta dan tun jiya da suka iso bata ganta ba,saidai abin da Meenal bata sani ba,mommynta tasa aka d'auke mata wayar su Hajiya Jamila suka tafi mata da ita.
Babu irin naiman da Meenal bataima wayar ba amma bata ganta ba,zama tayi tai tagumi tana mai share hawayan dake zubar mata.Meenal na awannan halin ne D'anjuma ya yi sallama ya shigo da plate d'in indomie d'in da yasa asoyo mata.D'anjuma gefan Meenal yanufa zai zauna Meenal ta d'aga mai hannu da sauri tare da cewa "Malam karka kuskura ka zauna kusa dani wallahi!"D'anjuma fasa zama yayi ya mik'ama Meenal indomie da ya soyo mata .
Meenal ko kallan plate d'in indomie bataiba sai cewa tayi "Ina zansamu waya ina son yin waya yanzun nan?."
Shiru D'anjuma ya yi dan basu dad'e da gama waya da mahaifiyar Meenal ba akan ko tatanbayai waya karya bata,hakan yasa D'anjuma ya kalli Meenal ya ce "Wayata babu caji ki bari sai na samu caji"Waya na ke son yi yanzun nan,dan haka kota aro ka aro min ina buk'ata da sauri".
Shiru D'anjuma ya yi sannan ya ce "Sai dai ki yi hak'uri gaskiya har lokacin da zan anso tawa Wayar dan ban iya aro ba".
Meenal tashi tayi da saurinta ta jawo gyalanta ta yafa ta kama hanyar fita,D'anjuma da sauri ya tareta tare da cewa "Haba Meenal ina zaki keda bikisan kowa ba,kuma ko bama hakaba kefa Amarya ce bai kamata ki fita yau ba."
Meenal jatai ta tsaya dan har sunajin saukar numfashin juna ita da D'anjuma ,dan sun yi kusa da juna sosai,Meenal cikin isarta da gadararta ta ce "Malam karka kuskura ka yi yin k'urin tab'ani fita kuma dole in fita alokacin da naso in dawo alokacin da naso ,kai baka isa kahanani yin abin da nayi niyya ba wallahi!".
Meenal na fad'in haka ta bangaje D'anjuma da sunan ta wuce,sai dai D'anjuma ko gezau bai yi ba.Ganin haka cikin sanyi alamun lallashi D'anjuma ya ce "Dan Allah kiyi hak'uri ki zauna daga wayata tayi caji zan kawomiki kiyi amfanin da zaki ."
Meenal da kema D'anjuma kallan tsananin raini dan dama ita mutum ce mai rana mutane ,hakan yasa cikin tsantsar rashin kunya irin tata da rashin ganin girman nagaba da ita ta ce "Kai D'anjuma kake ko D'anjummai yanzu nake son amfani da Waya dan haka bani hanya in wuce".
D'anjuma da arayuwarshi ya tsani raini daurewa kawai yake da kuma nasihar kakan meenal Alhaji kenan da yake tunawa,shi yasa yakasa cema Meenal komai,amma wannan Karan yadda ta kira sunanshi atsananin raina sai ranshi yab'ace hakan yasa ya ce "Bari in kawo miki yanzu"
D'anjuma na fad'in haka yafita,yana fita ya ciro wayarshi ya Kira mahaifiyar Meenal,bayan sun gaisane D'anjuma ya ce cikin sanyi "Mama dama Meenal fa ta amtsa akan saidai in bata Waya zata yi anfani da ita,dan harma ta d'auki mayafinta wai zata fita ta aro,yanzu haka dai sai cemata nayi bari in anso mata".
Shiru Mahaifiyar Meenal ta yi sannan ta ce "Abdurrahman karka bata Waya kuma karka bari tafita,sannan duk rashin kunyar meenal da kake gani tana da tsoro sosai dole sai kana mata jan ido gaskiya kila zata rik'abin umarninka,amma indai kabari Meenal ta rainaka gaskiya bazakaji dad'inta ba,sannan dan Allah ka k'ara hak'uri dan nasan zaka yi fama ba kad'an ba."Mahaifiyar meenal na kaiwa haka ta kashe wayarta.
D'anjuma ko gudin rigimar meenal bai koma gidan ba.Yana nan zaune ak'ofar gidan 'yan garinsu suka ciko mota guda wai sunzo ganin gidan Amarya.D'anjuma da fara'arshi ya tarbesu ya yi musu jagoranci izuwa cikin gidan ,amma a b'arin zuciyarshi cike yake da fargaba,dan yasan meenal bazataima 'yan'uwanshi tarba mai kyau ba.
A tare suka jera suka shiga gidan.Zaune suka samu Meenal,saidai ko sallamarsu bata amsa ba bare kuma susa ran zata gaida su.Yayar mahaifiyar D'anjuma ce ta kalli Meenal da fara'arta ta ce"Saninu Amarya,ya kwanan b'ak'unta?"Meenal batare da ta kalleta ba ta ce"Lafiya"Tom da yake dama tun kafin dangin D'anjuma su je gidan mahaifiyar D'anjuma ta sanar da su halin matar D'anjuma d'in ,hakan yasa basu wani ji haushi cancan ba,a cewar su "D'anjuma ya d'ebo ruwan dafa kanshi".
Haka suka gama kalle-kallan su dan sosai suka yaba da kayan d'akin da Iyayan Meenal duka zuba mata,duk da dama sun san 'yar mai kud'i ce D'anjuma ya aura.Iyayan D'amjuma da abokan arzik'i da aka zo ganin gidan Amarya sallama su kaima D'anjuma dake tsaye kunya duk ta damai ganin yadda amaryar tashi ta amshi 'yan'uwanshi .Haka dai cikin kunya ya yi musu sallama da godiya suka tafi.
Bayan sun tafine Meenal ta kalli D'anjuma ta ce"Malam kace zaka aromin Waya amma kuma naji shiru"D'anjuma cikin damuwa ya kalli Meenal ya ce"Yanzu dan Allah abin da kikai ma 'yan'uwana kin kyauta!"Meenal kamar bata ji abin da D'anjuma ya ce ba ta ce"Baka ji abin da nace bane? Nace ina Wayar da kace zaka aro min?"Amina ba maganar Waya nai miki ba,maganar abin da ki kai ma 'yan'uwana nake miki, banji dad'in haka ba!"Meenal tashi tayi ranta b'ace tana kallan D'anjuma ta ce"Maganar da ta dameka kayi ,nima kuma maganar da tadaman nayi,sannan abu na k'arshe karka kuma kirana da Amina idan zaka kirani da sunan da kaji iyayena na kirana ka ki rani da shi,sannan zaka samar min Wayar ne koko inje in samar ma kaina?"D'anjuma da ranshi ya fara b'acewa da kuma tuna maganar mahaifuyar Meenal da y yi ya ce"Amina wai biki ji abin da nake miki magana akai bane?"Meenal batare da ta saurari D'anjuma ba ta buga tsaki ta juya ta yi hanyar fita.D'anjuma cikin jin zafi ya fusgo hanun Meenal ta dawo baya da sauri dan tama kusa fad'uwa,cikin jin haushin yadda D'anjuman ya fusgota ta ce"Kai wana irin bagidaj