Showing 15001 words to 18000 words out of 47397 words
Chapter 6 - MEENALYN DADDY Complete Book By Fadila Sani Bakori.txt
akayi,ita kuma dama ba son shi take ba,nan fa yunwa ta fara damunta,dan ko sallar magriba da kyar tayi ,tana cikin sallar ne d'an juma ya shigo gidan,bai shiga d'akin ba daga waje ya gaida Mahaifiyar meenal sannan ya mik'ama mahaifiyar shi hurar da ya siyo ya ce"Inna gashi adamama mu su".
Hajiya Mariya cikin fad'ad'a fara'arta ta ce"Tom mun gode Allah yasaka da alkairi"
D'an juma fita yayi dan yin sallah Isha'i da ake kira,saboda ya k'osa yaje gidan Sarki yaji dangartakar dake tsakanin su da su Alhaji.
D'an juma masallacin k'ofar gidan su ya fara zuwa yayi sallar Isha'i sannan ya nufi gidan Sarki.Sai dai koda yaje badamar samun sanin abinda ya kawo shi dan Sarki fira suke da Alhaji sosai,bayan sun gaisa ne Alhaji wato kakan Meenal ya ce"Yauwa Abdurrahman dama yanzu zansa Malam Haruna ya kiraka,amma inda gaka kazo ai shikenan,maza kaje gidanku ka tafomin da Amina"."D'an juma tashi yayi ya fita yana mai jin dad'i zai kuma ganinta,yana tafiya zuciyar shi na ingiza shi da cewa" Ka gwada furta mata kallamar so mana ko zaka dace".Wata zuciyar ta ce"Gaskiya yaudarar kanka kawai kake,amma kaima kasan bazata amin ce ba".Can kuma sai ya ba kan shi amsa da "Darashin tayi akan bar arha,sosai d'an juma ya yadda da wanna kalma da hausawa ke cewa,hakan yasa cikin full Confidence ya idasa gidan su".
Meenal ko ta gama Shan furar da d'an juma ya kawo mata har tayi shirin bacci ta kwanta d'an juma ya yi sallama ya shiga d'akin.............โ๏ธ
Idan kin karanta ki Comment sister๐๐
๐ MEENALYN DADDY ๐
๐๐
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION๐*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*โ๏ธยฉJ.A.W๐๐๏ธ*
Na
Fadila Sani Bakori.
page 12 & 13.
Meenal ko ta gama shan furar da d'an juma ya kawo mata har tayi Shirin bacci ta kwanta d'an juma ya yi Sallama ya shiga d'akin.
Mommyn meenal zaune ita da mahaifiyar d'an juma sai fira suke,d'an juma ya shiga.
D'an juma gaida hajiya Mariya yayi sannan ya ce"Dama alhaji ne ya ce in kira Meenal,kuma naga tama kwanta"."A'a ai ba bacci tayi bari in mata magana"cewar hajiya Mariya"
Hajiya Mariya sunan Meenal ta Kira,dan ta san ba bacci take ba.Meenal na jin haka ta ce"Mommy wai lafiya?"."Tashi za ki yi ku je alhaji na kiranki".Meenal ba tare da tayi wani alamu da ya nuna zata tashi ba ta ce"Mommy nikam gaskiya babu inda zani".
Hajiya Mariya kallan d'an juma tayi da ke sauraran su ta ce"Meenal ki tashi,idan kuma kink'i babu ruwana tsakaninki ne da alhaji,kinji dai abinda yace bazaki bar garin nan ba har sai kin sha addu'ar nan dan haka ki tashi kije ki sha tun wuri kinga dai kin kusa fara practical asibiti tom".Meenal wurgar da abinda ta rufa tayi ta ce" Wayyo wai me nayi ma alhaji ne da ya tsanan haka,mutum duk yabi ya ta kura rayuwata".Meenal ta idasa maganar tana sakkowa daga kan gadon batare da ta kuma cewa komai ba tayi hanyar waje da wani zin bulelan hijab blue black na Mommynta.
D'an juma fita ya yi ya bi bayanta.
Tsaye ya sameta ak'ofar gidan tana wani cin magani,d'an juma kallanta yayi ya ce"Mu je ko?".
Meenal kallan sama da k'asa tayi ma d'an juma sannan ta ce"Ba dai ak'asa ba ko ?"."Beauty mashin d'in na gidan sarki ".
Meenal kallan d'an juma ta kuma yayi sama da k'asa sannan ta ce"Kar in k'ara jin ka kirani da wannan sunan,dan kaga rannan ka kirani ban tanka maka ba shine yauma ka sake kirana da shi,karka sake !".
Kai d'an juma ya jinjina ya ce"Tom ranki shi dad'e bazan kuma ba".Meenal tsaki tayi tana wani yatsine fuska ,ta wuce.
D'an juma cikin wani irin sauk'i ya tsinci kan shi ganin yadda suka jera suna tafiya da Meenal,duk da ba magana suke ba,d'an juma so yake ya sanar da ita sak'on zuciyar shi amma kuma yana jin tsoro.Kallan Meenal yayi ta gefan ido ya ce" Hijab d'in nan yayi miki kyau".Meenal da katawa da tafiya tayi tana ma d'an juma wani irin kallo da ya kasa fassara mai kallan ke nufi.
Meenal ta dad'e tana tsaye tana kallan d'an juma tama rasa abinda zatace mai dan ita gani take rainine kamarta d'an kyauye na yaba kwalliyarta.Meenal da ta rasa abinda zata cema d'an juma sai cewa tayi"Malam yi gaba muje".Wato ma'ana subar jerawa tare"
D'an juma kallanta yayi ya ce"Don me tafiyar mu d'aya kuma zanyi gaba?".Meenal cikin d'aga murya kamar tana magana da wani sa'anta ko kuma k'aninta ta ce"Malam kaga ba wai so nake ina sa'insa da kai ba,kayi gaba nace bana son doguwar magana na shiga tsakanina da kai".
D'an juma murmushi yayi ya ce"Saboda me?,ko kina tsoran afkawa ne?".
Meenal ja tai ta tsaya tana kallan d'an juma dan gaba d'aya tama rasa abinda zatace mai,sai zuwa can ta ce cikin alamun b'acin rai"D'an asabe ka ke ko d'an me?,Ka tsarkake har shanka,kasan da wadda ka ke magana, ana cewa d'an kyauyan mutum dabba ne ban tab'a sanin haka ba sai yau,in banda tsabar dabbanci kai ni zaka cema ko ina tsoran zan abka ka ne".
Sosai kalaman Meenal zuka b'atama d'an juma rai,amma sai ya danne yaci gaba da tafiya ba tare da ya k'ara cewa komai ba.Ahaka suka shiga gidan sarki d'an juma najin zuciyar shi duk babu dad'in kalaman da Meenal ta yi mai"
D'an juma cikin sanyi yayi sallama da alamun 'yar damuwa a fuskar shi.Meenal zama tayi tana mai gaida sarki,alhaji ko kakanta ko kallo bai isheta ba.
Alhaji murmushi yayi ya ce"Ja'irar yarinya wato ni kad'ai ne bazaki gaida ba ko?,Ohoo addu'a ce dai sai kin shata ".
Meenal ba takanma alhaji ba bakin nan dai ta turo.Shi kuma alhaji ya ce"Sarki bata ta sha".
Sarki tashi yayi ya d'akko addu'ar ya mik'ama Meenal,ya ce"Yauwa Amina amsa ki sha da bismillah kin ji".
Meenal amsa tayi tana turo baki ta ce" Ni alhaji sai naje gida zan sha".
D'an juma da ke neman hanyar rama abinda Meenal tai mai yayi carab ya ce"Alhaji ban yarda ba ko taje ba sha za tai ba,tasha agabanka ka gani".
Meenal cikin d'aga murya ta ce"Waye kai!? Wa ke neman yaddarka?, kada Allah yasa ka yarda d'in,Shane kuma bazan sha anan ba d'in sai naje gida".
Alhaji kai kawai ya girgiza Ya ce"Amina amsa ki sha".Meenal baki ta turo ta ce"Alhaji nifa lafiyata lau da zaka ce aban addu'a,cama nayi ban da lafiya ne?"."Amina koma ma lafiyarki lau ki amsa kisha,dan ko ubanki yazo gunnan sai kin sha addu'ar nan yau".
Meenal kallan d'an k'ok'on da akai addu'ar aciki tayi,ita bawai bazata sha bane, taji ta hak'ura zata sha,tom amma kyankyamin abinda akai addu'ar take dama ita kanta addu'ar,hakan yasa bata son sha,amma gudin kar alhaji yaja su k'ara kwana ,dan ita gobe take tunanin zasu wuce.Meenal runtse ido tayi sannan ta d'aga addu'ar ta shanye.
Meenal da gudu ta fita saboda aman da yazo mata,hakan yasa ta ruga da gudu waje taci gaba da kwara amai,kamar zata amaye hanjin cikinta,dan hatta furar da tasha sai da ta amayeta tass"
D'an juma ko ganin Meenal ta fita da gudu tana rufe baki,yayi saurin mara mata baya,ganin yadda take aman yasa duk ya damu.
Zuk'unnawa yayi kusa ita kamar zai rik'eta yana jera mata sannu.
Meenal ko tsabar aman da tayi ne yasa cikinta ya murd'e,zuk'unnawa tayi awajan kamar zata kwanta awajan,tana rik'e cikinta.
D'an juma cikin damuwa ya ce"Sannu tashi muje chamise abaki magani".
Meenal da maganar ma ta gagareta saboda yadda cikinta ya murd'e ,banza tai da d'an juma taci gaba da murk'usanta .
D'an juma ganin haka sai yaga kamar cikin wani hali take,hakan yasa cikin rud'ewa yasa hannu zai d'agota shi da niyyar shi ya taimakamata.
Meenal da ta ga abinda d'an juma ke son ai katawa da sauri ta matsa tana d'aga mishi hannu ta ce"Karka kuskura ka tab'ani Malam,cema akai ban iya ta shine da zaka wani bud'e hannu kai gaka mai taimako mai tausai,Wallahi da ka yi gangancin tab'ani ,da ka yi da nasani".
Alhaji da Sarki da duk suna kallan abinda ya faru,da yadda d'an juma ya nuna kulawar shi akanta na son taimakonta amma k'arshe ta b'age da mai maganganu marasa dad'i.
Alhaji wato kakan Meenal cikin nuna rashin jin dad'in abinda ya faru ya kamo hannun d'an juma ya ce"Sannu ko Abdurrahman,Allah ya baka ladar niyar taimakon da kayi,rabu da ja'ira naga uban da zai taimakamata ta tashi".
Meenal jin abinda alhaji ya ce yasa ta tashi tana cewa"Ko da ban iya tashi da ya tadani gara in shekara agun kwance".
Sarki dai murmushi yayi ya ce" Abdurrahman jeka maidata gida,ku biya ka sai mata magani ".
D'an juma dai bai ce komai ba.Ya dad'e tsaye yana kallan Meenal yana yana jiran ta tashi su tafi.
Meenal sai da ta mila ta milmile sannan ta tashi,daga zuk'unnan da take,tayi hanyar waje batare da ta tankama kowa ba.
D'an juma kallan Sarki yayi ya ce" Bari in rakata indawo".
D'an juma bin Meenal yayi da tabi hanyar gida,alamun ta gane hanyar.Sunyi tafiya har sun kusa gida d'an juma ya kalli meenal ya ce" Mu biya chamise mana abaki magani".
Meenal ko kallan d'an juma ba tayi ba taci gaba da tafiyarta,ahaka suka isa gidan.Suna zuwa Meenal ta zube kan Mommynta tana sakin kuka sosai.Mahaifiyar d'an juma cikin damuwa ta ce"Yayan su lafiya me akai mata?".
"Inna ba ai mata komai ba".
Meenal tashi tayi tana harara d'an juma jin abinda ya ce ba ai mata komai ba,ta ce ma Mahaifiyar d'an juma "Dan Allah kima sarkin nan magana haka kawai zai tasani da dole sai nasha wata addu'a ni ce mai akai Banda lafiya ne,ni dai dan Allah ki mai magana".Mahaifiyar d'an juma cikin lalla shi ta ce"Ki yi hak'uri kinji Amina ki daure ki sha kinji ,ba'ama tsofaffi musu".Haka mahaifiyar d'an juma tai ta ba meenal baki.Mommyn Meenal dai bata tanka musu ba.
D'an juma ko tun tuni ya fice daga d'akin.Ba dad'ewa sai gashi ya dawo da kayan tea a hannun shi,Mahaifiyar shi ya mik'amawa ya ce"Inna gashi a had'a mata tea ta yi amai a gidan sarki".Hajiya Mariya kallan d'an juma ta yi,ta ce"Sannu da k'ok'ari Abdurrahman" .
D'an juma murmushi yayi ya fice daga gidan"
Washe gari,d'an juma yana d'akin shi da ke gidan Sarki,bayan ya kai ma su sarki abin Karin kumallo bayan sun karya ne,yaga shigar alhaji woto kakan Meenal ban d'aki.D'an juma d'akin sarki kakan shi ya shiga,zama yayi kusa da sarki ya ce"Sarki wai ya kake da alhajin nan ne?".
Sarki murmushi yayi ya ce"Abdurrahman Malam Abdullahi,a nan garin mahaifin shi ya kawo shi karatun allo,tun da aka kawo sai tamu tazo d'aya muka k'ula abota mai k'arfi dan so dadama nike biyamai alllan shi saboda na wuce shi akaratu.Abdullahi ya yi nisa akaratu sosai ya tafi kaduna ganin gida,tom dama muna karatu da shi yana yawan sanar da ni ba da son mahaifiyar shi yake karatun allon nan ba,ita fati son yayi agabanta,tom tun daga zuwannan ne dai bai koma ba.Sai dai duk da haka alak'armu na nan dan duk lokacin da ya samu dama yana zuwa nan,kaji alak'armu da shi abota ce,kuma sai shi yama fi ni rik'e amanar abotar,inda ni ban tab'a zuwa wajan shi ba shike zuwa wajena.Kaji alak'ata da shi".Shiru d'an juma yayi sannan ya ce"Tom naga kana ma yarinyar nan addu'a me ke damunta?"."Irin lallurarka ke damunta,yarinya kamar wannan ace bata son aure ,batama son ai mata maganar auran,kamar kai agari".Cewar Sarki.
Dan juma murmushi yayi ya ce" Sarki ni kam daga yau kafara lissafi dan na samu matar aure".Allah sarki sarki da babu abinda yake son gani kamar auran d'an juma cikin tsantsar farin ciki ya ce"Alhamdulilah,Allah ya amshi rok'on mu,Abdurrahman ina yarinyar take?" D'an juma kallan Sarki yayi ya ce"Ni ka d'ai ke sonta sarki ita bata sona,ni kuma ita kad'ai na tab'ajin sonta araina,har nakanji idan tak'ini bazan yi aure b..." .Sarki da sauri ya rufe bakin d'an juma ya ce"Haba Abdurrahman wannan wata irin magana ce,in dai ba sokake kasani adamuwa ba,karka sake furta kallmar baza kai aure ba dan Allah,yarinyar kuma insha Alllah zata soka,ko ko ita tace bata sonka da bakinta?".
Kai d'an juma ya girgiza ya ce"Ina fargabar sanar da ita ina sonta,dan bana tunanin zata amince min"."Shurman banza kenan,waya fad'ama namiji na karaya wajan furta so,ai wanna mace aka sani ba namiji ba,ka cire fargabar komai ka tun kareta kai tsaye, insha Allah zata soka,ka cire fargaba ,da rashin tayi akan bar arha" .
D'an juma kallan Sarki yayi ya ce"Ka yi min addu'a ta soni Allah idan tak'ini haka zan ci gaba da zamana bazanyi aure b...".Sarki da sauri ya k'ara rufe bakin d'an juma ya ce"Abdurrahman kabar furta kallamar nan, dan wata tak'ika sai ka ce baza kai aure ba,idan fa Allah bai tsara aure tsakanin ku da ita ba fa?,shikenan ba za kai aure ba,dan Allah kabar furtawa ,ganin auranka shine burina .Ayanzu haka babu abinda nake fatan Allah ya k'aramin tsawan rai in gani kamar matarka, Abdurrahman dan Allah kabar furta kallamar nan mai fad'ar min daga ba".
D'an juma ganin yadda sarki ya shiga damuwa,yasa ya kamo hannun shi yana murmushi ya ce"Kwantar da hankalinka bazaka mutu ba sai ka ga d'ana insha Allah,daga yau sai ka fara k'irga ranar aure na nan da watani kad'an musu zuwa".Sarki cikin jin dad'i ya ce"Allah yasa Abdurrahman ,dan baka tab'amin maganar aure ba sai yau,ko ba komai insha Allah nasan ko mai ya kusa zama tarihi".
D'an juma har ya fita alhaji bai shigo ba yana ban d'aki ".
B'angaran Meenal kuma ta hura ma mommynta wuta ita fa bazata kuma kwana garin nan ba daga gobe ba.
Meenal sai nai man wayar da zata Kira daddynta take babu,gashi wayar mommynta tunda ta bugata da k'asa ta d'auke,wayarta kuma M.T.N gareta batayi hausar cire Sim d'in mommynta ba tasa awayarta ba.Mommyn Meenal kuma ta hana mahaifiyar d'an juma taba Meenal wayarta ta ce ta ce mata bata da caji.Sosai Meenal ta shiga damuwa dan so take tai waya da daddynta ruwa ajallo.Tana nan tana tunanin ya za tai d'an juma yayi sallama ya shigo"
D'an juma da ledar kayan tea d'in Meenal hannun shi,ya mik'ama mahaifiyar shi,sannan ya gaida su,ya kalli Meenal ya ce"Sarki na kiranki".Meenal har zatace bazata ba,amma da ta tuno d'an juma na da waya zata ara ta kira daddynta batare da mommynta bama taji abinda zatace ba,hakan yasa ta tashi ta yafa d'an kwalin abayarta ta fita,d'an juma yabi bayanta shima.
Suna fita daga gidan Meenal ta kalli d'an juma ta ce"D'an aramin wayarka". "Ayyah nabadata caji amma idan na amso zan baki idan kuma kin matsu da yin kira idan mukaje sai ki amshi ta sarki kiyi amfani da ita".
Meenal shiru tayi sannan ta ce"Badamuwa idan ka amso nayi kiran".Meenal na fad'in haka ta juya zata tafi.D'an juma yayi saurin cewa "Sarki na kiranki fa nace"."Bazan je ba".Meenal na fad'in haka ta juya tayi ta fiyarta.D'an juma d'aga murya yayi ya ce"Bari inzo in cema Mommy kince bazaki ba".
Meenal da dowa tayi taja ta tsaya gaban d'an juma tana kallan shi,shima ita yake kallo.Meenal tsaki ta yi ta ce"Uhm dan Allah ka d'an taimakeni magana,Wallahi bazan iya shaba,kuma alhaji ya sa daddyana indai ban sha ba sai dai in ci gaba da zama kyauyan nan,ni koma gaskiya bazan iya shaba,dan Allah ka san abinda zaka ce mai ya baka ka kawomin".Shiru d'an juma yayi sannan ya ce"Tom Mommynki fa ai zataga biki shaba".Meenal ta ce"Ai idan ka amso zuwa zan rik'ayi da sunan zanje amsowa idan nagama zamana in koma".Murmushi d'an juma yayi ya ce"Shikenan sai anjima,bari inje in amso".
Meenal juyawa tayi ta shige gida tana jan tsakin takurata d'in da duk akayi".
D'an juma gidan Sarki ya koma yace ya bashi ya kai ma Meenal ,yaje ya isketa batajin dad'i.Sarki ba d'an juma yayi ya ce ya tabbatar ta sha.D'an juma na fitowa ya kurb'e addu'ar acewar shi ayar Allah ce,inda yasan ko ya kaima Meenal ba sha za taiba,zubarwa za tai"
Yau d'an juma da wuri ya dawo daga funtua,yayi wankan shi cikin wani brown d'in yadi,masha Allah sosai d'an juma yayi kyau ya shafe kayan shi da aribian oud.
D'an juma ya fito zai tafi gidansu,suka ci karo da sarki ya fito ban d'aki.
Sarki murmushi yayi dan indai kaga sauri ya d'au wanka da daddare tom ba sai ya fad'aba kasan inda za shi.Sarki da fara'ar shi najin dad'in d'an juma ya fara nai man aure ya ce" Abdurrahman daga ganin kwalliyar nan nasan gimbiyarka zaka gani".Murmushi d'an juma yayi yana mai jin wata irin fargaba ya ce"Sarki yau ne zan fad'ama yarinyar da nace maka ina so,tom ina fargaba ka tayani addu'a Allah yasa ta amince".Sarki hannun d'an'juma ya kamo ya ce"Bacin kayi addu'ar fita gida,ka karanta izaja'a,insha Allah zaka samu nasara".D'an juma cikin jin dad'i ya ce"Nagode ,bari in tafi" .
Sarki Kiran shi yayi ya ce"Bari in d'akkoma addu'ar Amina idan ka dawo wajan gimbiyartaka ka biya ka kai mata".
Sarki d'akin shi ya shiga ya d'akko addu'ar yaba d'an juma.
D'an juma amsa yayi ya tafi ,azuciyar shi yana cewa"Sarki wadda zan ba addu'ar nan ita ce gimbiyar tau,amma kai kanka fargabar sanar maka nake yi".
Haka d'an juma ya kama hanyar gidan su ,zuciyar shi na cike da fargaba"
B'angaran Meenal kuwa ta k'osa d'an juma ya shigo ya bata wayar shi ta Kira daddynta,dan jin shirun yayi yawa,yasa ta ce ma mahaifiyar d'an juma "Wai yau ba zai zo bane?".Mahaifiyar d'an juma da bata gane abinda take nufi ba,ta ce"Waye ba zai zo ba?" ."Wanda ke ....".Sallamar d'an juma ce tasa Meenal ta yi shiru............โ๏ธ
Idan kin karanta ki daure ki Comment Sister.
Share & Comment please๐๐ป๐๐ป
๐ MEENALYN DADDY ๐
๐๐
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION๐*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*โ๏ธยฉJ.A.W๐๐๏ธ*
Na
Fadila Sani Bakori.
Page 17 & 18.
Daddyn Meenal tashi yayi yazo inda Mahaifinshi yake ya rik'e k'afar alhaji ya ce" Alhaji dan Allah ka canza wani abun ba wannan ba,na yi ma Meenal alk'awarin ba zan mata auran dole