Showing 33001 words to 36000 words out of 47397 words
Chapter 12 - MEENALYN DADDY Complete Book By Fadila Sani Bakori.txt
..."Marin da D'anjuma ya yi ma Meenal ne yasa takasa k'arasa abin da tayi niyya, ta dafe gun dan har ganinta sai da ya d'auke.Meenal cikin azabar jin yadda taji Marin ta fashe da kuka,dan tunda take ba'atab'a mata mari irin wannan ba.Meenal cikin kuka ta kalli D'anjuma ta ce"Dan anta kurama mahaifina ya had'ani aure da kai shine kake ganin har ka isa ka d'aga hannu ka maran?Tom Wallahi Allah sai kasan ni ka mara ,kai ka yi kad'an ka maran mu had'u a kutu da ka .............
📚 MEENALYN DADDY 📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hDDDDD
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*⚜️©J.A.W📚🖌
Na
Fadila Sani Bakori
Page 31
"Dan an takura ma mahaifina ya had'ani aure da kai shi ne kake ganin har ka isa ka d'aga hannu ka maran? Tom Wallahi Allah sai ka san ni ka mara,mu had'u a kutu da kai!"Meenal na gama fad'in haka ta jawo mayafinta ta yafa tayi hanyar waje zata fita.
D'anjuma da sauri ya sha gaban Meenal ya tare mata hanya.Meenal kallan D'anjuma tayi da jajayan idanuta ta ce"Ka bani hanya in wuce!" Ina za ki?"D'anjuma ya tambaye ta.
"Ka ba ni hanya in wuce Malam!"D'anjuma cikin sanyi da kuma nadamar Marin Meenal d'in da ya yi ya ce"Ki yi hak'uri meenal raina ne ya b'ace yasa har nad'aga hannu na mare ki ,insha Allah haka ba zai k'ara faruwa ba"Wallahi sai na fita ,indai kaga na fasa fita a gidannan ,tom saidai in waya ka ban nayi waya da daddyna"D'anjuma dan asamu zaman lafiya yasa ya ciro wayarshi yaba Meenal.Meenal na amsar wayar ta bar gun ta Kira daddynta.
Mahaifin Meenal na kwance kusa da mahaifiyar Meenal kira ya shigo wayarshi,saidai mahaifin Meenal yana d'agawa yaci karo da kukan Meenal.Dan Meenal najin daddynta ya d'aga Kiran ta fashe da kuka.Daddyn Meenal jin kukan Meenal a firgice ya tashi daga kwancan da yake,cikin rud'ewa yake cewa"Meenalyn daddy yi shiru kimin bayani me ya yi miki?"Meenal k'in magana tayi taci gaba da kuka .Mahaifin Meenal cikin rud'ewa ya tashi daga kishingid'an da yake yana cewa"Meenal lafiya?Ko wani abun ya yi miki?"Still dai Meenal ba tai magana ba tana mai ci gaba da kuka .Aifa nan take hankalin Mahaifin Meenal ya yi k'ololuwar tashi,cikin rawar hanun ya mik'a ma Mahaifiyar Meenal wayar ,alamun tayi magana da ita.
Mahaifiyar Meenal itama cikin damuwa ta fara magana kamar haka"Haba Meenalyn daddy kinga kin tadama daddynki hankali nima kin tadamin,ki natsu dan Allah ki min bayani me ya faru da ke?" Meenal cikin kuka ta fara magana kamar haka"Mommy ki ba daddyna wayar!"Daddyn Meenal cikin k'osawa ya amshi wayar dan wayar a speaker take yaji abin da Meenal ta ce ,ya ce"Meenalyna inajinki fad'amin ya a kai?"Meenal cikin kuka ta fara magana kamar haka"Daddy dukana ya yi"Duka!?"Mahaifin Meenal ya mai-maita.
D'anjuma ko na zaune yana kallan Meenal yana jin sherin da tayi mai.Mahaifin Meenal kuma cikin tsantsar b'acin rai ya kashe wayar batare da ya iya cewa komai ba.Idonshi jajir ya kalli mahaifiyar Meenal ya ce"Kinga abin da nake gudu tun farko ko? Amma Alhaji yak'i fahimtata,ace yarinya kwananta d'aya har ya farasa hanu yana bugunta!"Tom daddyn Meenal kadai yi bincike sannan,ni gaskiya bana tunanin yarannan zai iya sa hannu ya bigi...."Cikin tsawa daddyn Meenal ya ce"Ya isa haka! Kina son kice sheri tayi mai ko? Yanzu ko kukan da Meenal keyi bai isa yasa ki gane gaskiyar abin da ta fad'a ba,tom Wallahi yarinya d'aya bazan d'auka ba!"Daddyn Meenal nagama fad'in haka ya kashe wayar ya d'auki key d'in motarshi ya yi hanyar fita,da sauri Mommyn Meenal ta sha gabanshi ta ce"Haba daddyn Meenal da wowarka kenan fa! Ina zaka kuma?"Da yake da wowar daddyn Meenal kenan daga gudun auran Meenal da ya yi."Funtua zani"Ya bata amsa."Funtua kuma daddyn Meenal ? Me za kai a Funtua kuma?"Daddyn Meenal ba tare da yaba Mommyn Meenal amsa ba ya yi tafiyarshi.
Daddyn Meenal misalin k'arfe 2:00Pm ya shiga cikin garin Funtua.
Meenal ko dama tanajin daddynta ya kashe wayar
tasan wajanta zaizo,dan tasan wannan kukan da tayi ba zai lamince shi ba,gashi rashin cin abincin da bataiba yasa ta kuma zama wata iri idan ka ganta sai ka yadda da abin da tace.
Daddyn Meenal number D'anjuma ya kira. D'anjuma ko lokacin ya fita gidansu kenan ya hau mota zuwa Funtua.yana gaf shiga gida Kiran daddyn Meenal ya shigo mai .D'anjuma na d'aga Kiran daddyn Meenal ya ce"Gani a Jabiri ina ne gidanka?"D'anjuma shiru ya yi ,sannan ya ce"Daddy gani nima kusa da Jabirin bari in k'araso"D'anjuma na sauka a mota ya hango motar daddyn Meenal,k'arasawa ya yi kusa da motar .Cikin girmamawa D'anjuma ya gaida daddyn Meenal, amma ciki-ciki daddyn Meenal ya amsa mai ya ce"Muje gidan".D'anjuma shiga cikin motar ya yi yana nuna ma daddyn Meenal hanya har suka isa k'ofar gidan.Tare suka shiga gidan,Meenal ko najin sallamar daddynta ta fashe da kuka tana rik'e ci dan dama yunwa take ji kuma har yanzu bataci komai ba.
Daddyn Meenal da saurinshi jin kukan Meenal ya idasa shiga d'an madai-daicin falon nasu.Yana zuwa cikin tashin hankali ya tarbo Meenal yana cewa"Meenalyna meke damunki?"Meenal cikin kuka ta ce"Daddy yunwa nake ji mutu zanyi daddy!"Daddyn Meenal kamar zai yi kuka ya ce"Ba za ki mutu ba Meenalyn daddy"Meenal cikin kuka ta ce"Daddy gida ka kaini gida "Daddyn Meenal tada Meenal yayi ya ce"Tom ki yi shiru tashi mu tafi"Meenal tashi tayi daddynta na rik'e da ta suka fita daga gidan D'anjuma na kallansu ya kasa cewa komai har suka b'ud'e mota suka shiga suka tafi ........
📚 MEENALYN DADDY📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hDDDDD
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*⚜️©J.A.W📚🖌
Na
Fadila Sani Bakori
Page 33 & 34
"Sani in dai ni na haifeka,kuma na isa in fad'ima kaji,tom Amina ta tashi tabi mijinta su tafi"Daddyn Meenal kafin ya yi magana Meenal ta fashe da kuka ta ce"Daddy Wallahi ni bazan bishi ba!"Daddyn Meenal cikin sanyi ya fara lallashin Meenal ya ce"Meenalyna ki yi hak'uri ku tafi dan Allah"Meenal tashi tayi tayi shigewarta ciki ta barsu Daddaynta a nan.
Alhaji cikin fushi ya kuma cewa"Sani kaima Amina magana yamma fa tana yi!"Daddyn Meenal tashi ya yi ya shiga d'akin Meenal d'in ,kwance ya sameta tana kuka.Daddyn Meenal k'arasawa ya yi ya kamo hannun Meenal d'in cikin lallashi ya ce"Meenalyn Daddy ki yi hak'uri ki koma kinji nan da lokaci kad'an ni zansa yadda za ai auran ya mutu ma gaba d'aya dan nima ba san auran naki nake ba, fad'amin yanzu meye damuwarki a komawar?"
Meenal tashi tayi tana kallan Daddynta ta ce"Daddy ni fa bana iya cin abincinsu"Tom Meenalyna ba sai ki taida shi daga nan ba"Meenal tashi tai tana goge hawayanta ta ce"Daddy Allah indai ka matsamin na bishi tom Allah bana k'ara cin komai har yunwa ta kasheni in huta!"Daddyn Meenal cikin damuwa da jin abin da Meenal ta ce ya ce"A'a haka ma ba zai faru ba,yanzu inda har kin furta haka bari in je in ma Alhaji magana muji ya za ai"
Daddyn Meenal falon ya koma ya kalli Alhaji ya ce"Alhaji kasan rigimar Meenal nayi-nayi tak'i Wallahi,k'arshe abin tashin hankali cewa tayi "In dai na matsa mata ta tafi tom bata k'ara cin abinci yunwa ta kasheta ta huta,tom Alhaji kasan Meenal ba hankaki gareta ba zata iya aikata haka,dan Allah inda abin yazo da haka yayi hak'uri ya tafi ni zan san yadda zan yi in kaita da kaina dan Allah Alhaji"Daddyn Meenal ya idasa maganar kamar zai yi kuka.
Alhaji magana zai yi D'anjuma ya rigashi da cewa"A'a Alhaji babu komai ta zauna d'in kamar yadda Daddy ya ce idan ta yadda sai ya kawota nan gaba"Alhaji kai ya girgiza ya ce"A'a Abdurrahman baza ai haka ba,ni na san wacece Amina dan haka ta fito su tafi bana son shashansci kafin ranka ya b'ace kai da ita yanzun nan!"Abin mamaki kawai sai ga Daddyn Meenal ya zube ak'asa ya yana rok'on Alhaji yana cewa"Alhaji dan Allah kaimin wani taimaka inda Meenal ta riga ta tsani zaman garinnan nina san bazata tab'a kwantar da hankalinta ba,ni indai babu damuwa zan ba shi gidana da ke nan su zauna, kamar za tafi kwantar da hankalinta anan"Alhaji shiru ya yi sannan ya ce" Tom Abdurrahman kaji abin da Sani ya ce? Zaka iya aje Aminar anan Allah bashi shi da ya tsara hakan sai ya rik'a baka kud'in mota duk lokacin da ka buk'aci zuwan"Shiru D'anjuma ya yi sannan zuwa can ya ce"Shikenan Alhaji indai zamanta nan d'in zata kwantar da hankalinta ai ba komai bane"Masha Allah ,Allah ya yi maka albarka ,tom yanzu shi can gidan an gyara shi ne?"Alhaji ya tambayi Daddyn Meenal.
"Eh Alhaji a gyare yake dan kusan wata biyu kenan ma nasa komai a gidan ,dan tun lokacin da akai maganar nasa komai da niyyar hakan tom amma kuma sai Mariya ta hanani sai da Meenal ta b'ullo da haka na tuna da gidan" Tom ai shikenan yanzu saika d'aukesu ka kaisu gidan"
Daddyn Meenal bedroom d'in Meenal ya shiga,kwance ya sameta kamar yadda ya barta, kallan Meenal d'in yayi ya fara magana cikin lallami ya ce"Meenalyna kinga Alhaji ya matsa sai kinbi d'an'iskan yarannan dan haka kiyi hak'uri yanzu naima Alhaji magana zaku zauna a gidana da ke nan Tudunwada"Meenal tura baki tayi ta ce"Daddy nifa ko inane bazan zauna da shi ba "Daddyn Meenal zama ya yi yana kamo hanun Meenal d'in ya ce"Haba Meenalyn Daddy yanzu idan na koma nace ma Alhaji haka ai bazai yadda ba, cewa ma zai sai kin koma can Funtuwan ma,amma kinga idan ki kai hak'uri ki ka zauna can Tudunwadan ahankali-ahankali sai in kashe auran ma baki d'aya"Haka Daddyn Meenal ya yi ta lallab'a Meenal da kyar ya samu ta yadda ta tashi suka tafi.
Driver Alhaji mai dashi gida ya yi inda shi kuma Daddyn Meenal d'in ya d'auki Meenal da D'anjuma a mota suka nufi Tudunwada,ko a mota Daddyn Meenal kallan D'anjuma yayi ya ce"Kai D'anjuma ka gane ko Meenal yarinya ce dan haka indai kana son zama da ita dole za kai hak'uri da ita,dan muma hak'uri muke da ita ,in banda abin ka ma Meenal nawa take da har zaka wani d'aga hannu ka mareta,in ban da kai ba lallab'ata za kai ba ku zauna lafiya inda kaga dai yadda akai auran nan ba sonka take ba matsawar Alhaji ce,ai duk abin da tace bi za kai asamu ta hak'ura ta zauna,amma dan shashanci irin naka shine zaka mareta,waya cema irinsu Meenal haka ake musu ai lallab'ata zakai ku zauna lafiya"Haka Daddyn Meenal yayi ta yima D'anjuma nasiha akan ya lallab'a Meenal su zauna lafiya har suka isa gidan nasihar kenan.
Gida ne mai kyau dan dai bai kai wanda su Meenal suke ciki ba.Daddyn Meenal har falon ya kaisu sannan ya kalli Meenal ya ce"Tom Meenalyna zan tafi?"Meenal turo baki ta yi ta ce"Daddy Kayan sawana fa? Banda kaya fa?"Tom ki yi hak'uri gobe zan siya miki in kawo miki"Haka dai Daddyn Meenal ya tafi yana mai lallab'a Meenal kamar wata 'yar jinjira.
D'anjuma ko zama ya yi yana mai tunanin yadda zai b'illo masu Meenal ,tabbas yana son Meenal tom amma a yanzu ya fara tunanin hak'ura da ita,amma kuma yana tunanin in ya ce zai saki Meenal tom bai kyauta ma Alhaji ba.D'anjuma na nan zaune sai tunane-tunane yake har aka kira Sallar La'asar sannan ya fita yaje ya yi sallah ya dawo.
Meenal ko dama tun da suka shigo tai shigewarta ciki tabar D'anjuma a nan falon shi kad'ai.D'anjuma na nan har akai sallar Magriba,fita ya yi bashi ya dawo ba saida yayi sallar Isha'i a can, sannan ya je wani restaurant da ke kusa da masallacin yaci abinci. Har zai sema Meenal sai kuma ya tino mutuniyar tashi zata iya cewa wani abun take so,hakan yasa ya fasa ya dawo.D'anjuma bedroom d'in Meenal ya shiga,kwance ya sameta tana danna wayarta da Daddynta ya amsa ya bata.D'anjuma da sallamarshi ya shiga,amma Meenal ko sallamarshi bata amsa ba bare kuma yasa ran zata d'ago ta kallai.D'anjuma zama ya yi gefan gadon,sannan ya ce"Kin yi sallah ko?"Meenal banza ta yi da D'anjuma,shi kuma bai gaji ba ya kuma cewa"Amina na ce kin yi sallah ko?"Meenal cin jin zafin ya dameta ta tashi a fad'ace ta ce"Ban yi ba,kasanni Kristen ce bana sallah!"D'anjuma fisge wayar hannun Meenal ya yi ya ce"Tom ki tashi kiyi sallah sannan kici gaba da danna-dannan wayar taki"Ka ban wayata Malam!"Ba zan baki ba sai kin yi sallah"Meenal cikin tsiwarta da tashan rashin kunya da take yi ta ce"D'anjuma ka ke ko D'an'asabe kaban wayata Wallahi kafin raina ya b'ace!" D'anjuma da sosai yake jin zafin duk lokacin da Meenal ta kirashi da D'anjuma yake ko D'an'asabe,duk da itama Meenal lura da yana jin zafin hakan ne yasa take kiranshi da sunan.D'anjuma juyawa ya yi ya fita ya ce"Idan kin yi sallah ki zo ki amsa,sannan me zaki ce in siyo miki?" Har'abada ni Meenal bazanci abin da yafito daga hannunka ba, sannan kaban wayata wannan ma ai salan sata n...."Jawowar da D'anjuma ya yi ma Meenal ce tasa ta yi shiru,D'anjuma kuma cikin d'aurewa da nuna tsantsar b'acin ranshi ya ce"Wallahi koda wasa kika kirani b'arawo saina fasa bakinki!" Sannan ya saketa ta fad'i.Shi kuma ya fita d'akin ranshi b'ace sosai.
Meenal gyalanta ta d'auka zata fita.D'anjuma na zaune yana kallanta ya ce"Amina karki fita daga falon nan!"Meenal wani mugun kallo taima D'anjuma sannan ta ce"Ko a gidamu abin da nake so nake yi dan haka kai baka isa kahanani yin abin da nai niyya ba"Meenal na fad'in haka tasa kai tayi tafiyarta ita ala dole gida zata koma saboda ya yi mata tsawa ya amshe wayarta ya ce sai tayi sallah.
Meenal ta kama k'ofar gidan zata fita D'anjuma da gaba d'aya yake jin Meenal d'in ta na naiman fice mai arai dan shi mutum ne mai fushi.D'anjuma fusgo Meenal yayi ya jata ya maida ta falon ya wurgata kan coution d'in ya ce"Haba Amina ke wata irin yarinya ce ,ace tun da na aureki na rasa sukuni,shin so haukane?Koko dan nace ina sonki shine kike ganin kinsamu damar da zaki wulak'antani! Taya zaki rik'a zuyani kamar d'anki! Kin taho nan Kaduna bada izinina ba ko sanina,na kwaso jiki na biyoki ,kince bazaki koma garinmu da zama ba na yadda zan zauna inda kike so ko hakan zaisa asamu zaman lafiya amma duk da haka haka bai miki ba yanzu kuma kin kuma tada wata rigimar tom ya ki ke so in miki?"Meenal kallan banza taima D'anjuma sannan ta ce"So nake kasakan shikenan sai ka samu sukunin zuciya "Amina tabbas ina sonki amma bacin halaccin Alhaji agareni da nake dubawa da Wallahi tun tahowarki zan sake ki tom Amma Alhaji ya yi min halacci sosai a auranki"Meenal tsak'i tayi ta ce"Ni bana son ina doguwar magana da kai, matsamin in wuce dan tunda nasa ran fita agidan nan Wallahi bazan kwana ashi ba!"Meenal na kuma fad'ar haka ta kuma tunkarar k'ofar zata fita .
D'anjuma hannu yasa ya d'auki Meenal ya yi cikin gidan da ita.Meenal ko haka ta dake tana zaginshi tana cewa"Allah ya isa tunda ka sa k'azamin hanunka ka d'aukeni ".D'anjuma ko bai dire Meenal a ko ina ba sai bedroom d'inta, yana direta ya ce"Ni kike ma Allah ya isa !Kina kirana k'azami ko?"Meenal cikin tsantsar ranshin kunyarta ta ce"Eh d'in ,ance Allah ya isan k'azami kawai"
D'anjuma fisgo Meenal ya yi sannan ya had'e bakin shi da nata yana tsoso yana k'ara d'ura mata miyan bikinshi abakinta saboda k'azamin da ta kirashi.D'anjuma sai da ya gaji dan kanshi sannan ya saki Meenal da ta fashe da kuka tana mai goge bakinta tana cewa"Allah ya isa banza d'an k'yauye ! Mai tabi'ar dabbobi!"D'anjuma da duk yadda yaso ya danni zuciyarshi ya yi hak'uri kasawa ya yi ,rasa hukuncin da zaima Meenal ya yi.Jawota ya yi yana cewa"Zan nuna miki tabi'ar dabbobi"
D'anjuma na fad'in haka ya fincike d'an kwakin kan Meenal sannan ya fara k'ok'arin cire kayan jikinta.Sai da D'anjuma ya cire komai na jikin Meenal .Da farko tana zaginshi da taga abin ya yi nisa ta fara bashi hak'uri.Amma D'anjuma bai saurareta ba,sai da ya gama ya cire na jikinshi sannan ya ya d'auketa tana ihu ya d'orata kan kadon ya na ce mata cikin kunnanta "Zannuna miki t'abi'ar abbobi yanzun nan"Meenal ganin D'anjuma da gaske yake ta ce"Wallahi idan har kayi kuskuran min wani abu zaka had'u da fushin Daddyna dan Wallahi ba zai k'yaleka ba"Meenal ta fad'i maganar cikin kuka da tashin hankali ."Ni da kayana ,zan yi yadda nake so dake babu abin da Daddynmu zai min"D'anjuma na fad'in haka bai k'ara ba Meenal wata damar yin Magana ba sakamakon had'e bakinsu da ya yi.Meenal naji nagani haka D'anjuma ya amshi hak'inshi ta k'arfin tsiya.........
Idan kin shirya siye kiyi hanzari free pages ya kusa k'arewa sister.
Number marubuciyar
08063830828
📚 MEENALYN DADDY 📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hDDDDD
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*⚜️©J.A.W📚🖌
Na
Fadila Sani Bakori
Page 35
Asubar fari kukan Meenal ya farkar da D'anjuma daga bacci.D'anjuma cikin kulawa ya kamo Meenal yana cewa"Ayyah yi hak'uri Meenalyna ki bar kuka haka dan Allah kar kanki ya yi ciwo"Meenal hanun D'anjuma ta bige da ke rik'e da ita ta samu ta yunk'ura ta tashi ta shiga toilet d'in t ta yi wanka.Meenal har tayi wanka ta gama tana kuka.
B'angaran D'anjuma kuma bai kuma komawa ta kan Meenal ba sai da ya kimtsa jikinshi shima ya yi wanka ya yi sallah sannan ya dawo inda Meenal take har yanzu tana mai ci gaba da kukanta.D'anjuma cikin sanyi ya kamo hannun Meenal d'in ya ce"Amina dan Allah kiyi hak'uri da kukan