Showing 39001 words to 42000 words out of 47397 words
Chapter 14 - MEENALYN DADDY Complete Book By Fadila Sani Bakori.txt
sani rigima zatasa sai ta zubar da shi,yanzu haka tana kan hanyar zuwa wajan ki ki dubata,dan Allah ko ta zo ki sanar da ita wani abun daban karki sanar da ita labarin cikin"To Mommyn Meenal haka za ai sai ta zo d'in"
Meenal na zuwa Asibitin wajan Doctor Hafsat ta je,tana zuwa bayan sun gaisa ,Meenal ta yi mata bayanin abin da ke damunta.Bayan ta duba Meenal ne ta kalleta ta ce'Meenal shawara ce ta yi miki yawa da sanyi shike d'auke jinin hailan ki,sannan ki bar shan maik'o da zak'i"Sannan ta bata magungunan da duk ta b'anb'are bayansu dan kar Meenal d'in taga sunan su.
Meenal bayan ta dawo gida kallan Mommyn ta yi ta ce"Mommy kinji wai sanyi ne ya sa bana ganin period d'ina"To ai saki dage da shan magungunan da aka baki"
Haka rayuwa taci gaba da tafiya inda Meenal har cikin ta ya shiga wata na shida .Kuma har yanzu Daddyn Meenal na Asibiti jinyar Alhaji. Jikin Alhaji sai ya yi kamar ya ji sauk'i sai ciwan ya tashi.Daddyn Meenal ko kasan cewar yana cikin damuwar ciwan Alhaji ya sa ko Meenal d'in ta je Asibitin bai fargaba da cikin jikin ta, da yake kuma Meenal d'in ba mai girman ciki ba ce.
B'angaran D'anjuma ko lokaci zuwa lokaci yana Kiran Mommyn Meenal su gaisa.
Yau ya kama juma'a kuma yau ne ciwan Alhaji ya yi zafi sosai.K'arfe 10:00AM Allah ya yi ma Alhaji cikawa.Meenal ko na kwance kullum abin tsoro yake bata dan wata biyu kenan tana lissafi da fara jin motsi a cikin ta.Meenal zaune ta samu Mommyn ta a falo,kwanciya Meenal ta yi tana d'ora kanta kan cinyar Mommyn ta ta ce cikin damuwa"Mommy Daddy zan kira in sanar da shi Wallahi banda lafiya,sannan kusan wata biyu kenan abu na min yawo a ciki"Meenal tashi ta yi ta zauna tana d'aga rigarta ta ce"Mommy dubi fa kiga yadda cikina ya yi girma ni kam nafara jin tsoran kar inje wani mugun ciwan ne,sannan Mommy har yanzu fa bana ganin period d'ina"Meenal ta fad'i maganar tana share hawayanta.
Mommyn Meenal da Meenal ta bata tausai sosai kallan Meenal ta yi ta ce"Meenalyna ki kwantar da hankalin ki kinji Insha Allah babu wani mugun ciwo da ke damunki"Meenal fashewa da kuka ta yi tana cewa"Mommy Wallahi mugun ciwo ne koma meye nifa kad'ai nasan yadda nakeji,dan haka Wallahi fad'ima Daddyna zanyi"Meenal ta fad'i maganar tana mai jawo wayar ta za tai Kira Daddyn ta.Saidai kafin ta Kira Kiran Daddyn ta ya shigo wayar ta.Meenal d'agawa ta yi tana murmushi ta ce"Mommy ga Daddyn ma na kirana"
Meenal jin kukan Daddyn ta hankalin ta ya tashi sosai.
Daddyn Meenal cikin kuka ya sanar da Meenal rasuwar Alhaji yanzun nan.Allah sarki Meenal itama k'ara volume d'in kukan ta ta yi jin abin da Daddyn ta ya ce.
Haka dai suka gama kukan su suka yi shiru.Kasan cewar ba wani nisa tsakanin su yasa cikin lokakaci aka iso da gawar Alhaji.Haka aka yi Zana'idar Alhaji a gidan Daddyn Meenal aka kai shi gidan shi na gaskiya.
Sosai mutuwar Alhaji ta bugesu dukkan su.Ana gobe addu'ar uku ne Mommyn Meenal ta samu Meenal a bedroom d'inta tana kwance ta ce"Meenal ki tashi ina son za muyi wata magana ne"Mommy ki fad'a haka ina jinki"Yauwa Meenalyna dama cewa nayi kinga Daddyn ki yana cikin damuwa ta rashin Alhaji bai kamata ki b'ullomai da maganar ciwan nan naki ba,hakan zai k'ara d'aga hankalin shi,shine na ce ki shirya muje in samu doctor Hafsat muje ai miki scanning da duk abin da ya kamata aga abin da ke damun ki"Meenal cikin gamsuwa da abin da mommyn ta ta ce ta ce"To Mommy yau she zamu tafi?"Ki bari sai gobe bayan anyi addu'a sai mu tafi"
B'angran D'anjuma ko tun yana ma Manaifiyar shi k'arya akan Meenal har ya fito ya fad'i mata gaskiyar zamansu da Meenal d'in da komawarta gidan Iyayan ta, dan ta kwantar da hankalin ta ya ce"Mommy ai aure ma nake Shirin yi"Ita dai bata tanka mai ba.Muta nan k'yauyan ko haka su kaita gulmar maganar wai yaje ya d'akko 'yar masu kud'i Allah ya k'ara bai ga komai ba ma.kowa dai da abin da yake cewa.
Yau ya kama kwana uku kenan da rasuwar Alhaji.kuma yau ne D'anjuma ya shirya zuwa musu gaiduwa ,shi da kakan shi abokin Alhaji suka so zuwa to shima jikin sai a hankali hakan yasa D'anjuma ya taho shi ka d'ai.
Addu'a ko dama a masallaci aka yi ta.Daddyn Meenal yaje raka wasu abakon shi ne D'anjuma ya iso.D'anjuma na zuwa ya Kira Mommyn Meenal ya sanar da ita yana k'ofar gida.'Haba Abdurrahman ka shigo ciki mana"Mommyn Meenal falan Daddyn Meenal ta saukar da D'anjuma.Daga Meenal har Daddyn ta ba su san da zuwan D'anjuma ba.
Bayan D'anjuma sun gaisa da Mommyn Meenal ne ya yi mata gaisuwa ,sannan Mommyn Meenal ta ce"Abdurrahaman dama na dad'e ina son muyi wata magana da kai,mutu miyartaka fa ciki gareta har na tsawan wata shida,dan yana gaf da shiga wata bakwai ma"D'anjuma da mamaki ya ce"Ikon Allah,Da fatan tana lafiya ko Mommy?"Ya fad'i maganar yana duk'ar da kai."Tana lafiya klau Abdurrahaman,bari in turo maka ita"Mommyn Meenal na fad'in haka ta tashi, bedroom d'in Meenal ta nufa tana zuwa ta sameta kwance.Mommyn Meenal kallan Meenal ta yi ta ce"Wai Meenal bana hanaki yawan kwanciyar nan ba? Wallahi in dai biki bar yawan kwanciyar nan ba babu ruwana za ki ji a jikin ki,ki tashi ki shirya kije falon Daddyn ki da akwai b'ak'o zaku gaisa"Meenal kallan Mommyn ta tayi tana turo baki ta ce"Mommy su waye?"Ki je in kinje kin gani'Meenal tashi ta yi ta tafi tana turo baki.
Zaune yake kanshi ak'asa yana al'ajabin cikin Meenal .Meenal a hankali ta yi sallama ta shigo falon,har ta zauna bata lura da D'anjuma bane zaune,ta bud'e baki zatai magana suka had'a ido da D'anjuma.Meenal tashi ta yi ta sauri tana nuna D'anjuma ta ce"Dama kai ne?"Murmushi D'anjuma ya yi mata ya tashi zai zo in da take tsaye.Meenal juyawa ta yi da sauri zata fita ,D'anjuma ya cin mata da sauri ya sha gabanta yana mai rungumota ya ce"Haba Maman twins kar ki min asaramana"Meenal bige hannun D'anjuma tayi da ke shafa cikon ta ta ce"Da Allah can Malam kasakan kafin in maka rashin mutunci!"D'anjuma rufe bakin Meenal ya yi da hannu ya ce"Amina dan Allah ki bar rashin kunya da d'ana acikinki karki sa d'ana ko 'yata su yi gadon rashin kunyar ki,ki bari idan kika haifa min d'ana sai ki ci gaba da rashin kunyar ki"Meenal cikin jin zafin yadda D'anjuma ke ci gaba da sha cikin ta ta ce"Malam ka sakan da Allah can,d'a kuma ko 'ya da kake magana Allah ya sawak'e min had'a jini da kai"D'anjuma cikin murmushi dan maganganun Meenal d'in basa bashi haushi ko murnar cikin ce oho ya ce"Ni dai na fad'a miki ki bar min rashin kunya da d'ana acikin ki yarinya"Meenal cikin jin haushi ta ce"Sakanni Malam"Ki barni inji d'umin d'ana"Meenal kokwawar k'acewa take daga hannun D'anjuma ta kasa,ana cikin haka ne Daddyn ta ya shigo.D'anjuma da sauri ya saki Meenal.Daddyn Meenal kuma cikin jin haushin D'anjuma ya ce"Abin da kai mata bai isheka bane ka biyota nan!"D'anjuma cikin jin kunya ya sadda kan shi k'asa yana gaida Daddyn Meenal tare da ta'aziya.Daddyn Meenal sama-sama ya amsa ma D'anjuma.Meenal kuma dagewa ta yi tana kuka ta ce"Daddy ka ce ya fita bana son ganin shi"Daddyn Meenal cikin rufe ido da manta D'anjuma surikinshi ne ta'aziya ya zo mai ya ce"Fita kar in sake ganin ka a gidana in har ba takardar Meenal ka zo kawo min ba!"D'anjuma sosai ya ji zafin abin da Meenal taimai da Daddyn ta ya ce"Zan fita insha Allah ba zan sake zuwa ba har sai ranar da na zo amsar d'ana ko 'yata"Meenal kuka tasa tana cewa"Daddy kana jin fatan tsiyar da yake min ko?"Daddyn Meenal cikin tashin hankali ya mai da kallan shi ga Meenal,da sauri ya k'arasa kusa da ita yana cire k'aramin hijab d'in da ke jikinta Wanda Mommyn ta sata sawa saboda gudin Daddyn ta kar ya lura da cikin dake jikin Meenal d'in .D'anjuma juyawa ya yi ya tafi ya barsu.
Daddyn Meenal cikin tashin hankali ya ke kallan Meenal ya ce"Meenalyna me yasa biki sanar da ni ba?"Meenal cikin rashin fahimta ta ce"Daddy me?"Daddyn Meenal da ya lura Meenal bata San tana da ciki ba,waya ya ciro ya Kira Mommyn Meenal d'in ya ce ta samai a falon shi.
Mommyn Meenal zuwa ta yi cikin sauri jin muryar Daddyn Meenal kamar yana cikin fad'a.Mommyn Meenal na shiga falon Daddyn Meenal ya nuna mata Meenal dake tsaye ya ce"Mariya kina nufin biki san da cikin jikin Meenal ba ne ? Koko kin yi k'ok'arin b'oye min ne dan Meenal ta koma gidan shashasah yaran can ne!,to Wallahi in kin yi hakane kin yi a banza dan cikin jikin Meenal ba zai kwana ajikinta ba"Yana gama fad'in haka ya kamo hanun Meenal d'in da tashin hankali ya sa ta kasa cewa komai sai kuka.........
Fadila Sani Bakori ce.
📚 MEENALYN DADDY📚
Page 39
Daddyn Meenal na rik'e da hannun Meenal tana kuka har suka k'arasa bakin motar shi suka shiga suka tafi mommyn Meenal na kallo ta kasa cewa komai.Suna shiga cikin asibitin Daddyn Meenal office d'in shi ya yi da Meenal ,sannan ya nuna mata wani d'aki da ke cikin office d'in ya ce"Meenalyna ki shiga d'akin can ina zuwa"Meenal da gaba d'aya jikin ta ya yi sanyi tashi ta yi ta shiga d'ikin.Meenal na nan zaune Daddyn ta ya shigo da allurai da da wani dogon k'arfe mai lank'wasa sai kuma wani mai kamar scissors mai baki biyu shima.Daddyn Meenal d'an k'aramin gadon da ke d'akin irin na masu haihuwa ya nuna ma Meenal ya ce"Meenalyna kwanta nan ko?"Meenal kallan Daddyn ta ya yi kamar za tai kuka ta ce"Daddy wa'innan k'arfunan fa ?Me za ai da su?"Daddyn Meenal cikin kwantar ma Meenal da hankali ya ce"Meenalyna ki kwantar da hankalin ki kinji?Kinga cikin ki ya yi k'wari dole idan anyi allurar nan sai an burke shi sannan ajawo shi a fidda shi"Meenal cikin allamun tsoro da jin abin da Daddyn ta ya ce ta ce"A'a Daddy ni dai tsoro nake ji kai min allurar kawai"Meenalyn Daddy allura kawai bazatai miki ba saboda cikin ki ya yi kwari ko an miki allurar sai anyi miki wankin ciki"Meenal da sosai ta rud'e ganin k'arafunan tashi ta yi ta ce"Daddy ni dai na fasa indai allura ba za tai ba "Daddyn Meenal rik'o hannun Meenal ya yi ya ce"Meenalyna allurar da kike so idan nayimiki sai tafi wahalar da ke"Meenal fa haka ta burkecema Daddyn ta dan ganin k'arafan nan sosai ya birkitata hakan ya sa ta birkice ma Daddyn ta.Babu irin lallashin da baimata ba amma tak'i,dole ya hak'ura ya kyaleta yana kallan ta ya ce "Meenalyna kin hak'ura zaki haifi abin da ke cikin ki kenan?"Meenal kamar zatai kuka ta ce"Daddy ni dai tsoro nake ji"Daddyn Meenal baison matsama Meenal ganin duk ta furgice hanun ta ya koma ya ce"To tashi muje gida"
Mommyn Meenal na zaune tana ta tunanin zubar da cikin Meenal d'in Daddyn Meenal zai yi ,sai jin sallama ta yi ya shigo shi da Meenal.Momnyn Meenal cikin sanyi ta kalle su ta ce"Daddyn Meenal har an zubar da cikin ne?"Daddyn Meenal hararar Mommyn Meenal ya yi ya ce"Oho ko ba a zubar ba Meenal bazata shayar da abin da zata haifa ba kuma bazata raine shi ba a ranar da ta haifai zan d'auke shi da kaina in kai ma d'an iskan yaran nan d'an shi ko 'yar shi,dan Wallahi ba zai wahalar min da Meenalyna ba wajan raino, saidai shi ya yaraini abin shi ko ya ba uwarshi ta rainan mishi"Meenal ko jin haka kuka ta fasa,da sauri Daddyn ta ya rik'o hanun ta ya ce"Meenal ya a kai kuma?"Meenal cikin kuka ta ce"Daddy ni dai bana son in haihu"To Meenalyna ki yi hak'uri kinji muje a cire cikin?"Meenal kafad'a ta mak'e ta ce"Ni ai tsoro nake ji"Daddyn Meenal ganin ta furgita da ganin k'arafan da ta yi ya sa ya ce"Meenalyna ki yi hak'uri kin ji inda kin k'i yadda a zubar da cikin daga kin haihu zan kai mai d'an shi yasan yadda zai yi da shi"Meenal haka ta tasa Daddyn ta da kuka ita bazata haihu ba kuma ita tana tsoro a cire cikin.Haka dai Daddyn Meenal ya yi ta aikin lalla shi.
Tun daga ranar fa Meenal kullum haka zata tasa Daddyn ta da kukan bata tason ta haihu .Haka dai zaita aikin lallashi a haka har ta shiga watan haihuwa.
Yau ya kama Litinin Daddyn Meenal na wajan aiki.Misalin k'arfe goma na safe( 10:00AM ) Mommyn Meenal taji Meenal shiru har yanzu bata fito ba dan yanzu da wuri take breakfast amma shiru har yanzu bata fito ba.Mommyn Meenal shiga ta yi bedroom d'in Meenal d'in dan jin shirun ya yi yawa,saidai da gudu ta idasa d'akin sakamakon nishin Meenal d'in da take ji sosai .Mommyn Meenal ko da ta shiga halin da ta iske Meenal sosai hankalin ta ya tashi dan Meenal ta gama galabaita.Mommyn Meenal waya ta ciro ta Kira Daddyn Meenal ,yana d'agawa ta sanar da shi halin da Meenal take ciki.
Mommyn Meenal na nan tsaye kan Meenal tama rasa taimakon da zata bata Daddyn Meenal ya shigo da saurin sa.Kasan cewarsa k'wararre ne a fanin karb'ar haihuwa take ya ba Meenal d'in duk wani taimako da allurai da ya kamata ya yi mata amma shiru.Daddyn Meenal kusan hour shi d'aya akan Meenal amma har yanzu Meenal bata haihu ba .Mommyn Meenal ganin yadda Meenal d'in gaba d'aya ta fita hayyacin ta kallan Daddyn Meenal ta yi tana kuka ta ce"Daddyn Meenal dan Allah ka kaita asibitin ku ko akwai abin da zasu yi mata "Daddyn Meenal cikin goge zufar goshin shi ya ce"Haihuwar ce har yanzu da d'an saura ,kuma kin san Meenal kullum tana kwance bata son motsa jiki ,yana kawo doguwar nak'uda dama,amma idan har ta k'ara minti talatin bata haihu ba to zan tafi da ita asibiti ai mata theater kawai"Momnyn Meenal kuka tasa tana cewa"Haba Daddyn Meenal minti talatin ya yi yawa dan Allah ka kai ta yanzu "Ki yi hak'uri Mommyn Meenal har lokacin da na d'auka ya yi saboda Meenal da k'arfin ta zata iya haihu da kanta,amma idan lokacin ya yi bata haihu ba sai muje asibiti ayi mata theater.
Meenal haka ta kai har wannan lokaci da Daddyn ta ya d'iba bata haihu ba.Mommyn Meenal ko da tana nan tana kallan Agogo ,kallan Daddyn Meenal ta yi ta ce"Lokacin da ka d'iba ya yi fa,ya kamata mu tafi asibitin"Daddyn Meenal da mommyn Meenal rirrik'eta suka yi suka nufi yanya fita da ita.Meenal duk taku d'aya sai ta huta sannan ta k'ara ta kawa a haka suka kai har falo.Suna daidai k'ofar fita daga falon ne Meenal ta durk'ushe da sauri har Daddyn ta na saurin kamata ganin zata fad'i.Mommyn Meenal kallan shi ta yi tana goge hawaye ta ce"Daddyn Meenal mu kama mu d'auke ta"Kai Daddyn Meenal ya girgiza ya ce"Haihuwar ce ta zo.Daddyn Meenal allurar ajihun shi ya ciro ya kuma yima Meenal ,yana gama tsira mata kan d'a na fitowa.Da taimakon Daddyn Meenal Meenal ta haihu.Daddyn Meenal mik'ama Mommyn Meenal babyn ya yi sannan ya gyara 'yar shi .
Mommyn Meenal da murnata ta mik'ama Daddyn Meenal babyn ita kuma ta je ta a za ruwan zafi.Babyn ko ta dage sai kuka take.Meenal d'ago kai ta yi tana kallan babyn da Daddyn ta ya aje yana gyara wajan.Meenal cikin sanyi ta ce"Daddy ka bari ka d'auki babyn........
A yi manager dan Allah. A yi hak'urin jina shiru kwana biyu 🙏🏻🙏🏻🙏🏻
Fadila Sani Bakori ce.
📚 MEENALYN DADDY📚
Page 40
Meenal d'ago kai ta yi tana kallan babyn da Daddynta ya aje yana gyara wajan.Meenal cikin sanyi ta ce"Daddy ka bari ka d'auki babyn"Daddyn Meenal d'agowa ya yi yana kallan Meenal sannan ya saki kyayataccan murmushi ya ce"Meenalyna hannuna bashi da kyau, ki bari mommyn ki ta zo ta d'auke ta"Meenal kai ta d'aga ma Daddyn ta, kukan babyn na k'ara shigarta sosai.Ana haka ne Mommyn Meenal ta shigo,tana zuwa ta d'auki babyn tana jijjigawa ,ita kuma ta d'age sai kuka ta ke.
Bayan ruwan da Mommyn Meenal ta sa ya tausa ne ,ta kama Meenal ta wanke ta kamar yadda ake wanke maijego.Bayan Mommyn Meenal ta gama wanke ta ne ta wanke babyn ita ma.Meenal kallan Mommyn ta ta yi bayan ta gama wanke babyn ta ce"Mommy baby boy ne ko baby girl?"Abin da ki ke so ne Meenal Allah ya baki,'ya Mace "Meenal murmushi ta yi ta ce"Saidai mommy babu kayan da za'a sa mata"Meenal kenan ai ni ba irin ki ba ce,tun da cikin ki ya shiga watan haihuwa na je na siyo kayan jarirai ,bari ki gani"Mommyn Meenal bedroom d'in ta ta shiga, sai gata ta fito da jakar kayan jarirai da yawa su Pampers ,feader kayan sawa da sauran su,haka Mommyn Meenal duk ta siyo.Mommyn Meenal d'aya daga cikin kayan ta shirya yarinyar da su.Mommyn Meenal kallan Meenal ta yi da ita ma su take kallo ta ce"Meenal kinga babyn nan babu inda ta baro mahaifinta ,da hancin ,da idon ,da bakin duk na mahaifin ta ne "Meenal turo mitsitsin bakin ta ta yi ta ce"Mommy dan Allah ki bar had'a ta da shi "Mommyn Meenal ido ta zaro ta ce"Meenal zaki canza ma tuwo suna ne? Ai ba a canza ma tuwo suna"Abin mamaki Mommyn Meenal sai gani ta yi Meenal ta fashe da kuka .Mommyn Meenal baki ta saki tana kallan ta ta yi banza da ita ta ci gaba da shirya ya babyn.Daddyn Meenal ko jin kukan Meenal da ya yi ne ya shigo d'akin,kallan Meenal ya yi ya ce"Meenalyna jikin ne ko?"Kai Meenal ta girgiza tana mai ci gaba da kukan ta.Daddyn Meenal cikin lalla shi ya ce"Haba Meenalyn Daddy kinga jikin ki bai gama k'wari ba ki yi hak'uri ki bar kukan,fad'a min ya a kai?"Meenal goge hawaynta ta yi ,sannan ta ce"Daddy ba