Showing 45001 words to 47397 words out of 47397 words

Chapter 16 - MEENALYN DADDY Complete Book By Fadila Sani Bakori.txt

06 Jan 2025

2935

tare da b'ata lokaci ba aka karanto ma alk'ali shari'ar farko wadda ta kasan ce ita ce ta su Daddyn Meenal.
Alk'ali nai man wadda take k'ara ya yi aka sanar da shi saidai lauyanta,nan dai aka ba lauyanta damar magana,inda ya fara magana kamar haka"Amina Sani tana taiman mijinta ya saketa, saboda dama aure ne Wanda akai abisa tursasawa ta kakanta,manaifinta ma ba so ya ke ba,to shi ne mu ke so mai girma mai shari'a yaran ya saketa,amma ya k'i" Alk'alin lauyan D'anjuma ya naima,inda shima ya fara magana kamar haka"Abdurrahaman bak'in sakin Amina ya yi ba,ahalin yanzu mai girma mai sharia Abdurrahaman a shirye yake da ya saki Amina,saidai ya ce ba zai saki Amina ba saidai in ta yadda zata ba shi 'yar shi ,saboda yarinyar zata ragemai rad'ad'in rashin mahaifiyarta" to'fa nan ne lauyan Meenal ya tashi ya ce"Ya mai girma mai shari'a ita yarinyar da yake magana akanta jinjira ce ,ba su dad'e da arba'in ba,idan aka bashi ita yarinyar zata cutu kasan cewarta jinjira, k'arama sabuwar haihuwa"
Atak'ai ce dai kunsan shari'ar yanzu kud'i ce da kuma k'warewar lauyan da ka d'auka,kasan cewar lauyan D'anjuma sun turoma alk'alin kud'i tuntuni ya sa alk'alin ya ce"To,idan Amina tana son sakinta awajan mijinta ta bashi 'yar shi shi kuma ya bata sakinta......












Fadila Sani Bakori.










📚 MEENALYN DADDY 📚






Page 43 & 44










Daddyn Meenal na fita daga cikin kotin direct gida ya yi,yana shiga Meenal da saurinta ta yo wajan daddyn ta tana mai oyoyo ta ce"Daddy barka da dawowa"Yauwa Meenalyna,zau na ki ji"Meenal zama ta yi kusa da Daddyn ta alamun ina jin ka.Daddyn Meenal kallan Meenal ya yi ya ce"Ina Fatimar fa?"Meenal baki ta turo ta ce"Daddy teema fa ake ce mata"To ina teemar?"Barci ta ke yi"Kai Daddyn Meenal ya jinjina ya yi shiru sai zuwa can ya ce"Meenalyna duk kin rame ko dai babyn nan ce ke ramar da ke? Idan ita ce in kaima Mahaifinfa ita tabar ramar min da Meenalyna"Meenal turo baki ta yi ta ce"Daddy ko ma ita ce sai ka kai mai ita,bagara in taramewa ba da akaita wajan shi"Meenal ta fad'i maganar tana turo baki.Shiru Daddyn Meenal ya yi,yana kallan Meenal,sai zuwa can ya ce"To Meenalyna ai dole ma a bashu 'yarsu in dai muna so yaran nan ya sakeki,kinga ko a kotu ma antsaida magana sai dai a ba su 'yarsu sannan su ma su bada takardar saki"
Mommyn Meenal da tariga taji komai wajan yayanta ,sosai hakan ya yi mata dad'i,fitowarta falon kenan sai ta nuna musu kamar bata san komai ba ta ce"Daddyn Meenal kar dai ka ce min har kun shiga kotun? Na ji kana maganar sai dai a basu 'yarsu sannan su bada takardar saki?"
Daddyn Meenal cikin damuwa ya ce"Wallahi mommyn Meenal yaron nan lauya ya d'auka shima,to kin ji yadda abin ga kaya,shi ne nake tunanin ko dai kutu zan canza?"Hmm,ai daddyn Meenal ko ina kaje haka ne,dan kwanaki yarinyar friend d'ina ,na baka labarin dandai kana da mantuwa ne haka akai itama duk kotun da suka je shi akeba 'yar,ni yanzu shawarar da zan ba Meenal ta yi hak'uri a bashi 'yar shi shi kuma ya bata takardar ta shikenan.."Mommyn Meenal ba ta rufe baki ba Meenal ta rushe da kuka,da sauri Daddyn ta ya rungumota yana tambayar ta lafiya.Meenal cikin kuka ta ce"Daddy ni dai ban yadda ba a ba shi Fatima sai dai ya je ya yi ta ruk'on takardar kada Allah ya sa ya sakan d'in"
Mommyn Meenal da har yanzu a tsaye ta ke zama ta yi tana cewa"Meenal ai kuma ba zai yuwu ba kici gaba da zama da aure aka kanki,gara ki bashi 'yar shi watarana da kanta zata naimeki duk inda ki ke "Ai nan ma Meenal kuma fashewa da kuka ta yi tana cewa"Daddy kai ma Mommy magana ta bar cewa in bada Teema"Daddyn Meenal cikin fad'a ya fara magana kamar haka"Wai Mariya me ya sa ki ke haka ne? Ke har yanzu ba zaki rik'a lura da abin da Meenal ba ta soba ki rik'a kiyayewa ba,yanzu meye amfanin maganganun nan da ki ke? Inda kuka su ke sata ba sai ki yi shiru ba"
Mommyn Meenl ba tare da ta kuma tankawa ba ta tashi ta bar falon.
Meenal ko kallan Daddyn ta ta yi ta ce"Daddy ka kirashi kai mai magana kar ya kuma cewa a ba shi teema "Daddyn Meenal da bai iya kaucema umarnin 'yar ta shi waya ya ciro ya lalibo number D'anjuma,D'anjuma na d'agawa yana gaida Daddyn Meenal amma bai bi takan gaisuwar ba ya fara magana kamar haka"Hello,Abdurrahman dama akan zaman da mu ka yi a kotu ne ga Meenal nan na kuka ta ce ba zata baka teema ba dan haka ka jan ye maganar abaka teema kana jina ko? ,Inda ta ce bata sonka kuma ka kawo mata takardarta kana ji ko?"D'anjuma shiru ya yi yana sauraran son kai irin na Mahaifin Meenal.Daddyn Meenal ko jin ya yi shiru ya ce"Ka dai ji abin da na ce dai? In banda sakarci irin nakama ba abun murnarka bane da Meenal ta yadda zata rik'ema 'ya amma dan tsabar sakarci ka ce abaka 'yarka "D'anjuma murmushin da bai fito fili ba ya yi ya ce"Daddy maganar da na fad'ama bazan janye ba idan har Meenal ba ta dawo gidana da zama ba cikin satin nan to ni kuma zan koma kotu ta amsar min 'yata dan ina son 'yata kusa da ni"D'anjuma na kaiwa haka ya kashe wayar shi.
Kasan cewar wayar a speaker ta ke Meenal duk ta ji abin da D'anjuma ya ce,haka ya sa ta fashe da kuka tana turje-turje ita ba zata koma gidan shi ba kuma ba zata bashi teema ba.










Daddyn Meenal sosai hankalin shi ya tashi ganin yadda Meenal ke kuka.Mommyn Meenal da sauri ta fito rungume da teema da tashinta kenan daga barci jin kukan Meenal da ta yi.Mommyn Meenal da sauri ta k'araso tana tambayar Daddyn Meenal lafiya.Daddyn Meenal da ke rik'e da Meenal yana bata baki kallan Mommyn Meenal ya yi ya ce"Mariya Wallahi sai na d'aure yaran nan idan bai yi wasa ba!"Mommyn Meenal zama ta yi tana cewa"Lafiya Daddyn Meenal ya akai?"Mariya wai ni yaron nan ke sanar da ni in dai Meenal bata koma gidan shi nan da sati d'aya ba wai zai maka mu kotu aba shi 'yar shi?"Mommyn Meenal cikin sanyin murya ta ce"Daddyn Meenal,abin da hak'uri bai yi ba rashin hak'uri fa ba zai yi shi ba,ni gani nake inda yaran nan da alamun yana da hak'uri ku bishi a hankali da lallami da wayo sai kaga ya bata takardar ta kuma ya barmata teema cikin sauk'i"Bai isa in bashi a hankali ba ya kai ni kotun mu buga ni da shi mu gani ai ina da kud'in shari'ar"Meenal dai amsar teema ta yi daga hannun Mommyn ta da ke kuka ta nufi bedroom d'in tana mai ci gaba da kuka dan ita gani take har kotu ta anshe 'yar taba D'anjuma ita,to shi ne fa ta ke k'ara kuka idan taga kamar haka zata iya faruwa.










Meenal na zau ne ta gama shayar da teema tana zau ne ta yi ta gumi mommyn ta ta shigo.Mommyn Meenal zama ta yi tana dafa Meenal ta ce"Meenlyn Daddy kar ki biyema Daddyn ki har Abdurrahaman ya kai ku kotu,dan kin san Allah yawancin kotu uba tak'e ba 'ya,kuma kotu na bashi ita shi kuma gidan mahaifiyar shi zai kai ma 'yar,dan haka tun wuri tun kafin ya kai kotu ki kira shi ki karya wuyanki ki rok'eshi, idan kuma kinsa taurin kai kina ji kina gani kotu zata ba shi ita ya kaita kyauyan su ko kuma ya ba matar da zai aura ita"Meenal goge hawayanta ta yi ta ce"Mommy ba ni number shi in kirashi in rok'eshi d'in"Ki duba wayata zaki ga ansa Abdurrahaman sai ki d'auka"Mommyn Meenal na sanar da Meenal haka ta fita tabar mata d'akin.










Meenal wayarta mommynta ta d'auka ta ciri number D'anjuma,batare da tunanin abin da za ta ce mai ba ta maka mai kira,dan gani take idan ta b'ata lokaci zai iya kai kutun.










D'anjuma na zau ne a plazar da ya ke aiki kira ya shigo wayar shi,kasan cewar yana attending customers ya sa har kiran ya katse bai d'aga ba,haka Meenal taita kira bai d'agawa ta hak'ura ta aje wayar.








D'anjuma sai da ya gama sallamar customer sannan ya bi kiran Meenal da bai san mai Kiran ba inda ba shi da number ta.Meenal na nan zau ne inda take Kiran D'anjuma ya shigo wayarta,da sauri ta d'aga."Assalamu alaikum,an kirani kuma ina attending customers "Cewar D'anjum.Meenal shiru ta yi ta rasa abin cewa,D'anjuma jin haka ya ce"Hello wai wake magana ne"Meenal rasa abin cewa da ta yi kawai sai ta fashe da kuka,D'anjuma na jin kukan Meenal ya gane ta ,amma sai ya share ya yi kamar bai gane ba ya ce"Hello lafiya wai waye ne ? Ko dai wrong number ne ?"Meenal cikin shasshek'ar kuka ta ce"Meenal ce"Okay"Cewar D'anjuma ya ce"Da fatan lafiya na ji kina kuka?"Meenal cikin share hawayanta ta ce"Dan Allah dama ina son mu yi wata magana ne?"Okay,to yanzu dai ina kasuwa ne yanzu haka ga customers jirana su ke zuwa dare idan na koma gida sai mu yi magana"D'anjuma na kawai haka ya kashe wayar shi.










Meenal tana jiran Kiran D'anjuma amma shiru ga shi har 10:13PM ,waya ta d'aga ta kuma Kiran shi,D'anjuma ko lokacin yana waya da wata sabuwar budurwa shi ta ta lik'emai dan ita kema kiran shi,yana ganin Kiran Meenal ya sanar da ita zai yi barci sai da safe.Bayan ta kashe ne ya kira Meenal,Meenal d'agawa ta yi ta ce"Bari in Kira ka?"A'a ki yi maganar da za ki"Meenal tashi ta yi daga kwancan da ta ke ta zauna ta ce"Dama akan teema ne"Teema kuma? Wacece teema?"Dan D'anjuma bai san ana kiran Fatimar shi da teema ba.Meenal jin ya ce haka ta ce"Fatima na ke nufi"Okay,Fatimar ce kika sa mata teema , yarinya na da suna mai dad'i zaki wani canza mata suna da wata teema,me ake nufi da teemar?"Meenal da ba fad'a ta ke naima ba bazan ta yi da D'anjuma ta ce"Mu yi maganar da na kiraka dan ita"Oka,ni kuma ba zan saurareki ba sai na ji dalilin da ya sa ki ka canza mata suna daga Fatima zuwa teema?"Meenal dafa kai ta yi dan bata son damuwa ,amma sai ta danne dan tana tsoran ta yi saken da D'anjuma zai kai su kotu a ba shi teema,hakan ya sa ta ce"Teema Nick name ne kawai"Ba shi da dad'i ku rik'a kiranta da Fatimar ta yafi dad'i"Okay"Meenal ta ce dan so ta ke a wuce maganar ta yi wadda ke gabanta,Meenal cikin kwantar da murya abin mamaki kamar ba Meenalyn Daddy ba ta ce"Dama na kiraka ne akan maganar Fatima da ka ce sai dai a baka,shi ne na kira in rok'eka dan Allah ka yi hak'uri kabar min Fatima a hannuna dan Allah"D'anjuma sosai mamaki ya kashe shi jin yadda Meenal ke mai magana,amma sai ya kauda mamakin shi ya ce"Amina ba zan iya barmiki Fatima ba saboda nima ina buk'atar 'yata kusa da ni,sannan idan na bar miki Fatima kin ce ba zaki bari ta kirani Baba,kinga ni kuma ba zan so haka ba,ace 'yar da nahaifa bazata kirani da Baba, shi ya sa zan amshi 'yata ta ta shi a hannuna ,kin ga ni kuma zan barta ta kiraki da Mama"Meenal shiru ta yi tana shirin kuka dan ita aduniya babu abin da ke mata sauk'i kamar kuka,bata da wuyar kuka,hakan yasa cikin alamun kuka ta ce"Wallahi zan barta ta kiraka da Baba dan Allah ka bar min ita?"Hmm,Amina daga baya kenan bazan yarda da ke ba,kina so in bar miki Fatima?"Meenal da saurinta ta ce"Eh,dan Allah"To sai dai ki dawo gidana da zama"Meenal cikin kuka mai tattare da b'acin rai ta ce"Ba zan tab'a dawowa gidanka da zama ba kuma Wallahi inda kai baka san lallami ba bazan baka teema ba sai dai ba kotu ba duk in da zaka ka je ,dan kaga Allah ya baka nasara ne a wannan karan!" Okay haka kika ce? Shi ke nan mu had'u a kotu nasan zata kwatar min 'yata"D'anjuma na fad'in haka ya kashe wayar.










Kukan Meenal ne ya shigo da Mommyn ta,mommyn Meenal da mamaki ta kalli Meenal ta ce"Ke kuma dawa cikin darannan ki ke kuka?"Meenal goge hawayanta ta yi ta ce "Mommy ba ke ba ce ki ka ce in kira wannan in bashi hak'uri akan teema shine na kira shi ya ce wai sai dai in koma gidan shi sannan ,ni kuma bazan koma ba shi ne wai mu had'u a kotu zata kwatar mai 'yar shi ai"Mommyn Meenal zama ta yi tana ta dafa Meenal ta ce"Meenal ki fa cire girman kai ki rok'i Abdurrahaman da kyau ,ina ji miki tsoran ya kai maganar nan kotu ,kotu shi fa za su ba 'ya ,kwantar da kai zaki kinsan mai nema baya fushi ahaka-ahaka sai kika ya sakko dan Abdurrahaman yarone mai kirki da sanin ya kamata zai bar miki ita in dai kin yi hak'uri ba ki yi zuciya ba kuma ki ka cire girman kai,yanzu ki yi k'ok'ari ki dakatar da shi da kai maganar kotu"Mommyn Meenal na kawai haka ta fita ta bar Meenal.










Meenal kuma bayan fitar Mommyn ta kuma Kiran D'anjuma ta yi,sai da ta kusa katsewa sannan ya d'aga,yana d'agawa Meenal ta ce"To yanzu dan Allah nawa zan baka ka bar min teema?"D'anjuma kai ya girgiza ya ce"Lallai yarinyar nan haka ta d'aukan matsiyaci"D'anjuma kamar ba zai tanka ma Meenal ba,sai zuwa can ya ce"Amina kenan, talaucina baikai Wanda zan saida jinina ba,ko da ma ya kai ba zan iya saida jinina ba,idan kin gama fad'in abin da ke rankin zan yi barci"Shiru Meenal ta yi ,sannan ta ce"To Dan Allah ka yi hak'uri za ka bar min ita?"A'a bazan iya bar miki 'yata ba kamar yadda kema ba za ki iya dawowa gidana da zama ba haka nima bazan iya barmiki 'yata ba"Meenal fashe ma D'anjuma da kuka ta yi tana rok'on shi cikin kuka"Danjuma gyaran Murya ya yi ya ce"To shikenan inda dai kin matsa zan bar miki ita amma da sharad'i ?"Meenal goge wayanta ta yi ta ce"ina ji?" Sai dai in kin yadda za ki ban kanki..........






Free pages ya k'are sister idan kina buk'atar ci gaba zaki iya magana da marubuciyar ta 08063830828








Fadila Sani Bakori ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login