Showing 21001 words to 24000 words out of 56965 words

Chapter 8 - RETURN OF THE KING COMPLETE BY APHSERT KHAIREE .txt

28 Dec 2024

3346

free and safe insha Allah" yayi ficewarsa a dakin




************************
A durgukushe suke gaban wani k'aton bak'i mummunan mutum wacce halitta ta rikid'e ta chanza ta koma kamar wani dabba mafi muni da tsoro,zaune yake kan wata k'atuwar kujera wacce kafin ka hau ma sai ka taka wani steps uku dake jikin kujerar daga kasa.Kujerar da kanta abin tsoroce don kan zaki ne daga hannayenta sai kan mutum daga samanta an mishi ado da wani kyalle red and black kamar yanda komai na dakin yake bak'i sai ratsin ja²,dakin da suke kira da
'ROOM OF DARKNESS' (DAKIN DUHU)


A duk lokacinda suka hallaru a dakin tho tabbas wani Abu mai mahimmanci ne ya taso koh kuma za'a fida muku mutanen da aka fidda daga cikin en uwanka wa'inda k'unqiya ta buk'aci jininsu a matsayin sacrifice
*'ODUBARIBA'* shine sunan shugaban wnn kunqiya wanda koyaushe yake rayuwarsa cikin D'AKIN DUHU don baya taba fitowa,naman jarirai sune abincinsa tareda jinin al'umma.


Shi yake gabatar musu dukkan wani tsafi na kunqiyar shiyasa duk wani abu shi yake yanke yanda za'ayi,hatta en kunqiya basason ya kira meeting sbd tsoron abinda zai buk'ata don in sunji kiransa tho tabbas kungiya na buqatar jini wani daga cikin en uwansu koh akoi wani muhimmin aiki.


Sujjada suka mishi dukkansu cikin tsoro da mutuk'ar girmama,kana ganinsu kasan zuciyoyinsu sun bushe,hankulansu ya gushe haka ma imaninsu ya k'afe sun manta da akoi wani abin bauta basaji basa gani sai wnn shugaban nasu (wa iyazubillah)


"ODUBARIBA,ODUBARIBA,ODUBARIBA"


Saida suka kira sunansa sau uku kansu na kasa tukun suka mike,kowannensu ya maida hannayensa baya tareda sunkuyar da kai cikin tsananin girmamawa.


Cikin wata irin kakkausar murya mai ban tsoho da wani irin amo mai firgitarwa shugaban nasu ya fara magana cikin turanci


"Nan da 11days k'unqiya na buqatar jininta sannan dukkan ku 8 din nn sai kun shigeta don na mata aiki mai karfi a jikinta wanda duk zai zama babbar sa'a ga rayuwarku.Nan da 10days zaku kawomin ita DAKIN DUHU nima zan shigeta don zan hada jina da nata sbd kafuwar kunqiya kafin ranar da zamu yanka tho"


Hada baki dukkansu sukayi wajen amsawa


"ODUBARIBA,ODUBARIBA,ODUBARIBA. Your wish is our command"


Wani irin dariya mai ban tsoro yasa yana nuna daya daga cikin cultists din yace


"Ya aikin da kunqiya ta baka?"


Cikin tsananin girmamawa wanda aka nuna ya durqusa kan guiwarsa yana kara sunkuyar da kansa kasa yace


"ODUBARIBA, ina buqatar taimakon kunqiya sosai he's not accepting anything from me"


"Wannan aikin kane,sbd ba yanda za'ayi mu sameshi yanxu kamar da don ya tsayawa kansa yanxu sosai,dole ne ka kawo mana shi by all means.You have to and you must"




A firgice King ya farka yana salati sbd mummunar mafarki da yayi wanda ya mutakar bashi tsoro duk ya jik'e da gumi,alwala ya daura ya fito ya tada sallah.


Saida yayi raka'a shida tukunna ya zauna,ya d'aga hannayensa sama yana kuka sosai kamar yaro yace


"Ya Rahamanir Rahim,Ya malikan kuddus,Ya Allah ga bawanka mafi kasqanta daga cikin bayinka,Ya Allah ga bawa nka mai yawan aikata sa6o da zunubi,mai tsoron azabarka mai kwadayi da kaunar rahamarka.Ya Allah don girmarka da buwayrka ina rokonka ka yafemin kurakurai na.Ya Rabb ya Kareem ina godiya ga dukkan ni'imoninka gareni da aron lokaci daka bani,Allah na rokeki ka haska min gabana ka bani ikon cika burina cikin taimakonka.Ka daurani kan maqiyana,ka karemin Matata a duk inda take ka bani ikon cika mata alkawarina akanta da iyayenta.Allah na rokeka ka nunamin maqiyana ka daurani a kansu. Ya Allah kaine shaidata kaga zuciyata bani nufin kowa da sharri ka kareni daga sharrin masu sharri,Ya Allah...."


Kukane yaci karfinsa ya durgushe a wajen yana yin


"Who am I fighting, who's fighting me,meyasa suke son tarwatsa min rayuwa,meyasa suka rabani da dukkan farinciki na,meyasa haryanxu basu kyaleni ba,ina suka kaimin DIJAna,why me..why..."


Shi kadai yake yiwa kansa tambayar da bashida mai amsa musa sai wata zuciya yaji tana fadamasa cikin tsawa


"Kana kara azabtar da kanka while maqiyanka na cen suna cikin farinciki,kana nn kana zubar musu da hawaye su kuma suna cen suna celebrating.Kuka ba naka bane,you needs to do what has to be done.




_A NEW DAY A NEW BEGINNING_
_FAHIMA ALIYU at work_


Tunda ta shigo ma'aikatar tasu ake binta da kallo kamar sunga sabon abu with so much surprised on their faces don bbu wanda ya ta6a tsammanin zata dawo aiki upon all abubuan da suka sameta na rashin mahaifiyarta ga 6atan yaronta da kuma kama ex husband d'inta da ake suspecting akan mutuwar mahaifiyar nata.


Takunta takeyi daya bayan daya da murmushi a fuskarsa tasa farin glass a idonta cikin shigarta as usually palazzo da top sai baby hijab dinta ta ratayo wani mini side bag dinta da wasu files rungume a kirjinta.


Duk inda ta wuce saide ita ta gaishesu su amsa a daburce don kallo ya dauke musu hankali har ta iso office din boss dinta.Knocking ta farayi inda yace mata Come in kansa duke a kan wasu takardu yana dubawa bai ma san wanda yay knocking din ba


"Good morning Sir"


Ya tsinkayi muryarta,cikin mmk ya d'ago kai yana kallonta shi kansa bai dauka FAHIMA ALIYU zata iya dawowa aiki ba.Lalle sai yanxu ya k'ara yarda da nacin aiki irinna journalism da yake jikin kowanni journalist.Ajiye pen din hannunsa yayi ya yana girgiza kansa,nemawa kanta mazauni tayi kan kujerar dake gaban table dinsa tayi cross leg tana murmushi


"FAHIMA ALIYU are you back again"


Ya fada still sounds surprised, murmushi Fahima tayi tace


"When there's life there's hope"


"Hmmmm,FAHIMA ALIYU jajritacciyar er jarida wacce bata sarewa"


"Thank you sir"


"So, yakike,ya hakuri and where av u been all this while you're no way to be found don all d press munje miki ta'aziya da jaje ama gidanki is under security"


"As you can see Sir,am perfectly fine"


"Toh Alhamdulillah, yaronki fah?"


"He's fine too"


"Masha Allah,zaki iya komawa aikinki"


"Thank you Sir ama ina buk'atar taimakonka please ka saurareni"


"Ina fatan ba akan case din nn bane"


"Akanshi ne Sir"


"Ama kinsan career suicide ne koh?"




"I know Sir,ama wnn karan ba wani nakewa aiki ba am working on my own kuma zanyi aikine akan both candidates din.Dole ne en kasata su san irin mutanen da zasu za6a a matsayin shugaba,please Sir ina bukatar goyon bayanka"


Ajiyar zuciya yayi yace


"But you know it's dangerous"


"Insha Allah bbu abinda zai faru,wnn karan I'll be more careful bazan taba abinda cutar da ma'aikatarmu ba.I promise you Sir"


"OK then,best of luck"


Cikin jindadi Fahima tayita mishi godiya tareda fita a office din ta koma nata






_GOVERNMENT HOUSE_
_ZEE KAITA_


Zaune take gaban k'aton dressing mirror dinta da yake shaqe da kayan mayuka da turare kala² da kayan kwalliya iri² masu kyau da tsada kamar wani d'an karamin shago kayan cosmetics


Wani kyakkyawar pink towel ne d'aure a jikinta da alama yanxu ta fito daga wanka tana shafa mai a jikinta da alama yanxu ta fito daga wanka,a hankali take shafar kamar batason ta6a jikinta tanayi tana lumshe ido dirty mind d'inta na k'awata mata yanda takejin dad'in shafa man,ji take kamar King ne ke shafa mata passionately.


K'arar sautin shigowar message wayata ne ya dawo da ita daga qazantacciyar duniyar data tafi, kamar zata share sai kuma ta dauko tunawa da aikin da ta bayar a mata.Ta WhatsApp aka turamata saqon picture sai rubutu a k'asan data gani akan screen d'inta


"Keep the boy safe or else....."


Da sauri tayi unlocking wayar ta shiga saqon,cillar da wayar tayi ta tashi daga kan stool din tasa wani ihu ganin pics din da aka turamata jikinta na rawa har bataji shigowar AA ba saiji tayi an rungumeta ta baya ya zare towel din dake jikinta ba tareda ya kulada halinda take ciki ba ya fara sarrafa albarkatun jikinta,duk soyayyarta da abinda yake mata ji take kamar yana d'ana mata wuta a jikinta don a matuk'ar rud'e take


Juyawa tayi cikin hanzari zata mishi magana yak'i bata wnn damar don caraf ya cafke bakinta cikin nasa yana kissing dinta passionately and out of control har tsayuwa ya gagareshi ya jata zuwa gado.Suna zuwa bakin gadon kuwa ta hankad'ashi ya fada kai


"Stop please AA am not in the mood"


Da mmk yake kallonta wai yau itace take cewa bata mood,lalle akoi wani abu.Tashi yayi ya zauna a bakin gadon ita kuma ta dau towel dinta a kasa ta daura a jikinta ta d'au wayarta da haryanxu pics din yake fuskar screen din wayar ta kashe wayar gabadaya


"Meyafaru?" AA ya tambayeta


"Bakomai,I need to be alone please"


Tashi yayi ya matso inda take ya rike fadarta dukka biyu yace


"Tell me,me kikeyi koh me kike shirin yi?"


Sauke hannayensa tayi daga kan fadarta tace mishi


"Nace maka bbu komai,kuma ina ruwanka da abinda nakeyi koh nake shirin yi"


Gaban closet dinta ta wuce ta nemo gown da mayafinta,koh inner wears bata saka ba ta zura rigar ta yane kanta da mayafin da d'au wayarta da key din mota


"Ina zakije a wnn time din?"


Agogon jikin bangon dakin ta kalla taga quarter to 11,batace kala ba ta wuce ta kyalesa a wajen.Cije lips dinsa na kasa yayi,yana sosa goshinsa da karamin yatsansa.Yaso a yau dinnan ya samu kan Zee inda zai samu ta fara aiwatar masa da aikinsa cikin ruwan sanyi ba tareda itama ta sani ba...










I only see ur complains,page yayi kadan yayi kadan not an appreciation by comments, fine 🤷🏻‍♀️ I do what I can......
[1/6, 9:05 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*




ELEGANT ONLINE WRITERS


17


Yau ma kasa fita sallar asuba yayi sbd ciwon da kansa yake masa sai a d'akinsa yayi sallah,bayan ya idar ya gama addu'o'insa tare da azkar yana zaune still akan rug d'in dake shimfid'e a bakin gado.Wani tunani yazo kansa lokacin da yake tareda Dijansa.....


_Mid_night_ Bayan sun gama samun nutsuwa tana kwance akan kirjinsa wasa take da gashin chest dinsa dake kwance luff yana shafa bayanta cikin shauk'i da jindadin kasancewarsu tare.D'ago kanta tayi tana kallon kyakkyawar fuskar mijin nata da takeji tafi kowacce mace sa'a a rayuwa da wnn kyauta mafi daraja da Allah ya bata..


Saukar warm lips dinsa taji akan forehead d'inta yana mata murmushi


"Dijahna me kike tunani?"


"You"


K'ara cuddling d'inta tightly yayi a jikinsa kamar zai mayar da ita cikinsa yana jin kaunarta na ratsa kowanne sassa da mugadanar jini na jikinsa yana jin kamar bazai iya rayuwa da wata macen ba bayan ita


"Tunanin me kike akaina,bayan am all yours?"


Ajiyar zuciya tayi ta kwantar da kanta kan kirjinsa yana shafa gashinta na asalin Fulani da yake tsefe


"Tunda ka shiga harkar siyasan nn ka zama very busy,duk time d'ina ka rabawa jama'ar waje"


Tayi maganar tana turu bakinta alamar shagwab'a


"O'o am so sorry dear, kinsan yanxu ne muke kan campaign da zarar an kammala primary election komai zai zo da sauki i promise you'll be having my full time just like before,kinji"


"Gaskiya nide bana sonka da siyasa wlh don de ka dage ne,kuma a ina kake samun kudin da kake campaign din dashi?"


Shiru yayi yana nazarin tambayarta


"Ba ina aiki ba Dija"


"I know your salary won't be enough"


"Waya fadamiki ana kashe kudi a campaign"


"Nayi bincike ne"


Jan hancinta yayi yace


"Karki damu muna samun tallafi daga manyan committee"


"Please bad'd'o am, don't put urself into mess.Komai zakayi kayi da iyakar gaskiyarka da kuma abinda yake halal a gareka gudun jefa kanka a matsala don ranar mu'allim dinmu yace mana duk abinda aka ginasa ta hanyar k'arya da haram baya tab'a tasiri"


Jikinsa ne yayi matuk'ar sanyi da maganganun nata..


Wani irin iska mai hucin zafi ya fesar daga hancinsa tunawa da shawarar Dijah,tabbas maganarta haka yake duk abinda aka ginasa da haram baya ta6a tasiri dukda bashida haryanxu ya kasa tabbatar da hallaci da rashin akan tarin dukiyar daya tsaya takara da shi a baya har ya samu dubbin goyon baya daga kan talakawa har zuwa manyan kasa.knocking kofarsa akayi yace


"Come in"


Zaki cikin jallabiyarsa fara kal ya shigo da sallamarsa bayan ya gaisheshi ya amsa masa


"Lafiya baka fito sallah ba?"


"Headache ama zansha drugs yanxu na d'an kwanta kafin anjima hope yau bbu wani schedules?"


"Allah ya sawwake,saide in P.A ya iso"


Jigina yayi da jikin gadonsa yace


"Ka zauna inason muyi magana"


"Okay" ya zauna kan cushion dake fuskantar King yana sauraron sa


"Menene tunaninka akan takarar nan?"


"All is well insha Allah"


"Kana ganin bbu wata matsala?"


"On my on view,babu ama zamu tattauna da P.A muji ya abin yake daga 6angarensa"


"Okay,that's all bari na dan huta"


Mikewa Zaki yayi yace


"A huta lafiya"


ya fice a dakin,tashi yayi ya kuma kan gadonsa ya zauna daga bakin gadon wajen side drower.Panadol ya dauko daga cikin drowern ya 6alli biyu ya kora da ruwan dake kan drower yana jin yanda kansa ke sara masa,kwakwalwarsa na buk'atar hutu da nutsuwa koh dan ya samu yayi tunani da kyau sbd abubuan dake gabansa dole ne ya d'inga samawa kansa nutsuwa.Ya kwanta tareda runtse idonsa,bacci yayi awon gaba dashi.


Bai farka ba sai quarter pass 9,Alhamdulillah ya tashi wase bbu ciwon kan sai na zuci wanda bazai ta6a denawa ba har sai ranar da burinsa ya cika.Toilet ya shiga saida yayi kusan 30mins yana k'alk'ale jikinsa tukun ya nad'a towel a k'ugunsa karami a hannunsa yana goge jikinsa da gashin kansa,shiryawa yayi cikin favourite d'insa black colour suit ya fito tsaf kamar bbu d'igon damuwa tattare dashi ya sauko downstairs inda tarin guards dinsa,Zaki da P.A ke zaman jiran saukowar tasa ya nufi dinning direct bayan ya amsa gaisuwar da suke mishi


P.A da Zaki ne suka mara masa baya,Zaki ya fara serving dinsa breakfast P.A kuma na tsaye daga gefe.Tea ya fara hada masa,sai chips da fry egg daya zuba masa a plate bayan Zaki ya gama zai bashi waje yaji yace mata ya zauna,zama yayi yana fuskantar King


"Ka tattauna da P.A akan maganar da na maka dazu?"


"Ehh munyi ama bari ka sake ji daga bakinsa"


Kujera ya nunawa P.A shima ya zauna ya kallesa alamar ya masa bayani




"Campaign dinmu na tafiya lfy sbd kullum muna k'ara samun magoya bayan election d'inka,kana da jama'a da suke son fitowarka takara sosai ama fah duk masu karamin karfine I mean talakawa gashi ba muda means din da zamu cigaba da campaigning, the little we have komai yayi k'asa wanda hakan zai iya sawa party ya zama weak duba da yanda Governor AA KAITA ke 6arin makauniya da kudi wanda yanxu shine abu mafi rinjaya wajen al'umma shiyasa duk wasu manya k'asa suna bayanshi hakan kuma ba karamin barazana bane"


Tsap King ya gama sauraron P.A yana yiwa maganganunsa fashin baki dalla² yace


"Idan muka chanza party fah?"


"How can this be possible Sir?" P.A ya tambaya


"Party president fah?"


"You mean ANP?"


"Yes"


"Already suna da gubernatorial candidates dinsu daya fara campaigning kusan shekara kenan"


Shiru King yayi ya cigaba da cin abincinsa,shima P.A bai kara magana ba harya gama ya dau tissue ya goge bakinsa.Fita yayi gurds dinsa suka mara masa baya sai P.A dake gefensa don yanason kaiwa babban malaminsa SHEIKH IMAM MOHAMMED SULEIMAN ziyara..






_ZEE KAITA_


Gudu take shararawa cikin rashin nutsuwar jiki dana zuciya tareda tunani kala² a ranta hatta mayafin ma ajiyeshi tayi gefe gashi bbu gashin attachment d'in da take sawa akanta sai kwakwuidon kashinta da baifi tafin hannun ba a waje


"Who's behind all this,waye yake min haka,waye yake blackmailing d'ina? An sani nayi aiki ba tareda sanin wanda ya sani ba ama nasan koma waye he's close to me wanda yasan sirrina ne yasan komai nawa since from day1 yanxu kuma ance nayi freeing yaron.Sun sani kidnapping yaronta da mamanta daga baya kuma sun sace mamar sun kashe,why why"


Abinda yafi d'aure mata kai shine tho duk aikin mutum daya ne koh kua wani daban ne ya sata ta sake yaron


Ita kadai take magana kamar zautacciya tana rough driving har ta iso wani uncompleted factory wanda yake kamar store cikin wata anguwa da take kamar bayan gari sbd rashin jama'a ga koh ena duhu bbu haske wuta,parking tayi daga cen nesa ta fito daga motar cikin sauri ta karaso wajen.


Ta dade tana knocking shiru,tunawa da thugs d'in da tasa bazasu bude kofar ba inde ba waya ta musu ba ita shaf tama manta


"Ohh shit"


haka nn ta kara komawa motar ta dauko wayarta cikin sauri har rigarta na hard'eta kamar zata fadi.Kiran wayansu dukka ta dingayi ama shiru yanata ringing ba'a picking, inda ranta yayi dubu toh duk a 6ace yake dakyar d'aya daga cikinsu ta samu yay picking cikin muryar layi yace


"Alooo wai wani d'an shegiyar ne,don mai cin uwarsa zai dameni ina cen Paris tareda masoyiyata"


Tsawa ta daka mishi a wayar


"Kai dan iska kazo ka budemin ZEE KAITA ce"


"Oh oh sorry sorry"


Yana layin maye yazo ya bude mata sai faman sorry sorry yake ce mata sauran kua koh kansu bbu duk sunsha sunyi tatil.


Salim kuwa har yayi baccinsa a k'asan wajen, tun yana musu kuka harya hakura duk ya rame ya lalace


Cikin takaicin en daban Zee ta shiga tana zaginsu oho basu san ma tanayi ba sai dayan dake layi bai gama cakewa bane yake cika ta da sorry


d'aukar salim dake bacci tayi ta fito dashi.Haske ta gani kamar flash din camera cikin tsoro ta fara waigawa ama bbu alamun kuwa a wajen haka ta doshi mota tasa Salim a baya lokacin har 12 ta wuce ta bar wajen dashi


Tana hawa titi kira ya shigo wayarta da private number tayi picking cikin sauri


"Ki ajiyeshi a wajen ki wuce"


parking tayi a gefen titi kamar zatayi kuka duk ta rud'e ta fito a motar ta bude inda tasa Salim a baya tana ta6ashi kua ya tashi daga baccin ta fito dashi kan titi da yake shiru tayi ta waige² ama bataga kua ba ita de ta barshi a wajen taja motarta cikin wani wawan speed wanda ikon Allah ne kawai ya kaita gida,da mmk securities din government house din ke kallonta bbu damar tambayar daga ina take hakan nn suka bude mata ta shiga lokacin har AA ya koma dakinsa ama yana ganin time din data shigo yay murmushi kawai




A wannan daren a ranar da King yayi magana da Fahima kenan bayan su AA sun wuce yasa aka mayar da Fahima gidanta da aka ajiye mata securities biyu,tana zaune a parlor ta kasa shiga ciki har 12:30 taji knocking kofar parlor


Jikinta a sanyaye ta tashi ta bude inda tayi arba da Salim dinta a kafadar security, cikin tsantsar murna da farinciki ta kar6eshi sai kuma kuka tana kissing dinsa all ova his face da wani irin shauki na kewa.


Wanka ta mishi da ruwan zafi ta gaggasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login