Showing 51001 words to 54000 words out of 56965 words

Chapter 18 - RETURN OF THE KING COMPLETE BY APHSERT KHAIREE .txt

28 Dec 2024

3334

suce sharri ake yiwa King wasu kuma suce akoi kanshin gaskiya a maganarsu David na kusantuwar King da kunqiya


Fahima da Zee suna dage gefe jikin motar ta suna jiran Fu'ad,daman Zee tunda suka fito a asibitin suke tare a gidan Fahima


Basu fi 5mins ba sai gashi nn ya fito ya dosu inda suke


"Zanzo anjima na karbi laptop din naki,ki tabbata kin hada kan dukkan evidence din Insha Allah a zama na gaba zamu kawo karshensu"


"Insha Allahu zanyi kokari,na rasa inda nasa laptop din ne ama maybe a office na barshi yanzu zanje cen na duba sai na maka waya kazo ka karba"






_AA KAITA_


Murk'ushishi ya dingayi a qasa na azabar ciwon da cikinsa ke masa,ji yake kamar ana tsinka hanjinsa.
Tuni mutane suka cika a kansa ana tambayansa lfy,wani police dake gefe ne ya lura da cinkosun jama'ar wajen ya karaso yana tambayar meya faru


Shi ya daga AA da har jini ya fara fitowa ta bakinsa da hancinsa,yana ganin fuskarsa kuwa ya ganeshi don an kawo musu hotonsa nn headquarter su akan ana nemansa wanted
Yanxu haka patrol din daya fito dasu kenan


Wayarsu ta aiki ya ciro a aljihunsa ya kira motarsu inda sauran en uwansa suke


Suna zuwa aka saka AA a motar sai asibiti,kafin su karasa kuwa har sun kira headquarter sun sanar da ganin AA KAITA da sukayi nn take aka kira babban headquarter na Kaduna inda case d'in yake aka sanar




Bangaren Ema kuwa da farincikinsa ya sauka garin Kaduna,yasan may now maganin beran daya sawa AA ya gama dashi


sai da ya tsaya ya siya babbar Ghana most go tukunna ya dau taxi ya fadamasa inda zai kaisa,tafice mai nisa daga park zuwa anguwar da boyayyen gidan da AA yake


Bayan ya sallami mai taxi din baisha wahala ba wajen bude jam lock din gate d'in dama gwani ne wajen balle gidan jama'a don tsohon qungurmin barawo ne


Tsari da haduwar gidan har saida ya hadiye yawo haka ya dinga bin gidan da ido har ya nufi hanyar entrance nn ma karfe yasa ya balle kofar


Yana karasawa bedroom inda safe din yake ya saka pin din da AA ya fadamasa


Magudan dalolin kudade ya gani har saida yasa ihu don dadi,cikin sauri a jidesu a Ghana most go dinsa koh tsayawa rufe kofar naiyi ba ya fice a dakin ya fito compound


"You're under arrest, ur hands behind ur back"


Cikin razana ya saki jakan ganin en sanda a zagaye dashi koh ta ina






_KING_


Yanda jikinsa ya dau zafi ga wani rawan dari da fargici da King keyi ya mugun tsorata Dija


Hugging dinsa tayi sosai tana hawaye don bata taba ganinsa cikin wannan yanayin ba


Karatu ta fara masa a kunnensa cikin zazzakar muryarta dake hade da kuka, basu fi en mituna ba ya fara ajiyar zuciya a jajjere ya kwantar da kansa sosai a jikinta ita kuma ta cigaba da masa karatun tana shafa kansa har bacci mai nauyi ya daukesa


Batayi wani yunkuri ba dukda nauyinsa daya sauke mata hakan nn ta kyalesa sai ma kara makalesa a jikinta da tayi ta jingina da jikin kofar
[1/6, 9:17 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*


BY
Aphserteen khairee




ELEGANT ONLINE WRITERS




41


King ba shi ya farka ba sai pass 10 ama sai ya k'i bude idonsa yana jin kamar mafarki yakeyi,yana bude idon zai ganshi shi kadai a dakin dukda yana jinsa a jikin mutum


Wata zuciyar kuma na fatan ace mafarkin ne daya tuna da maganar doctor


_"He's no more"_


Bude idonsa yayi cikin firgici yana


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,Zaki"


Yanda ya firgita yasa Dija itama farkawa tana kallonsa da mamaki,kafeta shima yayi yana kallonta.
Tabbas ba mafarki yakeyi ba,wnn dijansa ce a gabansa


Ya rasa wani irin yanayi zuciyarsa ke ciki.Farincikin ganin DIJA koh alhinin rasa ZAKI


Higging d'inta yayi sosai tana ji yanda zuciyarsa ke tsananta bugu


"Ka tashi muyi sallah"


Ta rad'a masa a kunne,girgiza mata kai kawai yayi ta taimaka mishi ya mike


Tare suka shiga toilet d'in yana biye da ita. Har abin ya suma bata tsoro don ta tabbata yanayin king kam ba wai shock din ganinta bane akoi abinda ya faru


Saida ta taimaka masa yayi wanka itama tayi suka dauro alwala tukunna suka fito,jallabiya ta dauko masa a cikin closet dinsa itama ta zura daya ta saka hijab dinta King ya jagorancesu Sallah


Suna idarwa Kuka hawaye suka fara lalle marhabun a kumatun king.


"Allah ya jikanka da rahma Aliyu,Allah yasa wnn sadaukarwa da kayi ya zama sanadiyyar shigarka aljannah kenan, Allah ya kyautata makoncinka.
Ka yafemin Zaki,ka yafemin,ka yafemin.Ni nayi dragging dinta into all this mess"


Sai lokacin DIJA ta fahimci dalilin shigar King shock,tunawa da waye Zaki,alherinsa,sadaukarwarsa na komai akan King ga kuma tarin tambayoyin da takeso ta mishi ama gashi yanxu yama bar duniya.


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun"


Sai hawaye itama daga ita har King an rasa mai rarrashin wani


Daren da take burin gani da mafarkin samu ya zame musu daren alhini na rashin Zaki


Babu abinda King ke tunawa kamar irin tsantsar shaquwa da kaunar dake tsakaninsu.


Zaki wani irin mutum ne wanda kai tsaye baka isa karantar halinsa,bazaka taba cewa Zaki yana son wani ba shi kawai kullum cikin aikinsa yake ama kuwa deep inside him kaunar uban gidansa ne


Zai iya yin komai akan king,zai iya rasa komai akansa,zai iya halaka kowa a kansa danma King ya tausarsa don shi kadai yake iyawa halin Zaki


Idan kaga Zaki na hira tho da king ne,dariya kuwa daman baya cikin halinsa koh hiran ma da sukeyi da King saide a kan aiki koh wani abu


Yana da mugun zurfin ciki ga bawa lokacin mahimmanci snn baya taba yin abu cikin gaggawa komai akan ka'ida yakeyinsa duk abinda zaiyi saiya bashi isheshshen lokaci kafin ya aiwatar


Tunawa yayi da ranar da Zaki ya karbi Kalmar shahada da aka tambayeshi wani suna yakeso


"Dukda bansan sunanka ba My king,naka sunan nakeso don inason nayi kwatanta koyi da halinka na son kawo cigaba tsakanin al'umma da yawan alkhairi"


Har ransa King yaji kaunar Zaki ya shigesa a take yanajin sa kamar blood related brother dinsa.Sheikh Imam Suleiman da yace


"Masha Allah,tabbas kayi zabi na kwarai don tun daga kan mai sunan Sayyidina Aliyu RA wanda ya kasance Sahabi mafi kusanci da Annabi SAW snn suriki a gareshi.
Muna maka fatan koyi da wnn suna mai daraja snn ka zama asalin Zaki mai taimako da tsoron al'umma da dukkan karfinka da iyawarka


" Menene ma'anar ZAKI"


Zaki ya tambaya,King yace masa


" *LION*"


"Wowwww,you're LION My King"


Dafa kafadarsa King yayi yace


"You're the real LION"


_FAHIMA_


Gudu take shararawa a motarta daga office suke ita da Zee,rashin ganin laptop dinta duk ya firgitata


Toh ina ta saka,ya akayi ta nemeshi ta rasa.
Baya gidanta da ta buda tuntuni duk tsammaninta yana office gashi nn ma baya nn


"Easy Fahima,Insha Allahu zamu gani maybe yana gidan de"


Zee ta fada donta kwantarwa Fahima hankali


"Bazaki gane ba Zee,wnn ne kadai evidence d'in da zai wanke King daga mugun tuggun da suke kokarin kulla masa don tabbas idan court da yarda da zancensu na King na cikin kunqiya duk kusan hukunci daya zasu fuskanta kinga kuwa bazamu bari mutumin da tseratar damu daga masifar da muga shiga ba shi ya fada ciki
Badan shi ba da yanxu saide wasu ba mu ba"


"Hakane Fahima kuma,Allah kadai yasan dubbin rayukan da suka ceta.Allah sarki Zaki wallahi naji bbu dadi mutuwarsa ban rokesa ya yafemin ba na haushinsa dana dingaji a baya ina ganin shi yamin katanga da King"


Fahima de bata kuma magana ba har suka isa gida,nan ba bbu inda bata sake dubawa ba ama bbu laptop


Kiran Fu'ad ne ya shigo wayarta tayi picking a kasalance


"Ya ake ciki,kina ina zanzo yanxu na karba laptop din inason nayi printing out din komai kinsan de jibi ne 22 din so bamu da isheshshen time"


"Wallahi fuad banganshi ba"


Bakiga me ba?"


"Laptop din"


"Innalillah,Fahima garin yaya"


Take ta tuna da microphone din data Bawa King tace


"Alhamdulillah,there's another way out.kaje wajen king zai baka wani microphone"




Koda Fu'ad ya iso gidan King saida ya jirasa a parlorn qasa don yau kwana 5 knn da rashin Zaki,tunda Mario yace masa an kaishi washegari bai sake saukowa daga samansa ba


Gabadaya ya rasa nutsuwarsa,ya kasa dawowa seti dukda kokarin da Dija takeyi na kula dashi


TayiΒ² dashi ya fawwalawa Allah komai ya fita cikin jama'a yayi facing abinda ke gabansa ama ya kasa


Koh zuwan Fu'ad dakyar ya sauko qasan,bayan sun gama gaisawa Dija ta kawo masa Drink da rowa don yanxu kam guards basa zama a parlor tunda ta dawo


"Dama akan case dinsu AA KAITA ne,so munyi lacking evidence sosai gashi suna kokarin zan sunanka izuwa kunqiyarsu don har shaidu suka bayar"


King daya kwantar da kansa kan cushion idonsa ya lumshe yace


"Ka kyalesu suyi yanda suke so"


Tsaraf Dija dake zaune kusa dashi tace


"No way,Barrister Fu'ad ya kake ganin za'ayi?"


"Fahima Aliyu tace min akoi wani microphone data Bawa King a asibiti Wanda yake dauke da dukkan wani shaida da zai wanke King daga zarginsu shine nake buqata yanxu"


"Bad'd'o ina ka ajiye please?"


Dija ta tambayeshi,dago rinannun idonsa yayi yana kallon yanda ta marairaice yace


"Nima bansani ba,bansan inda yake ba"


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun"


Kawai Fu'ad ke maimaitawa snn yayi karfin halin cewa


"Ana buqatarka a zama na gaba,bamu da wani shaida da zamu iya wanke ka saide kai ka wanke kanka. Allah ya taimakemu"




Bangaren AA KAITA kuwa da aka kaishi asibitin likitoci sunyi iyakar kokarinsu wajen ganin sun dakatar da aikin gobar a jikjnsa ama ina ta rigada ta bata masa wasu kayan cikinsa


Yana cikin tsananin azabar haka aka sakashi a jirgi akayi Kaduna dashi bakin rai bakin fama haka yake fitar da wani ruwa mai wari ta bayanshi sbd lalacewar da hanjinsa yayi ga cikinsa daya kumbura


Koda aka kawoshi Kaduna asibiti aka saukeshi nn ma suka bashi treatment sosai sbd a samu a kasance a court a zama na gaba don shima ya karbi hukuncinsa.Yayi jinyar a gidan yari






_22 September...... FEDERAL HIGH COURT KADUNA STATE_


Duk an gama hallara a court daya cika yayi makil da jama'a har daga wajen sbd ana sa ran yau ne zama na karshe da za'a kawo karshen wnn sharia daya zama talk of town


Duk wata kafar sadarwa duk wani lugu da sako na ciki da wajen Kaduna maganar da akeyi knn


Shari'a tsakanin aminai biyu,tsohon gwanma kuma mai takara a yanxu da kuma gwamna mai ci a yanxu kuma Dan takara na gaba


Ga kuma en kunqiya da zargin da ake yiwa King na shima yana daga cikinsu,abinda yafi jan maganar jama'a knn don kaso 80 cikin 100 sun yarda da cewa King na cikin kunqiya tsafi da jinin al'umma








Muje zuwa a next page don jin yanda wnn Shari'a zata kaya...
Ina mai kara miko ta'aziyyata na rashin LION dinmu 😭😭😭
[1/6, 9:17 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*




BY
Aphserteen khairee


ELEGANT ONLINE WRITERS




42




Tsittt court d'in ya d'auka ina jiran mai gayya mai aiki CHEIF JUSTICE ISYAKU BARAU ya shigo.King,Fahima,Zee da en gidansu Fu'ad da suma yau suka hallaci zaman suna daga gaba


Tunda aka shigo da AA KAITA akan wheelchair anyi handcuffed d'insa ya d'aga kai ya kalli King sai hawaye,suna jere tare dasu David,Baban Fahima,gboy sai suleguy.
Daman su Samuel an kwana biyu a tare da walak'iri


Gabadaya kan Barrister Fu'ad Hashim ya d'au chaji sbd rashin kwakkwaran shaidar da zai wanke King shiyasa tun kafin su shigo Fahima ke tausarsa akan ya kwantar da hankalinsa Insha Allah,Allah na bayan mai gaskiya


Shigowar Cheif judge kowa ya mike kamar yanda al'adar court take,nn aka fara gabatar da shari'a dakiΒ²


Barrister Fu'ad Hashim ne ta fara daga yiwa sauran suspects d'in tamboyoyi,da akazo kan Baban Fahima kuwa k'in kallon wajen Fahima tayi suna hada ido sau daya ta kauda kanta


King kuwa tunda aka fara bai d'ago kansa ba,shi hatta tunaninsa da hankalinsa baya tare dasu.Alhinin rashin masoyinsa kadai ya isheshi


"MOHAMMED ABDULLAHI GIWA....MOHAMMED ABDULLAHI GIWA,Court na buqatar ganinsa"


Sai da Fahima dake gefensa ta d'an tabasa tukunna ya daga rinannun idonsa wanda ita da kanta saida ya tsorata ta snn ta mishi nuni da shi ake kira


Idanuwa dubbin jama'ar dake makeke dakin shari'ar ne ya dawo kansa, a hankali yake takawa harya karasa wajen amsar tambayoyi


Gyara tsayuwarsa Barrister Joseph yayi sannan ya fara magana


"Court zataso jin wanene King"


Nan King ya gabatar da kansa still idanunsa a qasa


"Koh mai zaka iya cewa game da zargin akan kunqiyar tsafi wanda kwararan shaidu sun nuna hakan"


"Bani da abinda zance akai illa abinda yake a zahiri"


"Menene a zahirin?"


"Bana daga cikin kowacce irin kunqiya balle kuma ta tsafi,hasalima ina daga cikin wa'inda suka jajirce wajen ganin mun kawo karshensu"


King ya bashi amsa with full confidence, and this time around idanunsa na kan Barrister Joseph




Yanda King ya kafe Barrister Joseph da ido yana aika masa wani irin kallo dayasa barrister sunkui da kai da sauri don har kamar wani majigi ya gani a idon King d'in


Cikin karfin halin barrister Joseph ya kuma wajen desk dinsa ya dauko wani photo ya nunawa King


"Me zaka iya cewa akan wnn photon,sauran en kunqiya sun bada tabbacin aiki aka baka a kunqiya na kawo jinin mutum washe garin saukarka a kasar nn?"


Kallon photo King yayi dakyau,tabbas ya gane ranar da aka dauka yayi murmushi yace


"Wannan photo tabbas an daukeshi ne a washegarin dawowa na,na kaiwa iyayena da al'umma Annabinmu ziyara makabarta"


"Koh zaka iya fadamana jinin menene a jikinka?"


"Yankata akayi da wukan akan hanyarmu ina daga cikin mota"


Juyawa Barrister Joseph yayi yana fuskantar mai sharia yace


"Ya mai girma mai sharia, Mohammed Giwa da lawyernsa basuda wata kwakkwarar shaida da zasu wanke kansu daga zargin da ake masa.Ga dukkan shaidu da kwararan hujjoji da muka bawa court sun nuna Mohammed Giwa nada hannu dumuΒ² a cikin wnn kunqiya duba yanda aka sameshi shima a wnn gida na tsafinsu,idan kuwa baya cikinsu toh tayaya ya isa ga wnn gida,waya kaishi?


Abisa binciken da mukayi ya nuna Mohammed Giwa ya zabi ya tsarwatsa wnn kunqiya ne sbd biyan buqatarrsa akan takararsa na gwanma da sukeyi tare da Amininsa AA KAITA.


Kamar yanda mukaji ta bakin AA KAITA,MOHAMMED GIWA yayi kokarin tsarwatsa kunqiyar tasu ne sbd duk shaidu da hujjoji da muka nunawa court akansa da suke nuni da yanada alaka da kunqiyar wanda takun da sukeyi da aminnasa yasa AA KAITA yi masa barazana dasu don ya hakura da takarar gwanma.


Ganin AA KAITA da gaske yake zai iya tuna masa asiri yasashi daukar mataki wajen tarwatsa wnn kunqiya batare da sanin shima kansa zai fada ciki ba"


Maida kallonsa yayi kan king snn yace


"Idan har kace baka cikin kunqiya,toh ya akayi iyayenka suka rasu a rana daya kuma likitoci sun tabbata bbu koh ciwon kai?
Ina kakai matarka da yaranka en biyu daga haihuwarta aka nemeta aka rasa?
Kai kuma sanin cewa dole za'a tuhumeka akan batar matarka da yaranka aka nemeka aka rasa na tsawon shekara 6"


King ji yayi Kansa na juya masa sai wani irin numfashi yake saukewa,fuskarsa da idonsa sunyi jawur.Hatta Fahima da Fu'ad mamakin Barrister Joseph dasu AA KAITA sukayi na iya hada irin tuggu haka don kawai suyi dragging dinsa cikinsu bama ta neman kubutar Kansu suke ba don sunsan bbu yanda za'ayi su kubutan shine suke neman yanda zasu jawo King.
Wato a mutu tare.




"Ina raye, babu inda King ya kaini sannan ba shi yayi sanadiyyar iyayensa da 'ya'yansa ba"


Sukaji murya na daukar dakin court,take kowa ya maida akalar kallonsa kan inda wannan murya kai fitowa.Wani wawan ajiyar zuciya Fahima,Zee da Fu'ad suka sauke a kusan tare


"DIJAH"


Zee ta furta cikin dubbin mamakin ganinta a raye kamar wani abin almara koh mafarki


"DIJAH"


Itama Fahima ta maimaita sai kuma sukace


"Alhamdulillah"


Har suna hada baki wajen furtawa,ga wani murmushin farinciki daya subuce musu


"Wacece ke kuma daga ina?"


Wani d'an sanda ya tambayeta a tsawace


"Sunana KHADIJA BUBA wato DIJAH,nice matar MOHAMMED GIWA wato KING"


Hanya Dan sandan ya bata ta karaso har inda King yake,kansa da yakeji kamar ya tsage yana k'asa kawai jinsu yake ya runtse idonsa.Hannu tasa akan hannunsa dake damke kan katon dake gabansa sai lokacin ya daga kai ya kalleta


Take idanunta ya taro kwalla ganin yanayin da baddonta ke ciki gashi daman yana tsaka da alhinin rashin Zaki,lumshe masa ido tayi a hankali da budesu alamar ya kwantar da hankalinsa sai kuwa ya mata Dan murmushi koh ba komai ya samu Dan sassaucin daga radadin da yakeji a ransa


"Zaki iya fadawa court hujjarki na fadar hakan da shaidar cewa bashi yayi sanadiyyar iyayensa ba sannan duk tsawon wannan lokacin ina kika shiga,ina kuma abinda kika haifa?
Don mun samu tabbaci a asibitin da kika haihu cewar an nemeku keda yaran ne an daga haihuwarki"




"Ni nake da dukkan shaida,hujja da amsar tambayoyinku"


Muryar da tafi kowacce daukar amon sauti ta bayyana a dakin shari'ar,wani ihun dadi FAHIMA ta saka wanda yake dauke da very surprised shock tana




" ZAKI"






πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»
Ina jiran ruwan comments 😘
[1/6, 9:17 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*



By
Aphserteen Khairee


ELEGANT ONLINE WRITERS




*JERIN LITATTAFAN ELEGANT ONLINE WRITERS MAI TAKEN ELEGANT 5STARS* ✨πŸ”₯


*IDAN ZUCIYA TAYI WAKE*- Meerah
*TUGGU BIYU*-diamond Aleesha
*ZUBAR HAWAYE*-Gimbiya Ayush
*MATA A YAU*-Aphserteen khairee
*NIHLA*-Mammy Kabeer


Akan farashi mai sauki
5_500
4_400
3_300
2_200
1_150


Zakuyi payment d'inku ta 0623151889 AISHA NURA MURTALA GT BANK sai evidence of payment ta wannan no 08148360851
Kati waya na MTN 09067211352


GA MAI BUQATAR MATA A YAU YA TUNTUBENI TA
07086037570


SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA 🀝🏻




43


Tsananin firgice,tashin hankali da d'imuwa AA ya shiga sbd yasan tabbas Zaki sai ya tune dukkan wani k'ulli right from the beginning.
Yasan k'ok'arin tarnishing image d'in King da suke zai juye kansu


Addu'a yakeson yaji ya tsafko a bakinsa ama sai yaji ya kasa sam kamar bai ma tab'a karanta kowacce irin addua a rayuwarsa ba gashi fah ya iya d'in don yana da sittin akansa ama shi kansa ba zai iya cewa ga ranar daya firta bismillah ba balle akai ga karatun surori daga cikin littafinmu mai girma ba


Hawaye ne suka fara kwaranya daga idonsa,tabbas yasan shi kam tun daga yau,tun daga duniya hisabinsa ya tsaya


Yau ga ranar da ake fada,ranar damana,ranar da baki bazai iya furta Kalmar tuba ba


Kaiconsa,kaicon rayuwarsa,kaicon idanuwansa da suke rufe don neman duniya,kaicon hankalinsa daya gushe don biyewa son zuciya da kwadayin abinda yake ba dawwamamme ba.


Zaki dake tsaye daga bakin kofa da farar jallabiya a jikinsa hannayensa dukka biyu rikeda sandar dake taimakawa masu karaya wajen tafiya makale daga hammatarsa


Kana ganinsa kasan ya raunato,ya jinyato don karayace a dukkan kafafunsa biyu danma karfin hali da zuciya irinna jaruman mazan nn wanda suke iya shanye zafi da rad'ad'in kowanne irin rauni ne kawai balle kuma shi da yake retired member AARE DAPO na AWAWA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login