Showing 33001 words to 36000 words out of 56965 words

Chapter 12 - RETURN OF THE KING COMPLETE BY APHSERT KHAIREE .txt

28 Dec 2024

3337

yana murmushi yace


"Ni Aliyu Giwa the words in my heart?" Sai kuma yayi shiru na en seconds tukunna ya cigaba


"Na taso a tsakiyar talakawa,na rayu da soyayyar al'umma,na gina zuciyata da murad'in taimako da kawo kowanni irin cigaba a k'asata baki daya,ina fatan da add'uar Allah ya cikamin burikana na alkhairi akan dukkan al'umma.Masoyana masu goyon bayana,en uwana da abokan arziki kai harma da mak'iyana masu son ganin bayana ina musu fatan alkhairi a koda yaushe.These are the words in my heart"


"Masha Allah"


Fahima tace tana kallon King daya cigaba da magana


"My desires?"


Shima ya fada da sigar tambaya nn ma ya cigaba


"Is to be a great and good leader to my good people and great nation.Sai me ma kika tambaya?"


"Your fears Sir?"


D'an lumshe ido yayi ya bude,yanayin fuskarsa ta chanza a take ama yayi kokarin controlling kansa da hanyar kwakulo fake smile yace


"Abinda nake tsoro a raina yanxu biyu ne,Na farko shine rasa matata,that's my first fear.Inason amfani da wnn d'ama wajen rokon barar al'umma da dukkan masoya na dasu tayani addua Allah ubangiji ya bayyana min ita cikin gaggawa da koshin lfy"


Shiru ya d'anyi wanda yasa Fahima yin shiru itama tana kokarin son karantar yanayin da yake ciki,hakama masu saurare daga kan radio da masu kallo a TV hakama masu bin shirin live a kowanne kafar sada zumunta duk sun tsaida hankulansu sun dakatar da comments dinsu suna sauraron King daya cigaba da magana


"Second fear d'ina shine ache nasamu mulki amma na kasa cika burikan talakawa na kasa riqe amanar da Allah ya danqamin nakasa yin adalci, naji son mulki da giyar mulki ita take juyani naji cewa zuciyata ita take juyani takesani yin abinda raina keso,naji cewa kaina nakeso nagini ba qasata da al'umma naba"


yadakata kadan sannan yaja numfashi murya na rawa yace


"Yah Allah karka bani waanan mulkin in har zansamu namanta dakai,Yah Allah karkabani wannan mulkin inhar zan sab'a maka ya zama sanadiyya halakata ta hanyar sa bayinka cikin kuncin rayuwa"


Ji tayi jikinta yayi sanyi,taji bazata iya masa tarin tambayoyin da tayi niyya ba don ya rufe mata baki da maganganunsa.Ajiyar zuciya ta sauke snn tace


"Ameen ya Rabbi,my last question is What's the secret that kept you in for so long Sir?"


"It's had been a while,na tsawon shekara 6 da nayi bbu wani sirri daya boyeni.A kullum ina kwana na tashi da kewar k'asata,Masoyana baki daya.Addu'ata kullum Allah ya dawo dani gida lfy cikin aminci,al'ummata su karbeni with their clean heart su bani damar jagorantarsu a karo na biyu da dukkan karfina.There's no secret that kept me in for so long"


Anan Fahima ta rufe shirin tare da yiwa King godiya,har yaje parking space jama'ar wajen na biye dashi a baya suna ce masa sai kayi tare da jinjina masa da addu'ar Allah ya bayyana masa matarsa da samun nasara kan takararsa.Hatta ma'aikatan wajen jikinsu yayi sanyi dajin kalaman King din haka Fahima ta dawo office dinta jiki a sanyaye ta tattara ta koma gida kawai don bataji zata iya wani aikin kuma tana buk'atar hutu don samun kwalkwalwarta tayi aiki da kyau.


Washe gari ya kama Thursday ta tashi as usually tayi shirin office dukda jikinta still a mace yake wanda ta rasa dalilin faruwar hakan,abubua dewa suke mata yawo a kwanyarta da takeson aiwatarwa cikin k'ank'anin lokaci wanda dukka yake buk'atar dogon nazari da bincike akai gashi tanaso a weekend dinnan taje ganin Babanta kamar yanda ya bukata dukda shima tafiyar a sanyaye take tashi tanaji kamar karta je ama dole ta kokarta taje din koh da kwana daya ne tayi ta dawo.


Harta shiga motarta sai taji buk'atar zuwa taga Salim tunda har yanxu 8am baiyi ba maybe ta samesu a gida bai tafi school ba,nn ta juya akalar motarta zuwa anguwarsu Fu'ad


Luckily kua ta samesu a bakin gate sun fito daga gida knn mai gadi ya rufe Fu'ad zai sauke Salim a school kafin ya wuce wajen nasa aikin.Ganin motar Fahima ya sashi parking a gefe itama tayi tareda fitowa ta doshi motar Fu'ad d'in


Salim na ganin mummynsa ya bude kofar motar dake zaune a gaba ya fito da gudu yana mata oyoyo inda tayi rungumeshi cikeda kewar d'an nata,fitowa shima Fu'ad yayi yana kallonsu yayi folding hands dinsa


"Mummy I missed you,when are you coming back to daddy ni banason gidansu grandma kullum tana yiwa daddy fada wai kar yaje wajenki kuma nima tace bazan koma wajenki ba"


Ya fada cikin muryar shagwaba da iyakar gaskiyarsa,kissing din cheeks dinsa tayi tace


"Don't worry babyn mummy, mummy is soon coming to take you back home"


Yeeyyyyy ya fada cikin jindadi yana tsalle,matsowa Fu'ad yayi kusada su ba tareda ya kalleta ba ya kama hannun Salim


"Oya let's go,we're late"


Saida Salim ya shiga mota snn Fu'ad ya juya ya kalleta


"Duk lokacin da kika shirya zama full house wife and caring mother,you'll always be welcome with an open arms"


Bye² Salim ya dinga mata har Fu'ad yaja motarsa ya barta tsaye a wajen cikin mutuwar jiki take taji hawaye ya fara sauka a idonta ta kusa 20mins tsaye a wajen dakyar taja kafarta ta karasa wajen motarta. Hakama a motar saida taci kusan 10mins tukunna ta tayar tana tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki a takaice saida takai pass 9 kafin ta iso office


Tun a nesa ta fara hango taron jama'a da motocin en sanda an kewaye ma'aikatar tasu yanda bbu wanda zai shiga wajen in ba jami'in tsaro ba.Daga dan nesa tayi parking ta fito tsorace ganin ambulance ana kokarin saka mutum cikin jini kaca² wanda har baka iya gane wanene yasa gabanta wani mugun faduwa har jikinta na rawa


Cen ta hango Boss yana magana da wani security, cikin tsoro ta karasa inda yake tana


"Meyafaru Sir,wanene wnn,meyasa meshi?"


Tayi tambayar a kidime tana kallon ambulance din da aka rufe suna kokarin fita dashi ga hayaki dake tashi daga compound din ma'aikatar hanyar shiga ciki harda jini a kasan


"Messenger Dauda ne"


Boss ya bata amsa shima da Kansa cikin tashin hankali yake


"Meya sameshi?"


"Boom ne ya tashi dashi,snn wanda suke zaune tare dashi yaji lokacin da akace masa yakai miki sak'on wanda ashe boom ne"


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"


Kawai take ta ambata.....








A cigaba da manage 🙈


[1/6, 9:08 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*




BY APHSERTEEN KHAIR


*ELEGANT ONLINE WRITERS*




25


Tana tsaye a wajen har kusan 5mins ta kasa motsawa,kwakwalwarta ta toshe ta rasa wani irin tunani zatayi.Wani iri takeji a jikinta da zuciyarta na zargin kanta akan mutuwar bawan Allah nn ta zama sanadin rabuwarsa da iyalansa,yaransa a lokacin da suke tsananin buk'atar mahaifinsu.


"Wayyo ni Fahima,kaico na dana zama sanadiyyar rugujewar farincikin wasu don kawai kokarin tono abinda yake binne gashi ance dana sani k'eya ce"


Hawaye kawai take ta zubar kamar an bude maceccen tap wasu na rige²n zubuwa,muryar Boss taji a kanta ya mata magana da kausasshiyar murya da take bayyanar da tsantsan 6acin rai dayake zuciyarsa akanta


"Daga yau nayi cancelling wnn so called program d'in naki and u have a 2wks suspension"


yana gama fad'a ya wuce ya barta tsaye a wajen itama dakyar taja kafarta ta karasa wajen motarta, dafe kanta tayi da sitirayin motar tanaji yanda kan yake sara mata taji wayarta na ringing daga gefe.Hannu tasa ta d'auko wayar ba tareda taga mai kiran ba don koh d'ago kan nata batayi ba


"Na turomiki address ki sameni a wajen idan kinason sanin, who's behind all this".


Kit aka kashe wayan, sai kawai tabi wayar da kallo tana tunanin waye wnn kuma? Wani kiran ne ya shigo wayarta na Fu'ad ta d'aga a kasalance tun kafin tayi magana ya fara a rud'e don ya samu lbryn abinda ya faru


"Heema are you ok, kina ina yanxu nazo na daukeki hope bbu abinda ya sameki? Please talk heema ina cikin tashin hnkl"


Ajiyar zuciya ta sauke wanda har Fu'ad na iya jiyota yace


"Alhamdulillah, please kina ina?"


"Am fine Fu'ad u don't need to worry"


"No heema you're not,u don't sound ok. Please lemme cum and pick u up"


"Karka damu Fu'ad wallahi am fine,basai kazo ba I've sumtin to attend to now"


"Wai kina nufin haryanxu baki daddara ba heema?"


"It's urgent kuma yana da matukar mahimmanci,so I've to"


"Hmmmm fine,Allah ya bada sa'a keep risking ur life.Ki sani heema idan kikamin sanadin na rasaki bazan ta6a yafemiki ba,I promise you that"




Ya kashe wayarsa,zuciyarsa na kuna da bacin rai na shegen taurin kai na Fahima,ga haushin kansa dayake ji daya kasa shareta taje tayi duk abinda takeso tunda ta nuna ita ta zabi aikinta again and again kuma kullum sake tabbatar masa da hakan take ama ya rasa meke damun zuciyarsa da bazata iya zuciya da ita ba,ya rasa wani irin so yake mata.


Wani huci mai zafi ya fesar daga hancinsa yana


"it's ova,am done heema daga yau bazaki sake jina ba na barki kiyi rayuwarki yanda kikeso tunda keda kike mace ma kin nuna u can live without me then why can't I"


shi kadai yake magana a office dinsa yana daga tsaye yaja tsaki ya kuma kan kujera yana kokarin fixing kanshi da son kawar da damuwar dake ransa ta hanyar janyo aiki ama ina koh takarda ya bude sai yaga kamar photo heema ne cikin tashin hankali, hanaklinsa ya kasa kwanciya gani yake kawai itace next attempt dinsu tunda yanxu ma ita akaso kashewa


"innalillahi wa inna ilaihi raji'un"


yaketa maimaitawa ya tashi yana zagaye office din yana tunanin kar wani abu ya sameta.




Bangaren Fahima kuwa Fu'ad na kashe wayar taji jikinta yayi sanyi,taji aikin ya fita a ranta gabadaya,taji bazata iya zuwa wajen inda ya kirata ba gwanda ta hakura kawai tabi mijinta da d'anta da suka rage mata yanxu suke tsananin buk'atar ta. Dialing call ta shiga zata kira Fu'ad saiga wani message ya sake shigo mata


"Koda kin karaya,tabbas bazasu daina bibiyarki ba tunda ke kika faro aikin kuma tabbas ki karasa shi.Just follow the address am waiting for you there"


Ji tayi gabanta ya yanke ya fad'i,cikin Sauri ta tada motarta tabar wajen tabi address d'in da aka turamata .Tana karasowa anguwan dake shiru bbu gidaje sai factories da uncompleted buildings tayi parking a gefe ta dau waya zata kira numbern taji ana knocking window ta


"Zaki,you?"


Ta fada da so much surprised on her face don bata taba tsammanin shine ya kirata ba,zagayowa yayi ya bude front seat ya zauna yana kallonta


"Kinason sanin wanda ya aiko miki da package din yau?"


Girgiza kai kawai Fahima tayi ta kasa magana,saida yayi shiru na en seconds tukunna yace


"It's King"


"King kuma?"


Ta tambayeshi da mamaki a fuskarta


"Yes shine"


"Ama meyasa,kuma kaima meyasa kake fadamin?"


"Sbd na tayaki aikin da kika fara na neman sanin wayeshi"


"All I know is kai loyal servant dinsa ne but why?"


"Sbd nafi kowa sanin wanene shi"


"Zanso sanin...
WHO'S ZAKI?
MENENE ALAKARKA DA KING?
FOR HOW LONG AV U BEEN TOGETHER?
WANI IRIN AIKI KAKE MASA?"


Fahima ta jero masa tambayoyin tana kafeshi da ido,cire bakin glass din idonsa yayi wanda ya kara fito da asalin kamaninsa da Yoruba ga wani tabon yanka daga kasan idonsa dake j baajir


"Ayau zaki sami dukkan amsan tambayoyinki"




ZEE KAITA
Tunda su King suka fice suka barta dukunkune cikin blanket take kuka kamar ranta zai fita,tafi hour tanayi har saida taji kanta ya fara Sara mata,bata taba nadamar rayuwarta irinna yau ba,bata taba danasanin abinda take aikatawa duk irin alfashan da takeyi sai yau.Yanxu in King ya watsata a duniya ya zatayi


"Ka cuceni AA,ka cuceni duk kaika jawomin wnn masifar"


Dakyar ta tashi ta zura rigarta tasa hijab ta dau jakarta koh niqab din bata tsaya sawa ba ta fice danma dare ne koh ena yayi shiru don kusan 12.
AA dake ta zagaye a dakinsa yana wani irin huci kamar zaki don takaici da bakin cikin abinda Zee tayi don yaga kadan daga abinda ya faru ta camera daya sa mata a gaban rigarta,daga shigarta dakin yaga lokacin da P.A ke tsaye ya juya mata baya shi da kansa da farko ya dauka King ne sbd shigarsa saida ya juyo tukunna yaga fuskar P.A yana murmushi harya karaso kusada Zee din.


Abinda ya bashi mamaki shine yanda Zee ta karbeshi knn plan ta hadamishi tace mishi King ne,yana kallon yanda suke iskancinsu har sai lokacin da ya cire mata shigar ya rufe camera daga nn bai kara ganin komai ba.


Banko kofar dakin AA tayi idonta shame² da hawaye ta karaso gabansa


"U ruined my life AA,ka cuceni ama wallahi wallahi kaji na rantse inde King ya bazani a duniya I won't hesitate to kill u da hannaye na"


"Will you shut up or else I'll slaughter ur motherfucking ass right here like the bitch u are, you think u can double cross me kinyi kuskure and I'll punish you right away kafin ki samu damar kasheni kin d'and'ana azabar da baki taba tunani ba.Tun daga nn duniya zaki ziyarci hell kafin na aikaki cen"


Zatayi mamaki knn ya rufa mata wani jen kyalle,take ta 6ace a wajen haka shima yay wani irin maganganu na tsafinsu ya 6ace.


******************
_FAHIMA_


Tabbas a yau zaki samu dukkan amsoshinki daga wajen,kamar yanda na fada miki asalina yanxu zaki san cikakken lbry na


_WANENE ZAKI_


Mahaifina ya mutu tun ina karami dagani sai mahaifiyata da take fama da ciwon daji a kafarta,tsananin talauci da yunwa ga rashin mai taimako ya jefani sata don neman abinda zamuci nida mahaifiyata haka nake zuwa gidajen jama'a nayi satan abinci muci tun ina 7yrs.


Gradually ina girma mugayen halayya da bushewar zuciya na d'aduwa min zuwa lokacin har na shahara a sata don har tare mutane nake da wuka na kwaci abin hannunsu kuma kamar yanda na fadamiki anguwarmu getto ce bbu mai kwabar wani a haka har na shiga kunqiyar AWAWA group.


Akoi watarana da en wata kunqiya ta tantirai suka shigo yankinmu wani yaronmu yazo ya fadamana


"Oga boxer dat area boys wey dey back streets dey our area looking for u now"


ana sanar damu en AWAWA muka shiri da wukake,makamai kala² muka nufesu lokacin ban zama shugaba ba munada wani shugaba ana kiransa BOXER wanda shi yake bamu aiki kowanni iri na ta'addanci.Muna karasowa suma gasu nn da makamansu,ina gefen Oga boxer yace


"Na wetin una dey do for this area?"


Daya daga cikinsu yace


"Bros we no here for fight,Na warning we came warn u guys"


"Who be ur bro,tani bro shey Wereni (are you mad)?"


Daya daga cikin wa'accen dayaga en AWAWA bazasu tsaya ayi maganar arziki ba yace


"Look,na war front we dey oo and my bullet no dey select"


Zaki da suke kira da stone yace


"See we no dey follow headless children dey talk,ur olori (shugaba) don die if u na get another one call us we go hear am later"


"Hey hey come back here Jere,if oga die na another one go born.We get another ilori"


Bubbudewa sukayi sai ga wani matashin saurayin mai karamin jiki na fito yana wani taku na tsantsar gajeri da dabanci jikinsa duk tatoo,suna mishi kirari da


"Chiki,chiki"


dariya en AWAWA suka sa mishi daya daga cikin su yace


"Taata.. U supposed dey house dey suck mama breast"


"Bring your mama breast make I suck am,see gari no get advert but dey sell pass anything.My name na CHIKI AKA small body big engine"


Stone(Zaki) yace


"Oloriburukuni (zagi da yarbanci)"


Nan en kunqiyar Chiki suka fara mishi kirari yana wani girgiza


"Chiki,chiki...Bike bigger than sienna,Boss on top bigger than 1million.He's an ever lasting father"


Chiki ya dakatar dasu yace


"Boxer me and u never meet,no proper introduction"


"And this land no be ur territory, so make una comot from here or else u Guy's go die.My screwdriver dey find blood"


Zaki ya katseshi,nan najiyo muryar wani bahaushe cikin en kunqiyarsu Chiki yana


"Kai dalla yi mana shiru anan don gutsun mai anguwar garinku.Ance zuwan gobara kafafuwa na kuncewa"


Daya daga cikin en AWAWA yace


"Who dey sell Suya,Yaro yi wuno(who're you?) You're wearing ur mama public hair as beard"


Fadane ya kaure tsakaninsu nn suka dinga jiwa kansu raunika har wani yayi nasarar sokawa boxer wuka,ganin haka yasa en kunqiyar Chiki guduwa don duk abinsu basa kisa. Haka en kunqiyar AWAWA suka rikice sanadiyyar sukan nn de ya kai Oga boxer lahira shine aka nad'ani sabon shugaban a kunqiyarmu.


Fahima data kunna record a wayarta tana nad'ar komai jin Zaki yayi shiru tace


"Menene alakar da king kuma har yaushe kuke tare?"


"Kamar yanda na fad'amiki banida alaka da King tho haka yake saide ina cikin rayuwarsa ne tun kafin ya San zai had'u dani.Ina aiki akansa tun kafin yasan wanene ni"


"Bangane nufinka?"






NIMA DE NA KASA GANEWA ZAKI,GASHI NA GAJI BALLE NA CIGABA DA JIN WNN LBRY NASA 🥴🥴




COMMENTS
SHARE FISABILLAH 🙏🏻
[1/6, 9:08 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*




BY APHSERTEEN KHAIREE




ELEGANT ONLINE WRITERS




26


Fahima de sai kallonsa kawai take batace kala ba don harya fara bata tsoro


"Kafin Oga Boxer ya mutu an kawo masa wani aiki da photo wani akan anaso ya d'auko shi ama karya cutar dashi,tho dayake in za'a kawowa Oga aiki ba ganin masu kawowar muke ba don ba hurumin mu bane saide shi Oga yazo ya bamu aikin kawai.


Kaf cikin yaran Oga nine amintaccen shi sbd jajircewata da rashin tsorona akan komai don duk hatsarin aiki matukar zan samu kudi toh zanyi shi kuma har gobe haka nake"


Wayar da take recording ya d'auka tare da kashewa ya ajiyeta a gaban motar tukunna ya cigaba


"Oga ya turamin photo mutumin a wayata,ba wani bane face KING akan ni zanyi aiki tare da wuraren da yake zuwa ama yace min mafi akasari yana cikin makaranta kuma aikin bazaiyu ba anan dole saide a wajen makarantar.Haka nake zuwa Unilag kullum kusada department dinsu kullum ka gansa tho sai kaga dubbin d'alibai tare dashi sun zagaye shi haka in ya fito daga aji ma suna tare kai koh fita wajen makaranta zaiyi baya fita shi kadai a takaice da shi mai farin jinin jama'a ne kota ina.


Haka aikin nn ya kaini tsawon kwanaki har ajalin Oga boxer yayi aka nadani sabon shugaba ban samu damar dauko King ba kuma wanda suka bada aikin basu kara zuwa ba koh sunji lbryn mutuwan Boxer bansani ba.


Ban dena shiga Unilag ba ama bada niyyar aikin ba sai don yanda King ke burgeni kawai tun ina tsaya daga nesa harna fara matsowa don sonjin mai suke tattaunawa da d'alibai haka.Mafi akasari akan karatu ne sai abubuan cigaba wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login