Showing 3001 words to 6000 words out of 56965 words

Chapter 2 - RETURN OF THE KING COMPLETE BY APHSERT KHAIREE .txt

28 Dec 2024

3344

ido harta koma na zuci dayafi radadi da quna. Daga jiya da safe zuwa yau duk ta zabge sai zuru zuru da idonta yayi, duk bayan daqiqa saita duba wayarta koh zataga saqo koh kira daga wajensu. Hanyar yanda zata kubutar dasu kawai take nema koh tayaya, haka ta kintsa kanta cikin riga da skirt koh wanka batayi ba ta dau abubuan buqatarta ta keys din motarta tasa hijab din da ta cire jiya ta fito parlor. Ihu tasa ganin qarten maza 3 zaune a parlor ta cikin baqaqen kaya, fuskarsu bbu annuri kamar kafiran farko.


Daya a cikinsu ne ya nunata da gun tareda sa hannunsa a baki alamar tayi shiru harya tako inda take. Runtse ido tayi ganinsa daf da ita sai qarqarwa kawai takeyi cikeda tsoro.


Ya ciro farin handkerchief cikin aljihunsa kafin da bude ido harya shaqa mata a hanci, luuu ta fada jikinsa....




_WACECE FAHIMA ALIYU_


Asalin mahaifinta UCHENNA JULIUS EKWONWA Igbo ne dan garin ABIA STATE wanda ziyara da yawon bude ido ya kawoshi Kaduna wajen abokinshi ABEL.Kullum da yamma kamar bayan la'asar inya fito shan iska kofar gida yana ganin wata kyakkyawar yarinya cikin uniform din islamiyyarta da take matukar burgeshi da daukar hankalinsa sbd nutsuwarta.Haka zaita gaisheta taki tanka mishi harta wuce, yau da gobe dole ta fara amsa mishi yana kiranta Nyayniya mai chau (yarinya mai kyau)


A kwana a tashi sabo ya fara shiga tsakaninsu da Maryam matashiyar budurwa da bazata wuce shekara 17 ba kullum zataje islamiyya shi yake rakata suna hira, sabo yay sabo ya kuma shaquwa har abin yaso rikidewa ya chanza salo dukda Maryam kullum tana tsawatarwa kanta akan zurfafa mu'alamansu sanin cewa bbu aure tsakaninsu.


Uchenna ya kasa jurewa har saida ya fito fili ya fadamata sirrin zuciyarsa akanta na son aurenta da iya gaskiyarshi nn ta fadamishi cewa bbu aure tsakaninsu kasancewarsa Christian.Nn take ya cemata sai shiga addinin musulunci inde zai zama sanadiyyar mallakarta ya yarda ya bar komai da kowa nashi ya kasance da ita, da farko taki amince masa saida yayta masa naci tukunna ta hadashi da mahaifinta Malam Hamza yay masa gargadi sosai da karin hankali akan lalle saide yasa aransa zai shiga addinin musulunci badan soyayya ba sai don gane cewar shine tafarkin gaskiya.


Uchenna ya karbi addinin musulunci Malam hamza ya zaba mishi sunan ALIYU tareda daurashi kan hanyoyi da koyarwa ta addini.Ganin yanxu bai isa ya tunkari garinsu ba yasa Aliyu fara bin abokinsa Abel wajen sana'arsa ta saida bread da yake karba wajen mai gidansa da yake da bbn gidan bread yana bashi akan sari.


Sana'ar saida bread ya karbi Aliyu sosai hakama mai gidan nasu yana matukar jindadi yanda kasantuwar Aliyu yasa gidan bread sa kara bunqasa da tarin costumers koh ta ena.


Bayan Maryam ta kammala secondary ta Malam hamza mahaifinta ya daura mata aure da Aliyu sbd jarabasa da yay tayi akan yanda yay riko da addini yasa ya bashi ersa, haka suka kasance tare lokacin Aliyu ya dan tara kudi bbu laifi ya nemi shawarar Surukinsa da yake tamkar uba yanxu awajenshi akan bude nasa gidan bread koh karami ne..


Alhamdulillah kamar wasa saiga gidan bread Aliyu mai suna TOPTASTE ya bunqasa duk costumers dinsu na tsohon gidan bread dinsu sun dawo nn wanda abin yay matukar qonawa Alh Saminu mai gidansu nada rai harya hada baki da Abel abokin Aliyu da shima yake qule dashi sbd yanda lokaci daya yazo ya cigaba ya barshi.


Nan suka hada baki Abel ya shiga gidan bread din Aliyu ya zuba maganin bera wajen kwabin inda ya jawo asarar rayuwa da dama kuma bincike ya nuna duk sanadiyyar bread din top taste da sukaci ne, nn jama'a sukayi ayarin zua daukar mataki akansa


Aliyu ya shiga matuqar tashin hnkl a dare ya tattara matarsa da FAHIMA tana er shekara biyu ya daukesu suka gudu zua garinsu ABIA STATE


Kin karbarsa en uwansa sukayi don sunji lbryn musuluntarsa awajen abokinshi Abel har saide in zai koma addinin Christian tukunna zasu karbeshi har su bashi jari.


Dayake daman musulunci ba ratsashi yay ba kuma soyayyace ta jashi nn ya yarda da buqatarsu nan ya qara komawa ruwa, Maryam kuwa ganin haka yasa ta saci jiki ta dau erta Fahima ta gudu gida Kaduna..


Bayan Aliyu ya koma Uchennan da en uwan nasa da suka masa alkawarin jarin da wajen zama suka juya masa baya daman iyayensa sun mutu tuntuni sai church ya koma yana burgima...
[1/6, 8:58 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*


BY APHSERTEEN KHAIREE


ELEGANT ONLINE WRITERS




4


_cigaban lbryn Fahima_


Haka Maryam ta cigaba da kulawa da Fahima agidan iyayenta tana sana'ar dinki da taimakon Mahaifinta Malam Hamza har fahima tayi wayo aka sata a makaranta mai kyau da tsada.


Fahima ta kasance irin yaran nn masu bin kokkofi akan Abu da nacin tambaya tun tana yarinya shiyasa da tayi wayo ta mallaki hankalin kanta bbu abinda takeso aikin jarida ga boyayyen burinta akan gano asalin gaskiya akan mahaifinta na lbryn da mamarta ta bata na dalilin rabuwarsu da baban nata.Tana part 2 a university inda take karantar mass communication suka hado da Fu'ad lokacin yana final year dinsa yana gama karatu kua bayan ya sami aiki sukayi aure ya cigaba da kula da karatunta harta kammala ta samu aikin a _Kaduna daily trust_


Jajircewarta ta kokarin yasa ta zama zakaran gwajin dafi a ma'aikartasu,ake ji da ita sosai.Tasha shiga hadarurruka da dama wajen bincoko gsky wanda yasa kullum suke samun matsala da fu'ad har yace da zabi daya tsakanin aikinta dashi.Dukda yanda take kaunarsa kua haka ta zabi aikinta akansa wanda ya zama sanadiyyar rabuwarsu knn,ta dawo gaban gaban mahaifiyarta dake zauna ita kadai bayan rasuwar iyayenta tareda yaronta Salim, har lokacin Maryam bata sake wani auren ba don haryanxu tana tsananin son Uchenna dukda kaddara ta rabasu.


Suna zaune cikin jindadi da kwanciyar hankali sbd kyakkywan tsaro da Fahima ke samo karkashin jagorancin King dayake bata goyon baya 100percent akan aikinta ya zama tamkar uba agareta don Daddy ma take kiransa tun akan wani aikin da tayi akan wasu en ta'adda da ta dau pictures dinsu.


Har King ya bar garin bata taba samun wani matsala ba dukda rashinsa na tsawon sheraka 6,ta shiga damuwan rashinsa sosai kullum addu'arta Allah ya dawo dashi lfy in yana yare in koma ya rigamu gidan gaskiyane Allah ya masa rahama..


Kwatsam a ranar da King zai dawo bayan ta dawo daga aiki da yamma kusan after 6 agajiye ta tarar da bbn tashin hankali na rashin ganin Maminta da salim agida sai sakon video ta WhatsApp dinta da tagansu a daure cikin azaba da fitan hankali sai koma ga call daga private number na qudorinsu akanta da aikin da suke so ta musu da gargadin kuskure daya a bakin ran Maminta da danta salim.....




_CIGABAN LABARI_


_GOV'T HOUSE_


_*GOVERNOR ABDULSALAM AMINU KAITA*_


Tunda ya fita ya bar Zee a dakin daddaren bai dawo ba sai yayi wucewarsa daya bedroom ya kwanta cikeda sake sake da tunani kala² game da dawowar King da matakan da ya kamata ya dauka tun wuri kafin abubua su kwacame mishi.


Bayan an idar da sallar asuba ya shigo ya samu Zee tayi daya² akan makeken gado dake dakin,wani dogon tsaki yaja cikeda takaicin halin Zee da mugun jaraba ace mutum bazai taba iya kwana daya without having sex ba,da zaiyi spending all the night akanta bazata taba nuna gajiyawarta ba saide shi ya gaji ya kwanta.Haka yana gani za tayta biyawa kanta buqata saide ya fita ya kyaleta a dakin,koh yau ma ya tabbata saida ta kwakwule kanta kafin tayi bacci..


Kallon yanda tayi daya² yayi,er ficiciyar sleeping dress din duk ya tattare ta wajen cikinta,kirjinta a bayyane hakama daga kasanta duk waje.Take yaji tsikar jikinsa ya tashi,yasan kuma yana tabata yanxu ya tabowa kansa aiki ne


Hadiye abinda ya taso masa yayi,ya hau tashinta tayi sallah.Dakyar ta bude ido ganinsa a tsaye akanta yasata bankaro kirjinta tana wani nishi cikin wani irin salo na tsantsar iya bariki da jan hankali.


Kwada kansa yayi daga kallonta,shiyasa yake bala'in kaunarta sbd inde ta harkar jan hankali ne Zee gwanace.Ta karanci iya karuwanci da bariki kala kala,ga gyara da takewa jikinta ciki da waje don koh sau nawa zeyi zamzam yake jinta.Ga wani fresh skin da figure 8 structure mai daukar hankali


"Tashi kiyi sallah don har rana ta fito" ya fada tareda juyawa ya fita


Tsaki taja kadan, haryanxu a matse take ba abinda take buqata kamar namiji.Namijin ma KING, tana da buri akansa tun ranar ta fara daura idonta akanshi take tsananin son sa da buqartasa.


Tasha kai masa kanta,tasha yi masa trap kala² ama bata taba cimma nasara ba,sbd ta mallaki King ta auri AA kaita.Shekararsu biyu da aure ita da AA aka nemi King aka rasa take dagon sonsa da sha'awarsa kuma take addu'a da fatan dawowarsa don cimma burinta kuma tayiwa kanta alkawari wnn karan sai burinta ya cika akan King,sai ta dandani zumarsa,sai ta maidashi mallakinta ta juyashi iya son ranta. Ta dandani dadin da matarsa DIJA ke bata lbry akan KING


"Wallahi wnn karan sai na kashe qishi da kwadayina akanka My King" tayi maganar tareda wani shu'umin murmushi


Tashi tayi ta shiga toilet don tsarkake jikinta tayi wanka tareda dauro alwala don gabatarda sallar asuba lokacin har 6:45am


Sai 8:30 ta sauko downstairs cikin wani arnan doguwar rigar na material Orange color da akayiwa dinkin fitted gown, lafe a jikinta ta fitowa da surarta Kamar a jikinta aka dinke.Tako take daya² sai qarar takalminta dake hills akeji,tayi kyau masha Allah abinka da mai kyau ga kudi ga mulki ga uwa uba gyara da jikinta ke sha..


A dining ta hadu da AA kaita yana breakfast don so yake ya fita dawuri,so yake ya hadu da KING ayau dukda aikin da yasa a fara masa tun daga yau akan King din don da farar safiya ake kama fara,kafin King ya dau wani steps yakeso ya rigasa don yasan tabbas da shirinsa ya dawo.








_KING'S MANSION_


10:30am
Zaune yake kan wata kureja da take daban da sauran cushions din dake parlorn,yayi cross leg cikin shigar kananan kaya da tushe idonsa da bakin glass as usually sbd boye halin damuwar da yake ciki wanda ya kasa boya a idonsa


Kallonta innocent face dinta kawai yakeyi tana kwance a 3seater,Zaki na zaune a kujerar dake kusada ita da waya a hannunsa har lokacin saqon da aka tura masa dazu a graveyard yake gani,kuma yaga anyi blocking dinsa da number da aka turu sakon, sauran gurds din koma duk suna waje


Da alama farfaduwarta kawai suke jira.A hankali ya fara bude idonta da suka mata nauyi ga wani irin sarawa kanta yake mata,tana bude idon gabadaya ta saukeso kan King ta kujerarsa ke facing dinta tayi.


Cikin razana ta mike,sai kuma ta dafe kanta sbd yanda taji ya koma sara mata tace


"Ahhh...wayyo Allah kaina"


Tambayar da King ya jefo matane ya sata dagowa da sauri ta kalleshi


"Wa ya saki wnn aikin FAHIMA ALIYU?"


Maimakon ta bashi amsa sai kawai ta fashe da kuka,Zaki ne ya daka mata tsawa da budaddiyar muryarsa da take abin tsoro don shi koh a hankali yay magana sai ka jita da girma


A rayuwar Zaki in akoi abinda ya tsana tho mata ne barin ma in yaji suna kuka abin na matuqar tunzurashi da bata mishi rai don gani yake duk wani kukan da mace zatayi na qaryane kawai son gwanance wajen iya karya da pretend ne
(Komai dalilin Zaki akan wnn ohoo 😏🤷🏻‍♀️)


Kallon daya King ya masa wanda ya sashi tashi ya bar parlor inya cigaba da zama zai iya kaimata mari don a kwullace yake da ita daman.


Kura mata ido King yayi kamar mai nazartar wani abu daga kukan nata ya qara mata tambaya


"I ask you for the last time,su waye suka saki?"


Dago idonta dake gaje² da hawaye cikin tsoro da rashin makama tayi,jikinta sai rawa yake da dunkule kafafunta akan kujera tace


"Ba kowa,bbu wanda ya sani don Allah ka barni na koma gida"


Cikin nuna rashin damuwa King ya mayda idonsa kan wayarsa zaiga Zaki ya shigo da alama kiransa yayi


"Take her back"


Tashi yayi ya haye sama ba tareda ya koma waiwayowa ba.Cikin tsawa Zaki yace mata ta tashi,jikinta na rawa ta tashi tabi bayansa har wajen motocin dake gida..




Suna zuwa kofar gidanta gurds dinda ke zaune tareda ita a bayan motar ya bude ya cillata kamar er tsana sukaja motarsu suka barta awajen


Er qara tasa sbd zapin da taji dakyar ta tashi tana kuka hamnunta dukya kurje ta shige gida,bedroom dinta ta wuce direct tana kuka kamar ranta zai fita,A bakin kofar dakin taci karo da handbag dinta da key motarta data dauko dazu da zumar tafiya aiki


Har zata shige dakin tayi wayarta na vibrate a cikin jaga,Private number ta gani tana dagawa aka cemata


"Ki bude WhatsApp dinki mun ajiye miki aikinki na wanda yake daidai da ran mahaifiyarki in bakiyi abinda ya kamata ba"


Kitt aka kashe wayar,hannunta na rawa da shiga WhatsApp inda taga tarin messages duk yawanci tambaya ake mata akan tambayar da tayiwa King jiya a airport har ta iso kan wanda take kyautata zaton shine nasu




Wani ihu tasa ganin sakon nasu, cikin razana batasan lokacin data cillar da wayar ba jikinta na rawa,ta durgushe a wajen tana wani irin kuka da mai cikeda tausayi..




More comments more typing guys 😎


Share fisabillah 🙏🏻
[1/6, 8:59 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*


BY APHSERTEEN KHAIREE


ELEGANT ONLINE WRITERS




5


KING


Yana shiga bedroom dinsa ya bude wardrobe ya dauko wani 'katon album mai kamar diary,before then he loves to captured every moments. Yanason taking pictures ya ajiyesu cikin wannan album din tareda short note akan kowanni picture,dukda ya taso yaga taking pictures a matsayin sana'ar mahaifinsa don har babban studio ne dashi ama shi ya dauki daukar photo one of his best hubby yana son abin sosai shiyasa ko ina zaije cameran sa na gefe koh akan hanya yaci karo da abinda ya mishi kyau sai ya dauka.


_*ALIYU MOHAMMED GIWA*_ Shine farkon abinda ke rubuce cikin album din wanda ya kasance asalin sunan shi daga baya KING ya boye sunan kowa yafi saninsa da KING.


Picture din farko dake cikin album din ya kalla,tareda shafawa cikin tsananin damuwa da kewar iyayensa lokacin yana jariri akayi photon shida Amminsa da Baban sa ya riko kafadarta suna kallo kyakkyawar fuskar jaririn nasu dauke da murmushi akayi capturing wanda pic din ya kasance black and White.


Cigaba da bude kowanne pages ya dingayi yana murmushi shi kadai har yazo kan wani wanda ya tsaya ya kura masa ido sosai yana kallo


Irin _*BARAROJIN*_ nan ne Uwa da erta akan titi,yarinyar bazata wuce 16yrs ba cikin shigarsu ta asalin fulani da buhunsu a rataye a hannunsu kamar jaka ya daukesu sai zabga murmushi suke wanda kana ganinsu zaka iya karantar tsantsar jindadi da farinciki dake fuskarsu




Shafa fuskar er yayi idonsa ya kada yay jaa atake,ya yamutsa fuskarsa kamar mai son yin kuka yace


"I really missed you my FULANI, please come back to me"


Tuna ranar da ya fara haduwa da ita yayi,cikin traffic yana jira a basu hannu su wuce da yamma lokacin ya tashi daga office zaije gida


Ta mirror glass din motarsa ya hangosu itada mamarta da take kira DADA yaga suna bin mota mota,yanda sukeyi da fuskarsu in sun bar gaban kowanne mota ne ya bashi dariya dukda baisan me suke fadaba ama daga gani yasan rashin kunya sukewa mutanen cikin motar har suka karaso tashi motar.




"Muna bara muna karuwa"


Cikin mamaki da bazata yaji muryar uwar da abinda take fada,dariyace ta subuce mishi ya kalli uwar da er da kyau


Gashi de uwar ta manyata,er kuma bazata wuce 15 to16 ba.Toh waye yake karuwar acikinsu,su kuma nasu salon baran kenan?


No wonder shiyasa suke barin sauran motocin a tsiwace,horn da aketa faman zabga mishi daga bayansa ne ya sanyashi tunawa da inda yake alamar an bada hannu tuntuni kenan har en bayansa sun fara fusata




Harya wuce kuma sai wata zuciyar ta sashi zagayowa ya dawo wajen wannan bararojin yaci sa'a kuwa suna tsaye daga bakin titi basu tafi ba.Waje ya samu yay parking ya fito har inda suke


"Sannu" yace musu


Uwarce ta amsa mishi da fulatanci wanda shi baimaji abinda tace ba,sai ya kara tambayarsu


"Mesa kuke bara ahaka?"


Itade er sai binsa kawai take da ido irin kallon burgewa din nan take ta mishi sai uwarce ta kara bashi amsa cikin gurbatacciyar hausarta da ake ganewa dakyar tace


"Ka'don (hausawa) binni kunfi son karuwa shiyasa muke hadawa duka biyu ama duk shegun wai sede an basu DIJA ta tai musu karuwa ni bashasho ni kuma wollah bani bada DIJA tayi karuwa,GAR'KO (Miji) mai cheu zan nema mata tayi aure.Kaina in karuwa kakeso saide ka shii ni tunda ni mijini ya tsufa"


Tunda ta fara KING yake gimtse dariyarsa bayaso yayi karya katseta har seda ta gama tukunna yace


"Zaki bani DIJA na aureta?" Da murmushi a fuskarsa yake kallon DIJA data kureshi da ido dukda ita bamajin mai suke fada shida DADAn nata takeyi ba ama kawai mutumin ya burgeta ne sosai har bata gajiya da kallonsa


Wani dadine ya cika Dada cikeda murnar jin wnn dan gayen binnin yace zai auri DIJANTA da fulatanci take cewa dijan ta samu miji wannan yace zai aureta take nunamata shi sai kuwa itama Dija ta hau murna yace zai aureta shide kawai kallonsu yake cikeda mamakin murnar da suke daga haduwa da mutum lokaci daya bakasan wanene ba bakasan irinsa ba lalle sai yanxu ya kara gaskata zancen mutane da suke fadar wautar Fulani shi da ya dauka duk sharrine kawai ake musu.


Ce musu yayi su tsaya yana zuwa,binsa sukayi da kallo har yaje motarsa ya dauko cameransa ya dawo kusada su ya sasu tsayawa da kyau suna zabga murmushi yayi snapping dinsu.


Zo kuga murna daya nuna musu kansu acikin camera...




Wata er karamar dariya CE ta subuce masa tunawa da dramarsu ta farkon haduwarsu da DIJAnsa,Fulaninsa,abar kaunarsa wacce ya bawa dukkan soyayyarsa da gangar jikinsa gabadaya.Ya wahala,ansha drama kala²,wauta,da shirme iri² kafin DIJA ta zama cikakkiyar mace kamilalliya.An rabasa da DIJA a lokacinda ya fara jindadi da girbar wahalarsa akanta,a lokacinda yafi muradinta da kasancewarsu tare


Wasu irin kwalla masu zafi ne suka zubo mishi wanda radadinsu ke fitowa deep inside his heart,kiran sallar azahar da aka farane ya fargar dashi da irin time din daya bata a zaune daga kasan bed dinsa kan lallausar rug din dake shimfide a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login