Showing 9001 words to 12000 words out of 56965 words
Chapter 4 - RETURN OF THE KING COMPLETE BY APHSERT KHAIREE .txt
ba mutumin da suka taso sukayi rayuwa tare ba. Wani irin kwarjini da cika Ido yayi masa, still yayi a wajen ya kasa motsawa kamar wani statue sai King ne ya tako cikin izza da kasaita ya karaso gabansa
Kafin AA ya ankara yaji King yayi hugging dinsa yana bubbuga bayansa
"I miss you friend" yace mishi a kunnensa, sai lokacin AA ya aro wata er karamar jarumta da kokarin boye shock dinsa yace
"Miss you more, am glad you're back"
Sakesa King yayi yana murmushi mai tarin ma'ana
"Bismillah" AA yace masa tare da nuna masa kan cushions din dake gefe a zagaye, bayan sun zauna AA ya kallisu PA da Zaki yace
"Exucuse us" fita PA yayi bayan ya gaishe da King shi da kansa acikin rudu yake ganin King yanxu a office din excellency ama baiso fita ba yaso yaga yanda zata kaya, juyawa AA yayi ganin gurds din King da Zaki su basu fita ba ya kalli King.
Kallonsu kawai King yayi suma suka fita banda Zaki daya kasa ya tsare
"So what's are your plans?" AA ya tambayi King
"Am sure, kaga first step din" king ya bashi amsa ba tareda ya kalleshi ba ya dau glass cup din da AA ya zuba mishi drink yana sha, kokarin seta kansa AA yakeyi yace
"Meyasa ka zabi ka chanza party, bayan kasan wnn kujerarka ce and am ready to step down"
Wani gutun murmushi king yayi ya kafe AA da ido kamar me son karantar wani abu cen kusan 10secs tukunna yace
"Allah ya bawa mai rabo sa'a, best of luck"
AA zaiyi kara magana knn sukaji sautin takun takalmi na shigowa, yasan ZEE ce cikeda takaici ya dago ya kalleta yaga yanda ta kafe King da idonsa ke kan wayarsa ama hnklnsa na nn tare dasu.
Kamshin turarenta ne ya fara musu sallama, tana sanye cikin wani arnan red gown sai wani dan mayafi data daura kan kafadarta. Fuskar nn kamar wata dan daren sha 15 sai wani shekin kyau na daukar hankali take, wani kyataccen murmushi tayi ta karaso wajen AA tayi mishi peck. Kallo daya Zaki ya mata ya dauke kansa ya mayar kan wayarsa, takowa tayi har wajen kujerar King tace
"welcome back my king"
Ta zauna daf dashi kan kujerar da yake, dago ya aika mata da wani irin killer smile yanaji tana gogan jikinsa ya basar. Wani dadine ya kasheta ganin yau king bai yarfata ba koh ya shareta kamar yanda yakeyi yake mata da, bata isa ta zauna inda yake ba dukda a farkon haduwarsu ba haka bane sai daga baya data nuna maitarta a fili wanda har mijinta ya sani
"Thanks, ZEE manya hope na sameku lfy?"
Wani fari ta mishi cikeda salon bariki, AA kua ji yake kamar ya shaqesu don bakin ciki. Zee tace
"Lfyr de dasauki my king, we missed you a lot"
Mikewa King yayi ba tare da ya kuma koh kallon inda take ba ya mikowa AA hannu yace
"friend ni zan koma, i av alot to do"
"Ok, zan shigo nima anjima daddare"
Suka fito tare Zaki na bayansu, ita kua Zee na zaune har lokacin kan kujera tana sake saken iska. Har wajen motocinsu ya raka KING sukayi sallama kowanne da abinda yake saqawa aransa
Saida suka dau hanya Zaki yace
"kana da ganawa da en jarida zasu maka tambayoyi gameda gubernatorial election dinka"
_FU'AD HASHIM_
Riko hannunsa tayi tana kuka shima yanayi kamar karamin yaro harda sheshsheka,acikin kwana daya da yayi a cell duk ya zabge idanunsa sun zurma sai tabon ciwon dukan da yasha wajen en sandan akan saiya fadi gaskiya
"Mummy please do sumtin,mummy wallahi zasu kasheni ne koma bani na kasheta ba kema kinsan bazan taba iya kisa ba koh bera bana iya kashewa"
Ya karasa tareda fashewa da wani matsanancin kuka kamar ba namiji ba don fu'ad irin ragwayen nn ne masu uban tsoro,cikin tsananin damuwa da tausayawa dan nata ga idonta itama sai zubar sa kwalla yake ta kasa controlling din kanta balle ta kwantar mishi da hankali.Dakyar ta saisaita kanta sanin ba wani lokaci mai yawa aka basu ba don dakyar ma aka yarda ta ganshi
"Fu'ad calm down,evrtin will be fine insha Allah ba abinda zai sameka kajii.Ka kwantar da hankalinka" ta shafo gefen fuskarsa tana hawaye
"Mummy kiyiwa lawyernki magana da wuri a fitar dani a wajen nn"
"Ka kwantar da hankalinka Son,naje wajen KING dazu yace zai taimaka mana zai fitar da kai anan insha Allah"
Zaro ido yayi yace "No mummy,King bazai fitar dani ba saide yasa a kasheni mummy shi ya.....
Bai karasa magana ba wani police yazo ya daka mishi tsawa akan lokaci yayi,haka Hajiya hawwa na kuka Fu'ad nayi suka rabu yana
" wallahi mummy King kasheni zeyi shi yasa aka kashe Mami"
Qurki wani police ya buga mishi akai sai kuma ya fadi luu....
*************************
Dandazon en jarida da ma'aikatar gidan radio da TV ne a cike a wajen kowannensu a shirye yake tsapp da tamboyoyi fal bakunansu,kowa fatansa ya samu damar yiwa KING tambaya
Cikin takunsu na burgewa da kasaita KING da tawagarsa suka karaso,yana gaba cikin shigar black suit ya tushe idonsa da bakin glass sai Zaki daga gefensa na dama da sabon P.A daya karancin harkar politics sosai Wanda Zaki ya dauko shi musamman akan takararsu.Daga bayansu kuma tarin guards din King ne fuskar nn a dinke as usually
Inda aka tanada musamman dominsu suka zauna KING na daga tsakiyarsu,wajen a zagaye yake da securities koh ta ena suna kallo motsin kua snn ga CCTV dayake dauke da kowanne lungu da saqo na wajen
Bayan an gabatarda duk abinda ya dace,aka fara bada damar tambaya ta hanyar daga hannu shi kuma mai gabatarwa sai ya zabi daya cikin en jaridar don dogace baka isa kayi cross question ba.Haka King ya dinga amsa tambayoyinsu kai tsaye
"A matsayinka na dan kasa mai kishin kasa,zaka iya zaben wanda yayi sanadiyyar iyayensa,matarsa tareda yaransa.Snn ya gudu na tsawon shekaru har shida sai dare daya ya dawo da neman kara mulkar al'umma,mutumin daya jefa rayuwar Iyalinsa cikin hadari yaya kake tunanin makomar sauran al'umma zai kasance karkashin mulkinsa?"
Tsitt wajen ya dauka don kamar saukar aradu haka sukaji saukar tambayar daga bakin wacce KING bai taba tunanin ganinta awajen ba don kafin su karaso saida ya biya ya dubata tana kwance
"U AGAIN?"
SHARE FISABILLAH 🙏🏻
[1/6, 9:00 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*
BY APHSERTEEN KHAIREE
ELEGANT ONLINE WRITERS
8
Kallo ne ya dawo kanta, kaf wajen kallonta suke da tsananin mamaki.ZAKI kuwa ji yake kamar zuciyarsa zata fito yanda take hantsilowa a kirjina na tsananin 6acin rai gashi he can't make any attempt sbd idon en jarida dake cike a wajen.She looks so sick don dakyar ta iya tsayuwa da kafafunta,kokarin controlling kanta kawai takeyi don ta samu ta aiwatar da abinda ke gabanta shine kawai burinta a yanxu.KING kuwa kureta kawai yayi da ido yana karantar yanayinta ba tare da nuna shock koh damuwa akan tambayar tata ba,gyaran murya yayi wanda ya dawo da attention din jama'a da suka kura FAHIMA da kallo kansa
"Komai na rayuwa na tafiya da lokaci,kaddara, sanadi, wanda bawa bai Isa ya tsallake kaddararsa ba kamar yanda kema kike fuskantar taki kaddarar. *FAMILY* sune ginshikin mutum Wanda bbu sacrifices da cikakken dan halak bazai iyayiwa danginsa ba kema nasan yanzu haka sukikewa fighting idan har zaki iya yin abinda kikeyi yanzu akan mahaifiyarki da danki meyesa Ni zankashe mahaifiyata, mahaifina, matata, sannan gudan jinina en biyun da bazasusan me duniyar ta qunsa da ababen cikinta ba idan harke ke dakike mace Mai rauni zaki iya fuskantar kowanne qalubale akan danki da mahaifiyarki meyesa ni da nake namiji fitacce sannan politician bazan shiga challenges da masifu kala kala ba"
Cen ya sauki numfashi tare da dan runtse idonsa ya bude,jama'ar wajen kua jikinsa yayi sanyi kowa ya hadiye maganar dake bakinsa.Bayan kamar 30secs King ya cigaba da magana da dakakkiyar murya wanda kowacce kalma take fitar da amon tsantsar gaskiya snn direct daga zuciyarsa
"Allah shine shaida snn madogarata kuma banyiwa wani dan qasata da garina tilas cewa sayya zabeni ba,ina kira ga talakawa daduk wanda yakeda yancin zabe kada kusiyar da quriarku, kuzabi abinda zuciyoyinku suke muradi Kuma kuke ganin shine daidai domin gobenku.
Next question please?"
Tsitt wajen ya dauka kowa yasha jinin jikinsa don maganar king ba kamarin kashe musu jiki yayi ba sai kallon kallo da sukeyiwa junansu,mikewa KING yayi yace
"Then,let's call it a day"
Takowa yayi gurds dinsa na mara masa baya,FAHIMA dake tsaye still kamar an kafata wajen yazo ya wuce ta gabanta ba tareda ya kalli koh inda take ba.Har aka watse tana tsaye a wajen,kafe kanta ta taji ya fara sara mata tayi sai kua ta zube a kasa....
Gida direct su KING suka nufa inda jama'a keta masa ihu sai kayi,suna isa ya wuce bedroom dinsa dake sama ba tareda ya tanka kua ba.Suma kansu guards din sun san ran maza ya baci,Album dinsa ya dauko yana kallon photon iyayenshi zuciyarsa na tafasa don ba karamin fami FAHIMA ta masa ba sai yakeji kamar yanxu ne ya rasasu komai ya dawo masa sabo fil. Tunawa yayi da rayuwarsa ta baya,abubuan da suka shude...
_*WANENE KING*_
_ALIYU MOHAMMED GIWA_ Shine asalin sunan KING,mahaifinsa MOHAMMED GIWA dan asalin Garin Kaduna ne karkashin GIWA local govt wanda GIWA ya zama inkiyar familyn su,Mohammed GIWA na rayuwa da iyayensa anan Unguwar gangare main house dinsu knn,kasancewarsu ba masu haihuwa sosai ba shiyasa Mohammed ya zama 'da tilo wajen iyayensa MALAM IBRAHIM GIWA da mahaifiyarsa AISHA wanda duk en gari dayane Sana'a da kawosu cikin garin Kaduna daga GIWA. Mohammed ya tashi da sun daukar photo harya zame masa Sana'a tun yana bin anguwan² har ya samu shagon kansa ana zua dauka,iyayensa sun rasu bayan yayi aure da matarsa RUKAYYA da shekara kusan 5 har lokacin Allah bai basu haihuwa ba,a takaice saida ya kusa shekara 8 da aure tukunna Allah ya basu cikin ALIYU wato KING.
Bayan haihuwar KING abubua alkhairi da arziqi yayta hauhawa ance kowanne yaro da irin arzikinsa yake zua don lokacin sana'ar daukar photo na mahaifinsa ya bunqasa sosai don ya bude babban studio,ya zama daya daga cikin gidan photo da ake ji dashi kaf garin.Har lokacin suna nn unguwar gangare sai renovating gidan kawai da akayi ya dawo na zamani
Ansa Aliyu a makaranta mai kyau da tsada don duk wani hope na Mohammed GIWA na kansa sbd shima tun bayan haihuwarsa Rukayya bata kuma koda bari ma haka suketa rainon ALIYU cikin nuna masa tsantsar so da kulawa wanda suka daura dukkan burinsu akanshi
Kaf anguwansu bbu wanda baisan Aliyu ba yarone shi mai garin jinin sbd fara'arsa da son jama'a gashi da son daukar photo abu kamar mahaifinsa duk abinda ya masa kyau sai ya tsaya yayi capturing shiyasa kullum yana makale da er cameransa da Babansa ya sai masa dukda yana yawan zua studio babansa bai dauki daukar photo a matsayin sana'ar da zai gina rayuwarsa akai ba shi.Ba abinda yakeda buri kamar yaga ya tara al'umma suna amfanowa da wani Abu da zai kawo musu na chanji da cigaban kasarsa shiyasa tunda ya fara yawo ya tashi da son harkar siyasa yake burin yaga ya zama daya daga cikin manyan kasa da al'umma zasuyi alfahari dasu.
Bayan ya gama secondary school ya takurawa mahaifinsa akan lalle University of lagos yake son zua,ba yanda Babansa baiyi dashi ba hakama Amminsa ama ya dage akan ra'ayinsa wanda su kuma soyayyarsu gareshi yasa su hakura aka nema masa UNILAG ya samu course din choice dinsa kua wato Political science, ya tattara ya koma hostel gabadaya sai Hutu ke kawosa gida.
Su hudu ne a dakinsu na hostel,David da Emmanuel en yaran Igbo sai shi da Abdulsalam Aminu kaita wato AA KAITA da asalin garin Katsina wanda ya zama amini sosai wajen ALIYU kasancewarsa musulmi kuma bahaushe gashi department dinsu daya shiyasa shakuwarsu tafi yawa sosai.
Yanda ALIYU keda farinjini cikin dalibai a makarantar harma da malamansu sbd kokarinsa gashi kullum a cikin qirqiran abubuan cigaba ga dalibai yake shiyasa har suka nadasa shugaban dalibai a makaranta suke kiransa da KING don kullum cikin kawo musu sabbin abubuan cigaba yakeyi....
Ajiyar zuciya ya sauke jin kiran sallar azahar dake tashi daga masallacin jikin gidansa yasa shi tashi daga kan gado don zua gabatar da ita.Bayan an idar da sallah ya tsaya gaisawa da jama'ar da suke masa fatan alkhairi a takarsa yana amsa musu cikin sakin fuska har ya musu sallama ya shiga gidansa,a parlor farko ya zauna kan cushions ya kalli ZAKI yana jiran bayani daga bakinsa.Gyara tsayuwa Zaki yayi yace
"She fainted,nasa an dauketa a wajen a chanza mata waje"
"Ya akayi tazo wajen nn bayan duk tsaron dayake inda take snn ina CCTV dake dakin?"
"Abinda nake bincike akai knn,don anyi disconnecting CCTV daga time din da tabar wajen.Ina tunanin akoi mai taimaka musu cikin mutanen mu"
"Wa kake tunanin zaiyi haka?"
"Banace ba,but am suspecting evr1 nasa ido kan kua.Zaka samu zua wajen nata ne?"
"Yeah,bari nayi freshen up"
Ya tashi ya haye sama,wani huci mai zapi Zaki ya fesar tare da ciro wayansa a aljihu yayi dailing wata number
*******************
_FAHIMA ALIYU_
Kuka take sosai kamar ranta zai fita, kallonta kawai King yakeyi ba tareda ya hanata kukan ba shi kua Zaki sai kananan tsaki yakeyi.Saida tayi mai isarta tukunna King yace
"Enough, I asked u for the last time su waye suka saki?"
Batada zabi daya wuce ta fadamishi gaskiya,haryanxu photo Maminta a kwance cikin jini take gani ga Salim dinta a daddaure.Cikin kuka da har muryarta ta dashe tace
"Sunce idan harna kuskura na fadamaka zasu kashemin yarona,sun kashe min Mami banaso na rasa Salim.Please ka taimakamin bansan ya zanyi ba wlh zasu kashemin yarona"
Ta karsa tareda fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi,ajiyar zuciya King yayi cikin tausaya mata yasan duk a sanadinsa ta Shiga wnn mummuna tashin hankalin
"Calm down ki kwantar da hankalinki ki fadamin su waye, had it been kin fadamin tun farko da bazan bari su kashe Maminki ba ama Allah ya kaddara lokacinta yayi bamuda wani zabi.Yanxu kiyi shiru ki fadamin su waye suka saki?"
"FIRST LADY ZEE KAITA"
COMMENTS AND SHARE FISABILLAH 🙏🏻
[1/6, 9:00 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*
BY APHSERTEEN KHAIREE
ELEGANT ONLINE WRITERS
9
"ZEE" King ya maimata sunan,murmushi yayi ya mi'ke tsaye.Kallon Fahima da har lokacin kuka take yace
"Bring her along" ya fice a dakin,wani tsawa Zaki ya daka mata wanda ya sata razana ba shiri ta mike jikinta na rawa tabi bayansu.Kasancewar da mota daya kawai suka zo ya sata shiga baya kusada King sai driver da Zaki daga gaban mota,tsit motar ta dauka sai driver dake ta aikinsa har suka karaso unguwarsu King bbu wanda ya gane motarsu King ce sbd bai cika fita shi kadai ba da mota daya gashi motar irin dark tint din nan ne, gate man ya wangale musu gate suka shige har kusada entrance na gidan.Jin motar ta tsaya yasa Fahima dawowa daga duniyar tunanin data tafi,ficewa sukayi suka barta cikin sauri itama ta fito tabi bayansu da dan gudu²nta harta cimmasu a parlor
"Ka kaita dakin Dija ta kintsa kanta,a sama mata abinda zataci"
Yana gama fada ya haye samansa dama shi kadai ke amfani da saman duk sauran dakuna na daga kasa,da kallo kawai Fahima ta bishi harya 6acewa ganinta sai muryar Zaki dake kada mata hanjin cikinta taji yana
"Tsayuwar uban me kike a wajen?"
Cikin sauri ta karasa inda yake,hanyar wani dan corridor suka bi inda dakuna yake a jere harya bude mata wani daga ciki da shiga. Tanaji ya sawa dakin key
Ajiyar zuciya ta sauke,bata cikin nutsuwar da zata tsaya karewa dakin kallo sai kofar toilet kawai ta nema ta shige.Cire kayan jikinta tayi, wani danko² takejin jikinta na mata ta tsaya a gaban shower ta sakewa kanta ruwa
Har lokacin photo gawar Maminta take gani a idonta kwance cikin jini, wani irin kuka tasa mai kamar ihu ta durkushe a kasan wajen tana rerawa
"Mesa zaku kashemin Mamina, me mamina ta muku,mesa zaku jefa rayuwar wanda basuji ba basu gani ba akan cikar burinku.Wayyo Mamina Allah ya jikanki shiknn sun rabani dake,shiknn bazan sake ganinki ba,shiknn sun raba Uwa da erta.Rabuwa ta har abada"
Ji tayi hawayenta sun 'kafe,zuciyarta ya bushe.Kuka ba nata bane yanxu,she really av to be strong.Cikin muryar mai cikeda 6acin rai tace
"ZEE KAITA,Wallahi wallahi sai na zama ajalinki,sai kinyi nadamar saka rayuwata cikin gagari"
Wanka ta tashi tayi cikeda karfin hali da dakewar zuciya tayi alwala ta fito,closet dake kusada toilet din ta bude.Kayane a Jere wasu a hanger wasu a jere a kasa kamar wani karamin shagon kaya.Gown mara nauyi ta nema tareda hijab ta saka ta dawo kan rug dake gaban gadon ta tada sallolin da suka wuceta,tana cikin sallah Zaki ya shigo ya ajiye mata tray da plate din abinci a rufe sai bottle water da cup akai
Bayan ta idar da sallah ta gama addu'o'inta tareda nemawa Maminta gafara,sai lokacin ta samu karewa dakin kallo.Kana gani kaga dakin mace don komai yana nn kamar mai shi na dakin haryanxu,a ranta tace
"Koh ina matarsa take,ta rasu ne itama koh haryanxu tana raye, mesa matar amininsa da kowa yasan hakan will chase after him,me dalilinta na kokarin tarnishing image din King,meya takashe iyayensa lokaci daya,garin yaya aka nemi matarsa da yaransa biyu aka rasa immediately her delivery kuma a hospital kuma daga ranar ba'a kara ganin KING ba sai bayan 6yrs,meyasa,ina yaje,ina yakai matarsa da yaransa?"
Numfashi ta sauke tareda kankance ido tace
"there's sumtin behind king's life,wanda harya shafi rayuwata yayi sanadiyyar Mamina ga Salim dina shima cikin hatsari.I must find out,dole sai na nemi duka amsan tambayoyin nn by all means"
Shigowan Zaki ne ya dawo da ita daga tunanin data fada, kallon juna suka fara ido cikin ido don ya cire bakin glass din da koyaushe yake idonsa. Fahima kuwa duk wani tsoronsa ne taji ya kau a zuciyarta sbd abinda tasa a ranta yanxu na cikar burinta wanda tasan Zaki shine first step dinta dukda batasan takamaimai alakar Zaki da King ba ama kowa yasan shine very close da King duk inda kaga King tho tabbas Zaki na wajen
Kan cushions dake dakin Zaki zauna yana facing dinta,juyawa yayi ya kalli tray din abincin daya kawo mata ya dauke kai.Har lokacin idon Fahima na kansa
"Meyasa bakici abincin ba?"
"I don't feel like eating" ta bashi amsa tareda mayarda kanta kasa
"Ranar yaushe suka