Showing 45001 words to 48000 words out of 56965 words
Chapter 16 - RETURN OF THE KING COMPLETE BY APHSERT KHAIREE .txt
baiba anan dan gidan yaci gaba da girgiza yana rushewa aguje suka fito awannan dakin
Suna fitowa kansu karasu wajen steps d'in da zasu bi wajen fita ginin steps din ya zubuwa Zaki dake gaba....
😭😭😭 _WAYYO ZAKI_
Wallahi a gajiye nake yau ba kadan ba 🥴🥴
COMMENTS
SHARE FISABILLAH
[1/6, 9:12 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*
ELEGANT ONLINE WRITERS
_ALHAMDULILLAH_
We're back again💃🏻💃🏻💃🏻it's been a while. Thanks all for ur prayers, love and concern. I really do appreciate ur cares towards me,am very glad to av u all habibties🥰😍😘Jazakallahu khair
Yawwa nace ba,kuna deji ai...🧏🏻♀️ ga fah masoyin ya dawo🤗My KING,ur KING,our KING is back💃🏻💃🏻💃🏻
_let's cut the bullshit_ 😎
33
Wani irin ihu King ya saka a gigice ya tahu inda Zaki ya fadi block ya danne kafansa.Kokarin daga block d'in ya fara ama ina nauyinsa yafi karfin d'agawan mutum daya ga jini sai zuba yake daga kafar Zaki don block din ya fasa har kashin kafarsa.Azabar da Zaki keji yasa ya fara lumshe ido kamar sai sume
"No no no...Zaki stay with me,karka rufe idonka"
King keta maimaitawa a gigice ya rasa ma ta ina zai fara gashi gidan zai kara tsatstsagewa yake, steps din da zai fitarsu daga underground din kuma ya rushe.Bangarensu Fahima kua securities sun fito dasu an dauko saudat dake yashe a kasa an sata cikin ambulance,sunyi kokarin kwashe gawarwakin da Wanda sukaji rauni sai sauran da suke lfy Uchenna,David,Gboy,suleguy an kwashesu suma a motar en sanda.
Fitowarsu Fahima taga d'and'azon en jarida a wajen gidan harda na wajen aikinsu duk tsoro ya hanasu shiga ganin yanda ginin me rushewa.Har zasu shiga taji wani police yana
"DSS ALIYU DAPO and KING are still inside,we have to save they lives"
fasa shiga tayi ta nufi hanyar komawa cikin gidan da gudu securities na kiranta koh ta kansu bata bi ba ta kutsa cikin tanayi tana kaucewa ginin dake zubuwa,tazo tsakiyar parlor knn ta hango King rungume da Zaki yana jansa
"Me kikeyi anan?out now"
King ya fada a tsawace,daga kan da zeyi ya hango wani gini na kokarin faduwa Fahima dasauri ya saki Zaki yana kiran security ya taho da gudu ya hankadata gefe
Kafin ya juya wajen Zaki yaji shima an hankadasa gefe da karfi ya fadi gefen Fahima,dagowan da zeyi sai ganin karfin globes d'in dake tsakiyar parlor ya zubuwa Zaki a kai India yay daidai da shigowar polisawan aka fara basu taimakon gaggawa
Da kansa King ya ciccibi Zaki duk nauyinsa yana
"Why Zaki,why"
"Till I die my King"
*************************
Siren din motocin polisawa dana ambulance ne ya karade ilahirin asibiti inda nurses da securities suka fara kokarin fitowa da don basu taimakon gaggawa
King na tareda Zaki da oxygen aka daurashi akan gadon asibitin akayi hanyar emergency dashi.Magana Zaki keta kokarin yiwa King cikin wahala dakyar King ya kagane abinda yake fada ta hanyar motsin bakinsa
"Gidanka,gidanka..gidan gona"
Har aka shige dashi emergency, Saudat ma emergency akayi da ita sai Zee da Fahima da suma akayi dasu daki don duba lafiyarsu hakama sauran guards din da sukaji rauni.Suspect da aka kama kuwa su Uchenna anyi babbar headquarter dasu for further investigation.
King kuwa kin zama a dubasa yayi sai kai kawo yakeyi a kofar ICU,maganar da Zaki ya masa na tsaye a kokon ransa.40mins later aka fito da Zaki daure da bandages koh ina a jikinsa akayi dakin hutu dashi.
"Doctor ya jikin nashi?"
"Alhamdulillah,he seriously needs ur prayers"
Ajiyar zuciya King ya sauke a wahale yace
"What's his condition now?"
"He needs surgery both face da left leg d'insa"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,Sauran patients din fah?"
"Yanxu zanje na duba conditions dinsu,akoi doctors akansu suma.You need to rest Insha Allah all is well"
"Uhmmm"
Kawai King yace ya nemi kujera ya zauna,dafe kansa yayi yanajin wani irin zugi a ransa na tausayawa halinda Zaki yake ciki duk akansu.Tunda suka hadu Zaki yake kokarin bashi kariya da dukkan karfinsa,yana jinsa tamkar jininsa.Zai iya jure rasa komai a rayuwarsa ama banda Zaki
Wasu shud'ad'd'un lokuta ne suka fara dawo masa kwanyansa
"Why do u choose to be a thug?"
"To survive"
Zaki ya basa amsa a takaici da turanci suke magana don lokacin Zaki bayajin Hausa koh Kazan
"Menene matakin karatunka?"
"Secondary"
"Meya hanaka cigaba?"
"Money"
"Meyasa tho baka nemi wani aikin koda dako ne kayi ba a maimakon dabanci?"
"Abinda yafi kawo kudi knn a areanmu"
"Will u change ur life and be a better person if u get the chance?"
"A yanxu bazan iya kowanni irin aiki ba am used to what am doing now"
"A taimakon saka rayuwar al'umma cikin hatsari mai zai hana ka kasance mai basu kariya da dukkan karfinka"
"Me kake nufi?"
"Ina nufin ka sama one of the securities da kasarka zatayi alfahari dashi ba wanda zai zama abin Allah wadai ba cikin al'umma"
Shiru Zaki yayi na en seconds yana tunanin maganganun King,tabbas zaiso chanja rayuwarsa
"Tayaya kake tunanin hakan zai faru?"
"Kamar yanda kake amfani da karfi,rashin tsoro da jajircewa wajen raba al'umma da mallakinsu haka zakayi amfani da wadannan abubuwan wajen basu kariya.Secondary certificate dinka yana nn?"
"Yes"
"Mai zai hana ka kuma makaranta?"
"Banida wnn gatan"
"Allah ne gatan kuwa snn nima zan zame maka gata da dukkan abinda na mallaka"
Koyi manage zuwa anjima Insha Allah
COMMENTS
SHARE FISABILLAH 🥰
"
[1/6, 9:12 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*
BY APHSERTEEN KHAIREE
ELEGANT ONLINE WRITERS
34
Tafiya mai nesa yayi sosai cikin dajin da gidan yake gashi ya bar motarsa ya barota a kofar gidan. Saida ya nitsa cikin jejin tukunna ya ciro jen kyelle a aljihunsa,surutun tsafinsu ya dingayi na kusan 20mins saide shiru daga yanda yaji jikinsa beyi respond ba yasan akoi matsala.
Shafa aljihunsa dukka yayi cikin 6acin rai yace "shit" tunawa da wayoyinsa da atm's dinsa daya bari a mota.
Dakyar ya fito bakin titi a galabaice sbd dogon tafiyar daya sha nn ma ya kusa 30mins kafin ya samu motar itace ya hau bayan inda ya kawosa cikin garin ABIA
Wani d'an joint ya gani da plastic chair na matasa sunata shaye_shaye ya zauna daga gefe kan kujerar robar yana ajiyar zuciya. Zuciyarsa sai tafasa take da bakin cikin shammatan da Zaki ya masa
Wato Zaki acts to be fool just to fool d fool that thinks he's fooling him. Ya dauka zai iya using dinsa wajen achieving goal dinsa snn daga baya shima ya gama dashi ashe shine biggest fool din
Tunaninsa yanxu ma tayaya zaiyi ya kuma Kaduna, yasan by now he's face was evrwia. Meyasa tun farko baiga bayan king ba ya tsaya biyewa kunqiya da buqatarta gashi buqatar bata biya ba babu tsontso babu tarko.
Haka ya shafe kusan awonni yana tunani na rashin mafita har duhu ya fara shigowa, wani iyamuri da shagon giyarsa ke gefen inda AA yake ne ya lura dashi ganin shigar suit na alfarma dake jikin AA da yanayin skin dinsa dukda wahala da gajiyar dayake ciki yasan bazai rasa maiko ba
Tahowa yayi gabansa ya dafashi yana washe masa hakwara cikin pidgin English yace
"How fa bro wetin una dey want or maybe i can help?"
Dago kansa AA yayi ya kalle iyamurin dukda bai yarda dashi ba ama sai yaji kaman an aiko masa da rahama ne
"please can u help me with water am really thirsty"
_KADUNA STATE GENERAL HOSPITAL_
Gaba daya an gama examine dinsu mutanen da aka dauko daga gidansu ABIA, Fahima da wasu guards daga ciki are well healthy don ita Allah_Allah ma take su sallameta taje tayi abinda yake gabanta
Microphone dake dunkule a hannunta ta bude tana kallo, one side of her heart is much excited and overjoyed na wnn abinda ya faru kamar wani miracle and the other side cike yake da kunci na ganin mahaifinta cikin one of the most wanted criminals
Saide kamar yanda tayiwa kanta alkawari da yarda Allah saita cika shi ta hanyar bada kwarara kuma cikakkun shaida akan dukkan abinda ta sani
Wani doctor da nurses biyu dake biye dashi a baya ne suka shigo dakin da Fahime ke kwance ya tambayeta yanayin jikinta
"Doctor am fine, please i need to go now"
"Hakuri zakiyi don ba'a bamu damar discharging kowannenku ba andthe hospital is on tight security"
"Doctor sauran en uwana fah i mean the first lady Zee kaita da dayar matar?"
"Duk suna hutawa, Zee is fine too saide dayar patient din is on critical condition just pray for her"
_KING_
Dakyar aka barshi ya shiga ganin Zaki, saida ya chanja kayansa zuwa na asibitin snn hatta takalmi saida ya cire don ba'a son making any possible sound
Ganin yanda Zaki yake nade cikin bandages daga fuskarsa har zuwa jikinsa ya idon King tara kwalla, tsananin so da tausayin Zaki na kara mamayar ransa. He's badly injured duk sbd shi kullum yana risking rayuwarsa
Ya tuna lokacin da DIJA ta haihu, lokacin da yayi accident koh yace AA yasa mota bin kansa yanda Zaki yasha dawainiya dashi har yayi yanda yayi ya fitar dashi a kasar ba tareda sanin kowa ba
"GIDAN GONA"
Maganar Zaki na karshe ne ya dawo kansa
"Me yake nufi da Gidansa na gidan gona?"
COMMENTS
SHARE FISABILLAH
[1/6, 9:13 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*
BY APHSERTEEN KHAIREE
ELEGANT ONLINE WRITERS
_Here we are_ 🤸🏻♀️🤸🏻♀️
35
Saida ya biya wajen sauran patients d'in ya dubasu,d'akin da Saudat take ya shiga last.Tsananin tausayin halin da yaganta a ciki yasa idonsa tara kwalla don saida ya tambayi likitan condition dinta
Tana kwance ringingine an lullubeta don koh kaya bbu a jikinta,wanke bayanta da akayi aka cire duk wani dauda yasa duwawunta kamar an tuna rami
Bacci takeyi cike da nutsuwa na saukin azabar da takeji kwanaki,fuskarta tayi fiyau sai wani uban haske datayi kamar farar takarda
Tunani yake a ransa
"Koh wacece wnn?koh wanene yayi sanadiyyar zuwanta gidan?"
Yana mata fatan tashi lafiya snn ya mata tarin tambayoyin dake bakinsa akanta.Sai kuma tunanin Dijansa ya fado masa rai.Tho ina suka kai mishi Dijansa,idan har dagaske tana hannunsu dole a sameta a gidan.Ina AA yakai masa ita? Bashida mai amsa masa dole ya fita daga dakin zuciyarsa na masa zugi
Compound din asibitin ya fito dukda dare ne don kusan 12 ama duk guards dinsa da sauran securities na zagaye a asibitin.Ganin King yasa su karasowa inda yake, wani guard dinsa mai suna Mario ya matso daf dashi yana tambayarsa koh yana bukatar wani Abu ne
"Ka kaini gidan gona"
Abinda yace masa knn ya karasa wajen motocinsa dake pake.Gudun da drivern yakeyi yasa cikin 20mins suka karasa gidan gonar tasa. A bakin gate din gidan dake jikin gidan gonar suka tsaye driver yayi horn saiga maigadi ya leko,ganin motocinsu King ya sashi budewa da mamaki don duk inda yaga motarsu zai ganeta shi kuwa King tun dawowarsa garin bai leko gidan gonar tasa ba sai yau kuma a daren nn.
Gabadaya motocinsu 3 suka shiga gidan kowanne yayi parking. Mario dake gaban motar da King yake ya fito da sauri ya budewa King dake zaune a bayan motar ya kwantar da kansa kan kujerar idonsa a lumshe.Saida yakai kusan 5mins tukunna ya fito
Mai gadi kuwa yana gama rufe gate din jikinsa na rawa ya karaso gaban king cikin tsoro abinda zai biyo baya sbd guduwarsu Dija, kafin King yayi magana yayi sauri cikin rawar murya yace
"Wallahi ranka ya dade shammata ta tsohon nn yayi,kafin na ankara ya bugamin sandar hannunsa suka gudu.Don Allah amin afuwa karna rasa aikina"
Cikin rashin fahimtar zancen nasa King yace
"Me kake nufi kuma suwaye suka gudu?"
"Ranka ya dade mutanen da Oga yake kula dasu anan shekara da shekaru"
"Su waye na tambayeka kuma wani oga?"
Cikin tsawa King yayi maganar wanda yasa har hantar mai gadi kadawa don tsoron yayin King daya gani
"Ranka ya dade wallahi nima ban sansu ba,kawaide Oga yacemin na dinga kula karna bari su fita koh nn da cen don Allah amin afuwa a yafemin kuskurene"
"Waye ya saka aikin,waye Ogan?"
"Ranka ya dade bansan sunanshi ba hasalima bansan shi ba don shekara 6 knn daya sani aiki saide shima da irin wnn motocin yake zuwa nn shi yasa na shaida taku kila yaronka ne"
"DIJA"
King ya furta da wnn irin tune
"Tabbas naji dattijon nn ya furta suna nn ranka ya dade lokacin da zasu gudu"
"Yaushe suka gudu?"
"Jiya da safe ranka ya Dade"
Wani hucin iska mai zafi king ya fesar, for all this while knn su Dija na hannun Zaki a cikin gidansa ama bai taba fadamasa ba.Meyasa Zaki zai boye masa abu mafi mahimmanci a rayuwarsa haka,meyasa zai barshi yayi ta fama da rad'ad'in zuciya na rashin matarsa.
Knn DIJANSA na raye tsawon lokacin nn karkashin kulawar na kusada shi ama bai taba sani ba.Ya rasa wani irin yanayi yake cikin,farin ciki jin Dijansa na raye karkashin kulawar Zakinsa koh kuwa 6acin rai na 6oye masa da yayi ga.
Saide kuma menene yasan Zaki nada tasa munafar na yin hakan wanda tashinsa lafiya ne kadai zai warware masa dalilin 6oye masa Dijansa na tsawon lokacin nn.
Wannan shi ake cewa ga koshi ga kwanar yunwa,yaga samu yaga rashi.Gashi de ya samu labarin Dijansa tana raye da inda take yasan tana cikin koshin lafiya da kulawa da tsawon lokacin nn sabanin mafarkinsa da tunaninsa dake nuna masa Dijansa na cikin tsananin ukuba saide kuma gashi ta kara su6uce masa a daidai gabar da zai hadu da ita.
Haka ya shiga mota suka kuma asibitin,zuciyarsa a cunkushe.Dakin da aka cemasa Fahima take ya shiga don dazu ita kadaice bai shiga ya dubata ba Zee kuma har lokacin allurar baccin da aka mata bai sake ta ba.
Fahima na ganinsa ta mike daga kwanciyar da take akan gadon asibitin tana tunani. Sallama ya mata ta amsa kanta a kasa sbd kwarjinsa da yanda taji gabadaya ya cika mata ido,kujerar dake ajiye gefen gadon ya zauna akai yana fuskantarta
"Ya jikin naki?"
"Alhamdulillah"
"Meya kaiki Abia?"
King ya tambayeta tarrda kafeta da ido don shi duk tsammaninsa bin kokkofinta kan aiki ne ya kaita Abia.Idonta ne ya cicciko da kwalla tayi kokarin maydasu don bata bukatar kowanne irin rauni da zai jawo mata ragontaka
Ajiyar zuciya ta sauke,ta dago kanta suka hada ido da King snn ta mayar gefe
"Mahaifina ne ya bada sacrifice dina ga kunqiyarsu"
With a little bit shock and surprise King ke kallonta,cikin mamaki yace
"Shima membern cults dinne?"
"Ehh,ban taba sani ba sbd ba zuwa wajenshi nakeyi ba saida ya kirani akan yanason ganina shine naje garin"
"Innalillahi wa inna ilayhi raji'un,shima musulmi ne kamarsu AA"
"Aa,sunanshi Uchenna"
"And ur surname?"
Nan Fahima ta bashi labari tun daga zuwan Uchenna garin Kaduna da haduwarsa da maminta kamar yanda ta bata labari har zuwa abinda ya faru dashi Wanda yayi sanadiyyar guduwarsa ya kuma garinsu da yanda akayi ya kuma Christian sbd gudun talauci da kwadayin dukiyar da kawunsa ya masa alkawari wanda hakan yasa maminta guduwa da ita da dawo Kaduna.Har labarin da Uchenna ya bata na sanadiyyar shigarsa kunqiya duk saida ta Bawa king
"Duk inda zanje ina saka microphone a jikina Wanda yake nadar kowanne irin magana da akayi a gabana,lokacin da Babana ya kaini gidan kunqiyar ma microphone din na jikina.Duk labarin daya bani na sanadiyyar shigarsa kunqiya da fansar raina dana yaransa jarirai daya bayar yana nade a ciki hakama maganganun da AA yayi na kawo wnn baiwar Allah kunqiya ya dauka matarka ce da kashemin Mamina dayayi duk yana ciki.Wnn na tabbata itama babbar shaidace da zamu amfani da ita wajen gurfanar dasu"
Ta fada tare da mikawa King microphone din,jinjina Kansa yayi kawai don yama rasa mai zaice a halin yanxu ya karba
"Saida safe"
Yace mata kawai ya fice a dakin.Dakin da Zaki yake ya kuma a hankali ya bude kofar bbu kowa sai sautin na'ura dake fita a hankali ya zauna agefen kafafun Zaki YANA kallonsa cikeda tausayi
_6YRS BACK_
Cikin sauri,d'auki,farinciki da murna na samun kyauta da ido koh mulki bazai taba baka ba.Kyauta tafi komai daraja,kyautar 'ya'ya har biyu a lokaci daya.In ba Allah ba wa zai baka
Hamdala kawai yake tayi daga zuci har baki ya fito daga asibitin inda ya nufi parking space ya shiga motarsa don dauko kayan da nurses suka buqata ya kawo cikin gaggawa sbd kid'ima da rudewar yanda yaga nukudar Dija ya tashi basa sun tuna da kayan haihuwa ba gashi dare ne don har anyi isha'i su Babaji da Dada kuma suna gefensa koh ta Kansu bai bi ba suka wuce
Haka yake ta sharara gudu a motar don titi babu wadatar motocin don lokacin har 11 ta wuce,wata katuwar trailer ya gani tana dososhi gadan².Take ya fara kokarin kaucewa ama sai yaga duk inda yayi da kan motarsa tana binsa kafin kace mai sai ganin trailer yayi a kansa,daga nn bai sake sanin inda kansa yake ba ...
_Not edited_🙅🏻♀️
_COMMENTS_
_SHARE FISABILLAH_
[1/6, 9:14 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*
BY APHSERTEEN KHAIREE
ELEGANT ONLINE WRITERS
.🤏🏾✍🏾5STARS NOVELS ELEGANT ONLINE WRITER'S✍🏾🤏🏾
Albishirinku masoya karanta zafafan litattafan Hausa, na ELEGANT ONLINE WRITER'S, muna tafe da wani zazzafan albishir gareku, ƙungiyar ta shirya fitar muku da fitattun litattafai guda biyar a wannan sabuwar shekara me kamawa insha Allah.
Kamar yadda kuka sani, wannan ƙungiyar ta saba kawo muku zafafan litattafai, masu ilimantarwa, faɗakarwa gami da nishaɗantarwa kamarsu
MOON ,AUREN KIYAYYA,YAR AIKIN GIDINA , SHALELEN BAFFA, NEEHAL, LOST PRINCE Dakuma FORBIDDEN LOVE haɗi da AUREN FANSA.
Da sauran litattafai wanda suka saba nishaɗantar daku.
To gadama ta samu, awannan karan ma kungiyar ta ware muku kayatattun littafanta na shekarar 2022,wanda zasu samar muku da nishaɗi ds ilimantuwa.
littafan daban suke suntattare da duk wani kalar nishadi,soyayya,cin amana,zamantakewa,dakuma ƙaddara.
Karku bari a baku labari, dan tabbas baza kuyi dana sanin siyan wannan litattafan ba.
1. TUGGU BIYU
Aleeshatulkhairi phone
Wacce ta zanzare ta nishadantar daku a cikin littafinta maisuna NAMIJI KENAN.
2.IDAN ZUCIYA TAYI WAKE.
(meerarh)
Wacce ta fadakar daku tare da nishadantar daku acikin littafinta na HUBBUR-RUH.
3.NIHLAH
Mammy kabeer
Fitacciyar marubuciyar nan wacce ta nishadantar daku da littafinta na NASREEN da GIDAN AIKINA.
4.MATA A YAU.
(aphsert)
Matashiyar marubuciyar nan wacce tazo muku da kayataccen littafin RETURN OF THE KING.
5. ZUBAR HAWAYENA.
(Gimbiya Ayshu)
Wacce ta nishadantar daku cikin littafin LAILAH
ne kacal dan jin dadinku.
Sannan gamasu biya ta account zaku turo kudin ku ta wannan account din
👉0623151889 Aisha nura murtala Gt bank.
Evidence of payment
👉08148360851
Ga maison littafi guda daya kuma saiya tuntubi lambar dake jikin littafin daya ke so.
Masu turo katin waya kuma ta nan
👉09067211352
Idan kana bukatar littafi daya ne daga ciki kawai ka tuntubi wannan number 08148360851
Littafan daban suke ko wanne da salonsa kada ku sake abaku labari ko ayi baku ,saikunzo💃💃💃💃💃💃💃
Insha Allah, litattafan zasu fara zuwa muku, ranar ɗaya ga watan Janairu shekara ta 2022
Kar ku bari a baku labari
36
Tunda yaji wayar da AA yakeyi na plan d'insa da aikin daya bayar