Showing 42001 words to 45000 words out of 56965 words
Chapter 15 - RETURN OF THE KING COMPLETE BY APHSERT KHAIREE .txt
muyi magana?"
Fahima ta tambayeta,dakyar ta bude bakinta tace
"Bana iya zama"
Take idon Fahima ya tari kwalla cikin tausaya mata tace
"Wanene yayi sanadiyyar zuwanki gidan nn?"
"Nima bansani ba kawai na farka na tsinci kaina ne a wannan dakin"
"Daga ina kenan?"
"Daga asibiti,nasan de labour ya tasomin daga gida surukata ta kawoni asibiti.Na wahala sosai har karfina na kare ban haihu ba harna fita a hayyacina daga nan sai farkawa nayi na tsinci kaina a wannan dakin"
"Mijinki fah?"
Saida tayi shiru kamar bazata tanka ba sai kuma ta sauke numfashi muryarta na rawa tace
"Allah ya mishi rasuwa tun cikina nada wata 4"
"Iyayenki fa da sauran danginki?"
Shiru tayi bata Bawa Fahima amsa ba
"Kiyi hakuri da tambayoyina ama yana da mahimmanci musan junanmu tunda kaddara ta hadamu"
"Sunana Saudat Ni marainiyace,iyayena sun rasu tun ina karama na taso a wajen kanwar babana. Na wahala a hannunta sosai har Allah ya kawomin miji nayi aure.Habib ya zame min mijin marainiya, don ya kula dani ya bani gata da kulawa da dukkan mace zata buk'ata wajen miji. Mahaifinsa shima ya rasu sai mahaifiyarsa da suke zaune tare
Habib ya rasu sanadiyyar hatsarin mota a hanyarsa ta zuwa Zaria shine na koma wajen Ummansa da zama na cigaba da rainon cikina wanda kullum yake bani matsala sbd mutuwar mijina daya shigeni sosai har zuwa lokacin haihuwa na"
Daga Fahima har Zee sun tausayawa labaryn Saudat.Gashi koh hawaye yanxu bata iyayi sai ajiyar zuciya,Fahima ta sake tambayarta
"Wani asibiti aka kaiki a ranar da zaki haihu?"
"Asibitin da nake ante natal HEALTH CARE"
Shiru Fahima tayi tana tunanin,asibitin da Dija ta haihu kenan
"Tsawon shekara nawa kina gidan nan?"
"Nima bansani ba sai dazu danaji mutumin daya fita yana fadan 6yrs"
Sai lokacin maganganun AA ya fara dawowa Fahima kai
_kin taka sawun barawo_
"Wato ba ita akayi niyyar daukowa ba kenan"
_Nida kaina bansan ya akayi kikazo gidan nn ba a maimakon DIJA_
"Ya shiga asibitin da niyyar dauko DIJA bai sani ba ya dauko wannan baiwar Allah.Toh knn sace DIJA plan din AA ne sai kuma yayi rashin sa'a
Idan hakane tho ina ita DIJAN take da yaranta?"
Ita kadai take ta maganganunta,cen kuma ta sake yiwa Saudat tambaya
"CS aka miki koh da kanki kika haihu don na tabbata koh wanne ne dole zaki gane bayan kin farfado"
"CS akamin,lokacin dana farka ina kokarin mikewa sbd dakin dana ga kaina a ciki baiyi kama da dakin asibiti ba sai naji zafi daga cikina ina dubawa naga alaman dinki.Haka sukayita kula dani na tsawon lokaci harna warke daga nan suka fara....."
Kasa karasawa tayi itama Fahima bata kara magana ba sai tunani data fada.Sun kai kusan 20mins dukkansu da abinda yake sakawa banda saudat data gama cire rai take yiwa kanta adduar mutuwa ta huta.Mayarda kallonta kan Zee datayi shiru tana kallon waje daya Fahima tayi ta dafa kafadarta,juyawa tayi tana kallon fahima cikin nauyi
"ZEE KAITA zaki iya fadamin wacece ke?"
Saida tayi shiru na en seconds tukunna tayi ajiyar zuciya ta fara bawa Fahima amsar tambayarta
"Sunana Zainab Yusuf,asalina ni er Katsina ce wato garinmu daya da AA KAITA hakama anguwarmu daya.Tun AA na secondary school SS2 lokacin ina JSS1 yace yana sona irin soyayyar yarintar nn,iyayena sunyi² su rabamu ama naqi haka harya gama secondary school muna tare.Da farko AA inyazo wajena haka zaita tattab'ani tun ina ki nima harna saba abin yakemin dadi, bana mantawa akoi ranar da AA ya daukeni mukaje dakin abokinsa muka fara wasanni kamar yanda mukeyi don yace bazai shigeni ba harsai munyi aure,bansan ina da karfin sha'awa ba sai ranar don na kasa jure wasan da AA yakeyi dani har saida na sashi yayi amfani dani a Wannan ranar.Toh tun daga nan nida AA muka saba da juna ta wannan fannin koh bai nemeni ba ni zan kai mishi kaina.Ana haka har nayi ciki wanda yayi sanadiyyar mahaifina zuciyarsa ta buga shine mahaifiyata ta daukeni mukaje aka zubar.
Bayan AA ya samu makaranta a Lagos ya tafi ni kuma na kasa rike kaina gashi bbu wanda nakeso na aura kamarshi haka na zama tamkar public toilet ina rabawa maza kaina,na zubar da ciki harsu 4 da kaina wanda ya zama sanadiyyar damaging mahaifata.Bakin cikina ne ya dasawa uwata hawan jini itama ta mutu ta barni ni kadai dama mu uku ne kuma dukkanmu mata nice karama,yayuna mata sunyi aure daya tana bauchi daya tana kano.
A wani zuwa hutu da AA yayi ne yaga yanda na koma shine ya daukeni muka tafi Lagos tare ya kamamin daki. Zuwa na Lagos ya kara budemin ido saboda irin kudin da AA yake kashemin,kowanni club ina nan duk wani bariki da yawon duniya ina gaba har AA ya gama karatunsa.Soyayyar dayake min da tausayina na tunanin shiya fara jefani a wannan harkar yasa shi aureni muka dawo Kaduna da zama inda ya samu aiki.Tun lokacin da na fara daura idona akan KING naji duk duniya bbu wanda nakeso kamarshi,babu irin dabarun da banyi ba akansa tun inayi a boye harna fito fili ama KING bai bani hadin kai ba dukda yanda surata da kyau na ke tasiri akan kowanne namiji shi kadaine daban a cikinsu shiyasa akullum yake kara shiga raina"
"Da sa hannunki a batan matarsa DIJA kenan don cimma burinki akansa?"
Shiru tayi kamar bazata tanka ba cen kuma tace
"Babu sa hannuna a batan DIJA ama bazan boyemiki ba nafi kowa farinciki a lokacin danaji labary saide farincikin nawa ya koma ciki lokacin da naji shima KING din an nemesa an rasa.Tsawon shekaru ina dakon soyayyarsa da burin dawowarsa har zuwa ranar da labarin dawowar tasa ya baza gari saide a ranar farincikina ya zama ragagge"
"Saboda me?"
"Saboda sex photos da videos dina da aka turamin da aikin sace yaronki da mahaifiyarki idan kuma banyi ba za'a yada wannan videos din da photo duniya tasan wacece ni"
Sauran maganar da AA yayi dazu ne ya sake dawowa kwanyar Fahima
_Ni nayi amfani da wannan bitch din tawa ta hanyar blackmailing dinta da past dinta,sabod tana tsoron kar a bata mata image a matsayinta na first lady_
"Kenan AA ne ya kashemin MAMI na?"
COMMENTS
SHARE FISABILLAH
[1/6, 9:11 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*
BY APHSERTEEN KHAIREE
ELEGANT ONLINE WRITERS
31
"Yanxu son zuciyar AA har yakai haka,me nayi masa da zayyi amfani dani wajen tarwatsa amininka,me nayi masa da zaai rabani da Mamina?"mena masa dazai so tarwatsa farin cikina akan abin duniya abin duniya fararre qararre abin duniyar da zamu mutu mubarshi dukiyar da daidai da kwayarta sai antambayeka yanda ka tarata dukiyar da ranar kiyama zakaji dama baka tarata ta wannan hanyar ba ranar da bbu wani mai cetonka ranar da halinka shine jarinka yahh subhanallahi Allah kayimana kyakkyawan qarshe karabamu da son zuciya ameeen
Kuka takeyi sosai mai ban tausayi Zee na tayata,Saudat kuwa sai mayarda numfashi takeyi dakyar.Karar bude kofa sukaji inda wani guards ya kawo musu abinci a takeaway guda uku ya ajiye.Zee ce tayi karfin halin janyo abincin sbd wani irin yunwa dake nuk'urk'usarta,kokarin tashin Saudat tayi ama ta kasa daga koda kanta ne sai numfashi take saukewa a wahale.Fahima kuwa koh kallon abincin batayi ba daman,addu'a kawai takeyi Allah ya kawo musu mafita kohta halin k'ak'a su bar gidan nan don ta dau alwashin matukar ta bar gidan nan sai ta tona musu asiri.Idan kuwa government sukayi burus da lamari don halin kasarmu kenan na rufe manyan laifuka,ita da kanta zata d'au fansa da hannunta koda hakan na nufin karshenta kenan.
_KING_
Tunda suka sauka a d'akin nan bai huta ba koh na minti daya dama da alwalarsa ya taho, sallah ya dingayi yana karatun Qur'an dake haddace a kansa ba qaqqautawa wanda sautin zazzaqar qira'arsa ke tashi daga dakin yana daukar gidan a hankali.Ji yayi an banko dakin nasa a gigice cikin rudewa don karatun da King yakeyi har ODUBARIBA na amsar sakon a jikinsa daman gashi karfinsa ya fara janyewa shiyasa yakeso a nada sabon shugaba tun fakin komai ya lalace musu.
Wasu guards ne biyu suka shigo dakin da bindiga hannunsu suna pointing din King,bai dago ba har saida yakai aya tukun ya daga kai yana kallonsu.Kasa hada ido sukayi dashi sbd wani kwarjini daya cika musu ido dayayi
"Stand up and put ur hands at back"
Daya guard din ya fada,ba musu King yayi yanda sukace
"Oya move"
Gaba ya wuce suna biye dashi a baya har suka fice a dakin,hanyar corridor din suka biyo inda dakuna ke jere suna zuwa dai² dakin dasu Zee suke King ya tsaya yana kallon kofar dakin,nishin Saudat da kukan Zee ke tashi daga dakin sbd bbu komai a dakin sai kujera kwaya daya shiyasa yake daukar sauti sosai
"I said move"
Dayan guard din ya sake magana yana taba keyar King da gun din dake hannunsa har suka karaso parlor dake cike da mutane,bin jama'ar parlor ya farayi da kallo.
Gboy da Suleguy ya fara daura idonsa kansu kana ganinsu kaga cikakkun hausawa sai AA KAITA dake zaune daga gefensu,idonsa ne ya sauka kan David da Samuel da koh a mafarki a gansu sai ganesu sai wata fuskar daya d'au kusan 2mins yana kallonta sbd tsantsar kamarsa da Fahima Aliyu.Dauke idonsa yayi ya aza kan Joseph da Marcus da bai shaidasu ba sukam.
D'an lumshe idonsa yayi ya bude inda idonsa ya sauka kan mutumin da ya daukeshi danginsa yanxu,yake jinsa kamar jininsa,mutumin da a yanxu yake jan zaren ragamar rayuwarsa,yake tafiyar da komai nasa,yasa masa Sunansa sbd shakuwa da soyayya dake tsakaninsu wato ALIYU sannan ya mishi laqabi da ZAKI akan jajircewarsa da rashin tsoronsa akan komai.Ji yayi kamar an sokeshi a ransa,runtse idonsa yayi ya sake budesu saboda ya qaryata abinda yake gani
"No Zaki,not you.Zan iya daukar kowanni irin cin amana a wajen koma wanene ama banda kai Zaki,please ka karyata min abinda nake gani da idona,kace min kaima daukoka sukayi"
Zaki dake zaune kan wata single chair dake daban kamar ta sarakuna yayi cross leg fuskar nan a toshe da bakin glass as usually ga guards din King a zagaye dashi ta bayansa.AA KAITA ne ya ari bakin Zaki ya fara magana
"U see our humble King hatta na hannun damanka ya zabi yayiwa Kunqiya aiki,so u have no other choice than to surrender"
"But ZAKI why,meyasa zaka siyarda loyalty ka?"
King ya tambayeshi still idonsa nakan Zaki
"Saboda zan iyayin komai akan kudi,zan iya siyarda komai nawa akan kudi har shi fucking loyalty da kake fada"
"Me kake buqata wanda na kasayi maka?"
"Mai kake dashi yanxu da zakamin?"
"Kasan de zan maka komai matukar na samu kujerar da nake nema"
"That will be too late my King"
Dariya sukaga King yasa wanda ya bawa kowa mamaki suna kallonsa wasu na tunanin koh ya fara tabuwa ne na shock din abinda Zaki ya mishi,yana daga tsaye a tsakiyarsu yana kare musu kallo daya bayan daya haryazo kan AA KAITA
Tafi ya fara yana
"Well played ama dukkanku kunyi babban kuskure har yanxu bakusan wanene KING ba har kai kanka My old friend.Ni ALIYU MOHAMMED GIWA,the real Lion har kuna tunanin zan karaya cikin k'ank'anin lokaci bayan tsawon lokacin dana dauka bananan,bayan dukkan abinda ya faru kuna tunanin zan dawo cikin sanya.
Ina sane da dukkan plan din enemy na before they even make it,ina sane da dukkan move dinku. Kai AA KAITA a tafin hannuna kake duk wani wasanka a gabana kake yinsa,duk inda zakaje a idona nake ganinka hakama duk wani plan da zakayi a kunnuwana nake jinsu"
Daga idanunsa da suka rine sukayi jaa nan take,jijiyoyin kansa suka fito rad'a² ya kalli Zaki daya cire glass din idonsa suka kalli juna ido cikin ido ya kira sunansa da wani irin tune mai gigitarwa wanda har saida gidan ya dauka gabadaya
"Let's cut the bullshit"
Wani irin mikewa Zaki yayi ya saita bindigarsa kan Joseph dake kusada shi ji kake
"Tauuu....."
_DIJA_
Tunda ta tashi yau gabanta ke faduwa,zuciyarta ke tsinkewa sai addua kawai takeyi.Ba abinda takeso kamar taga ta bar gidan nan da suke tsare cikinsa,a yau ta yanke shawarar guduwa kota halin k'ak'a.
Fitowa tayi daga dakin da take ta nufi nasu Dada,tun a parlor taga bbu guard tayi knocking kofarsu Dada.Babaji ne ya bude ya Dan kara tsufa, ganin Dija a tsaye da sassafe don koh 8 baiyi ba yace cikin fullanci
"Lafiya kuwa,koh kina bukatar wani abu ne?"
Batayi magana ba ta wuceshi ta shiga dakin inda Dada ke zaune kan cushion dake bedroom din
"Dada,Babaji ku shirya yau zamu bar gidan nan"
"Me kike fadane,idan muka bar nan muje ina kuma kina ganin mutanen nan zasu barmu mu fitane?"
Babaji ya tambayeta
"Tabbas yau zamu bar gidan,kota wani hali Babaji don na gaji da wannan tsaron"
Gashi nan loma daya 🤸🏻♀️
COMMENTS
SHARE FISABILLAH
[1/6, 9:11 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*
BY APHSERTEEN KHAIREE
ELEGANT ONLINE WRITERS
32
Da sauri Dada ta mike tsaya tana
"Yawwa bingel am daman kullum abinda nake fad'a masa kenan ama tsoro ya hanashi koh ina fullancin nasa ya tafi oho,kinga idan shi bazai tafi ba muyi tafiyarmu mu kyaleshi har shekaran yanka kansa yayi"
Kallon Babaji Dija tayi cikin fuskar magiya tace
"Don Allah don Annabi Babaji am kazo mu gudu kafin su dawo"
"Tho idan muka gudu daga nan ina zamuje?Kina ganin de duk tsawon shekarun da muka dauka a gidan nan babu wanda koh kallon banza ya tabayi mana, kullum suna kula damu,duk abinda muke buk'ata sunayi mana.Nide don Allah da kunyi hakuri har muga gudun ruwansu"
Magiya sosai Dija tayi Babaji ba yanda ya iya hakan nan ya dauki sandarsa,Dija bata bari sun dauki komai ba cikin sand'a suka fito parlor suna lekawa luckily kuwa gidan babu kowa daga cikin guards din.
Bayan sun fito compound d'in gidan suka hango mai gadi daga bakin gate,nan suka b'uya a bayan wani gini dake varander entrance.Kusan 20mins suka tsaye cen suka hango mai gadin ya mike ya dauki buta yayi hanyar toilet
Habaa kan kace meye DIJA dasu Babaji suka runtuma a guje inda maigadi yaji sautin gudunsu kafin ya shiga toilet din,Dija na kokarin bude sakatan gate din maigadin ya nufosu yana
"Kai kai ina zakuje? Ku tsaya,Ku tsaya nace"
Yana karasuwa Babaji ya maka masa sandan hannunsa a kai, nan ya fadi saboda azaba.
_ABIA STATE_
Jin karar harbin bindigan kota ina ne ya firgitasu Fahima da Zee suka hau ihu suna salati,ita kuwa saudat salati kawai takeyi daga kwance koh motsawa batayi ba ta runtse ido don ta saddakar kawai lokacinta ne yayi,abinda kullum take addua yau Allah yayi.
Sosai su Fahima suka firgita ba kadan ba don Zee kam har suma ta dingayi tana farfadowa da kanta,ta cukurkude kanta a jikin Fahima tana ihu
Bangarensu Zaki kuwa barin wuta aka d'ingayi tsakanin Guards dinsu danasu AA,Zaki yayi nasarar kashe mutum 3 daga cikin en kunqiya dake parlor don bbu bindiga a hannun kowannensu sai guards d'insu kawai kuma abin ya mugun zuwan musu a bazata
KING na tsaye a inda yake, koh motsawa baiyi ba zuciyarsa sai tafarfasa take idonsa yayi jajir gabadaya ya wani rikid'e yana kallo AA ya silele a gudu daga parlor. Wani murmushi kawai yayi
AA na fita compound d'in gidan ya farajin Siren d'in motar police koh ta ina da alama an zagaye gidan,zagayawa yayi da wani kofa dake bayan gidan ya gudu
Tun daga waje police suka fara bata kashi da guards din dake zagaye daga wajen gidan inda sukaci nasarar kama wasu,wasu kuma an harbeshi har suka shigo cikin gidan
"All hands behind ur backs"
Wani dake gaba cikin uniform d'in police ya fada bayan sun shigo parlor dayayi kaca² da jini, nan dukka guards din suka daga hannayensu banda Zaki daketa wani irin huci.King kuwa kujera ya nema ya zauna yana kallonsu Uchenna dake boye daga bayan kujeru
Takowa police din yayi har gaban Zaki,ya Sara mishi irin yanda akewa manya
"Weldone DSS ALIYU DAPO"
"Thank you,a fitar da corpses da wanda sukaji rauni.Ina fatan kun taho da ambulance?"
"Yes Sir"
"Kuyi checking dukkan dakuna da kowanni lungu na cikin gidan"
"Okay Sir"
Jami'in tsaron ya fada tareda sarawa Zaki.Cikin huci da tsantsar 6acin rai Zaki yake binsu da kallo don shi baiso king ya dakatar dashi daga cin uban wad'annan da bbu imani koh kwayar zarra a zuqatansu ba duk sun b'uya a bayan kujera sai karkarwa suke cikin tsoro. Juyawa yayi ya kalli king da rinannun idanunsa yace
"king akashe wadannan banzayen marasa amfani tun a nn bbu wanda zaiji kuma yagani, duk police nan are under my control barinsu bashida wani rana saima rage mugun iri da zamuyi"
girgiza kai king yayi ya kalli zaki yace
"Calm down my lion inaso a gurfanar dasu agaban shari'a saboda yanzu haka en jarida suna hanya dakuma en gidan television saboda komai live nakeso ayishi yanda koda manya qasa zasu rufe maganar mutane bazasu basu wannan damar ba"
Wani police ne ya shigo dakin ya sarawa Zaki yace
"Sir en jaridar sun karaso"
"Permission carry on"
yacewa police din nan akashigo da cameras masu video live nayi masu daukar photo nayi masu rubutawa nayi nan gidan ya cika maqil anata haskawa alabarai yayinda aka sako hoton gwamna maici wato AA KAITA ana nemansa wanted
Wani tulu dake kusada king ya tunkude baisani ba nan fah ya fashe sai qarar tussssh kikeji take dakin yafara girgiza wani zobe a hannun ODUBARIBA da tuni ya fadi kasa yana shure² ya fara cire wani jan hayaki sai kuma kukan wani irin abu kamar dodo dayake tashi kamar daga kasan gidan
Zaki cikin qarfin hali ya fara bin inda yake jiyo sautin,ta corridor nn ya d'inga bi harya kaishi wajen steps d'in da zai kaishi underground
Sauka ya d'ingayi a hankaki cikin kwarewar aikinsa yana duddubawa har ya karasa wajen kofar dakin da sautin yafi fita sosai.Shiga dakin yayi nn take kansa ya fara juyawa,jikinsa ya fara rawa
Addua ya d'ingayi harya samu ya denaji,ashe dodon da suke bautawa wannan tulun daya fashe kusan qarfinsa ne aciki. Da farko Zaki ya girgiza da ganin wannan halitta saboda wani irin kwatantanwa da ODUBARIBA keyi gawani irin abu da yake fita abakinsa kore mai shegen yauqi bbu kyan gani.
Daga idonsa da jini me fita daga ciki yayi ya kalli Zaki da kuma king daya biyoshi abaya,yana kallon king ya qurma wani irin ihu domin king yashigo dakinne yana mai karantar Ayatul kursiyu abakinsa, ganin addu'ar tana illata Odubariba yasa king da Zaki suka qara qaimi wani kabbara king yayi tare da harbin wanna dodon a idonsa na dama habawa wani irin girgiza dodon yayi tare da wani ihu mai amo nan yayi kan Zaki kamin ya iso yaqara sakar masa bullet a tsakiyar kai nan ya zube ko shurawa