Showing 15001 words to 18000 words out of 56965 words
Chapter 6 - RETURN OF THE KING COMPLETE BY APHSERT KHAIREE .txt
yayi ya dan kwantar da kansa kan kujerar yana driving a hankali kamar wanda kwai ya fashewa a ciki don wani irin kasala ne ya ziyarce shi a take
'Haka muryarta yake da d'an karan dad'i mai ga dad'in sauroro koh kuwa shine yake jin hakan?'
A ransa yake maganar take kuma yaji koli²n takaici ya tukare masa aransa tunawa da jiya daya fara ganinsu suna bara,knn haka kuwa yakejin muryarta.Ya godewa Allah daya tsaresu a inda suke rayuwa ya d'au d'amarar basu kariya da kulawa sosai iya karfinsa don he can't hide the fact,he's madly in love with the girl zai iya yin komai akanta
COMMENTS AND SHARE FISABILLAH 🥰🥰🥰
[1/6, 9:02 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*
BY APHSERTEEN KHAIREE
ELEGANT ONLINE WRITERS
12
Har suka iso makeken gidansa dake tsakiyar unguwar gangare bbu wanda yace kala sai Dada da Dija dake magana kasa² tsakaninsu suna rarraba ido,bayan yayi horn maigadi ya bude masa gate nn su Dada suka kara tsurewa ganin wnn aljannar duniyar mai ban tsoro a idanuwansu sai kukan Dada suka jiyo wanda yasa King da Babaji juyawa bayan King yayi parking a compound din gidan
"Sikenan,sikenan hande min bone ya tabbata yau kwananmu ya k'are. Allah ya jikanmu ya jikanki bingel am"
Ta kara fashewa da kuka tana rike Dija da itama tasa kuka ganin Dada nayi badon taji abinda take yiwa kukan ba,girgiza kai kawai King yakeyi yana murmushin halin kafiya irinna Fulani, wato su inde suka kafe akan abu tho dakyar a juya musa ra'ayi.A da yanajin lbrynsu bai taba yarda ba sai yanxu daya gani ra'ayal ayn
Fitowa yayi a motar ya zagayo ya budewa Babaji shima ya fito don shi tsabar takaicin matar tasa koh magana ya kasa, bude musu back site din yayi. Dariyace ta su6uce mishi ganin yanda suka dungule waje daya suna kuka,Dada kuwa sai girgiza mishi kai take tana kara makalkale Dija a jikinta
"Rabu dasu kayi wucewarka,Ai'se ta fiye taurin kai kamar kafuran farko"
Babaji ya fada cikeda takaici,murmushi King yayi yace
"Aa Baba ayi hakuri,kazo ka lallabasu su shiga ciki"
Tsaki Babaji yaja ya matso kusada kofar baya,fada ya fara musu da fulatanci kamar zai ari baki yacewa Dija in bata fito ba sai ya kwakwkwada mata sandar hannunsa ba shiri ta dirgo daga motar kamar mai sauka akan machine saura kadan ta fadi kasa King da hankalinsa ke kansu yayi saurin rikota dukda haka saida guiwanta ya gurshe da kasan ai kuwa ta tsala wani gigitaccen ihu da saida gidan ya dauka wanda yasa Dada fitowa da sauri itama kamar zata fadi tayo kan Dija dake durgushe tana tsala ihu a kasa dukda kurjewar kadan ne saide ita duk k'ank'antar jini ta gani a jikinta tada mata hankali yake bataso.
Guri Babaji ya samu daga gefe yay zamansa ya dauke kai daga kallonsu, Dada kuwa zaman dirshen tayi a agaban Dija dake zabga kuka ta zuba uban tagumi kamar wasu marayu.
Magiyan duniya King ya musu akan su tashi a wajen don har an fara kiraye² sallah magriba ama sunk'i, kwallawa Baba maigadi kira yayi ya taho cikin hanzari
"Baba a aka kaisu waccen flat din na baya ka hadasu da masu aikin nn su nuna musu komai don ALLAH"
Ya juya inda Babaji yake zaune shima a kasa yana kallon wani waje yace
"Baba, ga Baba Audu zai nunamuku inda zaku zauna bari na shiga ciki lokacin sallah yayi"
Mikewa Babaji yayi yace
"toh yaro mungode kaide Allah yayi albarka" King ya amsa da Ameen ya wuce ciki da sauri.
"Muje baba" baba audu mai gadi yace tareda yin gaba, kallo daya Babaji yayiwa Dada da Dija da suke ragu6e waje daya a kasa sai wuri wuri da ido suke yayi wucewarsa batareda ya tankasu ba. Mikewa Dada tayi da hanzari tana cewa Dija ta tashi suka bi bayansa da dan saurinsu.
Saida aka yayi sallah Isha'i tukunna King ya shigo gidan tunda ya fita sallah magriba daman ya fadawa kukunsa akan yau ya kara sanwar girki yana da baki a baya snn inya gama ya kaimusu nasu da wuri. Flat din da su Dija suke direct ya wuce dauke da leda a hannunsu, a parlour ya samu Dada da Dija raku6e a kasa koh sallah basuyi ba. Shi kuwa Babaji daman tunda aka nuna masa dakuna da toilet da yanda zaiyi amfani dashi yay shigewarsa ciki bai kara bi ta kansu ba.
"Ha'a ya kuke zaune anan basu nunamuku dakunan bane, ina Baba?" king ya tambayesu, Dada tace
"Mude kayiwa Allah ka kyalemu gashi daga zuwan mu gidanka har jini ya fara fitawa 'yata tun kafin a yanka mu"
Cikin soma gundura da zancen na Dada dayaki ci yaki cinyewa King yace
"don Allah Dada ki bar zancen nn haka, ki yarda dani wallahi ni ba mugu bane. Ku kwantar da hankalinku ku dauki nn tamkar gidanku don Allah, yanxu de ga kaya na siyo muku da dan abubuan amfani. Ku tashi muje na nunamuku daki sai kuyi wanka kuyi sallah ga abinci ma naga an kawo muku"
Badan hankalin Dada ya kwanta da maganarsa ba dande bbu yanda ta iya ne, koma me ya samesu Baban Dija yaja musu, hakan nn ta daure ta mike tareda cewa Dija itama ta tashi.
Ita kuwa Dija tunda King ya fara magana take kallon bakinsa kawai, cewa take aranta inama tanajin abinda yake fada. Dakuna ne biyu a parlour sai kitchen da toilet, daya dakin ya bude ya samu babu kuwa Babaji na dayan knn ya shiga har ciki suka bishi, ya nunamusu toilet da komai ga furniture masu kyau wanda yasa su Dada sake baki suna kallo dakin kamar shashashai
Har ya juya zai fita ya tsinkayi muryarta tace
"BAD'D'O"
Juyowa yayi dukda baida tabbacin da shi take sai caraf idanuwansu ya sark'e dana juna,lumshe nasa idon yayi yanajin wani irin yanayi a jikinsa ita kuwa da sauri ta mayar da nata idon kasa ta fara wasa da zara²n fingers dinta tana cakud'asu da juna.Kura mata ido Dada tayi cikeda mamakin sunan da taji Dija ta kira King tana jira taji mai zatace masa
"Inason nayi wanka,a ina zanyi,a ina akeyi,dame zanyi kuma tayaya zanyi?"
Ta jero masa tambayoyi kusan hudu akan abu daya snn dayace mai hankali abin takaicin ma da fulatanci mutumin da koh zo na kasheka bayaji da yaren ama ita koh oho don duk tunaninta daga jiya zuwa yau ya fara koyan yaren nasu shiyasa tayi mishi tambayarta kai tsaye.
Tunda ta fara magana King ya k'ureta da ido yana kallon d'an karamin bakinta yanda take motsa shi dakyar tana maganar kamar an sata dole sai yaji ta k'ara burgesa sosai har baisan lokacin da tayi shiru ba saida yaji hargaggiyar muryar Dada tana mata magana cikin fada da fulatanci
Turo baki gaba Dija tayi irinna shagwa6a66un yaran nn
"Malam ki tafi kawai mungode,jeki abinki mun gane komai"
Murmushi King yayi ya fita tareda rufo musu kofar.Bangarensa ya wuce direct ya haura samansa sai lokacin ya shiga yayi wanka yasa jallabiya mara nauyi ya fito parlornsa dake hade da bedroom dinsa daya hannunsa glass cup ne filled with fresh milk yana dan sipping sai dayan kuma wayarsa ce yana dannawa,wata number da kana gani kasan bata nn kasar bace yayi dailing ringing daya biyu maishi yayi picking
Shiru yayi yana murmushi da alama maishi kai magana daga dayan bangaren,king ya yace
"So ya karatun, yaushe zaku samu hutu? I missed you here"
Murmushi ya kuma yayi yana sauraren mai magana
"Okay tho Allah ya nunamana,best of lucks"
Yayi cutting off,sai kuma ya kara dialing wata number bayan an dauka yace
"Yane guy,koda yake yanxu tsoho ne kai" dariya yayi bayan maishi yayi magana yace
"Nide ba wnn ba please inason gobe ka turomin Zee zata min wani taimako"
Tsaki yaja bayan maishi yayi magana yace "an gaya maka ni d'an iska ne kamar kai kuma in zanyi iskancin ma sai na rasa wanda zanyi dashi sai matarka ai saide kace nabi a hankali kar matarka tamin fyade a gidana"
Dariya yayi yace "OK OK sorry man,please tho tunda weekend ne goben sai kuzo tare it's urgent please"
"Yawwa ko kaipa,Allah ya kaimu Bye"
Shima ya yanke call din,TV ya kunna ya danyi kallo duk rabin hankalinsa yana cen wajensu Dija yanaso yaje ya sake dubasu kuma yana tsoron hargagin Dada,murmushi yayi ya ajiye cup din hannunsa kan table ya zura slippers dinsa tareda ficewa ya sauko kasa,saida ya duba koh ena masu aiki duk sun tafi part dinsu ya duba abincin da kuku ya jera kan table tukunna ya fice a flat din ya nufi nasu Dija.
Yaji dadin yanda yaga BABAJI a parlour yayi wanka ya chanza kaya ya sake yana kallo abinsa dama yacewa Bala mai gyaran gidan ya kunna musu TV,zama yayi akan kujera suka kara gaisawa da Babaji yana kara sa masa albarka.Cen suna zaune suna hira jifa² ama hankalin King ya kan kofar dakinsu Dija sai jin ihu sukayi daga cikin dakin kuma kamar muryar Dija......
More comments more typing 🌚
Share fisabillah 🙏🏻
[1/6, 9:02 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*
BY APHSERTEEN KHAIREE
ELEGANT ONLINE WRITERS
13
Da sassarfa King da Babaji suka k'arasa kofar bedroom d'in nasu, kicibis sukayi da Dada itama ta fito aguje dan fa ita har yanzu bawai ta gama yarda da gidan bane fadi take
"Babaji kazo ka duba meye samu Dija,na shigu uku ni A'ise"
kai tsaye king ya shige dan ya tabbatar da babu wani abin cutarwa a gidan,kusan karo sukayi da Dijan ma king yaja burki.Tsayuwa yai yana binta da kallo dan so yake ya gano abinda ya firgitata ganin a jike take jagab kayanta yamanne a dirarran surarta kamar ba er sweet 16 ba,kasa daukarsa kafafunsa sukayi sbd wani irin bakon yanayi daya kawo mishi ziyarar bazata cikin en seconds sai neman jikin bangon toilet din yayi ya jingina jikinsa don wani irin abu yakeji tunda ga yatsar kafarsa har tsakiyar kansa yana bin dukkan wani magudanar jinin jikinsa tareda aikawa zuciyarsa da kwakwalwarsa wasu irin sakonni masu wuyan fassara,jan kafarsa yayi ya juya yaci sa'a kuwa cikin kayan daya kawo musu sun bajeshi kan gado ya dauko hijab.
Daga bakin kofar toilet din ya wurgo mata hijabin din kawai komai bace ba sai wani lumshe ido kawai yakeyi,har lokacin Dija bata cikin nutsuwarta hannunta na rawa ta saka hijab din wajen wuyan na gefe.Sa hijab din yayi daidai da shigowarsu Babaji da Dada dakin magana king yayi yunk'urin yi sai yaji muryarsa ashak'e saida yayi gyaran murya ya had'iye abinda ya tuk'are masa a mak'oshi dakyar tukunna yana kallon Dija badan yanada tabbaci zataji shi ba yace
"Meyesa ki ihu?"
Babaji ne ya maimata mata da fulatanci sai lokacin Dija ta budi bakinta cikin sanyayyar muryarta daya hadu da kuka a take cikin fullanci take fadawa Babaji
"Na shiga zanyi wanka zan tari ruwa a waccen karfen da Dada ta nunamin ina murd'a wurin ruwan sai kawai naji ruwan zafi a kaina, garin gudu kuma santsi wnn ledar dake shinfide a k'asa da ruwa ya zubo akai yaso kayar dani toh garin qoqarin na gyara tsayuwata na sake murd'o kan wnn k'arfen sai ji nayi ana ruwan saman ruwan zafi daga kaina sai jin ruwan zafi nayi a gadon bayana da gefen fuskata,kamar an watsa min garwashi haka naji don azaba har na kusa fita hayyacina.Wajen gudun kuma nn ma ban tsiraba saiji nayi santsin ledan nn ya debeni ya watsar dani gefe,kaga gwiwar hannuna ma ya bugi wnn tukunyar dake ciki sannan na fadi dabas a qasa shine nasa ihu"
Ta karashe zancen da fashewa da wani sabon kuka,kallonta dukkansu sukeyi cikeda takaici babaji ya tambayeta
" Meyesa baki tambaya ba tunda bakusan yanda ake amfani dashi ba?"tace
"Na tambayi bad'd'o shine Dada ta ce tasani zata nunamin"
har lokacin kuka take sbd zugin da hannunta ke mata,tsaki Babaji yaja yace Allah ya kyauta muku yayi ficewarsa a dakin shi kuwa King kamar ya dawo dashi ya tambayeshi abinda ya samu Dijan har ransa yakejin kukan nata,ji yake kamar yazo yayi cuddling dinta ya sharrashi abarsa
"Kinga ya isa dena kukan haka,meya sami hannun? naki in gani"
Dasauri Dada ta rikota yace
"Aa k'ad'o yi tafiyarka kawai mun de mun shiga ukun mu mun lalace tunda mukazo gidan mutuwa gashi har mun fara ganin bala'i"
Girgiza kansa kawai yayi yace
"Bari na kawo mata magana"
Da harara Dada ta raka bayansa harya fice a dakin bai samu Babaji a parlor ba ya fita a flat din ya wuce nasa,harya dauko ointment din zai kawo musu sai kuma ya fasa.Wayarsa ya dauka ya kira Bala mai aikin dake bangarensu baifi 5mins ba sai gashi ya bashi maganin yace ya kaiwa bakin nn da paracetamol sachets har zai mika masa dukka sachet din saiya fasa ya b'alle dukka ya bar kwaya biyu kawai a jiki..
_Washe gari_
Tunda ya dawo daga masallaci ya koma bacci sai 9 ya farka cikin shauk'i don jinsa yake kamar wani sabon angon da aka kawo masa matarsa jiya, wanka ya shiga yayi ya shirya cikin Jersey black da wandonta iya guiwa ya mishi kyau sosai ya k'ara fito da ainihin chocolate fresh skin dinsa, ya brushing d'an gashin dayake tarawa kadan akansa da sajensa.Slippers dinsa ya zura ya fito madaidaicin parlornsa dake sama,dinning ya nufa direct sanin cewa duk weekend anan yake cin abincinsa hankalinsa duk yana kansu Dija koya suka kwana suka tashi oho? kwarmaton Dada ne ya hanashi zua dukda ya had'u da Babaji a masallaci da asuba don ya fito sallah yace mishi suna nn lfy ama hankalinsa bai kwanta ba ya fison yaje ya gansu da kanshi ya tabbatar da lfyrsu wanda yakejin yanxu kamar hakkine akansa yanxu tunda sun dawo karkashinsa.
Saida yaci ya koshi dam don baya wasa da cikinsa koh kadan tukunna ya bar kan dinning ya dawo kan cushions din dake parlor dama weekend sallah kawai ke fitar dashi waje yini yake a gida abinsa.
Favourite channel dinsa yasa mbc2 don yanason action films sosai,yayi lucking kuwa ana Ninja Assassin one of his favourite movies.Yana cikin kallo wayarsa ta fara ringing, AA KAITA ne a rubuce jikin screen din da murmushi yayi picking
"Muna downstairs"
Cutting kawai yayi ba tareda ya amsa ba ya kashe TV ya nufi hanyar stairs,tun kafin ya karasa sakkuwa idonsa ya sauka kan Zee data kafe kan stairs din da ido tana jiran fitowarsa.
Tunda King ya kira take Allah² gari ya waye,ta so AA ya barta ta taho ita kadai da koh bata kashe ishinta ba sai ta jiyarda kanta dad'in King ko kadan ne.Sanye take cikin wani arnen peach colour lace da akayiwa dinkin Riga da siket daya lafe kamar a jikinta aka dinka ga wuyan off shoulder ne wanda ya bawa lafiyayyen fresh white skin dinta bayyana ga boobs dinta kusan rabi a waje don mayafin ma one side ta yafa shida bbu duk daya ta bazo attachment har gadon baya tayi daurin ture kaga tsiya ga wasu shegun hills a kafarta tana taunar chewing gum cikin wani irin salo na riqaqqun en bariki.
Kallo daya king ya mata ya dauke kai harya wuce ta gabanta inda ya ajiye mata kamshin turarensa daya kara tafiya da ita wata duniyar ya doshi inda AA yake zaune yana masa murmushi shima yana mayar masa, hannun ya mika masa suka gaisa ya zauna kusa da shi suna hirarsu koh kallon inda take baiyi ba.Ita kuwa wani kasala ne ya ziyarceta ta kasa magana ta lumshe ido tanajin wani irin feelings a jikinta, ji take kamar ta tashi ta fada jikinsa ta masa tight hug tayi kissing warm soft lips dinsa wanda taga gani zasuyi shegen dadi.
Ajiyar zuciya ta sauke tana kokarin saita kanta wajen aro nutsuwa data rasa meyasa duk randa ta hada ido dashi snn ta shaqi daddadan kamshin turarensa take rasa dukkan wani nutsuwarta ba wnn inaga body contact ya hadasu fah?
Dakyar ta bude bakinta tace
"Morning my King"
Shi kua bayason My da take kiransa sam² ba tareda ya kalleta ba yace
"How're you Zee"
"Somehow"
Ta bashi amsa,still bai kalleta ba sai AA ne ya aika mata wani irin kallo na gargadi sarai ta gane ama ta basar.AA yayi saurin cewa King
"Man kace kana neman mu,hope lfy?"
"Klau, kawai wani taimako zaku min"
Caraf Zee tace "you're always my king,kuma menene just consider it done"
"Thanks" kawai yace mata ya mayar da kallonsa kan AA kamar shi zai masa aikin
"Dama inada baki ne a flat din baya da nakeso ki taimakawa yarsu tunda naga macece er uwarki"
Nn de ya basu labarinsu Dija ama bai fadamusu burinsa akan dijan ba yade ce kawai yanaso Zee ta taimaka mata wajen nunamata wasu abubua kuma yanason sata a school
[1/6, 9:02 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*
BY APHSERTEEN KHAIREE
ELEGANT ONLINE WRITERS
14
Flat dinsu Dija ya kaisu suna biye dashi a baya har AA daya kasa zama yanaso yaga wani irin aiki matarshi zatayiwa King din.Babu kowa a parlour don BABAJI na cen wajen Baba Audu mai gadi
"Ku jirani ina zuwa"
King yacewa su Zee ya wuce bedroom dinsu Dija yasan suna ciki,suna raku6e a k'asa dukkansu sai Dija daketa gabzar kuka Dada kuwa ta zuba uban tagumi kamar marayu.Hankalin King ne ya tashi ganin kukan da Dija takeyi "lfy?" Ya tambayi Dada,harara ta zuba mishi ta dauke kai daga kallonsa.Cikin fullanci Dija tace
"Yunwa nakeji Bad'd'o,Dada ta hanani fita a dakin kuma Babaji ma bai shigo ba tun jiya"
Cizan lips nashi King yayi sbd takaicin rashin jin abinda ta fada kuma yasan Dada bazata fassara mishi ba
"Dada don Allah ki yarda dani koh kadan ne wallahi banida niyyar cutar daku ki saki jikinki kiyarda da Allah zai kareku a duk inda kuke kuna tareda kariyarsa da yarda Allah bbu wanda ya isa ya cutar da ku"
Kallonsa Dada takeyi ido cikin ido harya gama,Allah daya ambata yasata jin nutsuwa a ranta da d'an kwanciyar hankali.Tabbas su kansu sunsan Allah ne kawai yake karewa irin gararin da sukeyi daga nan zuwa can kuma bbu guri daya dayake safe gwanda ma nan za'ace gidane saide zukatan masu gidan ne haryanxu bata da tabbas akai don ance mugun mutum ba shida kama.
"Toh sikenan k'ad'o na yarda da Allah ama ban yarda dakai ba,nasan Allah ne ke karemu a duk inda muke haka a nan ma shi zai cigaba da karemu.Bansan me a zuciyarka ba daka nace mana lalle saika taimaka mana ama mun yarda zamu zauna a gidanki Idan kika