Showing 54001 words to 56965 words out of 56965 words
Chapter 19 - RETURN OF THE KING COMPLETE BY APHSERT KHAIREE .txt
group sannan kuma recent Chief of securities DSS ALIYU DAPO
Sautin karar tafiyar sandarsa ce kawai ke tashi a dakin shari'ar,duk idanuwa sun dawo kansa da tsananin mamakin ganin ashe yana raye ya karaso har tsakiyar dakin ya tsaya facing din alkalin alkalai
"Sunana DSS ALIYU DAPO wato ZAKI,babban yaro,amini kuma mai tsoro da bawa MOHAMMED GIWA kariya a kodayaushe a kuma kowanni irin yanayi"
Daidai lokacin da King ya bude idonsa daga lumshe da yayi sbd ciwon da kansa ke masa ya saukeso kan Zaki,mamakin ganin Zaki da jin muryarsa Wanda ya tabbata ba mafarki yakeyi ba
Ajiyar zuciya kawai ya sauke ya had'iye tarin tambayoyin da suka ziyarci bakinsa a take sai hamdala kawai yake yiwa Rabbi daga zuci har bakinsa
Kujera wani daga police d'in ya Kai Zaki ya taimaka masa ya zauna sbd condition d'insa,Fu'ad kowa bakinsa har kunne sbd murna hakama Fahima sai hamdala take tana kara godewa Allah gagara misali mai yin yanda yaso a kuma lokacinda yakeso.Tabbas Sarkinmu baya barin zalunci da masu yinshi
Dija itama godewa Allah kawai take sakeyi ta kafe mijinta da ido cikin shauki da son abinta daga inda aka nuna mata ta zauna kusada dasu Fahima
Barrister Joseph kowa ba karamin karaya shima yayi ba don ance masa shine mai tarin shaidun da zai iya wanke King ama dadin abin ya mutu ashe yana raye
Kasa motsawa kusada Zaki yayi don sai yaji duk kwarewarsa a yanxu kwakwalwarsa ta toshe, tsoron amsar da zai samu yake daga tambayar da zai masan
"Barrister Joseph koh kanada abinda zakace game da DSS ALIYU DAPO"
Alkali ya tambayesa
"Baaabbbuu ya mai shari'a"
"DSS ALIYU DAPO zaka iya fadamana abinda ya kawoka kai tsaye"
"Nagode ya mai shari'a"
Zaki yace, juyawa yayi inda wani inspector da suka shigo tare ke tsaye ganin Zaki ya kalleshi ya sashi karasowa inda yake tare da mika masa laptop d'in hannunsa.
Bayan ya karba ya budeta tare da kunnawa ya shiga wani waje
"Ya mai shari'a,wannan laptop d'in FAHIMA ALIYU ne er jaridar dake aiki akan rayuwar MOHAMMED GIWA sbd kashe mata mahaifiya da akayi akanshi wanda yake aikin Governor AA KAITA.Duk wani shaidu da hujjoji yana cikinsa,nina sace laptop a gidanta a ranar data tafi ABIA STATE"
Fahima cikin tsananin mamaki ta zaro ido tana kallon Zaki da kai tsaye baka isa kace ga inda ya dosa ba saide kawai kuwa ya zuba masa na mujiya da kunnen basira wajen sauraronsa
"Na had'a da shaidar dake wajena na pictures d'in FIRST LADY ZEE KAITA Wanda na dauketa a lokacin da muka sata ta mayar da yaron fahima wanda yake aikin King ne snn yayi kokarin wajen ganin ya kawo karshen bibiyarsa da takeyi da alfasha"
Kunyace ta lullube ZEE kaita,bataso Zaki ya tuna wnn cikin baynin nasi ba sai kawai ta sunne kanta qasa tana mamakin irin zuciya ta Zaki da shide babu ruwansa abinda yasa a gaba kawai yakeyi.
"AA KAITA yayi amfani da ita wajen sace mahaifiyar Fahima Aliyu da yaronta ba tare da sanin shine yake sakata ba,shi da kansa yayi confessing hakan a gaban ita Zee da Fahima ta wannan microphone d'in,na'ora mai nadan sauti da FAHIMA ALIYU ke yawo dashi a jikinta sbd kwarewarta da jajircewarta da takeyi akan aikinta a koh ena"
Murmushi FU'AD yayi shima yana qara jinjinawa matar tasa akan jajircewarta don shi da kansa sai yanxu yake sake ganin kokarinta da yaba mata snn yake jin haushin kansa na rashin bata goyan bayansa a lokacin da take buqatar hakan sai ma nisanta kansa da yayi da ita akan aikinta yaso yin amfani da son da take masa yana tunanin zata zabishi akan aikinta ama Jaruma FAHIMA ALIYU ta nuna masa ta zabi gaskiya da kawo karshen zalunci akansa.Dole ya mata kyauta na ban mamaki wanda zai wanke kansa a wajenta bayan an gama wnn shari'ar.Yana murmushi ya cigaba da sauraron Zaki
"AA KAITA ya nemi mu hada kai dashi wajen kokarinsa na ganin ya saka Mohammed Giwa cikin kunqiyarsu inda ya bani miliyoyin kudi,na amince dashi ba tare da sanin nida King muna aiki akansa bane har ya sani na sato masa King
Nayi kokarin siyan daya daga cikin guards dinsa inda na bashi CCTV ya sakamin a dakin da AA kaita ya kai King lokacin dana sato masa king,luckily kuwa AA KAITA ya saki bakinsa wajen tunawa kansa asiri a wannan dakin a gaban King ga camera ta nado min komai Wanda na hadashi a cikin wnn laptop din
Inaso a junashi a kowa yaji kuma ya gani irin tuggun da AA KAITA ya kullawa aminsa Mohammed Giwa tun suna jami'a
Yayi sanadin Iyayensa da yaransa jajirai biyu.A lokacinda AA KAITA yayi plan din sace mai dakin King da jajiran en biyunsa snn ya bada aikin kashe aikin a kashe King inda yasa trailer nabi takan motarsa wanda dakyar muka samu aka ceto King da taimakon Allah kuma Allah yayi kwanansa na gaba,shine muka fitar dashi kasar waje inda yayi jinyar shekara da shekaru ba tare da Sanin matarsa na raye ba don shi da kansa ya dauka ta mutu kamar yanda kowa ya dauka.
Na dauke ita matarsa daga asibitin da taimakon Doctor Sa'id na boyeta tare da iyayenta a gidan gonarsa dake bayan garin sbd sanin cewa inde wani yasan tana raye tabbas sai AA yasan yanda yayi ya cimma mummunar manufarsa akanta ama sai akayi rashin sa'a AA KAITA ya sace wata baiwar ALLAH da akayiwa aiki aka fitar mata da yaro daya mutu a cikinta wacce mijinta ya rasu take gaban Uwar mijinta.
A labarinta dana samu daga bakinta a asibiti da haryanxu take jinyar cutarda rayuwarta dasu AA KAITA da sauran en kunqiyarsu sukayi mata
Ta hanyar luwadi da ita na tsawon shekara 6 da take tsare a gidan tsafinsu duk suna tsammanin DIJAH ce matar King"
Hawaye Dija,Fahima,Zee da wasu daga cikin masu sauroron Zaki kawai sukeyi barinma Dijah da tsananin tausayin wnn baiwar Allah ya shigeta dukda bata ganta ba
Zaki ya cigaba
"SAUDAT ta kasance marainiyya,ta taso gaban kanin mahaifinta wanda bayan ya aurar da ita shima ya bar garin Kaduna.
Mijinta ya rasu tana da cikin wata 5 wanda tsananin damuwa da tunanin rashin mijinta nata ya haifar mata illa itada d'an cikinta ga rashin isheshen kulawa don tana gaban mahaifiyar mijin nata wacce itama da taimakon d'anta take rayuwa.
A ranar da ciwon ya turnik'e Saudat d'in aka kaita asibiti da taimakon mak'ota akace aiki za'a mata don yaron cikin ya mutu, ranar aka kai Dija haihuwa.
Kuma a binciken da mukayi a asibitin bbu wanda ya dawo don tambayar ita saudat d'in har yau duk tsawon shekarun da ta dauka a hannun azzaluman,Muna rokon court a cikin hukuncin da zatayiwa wnn mutane a kara sbd hakkin wnn baiwar Allah da sauran jama'a
Wani huci iska mai zafi ya fesar daga hancinsa cikin bacin rai
"AA KAITA yayi nasarar kai yaran King kunqiya"
Sai kuma yayi shiru yana aikawa AA wani irin kallo,ji yake inama zai iya da yau sai ya kusa halaka shi,King da kansa wasu abubuwan sai yau yake jinsu
Dija kuwa Kuka kawai takeyi kamar ranta zai fita su Fahima na tausarta dukda suma kukan sukeyi.....
Masoya Aphserteen khairee,masoya King ππ»ππ»
Show some love and support.A garzayo ayi payment MATA AYAU salon na daban ne tabbas na shirya muku da sabon sanfurin baku nishadi Fanmily akan farashi mafi sauki 150 kacal
3140418863 First bank
Hafsat Yahaya
07086037570 evidence of payment
[1/6, 9:17 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*
By
Aphserteen khairee
ELEGANT ONLINE WRITERS
ALHAMDULILLAH AM BACK AGAIN π€Έπ»ββοΈπ€Έπ»ββοΈπ€Έπ»ββοΈ
_INSHA ALLAH ZUWA GOBE ZAKU SAMU KARASHEN LAST FREE PAGE NA MATA A YAU_
_A GARZAYO AYI PAYMENT MY BEAUTIFUL FIFUL_ π₯°
_contact me via 07086037570_
44
Take court ya rud'e da hayaniyar mutane,kowa sai jifan AA yake da kalaman Allah wadai saide alkali ya buga gudumarsa kusan sau 4 tukunna jama'a sukaja bakunansu suka tsuke
Registrar ne ya karb'i laptop d'in hannun Zaki sbd shirun da yayi wanda yake nuna alama ya gama maganarsa don ya kuma d'inke fuskar nn tamau kamar wanda bai taba darawa ba daman ya lafiyar kura balle tayi zawo
Gani da jin irin badakala da tuggun da AA ya jima yana yiwa aminin nasa ya karasa court kaurewa da zantuttuka nn wani dattijo ya tashi tsaye rai a bace yana
"Kai ku wannan yaro Allah ya tagayyaraka ya kacencana maka rayuwarku duniya da lahira,bakin haihuwa bakin asara,bakin mu'ayyabi,jikan qaruna,yayan fir'auna"
Gudumarsa alkali ya buga yiwa dattijon tsohon gagardin a court yake, ya kiyaye
"Kai dallah kyaleni,kaima kayi wani kikip dakai akan kujera nasan dakyar ka yanke masa hukuncin kisa tunda yanxu duniyar gabadaya ta zama ta shu'umai.
Gwanda nayi ta tsine masa har saiya zama alade mafi kaskancin dabba abin kyama da la'ana"
Nan fah dattijon nn ya d'inga zazzagawa AA zagi har saida securities suka fitar dashi daga dakin court koda ya fita waje inda ya tarar da dandazon jama'a da en jarida ya hau basu labari A_Z harda kari,yana kwakwulo hawaye yace
"Haka bak'aken mu'ayyaban nan suka saka yaran wannan Dan albarkan Kinsh suka dake a turmi suka kirbesu"
En jarida kuwa da jama'a an samu abinda akeso nan take labari ya fara yad'uwa a kafafen sadarwa game da Governor Dan takara kuma mai ci a yanxu tare da sauran en uwansa en kunqiya wanda har sunan Baban fitatciyar er jarida FAHIMA ALIYU saida ya fito tundaga sharrin da aka masa na farkon zuwansa garin Kaduna,wanda suka san labarin daman na kullace dashi.
Nan hayaniya ta kaure daga wajen FEDERAL HIGH COURT,jama'a suka fara
"A miko mana mu konasu,a miko mana mu konasu.Mu bazamu yarda baΒ².........
WasaΒ² sai ga gari ya dauka kowa da irin tofin Allah tsine da yakewa su AA.
Bangaren court kuwa Alkali ya yankewa su Baban Fahima,David,Jboy,suleguy life in prison tare da kwace dukkan wani abinda suka mallaka shi kuwa AA KAITA an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samunsa da laifuka mafi girma a cikinsu dukkan hakama sauran guards dinsu da aka kama dukka an yanke musu shekaru masu yawa a gidan yari tare da huro mai tsanani.
Alhamdulillah dukkan wani masoyin King da al'umma yake ambatawa,Dija dasu fahima kuwa hawayen farinciki suka d'ingayi wanda baki bazai taba iya misaltawa
Babu abinda ya sake karyarwa da jama'a zuqata sai da sukaga King ya kalli gabas yayi sujjada ga mahalliccinshi na tsawon mintuna yana hawaye jikinsa har rawa yakeyi wanda yasa jama'a da dama zubda nasu hawayen suma
Lalle dukkan tsanani yana tare da sauki haka kuma babu yanayi mai daurewa duk daren dad'ewa.Yah Rabbi karka kawo mana abinda bazai wuce ba,Allah ka tsarkake mana zuqatanmu,ka cire mana kyashi da hassada a cikinta ka sama mana kaunar junanmu.
Yah Allah kasa muyi koyi da kyawawan halayyen na shugaban mu Annabi Mohammed SAW,Yah Rabbi....
Kuka ne yaci karfinsa sosai wanda ya sashi kasa karasawa,AA kuwa dan kukan nadama kamar zai hadiye ransa,ji yake inama mutuwa zatayi gaba dashi a yanxu a nan tafe. Koh ba komai wnn hukuncin da aka yanke masa ya masa matukar dadi don baisan maiya rage masa ba anan duniya
Hattasu David saida jikinsu yayi sanyi sukayi mugun karaya,nan aka fita dasu cikin handcuffed dukkansu.
Suna fita kuwa jama'a suka hau jifansu kamar daman sun shirya hakan dakyar aka sakasu a mota
King na mikewa idanuwansu cikeda kwalla ya kalli masoyinsa na hakika,amininsa bilhakki sai wani irin murmushi mai dauke da tsantsan farin ciki ya subuce masa dukka hawayen dake idonsa
Baya farincikin wankesa a zarginsu AA kamar yanda yakeyi ganin Zakinsa a raye
_Alhamdulillahi bi ni'imatillahi kasiran_
Karasowa yayi gaban Zaki ya durgeshe inda yake zaune a kujerar yayi hugging dinsa tightly har saida Zaki yace
"Awwcchhh,Oga zaka karasani"
Cikin zolaya abinda bai taba ganin Zaki yayi ba wato wasa koh zolaya,nan dukkansu suka fashe da dariya harshi Zakin first time in history har dasu Dija na tayasu.Zee kuwa galala tayi tana kallon Zaki cikin mamaki ganin fusakarsa dauke da dariya,sai taga wani irin kyau da cikar haiba tartare dashi
Wani murmushi ne ya subuce mata bbu zato ( uhhmm uhmm Zakinmu de yafi karfin fyade,su kwartowa Zee π€π₯± au,Ashe ta tuba ππ»ββοΈ)
Masha Allah
Tho mutanena na dawo π₯±
Mu hade gobe,insha Allah ππ»ββοΈ
[1/6, 9:17 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*
By
Aphserteen khairee
ELEGANT ONLINE WRITERS
_*LAST PAGE*_ ππ»ππ»π€
45
Kwatonto yanda zuk'atansu ke dilmiye da tsantsan farinciki ma bata baki ne barin ma shi kansa uban gayyar da inya juya nan yaga Dijansa hakama ga Zakinsa a kusada shi.Sai iyayensa da yake musu fata da rahmar ubangiji da ma duk wanda ya rigamu gidan gaskiya
Mutanen daya gama cire rai da sake rayuwa dasu sai gasu zagaye dashi cikin falala da ni'ima ta Rabbi mai jaraba bayinsa ta kowacce siga,Allah ya bamu ikon cinye kowacce irin jaraba a rayuwa yasa ya zama sanadiyyar shigarmu aljannah kenan.
Ga kuma nasarar da suka samu na durgusar da manyan azzalumai masu amfani da jinin al'umma don biyan mummunar buqatarsu.
Sun yanka bayin Allah,su sha jininsu,sunyi luwadi dasu ga tsafi.Duk wasu laifuka mafi muni kuma manyan kaba'ira sun had'a.Yah Subhanallah,Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.Duniya ina zaki damu,biyewa dunqulallen tsokar dake kirjinmu yasa dan adam jefa kansa cikin halaka.Allah ubangija ya cigaba da tonawa masu irin halayyensu asiri ya kuma tsarkake zuqatan bayinsa salihai da fadawa mummunan halaka,Ameen yarabb..
Kyakkyawar rungume barrister fu'ad Hashim yayiwa Fahima,itama rikesa tayi tightly tana maida numfashi a hankali na samun nutsuwan zuci da gangar jiki
Hamdala fu'ad yake karayi a ransa da bai tafka kuskuren rabuwa da heemansa ba ma'ana bai saketa ba da yayi babban nadama a rayuwarsa.Tabbas a kowacce irin zamantakewa barin ma aure da shine ginshiki ana buqatar fahimtar juna da kyakkyawar mu'alama na kyautatawa juna.Allah ya karawa mana fahimtar junanmu tare da abokan zamanmu
"Kwa bari ku k'arasa gida koh Mr and Mrs Hashim"
Suka tsinkayi muryar Zaki da bayan ya gama maganar ya dauke kansa daga dubansu kai kace ma bashi yayi maganar ba,dariya dukkansu sukasa har Dija itama dake makale da mijinta ita kuwa Zee sai binso da ido kawai takeyi, duk sai taji ta daban.Kewa da nadama na Kara nukurkusarta na sanin AA a ayuwarta tun farko Wanda bai taba zama alkhairi ba.Ya Rabbi Ya Karim ka rabamu da aikin dana sani a rayuwa
_A YEAR LATER_
Ihunta ne ya karade ilahirin compound d'in da shashin GOVERNOR MOHAMMED MOHAMMED GIWA yake tare da surukansa daga kusada su wanda yake daga cikin Government House din.
Harsu Dada da Zee dake zaune tare dasu suka jiyota daga flat dinsu suka fito a rude jin muryar Dija tana kurmoton ihu da turtsetsen cikinta ta shaqo wuyan King ta hammatarta sai aika masa cizo take a kafada,yayi yayi ta sakeshi ya sata a mota suyi maza suje asibiti ta tsaya bala'in duk shi ya jawo mata
Da taimakon Zee aka samu Dija ta shiga baya donsu Dada da suka fito kunya da kara ya hanata karasawa dama King ya hana securities da guards shigo bangaren idan bashi ya nemesu ba.Zaki kuwa ya tafi aiki daya rike masa wuya sosai yanxu don yana daga cikin manyan jami'an tsoron da ake ji dasu a kasa baki daya sbd jajircewarsa da kokarinsa kan aiki.
Zee ce tayi driving d'insu zuwa asibiti kafin su karasa kua King yasha cizo da mintsini harya gode Allah
Babu wani bata lokaci akayi labour room da ita inda King ya tsaya kafaΒ² ya kafe babu inda zashi har saiga matarshi ta haihu tukun
Zaki da Zee ne sukayi ta wani shiga da fice a asibitin dukda magana bata hadasu saide ido kawai
Kapshara!Yanda Dija ke ihu haka King keyi shima,yau de ya ajiye mulki ya taya matarsa labor wanda har nurses din dariya suka dinga masa. Wani gigitaccen ihu na karshe da suka saka wanda ya cakude da kukan samb'alelen yaronsu shima yana tsala nasa ihun kuka da muryarsa data karade ilahirin dakin yasasu sakin wani ajiyan zuciya wanda Dija da king suka sauke a tare sai kuma hamdala ga Rabbi,dakyar nurses din suka lallabashi ya bar dakin akan za'a gyrasu
Yana fitowa waje kuwa ya rungume Zaki dake tsaye a gefe
"It's a boy,Alhamdulillah alhamdulillah.A new lion is born again"
Haka sukaita murna,take Zee ta kirasu Dada ta sanar dasu Dija ta sauka lfy bayan nn ta kira Fahima dake kwance jikin fu'ad itama da d'an matashin cikinta ta Sanar da ita haihuwan
"Allah sarki,Allah ya jikanki Saudat ya kai Rahama kabarinki"
Fahima ta fada idonta na tara kwalla tunowa da kiran ajali wanda yayi sanadiyyar fadawar Saudat hannunsu AA a ranar data haihuwa
Kafin kace mai garin ya dau amon haihuwar First lady DIJA GIWA ta hanyar picture kyakkyawan yaron mai kama da babansa sak da Zee ta daura a social media tun suna asibitin tasa
"Welcome to the globe Prince"
Nan aka fara kururuwar cika a asibitin danma securities da sauran guards dinsa suna tsaye tsayin daka aka hana mutane shiga
Duk wani hidima da shiga da fice Zee da Zaki keyi,duk da irin daure mata fuskar da yakeyi sai daya sassauta yau sbd d'a kuma takwara da yayi wanda farincikin hakan yaki boyuwa a fuskarshi
Tun suna magana kasaΒ² shi da Zee sai gashi Zaki ya sake harda d'an hira da wasa da dariya.A cikin satin haihuwar kuwa shakuwa ta ban mamki ya shiga tsakaninsu
Nan su Fahima da Dija suka fara shigewar Zee da tsokana
"Nide tambaya daya nakeso ki masa akan maganar daya taba fadamin na ya tsani kukan mace shine nakeso naji dalilinsa"
Inji Fahima suna zaune a bedroom din Dija ana gobe suna suna duba dinkunansu,Dija na shayar da baby.Dariya Zee tayi tace
"Dadinta nide ba er jarida bace gidan bin kwakkwafi da nacin jaraba"
Masha Allah,Barakallah.Masu jego King da Dija babu dama sai godiya ga Rabbis samawati mai kowa mai komai,mai yin yanda yaso a lokacin dayaso
Yaro yaci sunan mahaifinsa kuma aminintaccen mahaifinsa wato ALIYU ALIYU GIWA (AA GIWA)
Dakyar Zaki ya yarda ake kiran takwaransa da AA sai da King yace masa Insha Allah abinda yake tsoro bazai taba faruwa ba,shima AA KAITA muna masa fatan gafara da rahamar ubangiji masu irin halayyensu na Hassada,son zuciya,cin amana da ha'inci Allah ya ganar dasu gaskiya ya tsarkake mana zuqata
_AMEEN YA HAYYU YA QAYYUM_
_TAMMAT BILHAMDULILLAH_
_SAI MUN HADU A MATA A YAU,ER UWA KARKI BARI AYI BABU KE.A SHIRYYE NAKE TSAF DA SABON SALO WANDA SAI ILIMANTAR YA KUMA NISHADANTAR DAKU INSHA ALLAH DUK AKAN FARASHI MAI SAUKI_ 150KACAL
CONTACT ME VIA 07086037570
_YOURS APHSERTEEN KHAIREE_