Showing 15001 words to 18000 words out of 43872 words

Chapter 6 - SURUKATA HORROR BOOK COMPLETE DOCUMENT 2025.txt

27 Dec 2024

3509

dawo min a kai,amma sai na zaɓi na ɓoye mata na ce “ dama...dama ina da yawan shan ruwa ne”




“Ok to ki kula sosai ba kowane ruwa ne ke maganin ƙishi ba”


“Me kike nufi Hajiya?”


“Babu komai,je ki yi wanka ki fito ki ɗora girkin rana” ta faɗa tare da ficewa.




Can ciki na koma na shiga toilet,bokiti na ajiye tare da buɗe ƙaramin pampo sai na ɗauki soson wanka na zuba sabulu na soma cuɗa jikina.Ina saɓa fuskata da sabulu sai na ji tamkar wani na kallona,da sauri na sa ruwa na wanke fuskar ina gwalar ido.Babu kowa kawai tunanina ne ya bani hakan.A gaggauce na ida na fito,cikin sabbin kayana na lefe na zaɓi doguwar rigar atamfa na saka.Tunani na soma a kan abin da ya rage a ɗakin nan amma sam na kasa tunawa,trollyn da aka zuba min kayan kwalliya na buɗe na shafa mai da turare kafin na fita can kitchen.






Tsaye na yi ina kallon uwar garar da ke cike da store ,ina mamakin duk me ake yi da su har haka kamar mai wani gidan marayu.Ban san me zan dafa ba,kawai sai na yanke shawarar bari na je na tambayi Hajiya .




Yin sallama ba ta cikin tabi'ata,wannan yasa yanzu ma ina isa ɗakinta kawai na kutsa kai.Kusan daskarewa na yi saboda tarar da Hajiya da na yi zaune kan wani tsumma ,kan kafaɗarta kuwa wani tsuntsu ne manyan ido jajaye .


Na ɗan ja da baya da nufin fita,amma sai na ga tsuntsun ya buɗe baki yana magana amma muryar Hajiya Luba ce ke fita.


“Ƴata Janiki,matso mana ki zauna a gefena” ta faɗa .


Jikina ya ɗau kyarma,na ce “ dama abin da za a dafa na zo nem...” ban ida kai ƙarshen maganar ba wannan tsuntsu ya tashi sama bai dira ko ina ba sai tsakiyar kaina.Daga nan kuma ban ƙara sanin abin da ya faru ba sai tashi na yi na gan ni kwance kan gadano,duk yadda na so tuna abubuwan da suka faru kuma na kasa.Abu guda na riƙe na je kitchen zan yi girki amma kuma ban yi ba.




Aka buɗo labule,Aliyu ne ya shigo fuskarsa kamar kullum a murtuƙe.Kakin sojansa ya soma cirewa ni kuma na zuba masa ido ina kallo.A siffa ga namiji har iya namiji sai dai raggo ne a shimfiɗa,ga kuma fitsarin kwance.




Na shagala sosai a kallonsa sam ban ga lokacin da ya zo gabana yayi tsaye ba,sai saukar muryasa da na ji “ ke ba ki san ki gaida mutane ba ?”


“Ka yi haƙuri” na faɗa da sauri,ya ja tsuki kafin ya shiga toilet.Bayan ya fito ne yake cewa “ Hajiya Mama ta ce bayan fitata kin zame jiki kin faɗi a kitchen,shin dama kina da cutar farfaɗiya ne?”




Shiru na yi ina tunanin ‘ to yaushe hakan ya faru ban sani ba? ’


“Ta ya kuwa za ki sani tun da hankalinki ya gushe” ya bani amsar tambayar da na yi wa kaina a zuci,cike da mamaki na ce “ ni fa ban yi magana ba” cikin ido ya kalle ni kafin kuma ya juya ya soma kimtsa wa .




Na dafe kai ina jin can ƙasan zuciyata kamar akwai abin da ba normal ba,amma sam an ƙi bani damar yin tunani ballantana ma na san gaskiyar abin da ke faru.


Daga can bakin ƙofa Binta ta yi sallama,da sauri na tashi na fita.Ta saki ɗan murmushi kafin ta ce “ ku fito lokacin cin abincin dare yayi”


“To ga mu nan” na faɗa tare kuma da zancen ‘ kenan har dare yayi?’


“Mu je” na ji muryarsa tare da wani jan hannuna kamar wata ƙaramar yarinya.
Muna fitowa sai na ga duhun magrib ne kawai ya keto amma kamar wasu kaji wai abincin dare za a ci.
Har muka shiga falon cin abinci bai saki hannuna ba,wannan karon kusa da Hajiya Luba ya zaunar da ni shi kuma ya zauna gefena sai ya zamana sun saka ni tsakiya.






Da ido kawai Hajiya Luba ta dube ni amma abun mamaki sai na ji sautin muryarta tamkar da baki ne ta yi maganar.
“Ki buɗe kwanon abincin ki bai wa kowa umarnin ci” shine abin da idon nata suka faɗa min.




A hankali na kai hannuna tare da buɗe ƙaton murfin,nan tururi da ƙamshin naman kaji ya cika wurin da kuma na wainar shinkafa.Na aro murmushi na yaɓawa fuskata mai cike da mamaki na ce “ kowa ya ci ya ji dadaɗan girkin da na yi mana,fatan za ku ji daɗinsa sosai”


Duk suka yi murmushi kuwa kafin a soma ci,ni ma cike da zumuɗi na soma ci saboda yunwa da na kwaso.Bayan mun gama ci Hajiya Luba ta ƙara bani wani umarnin na kawo jus,haka na miƙe na fita zuwa ɗakinta.


Da na shiga ɗakin duhu ne da shi ɗif,sai dai abun mamaki duhun bai hana ni ganin komai na ciki ba tamkar safiya.Ban wani damu ba tun da ni dai burina shine na ɗauko abin da aka aiko ni don shi,wannan yasa jus ɗin kawai na ɗauka na koma can haka na rarraba wa kowa kafin na koma wurina na zauna na sha.


Muna gama sha aka kira sallah,sai duk suka fita wannan karon har da Aliyu.Ni kuwa tamkar wacce aka riƙewa mazaunai haka nake ji sam ban yi ƙoƙarin tashi ba ma.




“Ungo ki sha” Hajiya Luba ta faɗa tana miƙo min kofin nan na ɗazu,na karɓa na shanye tass kamar jira kuwa ake sai na soma jin duk abubuwan da ni ɗazu sai dai na yanzu na ga wani banbanci shine yadda kawai na kwanta shanɗam kam capet.


Ba bacci nake ba,haka kuma ba zan ce idona biyu ba .A takaice dai ina tsakanin duniyoyin biyu,ina kallon lokacin da Hajiya Luba ta miƙe tsaye ta soma zagaye ni tana faɗar wasu ɗalasimai kafin kamar almara ta soma yi wa ruhina magana.




“Fito zuwa gare ni,zo ka yi min hidima ,lokaci yayi da nake ta faman jira” ta faɗa tare nuna tsakiyar ƙirjina,tamkar yadda ƙasa ke tsagewa haka na soma ganin gangar jikina na buɗewa kafin wani abu mai kama da inuwa ya fito,wanda ba komai ne shi ba sai ruhina.....






Littafina na kuɗi ne,ki ɗaure ki biya 500 Hajiya via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank


DM +22795045822
[24/12 à 08:16] MRS SADAUKI: My book is only 500 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank


DM +22795045822






Free 09




Tamkar a mafarki dai ruhina ya fita daga gangar jikina ya je gaban SURUKATA ya zube,yatsan hannunta ta tsaga nan jini ya soma tsirta haka ta soma shayar da ruhina shi na wani lokaci kafin kuma ta basa umarnin ya je ya koma inda ya fito.
Yadda in mutum ya suma in an zuba masa ruwa yake zabura haɗi da jan numfashi da ƙarfi,to ni ma hakan ce ta faru da ni bayan ruhina ya dawo cikin gangar jikina.


“Ƴata Janiki kin tashi?” Hajiya Luba ta faɗa ,wacce a yanzu na gan ta zaune kusa da ni.Kai na gyaɗa mata ba tare da na ce komai ba,don ji na yi kamar na rasa tunanina.


Ta saki murmushi ta ce “ tashi ki je ɗakinki zan aiko miki da magani domin magance ciwonki” ba tare da na san wane ciwo take nufi ba na tashi na fita zuwa ɗakina.


A falo na tarar da Aliyu yana waya da dukkan alamu kuma da Ogansa ne duba da yadda yake magana cikin ladabi.Har zan wuce bedroom amma yayi min alama da hannu a kan na je.Sam jikina bai da wani ƙwari tamkar zan faɗi haka na je na tsaya a gabansa,ya jawo ni tare da ɗora ni kan cinyarsa.Yana waya yana yawo da hannunsa a jikina can ya ajiye kafin ya maido hankalinsa gare ni,wani irin kallo yake min kamar mai son ya isar min da wani saƙo.Ina ganin ya matso fuskarsa gare ni na yi saurin lumshe ido,ai kuwa abin da na yi tsammani ne.Sumbata na yayi ta yi haɗi da romance ,ba tare da neman izini ba kwatsam aka shigo ɗakin.Da sauri na zabura na tashi ina raba ido,ita kuwa Hajiya Luba kicin-kicin ta yi da rai tana wani kallonmu kamar ta ritsa kwarto.




“Hajiya Mama ko da abin da kike buƙata?” Aliyu ya faɗa a kunyace ba tare da ya tashi ba.


“Sai in ina buƙatar wani abu zan shigo ɗakinka Aliyu? Tun yaushe ka yi min iyaka da shigowa ba tare da na sani ba?” Hajiya Luba ta faɗa ,amon muryarta na fitar da hucin baƙin ciki.




“Ki yi haƙuri Hajiya ba haka nake nufi ba,dama ai ko ba ki shigo ba yanzu zan je na sanar da ke zan je mission jibi ” Aliyu ya faɗa .




“Ai ban ga alamun za ka je ba ɗin,ke kuma uwar me kike jira da kika yi min tsaye ko banda ikon yin magana da ɗana sai a gabanki?” wannan karon sosai fushinta ya fito,jikina na rawa na nufi bedroom ba tare da na ce mata komai ba.




Kan gado na zauna ina haƙi kamar wacce ta yi gudu,wani abu nake ji tamkar zan faɗi.Dukkan jikina ya ɗauki rawa,murya na ɗan rawa na ce “ Aliyuuu!” da ƙarfi na yi maganar ta yadda zai ji.


Ai kuwa ya shigo a guje yana cewa “ me aka yi?”


“Zan faɗi jiri nake ji” na faɗa tare da tashi tsaye ,yayi saurin tallabo ni .Hajiya Luba ta shigo tana cewa “ dama maganinta na zo kawo mata ungo ka bata ta sha” ta faɗa tare da miƙa masa wata kwalba,Aliyu ya zaunar ni sannan ya dangwalo maganin da yatsansa ya saka a bakina kamar ƙyaftawar ido haka na ji komai ya dawo normal.Na ja wata ajiyar zuciya,cike da tausaya wa Hajiya Luba ta matso kusa da ni tana mai cewa “ ki kwanta ki huta Ƴata Janiki, Allah ya baki lafiya.Ki riƙe maganin nan wurinki duk lokacin da kika ji wannan yanayi to ki dangwale shi da yatsa ki sha za ki samu sauƙi”




“ Na gode sosai Mama ” na furta cike da jin daɗi.
“Aliyu ina ga ya kamata a ɗaukar wa da Janiki ƴar aiki wacce za ta kula da ita da kuma yi mata hidima,ciwon nan nata bai son yawan motsi da zirga-zirga ”




“To Hajiya Mama ” ya furta kafin ya miƙa min kwalbar maganin.A tare suka fita shi da ita,ni kuma na kwanta kan gadona tare da rungume kwalbar a ƙirji.


Na saki wani murmushi na ce “ wai Janiki ce za a ɗaukar wa ƴar aiki, na gode abun bauta da ka nuna min ranar da zan yi farin ciki” sai kuma na yi shiru na koma zancen zuci ‘ to yanzu a haka zan zauna da Aliyu ba tare da mun mori rayuwar aurenmu ba? Ko ya san bai da lafiya? Ƙila kuma shi wannan saurin inzalin bai ɗauke shi matsala ba don ban ga ya nuna alamun damuwa ba’ sai kuma na ji tausayin kaina.




Ina nan kwance ya shigo, trolly ya jawo ya soma zuba kayansa yana yi yana waiwayena har ya gama ya zo yayi tsaye kai gare ni ya tsura min ido.Duk sai na ji na tsargu,ga kuma wani tsoronsa da ya dirar min lokaci guda.


“Ki tashi ki yi wanka ki canza kayan nan zuwa na bacci ” ya faɗa yana furzar da huci.Ba tare da na ce masa komai ba na sauko,har zan wuce amma sai ya riƙe min tsintsiyar hannu.Wani irin kallo ya soma aiko min kafin kuma ya sakar min hannun,da sauri na shige toilet ina mamakinsa ko me ya shiga kansa yau.
Bokiti na tara a pampo kafin na soma yin wankan,ana buɗe ƙofa na san da shi ne.Ko juyawa ban yi ba haka na ci gaba da yin wankan a takure ina jin idonsa gare ni.Na jawo towel zan ɗaura yayi saurin fizge shi daga hannuna,daidai kunnena ya min raɗa “ ina so mu yi wanka tare” ban kai ga yin magana ba ya buɗe shower ruwan suka zuba gare mu.Na ja wani numfashi saboda sanyin ruwan ina shirin guduwa ya riƙe ni gam tare da juyo ni muna facing juna,“ mene ne?” yayi min tambayar a dake .Idona suka kawo ruwa na ce “ ban so na jiƙa gashina” sai ya sa hannu ya cire hullata wacce ko bacci bai raba ni da ita yayi cilli da ita.


Gashina da na laulaye na yi masa naɗin tayar mota ya warware tare da cire ribob ɗin,ido ya waro ganin sumar kaina.Kamar wani sakarai ya soma shafa ta yana jan ta cike da mamaki,yana tallabo fuskata na lumshe ido.


Wanka muka yi cike da salon romantic,yadda Aliyu ya tafi da ni cikin shauƙi da tausasawa kamar ba shine na jiya ba da yayi ta yi min tsawa.Yadda ya manne ni a ƙirjinsa yana sauke min huci a kunne shi ya fi ɗaga min hankali,kamar wata ƴar baby haka yayi min wanka.Karon farko da na ga soyayya gun ɗa namiji don ban taɓa yin saurayi ba,bayan ya gama yi mana wankan muka ɗaura towel har zan taka da ƙafata amma sai ya ɗauke ni.A zuci na ce ‘ ka ga wani sabon salo’ kan bed ya shimfiɗe ni,yana shirin warware min towel na ce “ ka rufo ƙofa”


“Na ru..fe ta ca..cccan falo ” ya faɗa muryarsa na rawa,haka kawai na ji tausayinsa saboda tsantsar buƙatuwa da na hango cikin ƙwayar idonsa amma na san ba za a je ko ina ba saboda bai da wani ƙarfin.


Ido kawai na lumshe tare da yin shiru ina karɓa saƙonsa,ko ta ina yake min sumba jikinsa na yin rawa.Ɗumin hawayensa ne suka sa na buɗe idona,da dukkan alamu ya ji takaicin yadda yanzu ma da ya so kusantata kawai komai ya tsaya cak babu biyan buƙata.Fuskarsa na tsure ina kallo ,kyakkyawa ne shi duk da yana baƙi hakan bai ɓoye kyawun nasa ba.Ya koma gefe tare da kai hannu ya kashe ƙwan lantarki,ɗakin sai yayi duhu.


“Zahra!” yayi furicin ,ban amsa ba don ba haka ne sunana ba.Ya jawo ni ya maido ni kan ƙirjinsa tare da cewa “ shine kika yi shiru?”
“Ni sunana Janiki” na faɗa .
“Ban sonsa ne shi yasa na zaɓa miki sunan Zahra shi ya fi yi miki kyau,tun da kin ga kai tauraruwa ce”


“ Zahra na nufin tauraro?” na tambaye shi.
Ya ce “ eh mai mugun haske ma kuwa”


“Kenan ni tauraruwa ce?” na sake jefa masa tambayar.Shiru yayi kafin can ya ja numfashi ya ce “ eh ”
“Saboda me?”


“Me yasa kika aure ni?” shi ma ya jefo mini tambayarsa.Sai na kasa cewa komai,hasken ɗakin ya kunna kafin ya ƙara maimaita min tambayar yana kallon cikin idona a dole na amsa masa da “ Mama ce ta ce na aure ka”


“Hajiya Mama?”
Na girgiza kai na ce “ a'a Mamana”
“Kafin su aura miki ni sun yi miki bayani kaina ba?”
“Wane bayani?”
“ Komai!” ya faɗa tare sake kashe hasken,ina jin yadda bugun zuciyarsa ke tafiya da sauri-sauri.


A hankali na ɗan janye daga jikinsa kafin na juya masa baya,amma kamar wani ƙaramin yaro haka ya zo ya ɗora min ƙafarsa ɗaya tare da zagaye cikina a dole dai ya mayar da ni cikin ƙirjinsa.A haka muka yi bacci kafin lemar fitsarinsa ta tashe ni,na janye jikina da sauri tare da kunna hasken ɗakin shi ma ya farka sai muka fara ƴar kallon-kallon kafin kuma ya sauka ya je ya shiga toilet.Ni kuwa tsaye na yi ina kallon gadon da yayi shaɓe-shaɓe da fitsarin,a yau maimakon takaici sai na ji tausayinsa....






My book is only 500 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank


DM +22795045822
[26/12 à 09:10] MRS SADAUKI: My book is only 500 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank


DM +22795045822






Last free page 10




Zanen gadon na cire ,sai na dubi ƙofar toilet da nake ta jin ƙarar zubar ruwan shower da alamu wanka ne yake don dole sai wankan tun da uban fitsarin nan da ya shashaɓa min.Ganin ba zan iya jiransa har sai ya fito ba kawai na yi niyya fita waje na ciko bokiti da ruwa na goge ledar da ke kan katifa.Ba tare da wani tunani ba na suturta jikina kafin na je na buɗe ƙofa na fita tsakar gida.Wani irin mugun haske ne na jar wutar mai kamar ta murhu ya min maraba,kaf tsakar gidan ya ɗauki kalar ja yayin da sararin samaniya yayi baƙi ƙirin kamar bayan tukunya sai giza-gizai ke gudu .


A tsorace nake kallon giza-gizan masu kamar zanen fuskokin mutane,na toshe kunnuwana saboda wata gurɓataciyar murya da ke rera waƙa cikin wani kiɗa marar daɗin sauti kamar ana kiɗa goge.


Baya-baya na soma da na ƙasa na darewa tana tsagewa kamar yadda in an yi girgizar ƙasa za ka ga wuri na ɓaɓarewa.Ihu nake son yi amma tamkar wacce aka riƙewa murya na kasa,hatta motsa ƙafafun haka na kasa gusawa saboda yadda nake jin tamkar an ɗinke fatata da kuma ƙasa.


Wani haske ne ya tawo daga sama kamar tauraro ya hankaɗa ni na yi baya tare tashi sama ban dira ko ina ba sai cikin ɗakina,yayin da kuma ƙofar ɗakin ta bada ƙiiii tare da rufe kanta.


Na dafe saitin zuciyata ina jan numfashi kafin na tashi dakyar na koma bedroom,sai na tarar tuni Aliyu ya fito daga wankan yana tsaye kan dardduma yana Sallah.Toilet ɗin na shiga na ciko bokiti da ruwa na goge ledar tare da saka wacce ta ɓace cikin bokitin,tun a cikin daren na wanke ta sannan na yi wanka na fito.Har yanzu yana kan dardduma ,kayan jikina na saka sannan na shimfiɗa wani zanen gadon.Can ƙarshen gado na hau na kwanta ,abubuwan da suka faru yanzu da na fita suka faɗo min a rai.




‘ To wannan ɗin duk na mene ne? Ko dai gamo na yi?’ sai kuma na watsar da tunanin don banda wanda zai ban amsa.Ina nan kwance shi ma ya zo ya kwanta tare da kashe hasken ɗakin.A tsorace na tashi na ce “ Please ka kunna haske tsoro nake ji”


“ Zo nan ” ya faɗa tare da jawo ni cikin ƙirjinsa,ido na rufe ruf ina jin zuciyata na bugawa da ƙarfi.“ Me ya tsorata ki?” ya tambaye ni.


“Babu komai kawai ban son duhu ne” na basa amsa.
“To ko ma mene ne ba zai taɓa zuwa nan ba don cutar da ke muddin kina kusa da ni” ya faɗa tamkar ya shiga raina ya ga abin da nake tsoro.
Lamo kawai na yi ina sauraren bugun zuciyarsa,a hankali yake dadaɓa ni alamun na yi bacci.Na yi murmushi ina tuna can gidanmu yadda nake bacci ni ɗaya,ga shi kuma yanzu na samu abokin kwana duk da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login